Showing 105001 words to 108000 words out of 186303 words
ALKHAIRI ce ita, kuma tana mata Adu'ar gamawa da duniya lafiya, wani gefe na cikin zuciyar Tata kuwa tarin mamakin yannayin auntyn nasu ya gama rike mata wuya, yanzu wace mace ce zata ki yayansu? Menene dalilinta na nuna kiyawarta a lamarin? Allah shi kyauta
"Kin ga, ki rufawa kanki asiri da koke koke, tunda kin ga auren nan dai an daura shi ba kuma za'a kwonce ba da izinin mai sama, kar dan zuwan da zan yi in dawo ta shigo ta dakeki a banza a wofi kin ji? Ba dai Magidancin bane bai maki ba? Ai shan koko bukatar rai ba sai kin daga hankali ba idan ya ji da shi aka daura auren ki rintse ido ki masa jan ido ki ce takardarki, da bakinki sa komai? Yanzu ki daina wani kuka dan bashi da anfani kin ji y'ar albarka?" HAJIA ta fada bayan ta rike hannun KHausar ta tausasa muryarta ainun
KHausar a hankali ta ce" HAJIA, Kennan shima bai san da wannan abin ba?"
HAJIA cikin hikima Tata ta amsata da" Eh, bai sani ba, hasalima iyayenku suka tsayar da hakan bisa rokon mahaifinsa "
KHausar cike da mamaki da wani firgicin ta ce" HAJIA aba na cen gidan ne ya nemi auren?"
HAJIA ya ce" Eh, shi da kansa mai kwanoni ba"
KHausar ta shiga gyada kai cike da kalar tausayi ta ce" Na san bai san inada saurayi ba, Ama HAJIA shima TAUFEEK din ai an cuta masa, auren dole ai akai masa shi dinma ko?"
HAJIA ta gyada kai ta ce" Wannan haka yake, Ni Bama abinda zai batan rai a zo ana fadin kuma daga aurenki an sake ki y'ar nan, ke dai yanzu ki share hawayen ki ki tausayawa kanki, komai dan a bi a hankali ne, duniyar nan akoy mai gudun bacin ranki irin Magidanci? Idan kuka zauna sai ku yanke abinda ya dace da ku ko?"
KHausar ta ringa jan hanci tana sauraron yar hayaniya bayan fitar Hajiya
Gaba daya abin yana nema ya girmami tunaninta
Ta rasa a inda zata ajiye wannan sabon abin
Abu daya ta sani shine ita da TAUFEEK *HARAMUN DIN JUNNA NE*!, idan ta tuna menene aure da tsarabe tsarabensa sai ta ji hankalinta na neman sake tashi , da sauri ta ringa kade tunanin tana jin tamkar wace ta tafka sabo tuna abinma a ranta, 'Hum, Allah ya kiyashemu abin kunyar nan ba da mu ba, bawan Allah in ya ji wannan aiki ta yiwu saima ya yi kukan takaici!' ta ayyana a zuciyyarta ta kuma dauri zaman daki ba tare da ta fito ko ta kimtsa gashin kanta ba, ita bata ga lokacin ba wani abu wai shi gashi ba a yanzun kam, ana ta Kai wa yake ta kafa?
Murmushi kawai HAJIA ke yi a ranta tana Ayana ' Tirkashi, ai Inaga Bama sai na wani boye masa ba, tunda har Allah ya yi yarinyarma ba zata amshi abin da dadin rai ba koda ta amsa din, ama ba Ni zan sanar maka ba zan bar mahaifinka ya sanar maka, abinda na sani daya ne tak a yanzu ka yi aure, a yanzu ka auri yar mutuncin da ta san darajar iyayenka, babu ruwana da kyan banza da farin fatar banza da iyayi na gayu, abinda na sani shine wannan yarinya itace daidai da kai, kuma bi izinillah itace haske a cikin hasken gidan Mai kwanoni!'
