Showing 123001 words to 126000 words out of 186303 words

Chapter 42 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18745

zaune gefe daya da carbinta baki tana ja hankalinta a kan HAJIA dake magana daga cen cikin kicin


TAUFEEK kam shi da kansa abin nan yana daf da saka shi nuna hali irin na fitsararu, Bama kamar yadda ya kula a tafiyar nan ana so ne a kawowa mahaifiyarsa raini, a shigeta ta inda aka san tana da karra da kawar da kai


Bayan Salama bai karra komai ba sai ya karasa cen inda mahaifiyar tasa take zaune ya zauna a kasa daf da Ζ™afarta a hankali ya dan rabu kafarta kasa kasa ya ce" Matar mai kwanoni ina yini?"


Mama ta yi murmushi, gannin HAJIA ta fito da kaskonta kato ta bada hantiti ta karaso ta mikawa maman tana fadin" Badeshi, hau da hawa'i, bakin duniya da saka ido, jarabar kishin matan uba da asiri ya komewa mai aikatawa dan ubansa, bade shi sosai Ni ba zai zauna da kyau ba"


Mama kuwa ta amsa har yar dariya ta kubce mata gannin zaburar da ya yi ya zubawa HAJIA ido hade da hararan da ya saka ta kawar da kai kasa kasa ta ce" Da ubaanka kake!"


A hankali Mama ta ce" Ka buda bakinka mana harda baki ko HAJIA?"


HAJIA ta ce" Da so samu na yi in da ace daga Ni sai ke ne sai mun tube shi mu masa wankan magani , to a wajen nan harda haramunsa , bayan wannan Magidanci da aka masa yanka ai Ni ke goye shi , Ni din ba damuwa bane ama kin ga gaya irin ta bakin ciki to yau ko Ni ko du wani dan iska a wajen nan , a kan Magidanci babu abinda ba zan aikata ba!"
A wajen wadda HAJIA take bakuwa a wajensa mahaifin Yumnah ne, shi kuwa tasa mahaifiyar ta rasu, tunda HAJIA ta fara magangannun nan ya samu kansa da jin wani irin girmanta a zuciyarsa, Walahi sai da ya ji yar kwala ta taru a idannuwansa, a ce kasan zuciyarsa kuwa sai yake ji inama inama ace tasa uwar ce yake kallo a haka,
A sanyyaye ainun ya dubi mai kwanoni dake duban yannayinsa ya saki murmushi a hankali ya ce" Allah ya karra mata lafiya, Allah ya sa ka rabu lafiya da ita, Allah ya sa ta yi dace da kasancewa a aljana gobe kiyama"


Mai Kwanoni ya yi murmushi sosai a hankalin shima ya ce" Amen ya Allah, Allah ya jikan HAJIA Laraba "


Aban Yumnah ya amsa da amen


Basu fara magana ba sai da aka gama turaren nan HAJIA ta dawo ta yi zaune a tsakiya saman kujera ta harde tana fadin" Kai zo daf da Ni"


TAUFEEK ya yi tamkar bai jita ba, sai da Baba ya masa alamun ya je fa, sannan ya mike ya je ya zauna saman kujera kafadar HAJIA kafadarsa, HAJIA ta wani riko hannunsa kasa kasa ta ce" In suka ce a basu takarda in baka basu ba ina iya daga maka nono"


Kasa kasan ya sake harararta ya ce" Tabas ta tabbata sai na maki aure a Saudiya, ki daga mana haihuwata kika yi yo?"


HAJIA ta masa zuru sai kuma ta cika hannun tana cika tana batsewa ta ce" Na ga ubanda zai Hanna a saki wancen laujen, iskancin banza da wofi"


Shi dai ya kyaleta yana sauraron salamar da mahaifinsa ya sake yi kafin ya ce" Elhaji Abdullahi ne ya nemi a yi zaman nan, a sanina na gayyaci HAJIA da mahaifiyar TAUFEEK ne, me yasa taron nan ya taru har haka?"


HAJIA marwa ta dauke kai a ranta tana ayana' sai dai ku yi du abinda za'a yi a wajen nan sai an yi shi da mu!'