A baban gida shagali ake yi wanda ya daure kan daidaiku daga cikin ahalin gidan, domin babu abinda ya fi basu mamaki da daure masu kai irin yadda suka ga Mama na shige da fice cikin fara'a da farin cikin da suka gaza hade mahadar abin, to su basu ga hadi ba, inma zaman bikin karar kawar danta ta yi niyar yi ta je gidan su yarinyar su yi zaman mana? Ta yi zamanta a nan harda girki da samun baki? Lalle, wani shagalin sai a gidan mai kwanoni! Gefe guda kuwa ga Hajia tana nata itama shagalin, dan kuwa ita din tuya ake ta yi ta masa ana fitarwa sadaka sosai , dan hakan ta shirya wunin yau din dama, sai da yama ta yi sosai ta kimtsa ta nufi bangaren TAUFEEK, domin ta tambayi yan matasan dake zuwa wajensa inda yake sun tabbatar mata yau din bai fito ba, sai kuma ta karra tabatarta a wajen mai gadi dan haka ta mike ta nufi bangaren nasa hankali kwonce
Kamar yadda ta saba bayan sun gaisa da Yumnah ta sanar mata ta sanar masa itace, ama bayan zamanta a kalla ta dauki minti ya fi Ashirin bai sauko ba, hakan ya sa ta rasa shin hawa zata yi ko dai zaman zata ci gaba da yi ko Allah zai sa ya sauko? Gashi Yumnahma tunda ta hau bata dawo ba shiru kake ji
Har HAJIA zata yi tafiyarta gannin shirun ya yi yawa ta tuna waye jikanta, idanma dodo yake a wani wajen banda a gareta da ahalinsa baki daya, ta tabbata in dai ya san da zuwanta ba zai dauki lokaci kalau haka bai sauko ba, dan haka ta juya jiki ba karfi ta shiga hawa tana salama dan gudun shiga hakin kowa
A kofar dakin ta dakata ta yi bugu ya fi a irga tana Salama, ama yarinyar nan da dakinta ke daf da nasa bata fito ta nuna mata ta san da mutun a wajen ba, ita kuma ta ki ta hakura dan jikinta ke bata ba lafiya ba
A bangaren Yumnah kuwa tana sauraron HAJIA, hasalima a tsaye take jikin kofarta tana murguda baki kasa kasa ta ce" Yau na ga jarabar naci, ba zan kira maki shi din ba, Ni kam Inaga bayan rabuwata da wancen a nacin saura wannan masifafiyar tsohuwar, a wuni sai ta mana shigowa uku in yana nan ta zo ta ishe shi da surutu ta tafi, ko mahaifiyarsa bata masa zuwan nan kamar yadda wannan mata ke yi, ba abinda ke bani haushi irin turare turaren shirmen da take masa, ko me take tunani?, Inma menene bata isa ta nunan son mijina ba ama sai tana abu kamar wace bata san me take yi ba, a barshi ya huta tunda bai fito ba ai damu ne baya so zan gani in har zaki shigo dakin kai tsaye ne, inama ace dakin na shige na same shi koda wani abin yake in dauki hankalinsa !"
HAJIA kam jin shirun ya yi yawa ta shiga tunanin ko sauka take yi ta koma bangarenta ta yi kiran mahaifinsa ya mata kiransa ta ji yana kalau? Idan har ta ji an gama wannan ne kaΙai damuwarta dan bata son abinda take ji a ran nan nata
Sai kuma ta shiga tunanin yaushe ta koma cen?, Kai ina , a dan daburce ta juyo ta kama kofar ta bude tana Salama da karfi hadi da Hanna idannuwanta dagawa koda taka tarda wani abin to fa ya zamto idannuwanta basu gani ba
Shirun ya yi yawa, a hankali ta shiga bin dakin da kallo
A gyare yake tsaf tsaf ga kanshin turare da sanyi mai karfin tsiya a ciki har idannuwanta suka sauka kansa wajen kujerar dakin ta gaf da gado kansa a saman kujerar yana zaune a kasa jikinsa ba riga dan ya samu ya cireta da ya raarafa ya yi sallar azahar daga ita bai samu yin ta la'asar ba domin yana kwatanta mikewa sai ya ji kamar za'a maka shi a kas ga wani ciwon kai mai tsanani da bugawar zuciyar da sam bai san zasu iya riskar shi a irin wannan lokacin ba
Gaban HAJIA sai da ya fadi, ta dakata tana kiran sunansa ama ya kasa amsa mata
Da sauri ta daga kaffarta ta karasa inda yake ta shiga tabashi da ambaton sunnansa
A hankali ya iya buda idannuwansa ya sauke kwayarsu a saman fuskarta a lokacin da ta duko tana taba wuyansa ta ce" Subahanallah, Magidanci baka da lafiya ne dama ban sani ba? Ama dazun fa da na Barka kalau na tafi"
Idannuwansa ya lumshe yana sauke numfashi a hankali yana lumshe sunansa kasa kasa , muryarsa cen ciki ya ce" HAJIA......, Kin dawo?"
HAJIA ta gyada kai ta ce" Bari in kira a kaika asibiti kai fa baka iya ciwo ba, na shiga uku ka ga yadda idnanuwanka suka kade kuwa? Jiki du ya dime da zafi jijiya ta yi rado rado, kai subahanallah wannan yarinya da kake aure Ni tana da hankali kuwa? AI sai ki fada bashi da lafiya ko?"
Da kyar ya iya karasa jin maganar da HAJIA ke yi, a hankali ya dan mirgina ya dora kansa saman kaffafuwanta dan hakan yake da bukata, shi dama mutun ne da bai iya ciwo ba sam, kuma idan yana ciwo ta yannayin shanyuwarsa ake ganewa ba zai zo da kansa yace ciwo yake ba har sai ciwon ya kayar da shi tamkar ba likita ba, HAJIA kam ji ta yi hankalinta ya kara tashi, domin ko yana ciwo bai cika yin laushi da ita haka ba, abinda tana ihun a kaishi asibiti yana fadan ba inda zai je? Ama yanzu jikinsa kamar ana rura wuta?
Hankali tashe take janyo abin gadon dan hango salularsa da ta yi karamar , dan kuwa tana iya kamo lambar mai kwanoni da tasa tsaf a kanta
Tana ta rubuta numbobin muryarsa cen ciki da kyar ya iya budar bakinsa a hankali ya ce" HAJIA, KHausar.....yanzu ta daina kukan ko? An mata auren ta huta ko?"
Da sauri HAJIA ta yi cakkkkk daga abinda take yi tana kallonsa
A raunane ta ce"
Kai dai gaskiya bana so ma nace an ji kunyatu sai an saka nace, fisabililahi kar dai kace ciwon Kauna kake? To wai kai dilla mikeππππππππ
π¨π¨π¨π¨ Akoy fa rikici, watau ita Bama ta hango halal a ita da Magidanci ba, magidancinma nawa yake in ji matar jikan HAJIA!π¨π¨π¨π¨
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
*DA CIWO A ZUCIYATA*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 4οΈβ£1οΈβ£
*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*
1: Duk karyar kada
2: Yar mahaukaciya
3: Neman na kaina
4: Bani da zabi
5: Bak'a ce
6: Kutkale
7: Makauniya ce
8: Mage
9: Duk nisan jifa
10: Idan ka raina inda kake
11: Dutse
12: Alkalamin kadarata
13: Bani da zabi
14: Dakika Biyar
15:Wata kokowar
16: Aure yakin mata
17: Ni zan ladabi
18: Daga tafia daukar soja
*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicΓ©
Lait de nuit
Parfums dΓ©sodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaΙannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiππ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mataπππππ
A raunane Hajia ta ce" Eh an daura ama tana cen tana ihun bata so kuma, y'ar nan dai sai addu'a sosai abin nata sai addu'a dan nan, gashi aure ya dauru kuma"
Idannuwansa da sukai masa nauyi ya bude yana kallonta, ya dan dauki lokaci yana nazarin maganarta kafin ya ce" bata so? Auren da ta kawo mutumen da kanta ne bata so Hajia..........
........." Ya karashe yana sake rintse idannuwansa da karfi saboda sara masa da kansa ya yi
Hajia ta so cicidawa da shi ama ta gaza dan gaba daya yana son sage mata gwuiwoyinta da nauyinsa da kuma rigimarsa, da kula sosai ta ce" Eh wai bata so ina ita ina mijin , yaro ne meye meye, kai dai abu sak irin na kamun aljannu da kyar na fito dan na ji a raina kamar kana wani hali "
Shiru yanzun ya mata, shiru sosai ya mata banza, ta ci gaba da maganarta ya kyaleta
Jin ya yi shiru ya saka Hajia taba wuyansa, sosai jikinsa keda zafi haka kuma ita da ya ajiye kansa a saman kafafuwanta tana iya jin yadda zuciyarsa ke bugawa
Da kula ta ce" Bari in kira mai kwanoni mu je a kaika asibiti magidanci ka ji?"