HAJIA baba ta ce" Barsu, barsu ai ba komai, su zauna , ina son du wani makiyin ya ringa gannin ci gabansa a gaban idannuwansa, ku sani in har dayarku ce ta hadasa fitina kun yi aikin banza, Magidanci sai ya jera hudu sai dai a yi abinda za'a yi"


Yumnah dake kwonce jikin adarta harara tamkar idannuwanta zasu fita daga jikinta, a ranta kuwa addu'a take yi Allah ya karbi HAJIA KOWAMA ya huta, dan bata tunanin in har HAJIA na kusa zata bari su rayu cikin Salama ita da mijinta


Mahaifin Yumnah ya fitar da iskar bakinsa, a tausashe sosai ya ce" A yi hakuri HAJIA, a yi hakuri, Ni dama na nemi zaman nan ne dan na bada hakuri, domin ban san iya girman abinda mahaifiyar Yaren nan ta aikata ba, sai dai kamar yadda kika sani wani lokacin mata kan yi gaban kansu su manta du wani girma da ALKHAIRI su aikata aiki irin na son zuciya, Aure babu inda zai je, wannan yarinya Allah ya kadarta matar Elhaji ce, babu mai raba auren nan sai in Allah ne ya hukunta, in banda son kai irin nata da ace Tata ce aka aura zata so a maishe mata ita karamar bazawara?....."


"Elhaji, Walahi, Walahi Walahi da a mata irin wannan auren gwara ace ba'a yi ba ka ji na rantse, nawa take ne Yumnar? Gata da yaron ciki, ba'a duba halin da take iya shiga ba shikennan sai ace an mata kishiya ko sanar mata ba'a yi ba?, To Walahi in saki take so a sakar min y'ata cen ya karata da uwar matan!" Mahaifiyar Yumnah ta fada tana fashewa da kuka tana duban mijinta, wanda ya yi mutuwar zaune harda dafe baki


Da mamaki ainun HAJIA ta ce" Ahaf, Allah dai ya sa ba irin yan iska ka auro ba Magidanci!"


Mahaifin Yumnah da mamakinta ya ce" Kennan du irin nasihar da na maki bata shiga kunnenki ba? Du irin rarashi da ban baki da nuna maki cewar hakan ba laifi bane tunda ba haramun aka aikata ba baki ji ba? Na nuna maki cewa ki guji janyowa yarki wulakancin namiji wani auren yake karawar ya kuma zane matar gidan a zauna babu abinda za'a yi baki yarda ba Kennan? Nan na fada maki in me kike takama da shi ke da y'arki ku ringa jin tsoron Allah a mu'amalarku ta yau da kullum baki fahimta ba Kennan?, In me kike takama da shi Akoy wace ta dama ki ta shanye, ke dinma da kike wannan ikirarin an fada maki tsoronki ya hannani karra aure? Bani da halin hakan ke kin san dalili da inada hakan da na karra , shine kike jinginuwa da wannan kina neman yiwa kanki mugun abu? Saki ko? Ba laifi, in sakin take so ya saketa ta tashi mu je, kema ki kwashi naki kayan ki barta a nan tunda nine ubanta ki tafi kema gida ki koyo hankali, Ni zaki mayar mutumen banza? Ni zaki wulakanta dan ina rarashinki? Bari ki ji in har Elhaji nada wata wace yake son karawa na rantse maki da Allah sai na yi gaya na tara jama'a kin dora abincin taron karin aurensa, da ke kika haife shi ai ba zaki ce haka ba, kuma da ke kika haifi KHausar din ba zaki ce a zaba ko ita ko matar gidan ba!, Ki kula in bakinki ya kuma budewa kika furtan shashanci a nan zaki gane shayi ruwa ne!"


Shi yake fada HAJIA na sakin murmushi harda mikewa, su Baba kuwa hakuri suke bashi harda Akilah, su HAJIA nawarah kuwa kawunnansu nema suke su fi karfin gangar jikinsu dan kunya da tsoron wannan lamari


Yana huci ya maida dubansa kan TAUFEEK ya ce" mun fi karfin mu zauna muna tambayarku daya bayan daya zata zauna ko a'a, gakanan gata in ta ce ka saketa na rokeka ka saketan ta zo gidan ta sameni ina jiranta, kuma ina neman alfarma Elhaji dan girman Allah yarinyar da aka aura masa ta tare gobe ko jibi, tunda ai ba wata bazawara bace bale ta kama zama a gidansu, dan Allah ka taimaka ta tare , itama mutun ce idan ya so in ta zo Yumnah ki hadiye zuciya ji mutu!"
Daga nan ya mike yana kade babbar rigarsa ya umarci Akilah da HAJIA su mike su tafi


Du yadda baba ya so dakatar da shi kiyawa ya yi a haka suka tafi suka barsu sai su ya su


Ajiyar zuciya Baba ya sauke yana kallon Yumnah dake duke yanzu a tausashe ya ce" Tashi daga duken nan y'ata ki je kusa da Mamanku tashi kin ji?"


Yumnah ta mike daga duken, maimakun ta je kusa da Mama sai ta je kusa da HAJIA ta zauna jikinta har rawa yake yi


Baba ya sauke numfashi ya ce" Allah ya sanyaya, a yi hakuri dai, in sha Allah ko menene ALKHAIRI ne, ku ku tashi ku je bangaren ku tunda an gama, Allah ya sawaka"


Jiki ba karfi su HAJIA suka tafi, aka bar su Mama da HAJIA baba, da Taufeek da baba da Yumnah


Baba ya mike shima yana fadin" Sai da safe bari in je inada aiyuka a gabana, ka sameni da sasafe in sha Allah in baka takardun gidajen nan"


"Kai d'an nan maganar tarewar fa?" HAJIA ta fada tana kallon Baba,


Baba ya dakata ya dan juyo yana rage tsayinsa kadan ya ce" eh in sha Allah zan yi kiran Malam din abinda yace sai a yi"


Mama kanta wasai take jin ranta, baba na ficewa ta mike tana gyara lafayarta ta dan rage tsayinta ta ce" Sai da safe HAJIA "


HAJIA ta ce" Allah ya tashemu lafiya, ki yi addu'a dai kafin ki KWONTA kuma ki rufe dakin da ky, wannan kiyayar fa ta fara bani tsoro kar a bi dare a kasheki in shiga uku, baiwar Allah dubeta Magidanci solo solo da ita tsaf fa ake iya zane maka uwa dan da wahala in tana da karfi"


Mama kam tafiyarta ta yi tana murmushi


TAUFEEK ya juyo ya zubawa HAJIA ido bayan Yumnah ta mike ta haye da gudu gudu tana sakin kuka hajiar ta wani bankare ta ce" Ji abu ana guduma basa juyawa, wai Magidanci haka kake shaΖ™ar bakin ciki?"


A kausashe ya ce" Ke dai ki ji tsoron Allah, kina waje maimakun ke baba in kika buda baki kika yi magana dan ki kashe wuta ne, a'a, kina buda baki dan ki asasata ne, tsufa kike yi kina masifa, ki tuba kar ki mutu a haka !, Kuma ki yarda ki bi Ni Saudiya ban san yaya zan jijigaki kafin na sake ki a zagaye ba, kuma da kike cewa zaki aura min mace hudu kika kuskura kika karan aure sai dai ki zauna da su , a tsaya ana min auren dole dan an ga bana cewa komai, to Mama kika haifa da mai kwanoni ba Ni ba, dilla tashi ki tafiyarki Ni in je in bata hakuri kin wani rikitata"


HAJIA ta yi zuru tamkar ta summa tana kallonsa ya mike yana harhada mata kayan turarenta


Wani haushi ya tukota ta ce" Kai dai munafiki ne, auren dole? Eh lalle munafiki ne kai, yanzu Magidanci Ni zaka Duba kace an maka auren dole? Khausarar nan in tana waje idannuwanka a kan murje bakin siririya yake, in ta mike ka wani yi KISKIRIM kana leke ko dan ina rufa maka asiri? Munafuki sai na karra maka auren , ana maka gata kana ki, kuma zan je in fadawa mai kwanoni cewar kace a zagaye zaka batar da Ni kuma ka min aure, Allah dai ya shiryeka , kuma in ka ba wancen abar hakuri sai na kaika kotu!"......ta karashe tana jan habar zani tana share yan kwallah ta fice cike da haushi, ita ba komai ya fi bakanta mata ba irin wai ya je ya ba wancen hakuri, du irin rashin da'ar da ta maka masu? Lalle






Bai nufi dakin Yumnah ba sai da ya je nasa ya yi wanka ya kimtsa kansa ya gama dukkan abinda yake sabo a gareshi sannan ya nufi dakin sai baza kanshi yake yi


Fitilar a kashe take, ama kuma har yanzu shashekar kuka take yi a saman gadonta a dukunkune


A hankali ya hau gadon bayan ya dafa ya ji daidai inda take kafin ya shige bargon a hankali ya shiga kokarin dago fuskarta a tausashe ya ce"


























Kai ina , Ni fa Ni fa Daf nake da gamawa in fara *AZAL* IN SHA ALLAH 😌😌😌😌😌😌


[7/19, 3:17 PM] Maman Aslam: πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”β€β€πŸ©Ήβ€β€πŸ©ΉπŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”




*DA CIWO A ZUCIYATA*




πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”β€β€πŸ©Ήβ€β€πŸ©ΉπŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 4️⃣8️⃣


*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*


1: Duk karyar kada


2: Yar mahaukaciya


3: Neman na kaina


4: Bani da zabi


5: Bak'a ce


6: Kutkale


7: Makauniya ce


8: Mage


9: Duk nisan jifa


10: Idan ka raina inda kake


11: Dutse


12: Alkalamin kadarata


13: Bani da zabi


14: Dakika Biyar


15:Wata kokowar


16: Aure yakin mata


17: Ni zan ladabi


18: Daga tafia daukar soja


*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicΓ©
Lait de nuit
Parfums dΓ©sodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaΙ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiπŸ’ƒπŸ’ƒ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙ“i wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan MataπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ






A tausashe TAUFEEK yana kallon yadda gurbin idannuwanta suka yi rado rado fuskarta kuwa har wani hucin zafi take fitarwa ya talabeta sosai a jikinsa ya ce" ya dace zuwa yanzu ki yi hakuri da rigimar nan haka Yumnah, ya dace ki yi hakuri ki dauka haka Allah ya hukunta, kin ga ba ke kadai bace, saka abu a rai kin kusa min asara, bayan wannan fushin nan naki babu abinda baya saka ki, ya dace ki yi hakuri ki yi hakuri an bata maki ama Nima ki min uzuri ki kuma roki ALKHAIRIN dake tare da KHAUSAR a zamantakewarmu"


Yumnah ta lumshe idannuwanta wasu hawaye suka sake biyo wa saman kuncinta, a raunane ta ce" Ta yaya zan iya danar zuciyar tawa? Na rasa ta yaya, tun kafin ka aureni na san cewa ina cin alfarmarta ne, a yanzu da ka aureni ta zamo itama matarka na tabbata zan zamo ne tamkar bola a gidan mijina, ban taba jin kishin mutun da kin kasancewarsa a waje irinta ba, TAUFEEK bana so, bana so Taufeek"


A hankali ya sakata a jikinsa, hannunsa mai dauke da yalwantacen gashin hannu ya saka a hankali ya tare bayan keyarta, da dayan hannun kuwa ya ringa shafa bayanta a hankali idannuwansa a lumshe
Shashekar kukanta ne ya fara daidaituwa sakamakon jinta a jikin da take gannin darajarsa da girmansa fiye da kowani jiki duniya, kanshin jikin da duminsa na sakata barci koda bata yi niya ba, fafadan kirjin na saka tsigar jikinta tashi, a hankali kunnayenta suka ringaa jiyo mata dadadar iskar bakinsa mai dumi a kunnenta
A hankali ya juye da ita a cikin bargon ya zamo tana kasansa shi kuwa a sama
Idannuwanta da sukai shame shame da hawaye yake kallo, cen kasan zuciyarsa kuwa kokowa yake yi da tarin tunanin wace take kila wa kalar rayuwarsa, wace bata kallonsa a matsayin katon dake iya kai keyarta kas,
A hankali ya dan matsewa junnansu waje sosai , yana sinsinar wuyanta a tausashe cike da rarashi ya ce" Idan kika ga mace ta zama banza a gidanta, ita ta fara banzatar da kanta, ko a soyayata da ke ke ba banza bace da ban aureki ba, Yumnah, KHausar ta shigo rayuwarmu, Please kar ki ja, Bana so ki ja, bcz ni da kaina ban kwatanta ja ba, ki yi hakuri zan kasance mai KAMANTA adalci a tsakaninku ko dan gobena, I'm sorry wife "
Kwarai ake cewa, dadadan zance na sanyaya zuciya haka ne,
Yumnah na tare da tashin hankali da bakin cikin auren mijinta, sai dai irin yadda ya bata kulawa ya matukar saka ta ji yar Salama a zuciyyarta, ama tana kan bakanta, ba zata taba son KHausar ba, KHausar makiyaya take a duniyarta, kuma in sha Allah sai ta ci galaba a kanta, ba an aurawa mijinta ita ba, ta yi alkawarin sakata barin gidan nan da kaffafuwanta, in ta san wata bata san wata ba, ko ba komai ta rigayeta tashi tunda har ta rigayeta Sannin waye TAUFEEK a badini!


Da kyar ta samu barci, shi kuma ya mike ya koma dakinsa yana jin yannayinsa du a takure


A kan salaya ya kusan raba dare , yana fadawa Allah dukan damuwarsa
Sai da ya gama sannan ya KWONTA da layin KHausar a hannunsa
Yana so ya saka layin a wayarsa wani abu na hannashi, bai san me yasa yake so du wani abinda ya shige nata ya zamo nasa ne! Shi fa baya tunanin zai iya kawar da kai da wasu abubuwan, ama zai bi a hankali yadda komai zai zamo masa yadda yake so




Washe gari kusan karfe goma ya sauko


Yumnah ya samu a falo tana zaune da wayarta a hannunta
Amsa wayar take yi, gannin ya sauko ta yi salama da wace suke wayar ta ajiye a gefenta tana kallonsa tamkar ta daukeshi da idannuwanta dan ya mata kyau sosai


Zama ya yi gefenta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login