Shiru ya mata bai ce mata eh ko a'a ba, shi kadai ya san irin nauyin da karfin da kansa ya masa, jikinsa kuwa tamkar ba nasa ba haka yake ji
Hajia ta samu da kyar ta sauke kansa ta Ιora saman filo harda rufa masa abin rufa sannan ta fita ta sauko kasa tana faman duba wayarta
Turus ta yi tana kallon Yumnah, wace ke zaune a baban falon kafa daya kan daya tana amsa waya, yannayinta na iya fasara maka halin farin cikin da take ciki,
Itama Yumnar da mamaki take kallon Hajiar, domin a tunaninta Hajiar ta jima da barin gidan ai
Bata ce mata komai ba ta yi hanyar fita sai sake riΖe hijabinta take yi, ita yanzun ai bata da lokacin uban kowa tunda magidanci ba lafia , bari dai a kaishi asibiti a dawo sai ta rikita kowa a gidan nan, ta kula yarinyar nan banda abinda ke damunta na rashin auki harda hauka take fama da shi, wannan ai ba matar auren magidanci bace, ace magidanci ba lafiya matarsa zaune tana waya? Sakarcin banza sai fama da kashi a wuya ita ga mace, shirme zata ga mata gannin idonta
Karasawa ta yi har bangaren su Mama ta hadu da yarinyar wajen kishiyar maman wace take riko wato Hamdiya
Wayar ta mika mata ba tare da ta iya amsa gaisuwarta ba ta ce" Ke Hamada dubo min lambar mai kwanoni kaina ya fashe na gaza ganewa dama Ni a duniya lambar magidanci kadai na hadace a kaina"
Cike da ladabi Hamdiya ta amsa ta fitar da numbar aban ta aika kiran sannan ta ba Hajiar
Hajia ta dakata har Aba ya daga wayar ta dan matsa tana rage murya ta ce" Kana ina ne Ni?"
Aba ya sanar mata cewa yana tare da baki ne dan bai zaci yar gayar da ya yi za'a taru haka ba
Hajia ta ce" To ko me kake yi ka bari ka zo ka kaimin magidanci asibiti, ka ganshi cen rai a hannun Allah jikinsa zafi rau, Ni abin ya bani tsoro tunda Ni din nan ya dora kansa a kafata yana min magana a sanyaye ka san kuwa ba lafiya ba dan in dai lafiyar Allah ai bama magana a hankali da Magidanci ko?"
Aba ya yi dan tsai jin TAUFEEK ba lafiya, ga yadda Hajia ke kwatancen kamar sosai ne
A tausashe, da ladabi irin na d'a da mahaifiyarsa Aba ya ce" Subahanallah, kin ga kuma lafiyar Allah na baro shi dazun, to ganinan zuwa sai mu gani in asibitin za'a kaishi Hajia"
Hajia ta ce" Shine ai , ka ga magidanci ba hakurin ciwo ama wannan baba ne, kafin ka dawo bari in masa turare kar aje wani kafurin marar mutunci na son cinma jikana, sambatu daya yake yi bawan Allah, ama duda haka sai da ya yiwa Khausara fatan alkhairi , ina jiranka ka ji Elhaji baba?"
Daga nan suka yi salama, Aba ya yi murmushi ya gyara zamansa ya ci gaba da kulawa da bakinsa dan kuwa cutar da akace Elhaji karami na yi bai sakata a ransa ba, bale ta dame shi
Hajia ta kashe kiran suka yi ido hudu da Hamdiya dake tsaye yannayinta du wani iri
Hamdiya murya a raunane ta ce" Hajia Yayan namu ne ba lafiya?"
Hajia ta karra zuba mata ido, irin yadda idannuwanta suka cika da kwala sai da abin ya bata mamaki, a gidan nan tana iya cewa yadda take shiri da yarinyar ko da jikokinta sauran su Ishirat basa yi haka, domin yarinyar akoy hakuri da son shiga jikin Hajiar, du irin yadda marikiyarta ke hannata kulun tana gindin Hajiar
Hajia ta dauke kanta ta ce" Eh shine, ama da sauki in sha Allah dan yanzu zan turara masa hantiti da kaka ka yi ka fito ba komai bane sharin masharanta ne!"
Daga haka ta yi gaba, ita kuma Hamdiya ta nemi waje ta zauna hankalinta na neman tashi, sosai ta ji hankalinta na neman tashi, dan kuwa a jiyan nan Hajia Fatahiya ta yi wata magana a gabanta wace ta tsaya mata a rai ainun, kuma tana matukar tsoron ya zamto shirmen da matarsa ke yi a baibai ya zamo ila a gareshi, bata jin zata iya hakurin kawar da kai har wannan abu ya tabata, domin bata san girman laifin abin da irin inda zai kai ba, a da tana duban Yumnah da duba kala biyu, gagarumar wace ta shiga tsakaninta da abinda ya zamto buri, fata idan har allhairinta ne, sai kuma kallon wace ya zama wajibi ta girmamata dan ta zamo baba a cikin manyan gidan, daga baya da ta ga wacece Yumnah matar da Allah ya bata dama take wasa da ita, wace idan hanyar kirsar nema bata dauko ta kirki ba, tunda ta yi wasa da abinda mahaukaci kadai zai yi wasa da shi watau mahaifiyar mijinka ka dauketa abar gaba ko wata abar ka yi kishi da ita, sai ta fara saka ayar tambaya a kan hankalinta, a hankali ta ga take takenta a kan Hajia kaka , hakan ya