Showing 99001 words to 102000 words out of 186303 words

Chapter 34 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18753

kujerar nan ya lumshe idannuwansa
Tabbas ya san bashi da lafiya, zai kirayi docter ta dauki jinninsa may be rashin isashen hutu ne ke neman sakashi kwonciya


Khausar na tare da ahalin gidan mai kwanoni har aka salame su daga asibiti
Mota uku suka cika har ita suka nufi gidan domin dangin Hajiar sun fara halarta summa ta ko'ina, baby dai gata dangi na maraba da ita ama jikin uwarta du ya yi sanyi tamkar ba karuwa ta samu daga Ubangijin talikai ba wanda shi ya isa fitar da na kirki tsakanin mace da namiji, yana iya baka namijin ya zamo baban tashin hankalinka duniya ya kuma kaika wuta gobe kiyama, yana iya baka macen ta zamo itace jin dadinka mai jin kanka duniya da kiyama, har ta manta karin maganar da a haifi gwama gwara a haifi matar gwamna, ta gagije ta hade rai ko magana da kyar take yi, uwa uba abinda ta so bai samu ba cewa sai dai kishiyoyi su ga ta haihu, haihuwa mai dadi sai da ta tara mata kaf kishiyoyin ya zamo sunne suka kaita asibitin mijin yana gida yana hutawa dan ba dan fari kuma dan da bai taba samu za'a kawo masa duniya ba, ya zamana itace a ragaya itace a mumunan halin da ta saka zuciyyarta dan jin dadi, kamar zata mutu haka take ji saima idan ta bi Mama da kallo ta ga yadda take car car da ita kamar wace bata girmeta ba, dan kuwa ba zaka ce ta haifi taufeek ba, haihuwa daya haihuwar ta tsaya sai gayu da kanshi ke fita du inda ta tsaya tana walwali ita ga uwar dan masu gida ko?, Ba zaka taba cewa ta girmeta nesa ba kusa ba dan kuwa ita HAJIA yarinya ce haihuwar nan itace ta fari amarya take a gidan mai kwanoni cike da burika nata na kanta masu zaman kansu, sai fatan Allah ya bata Sa'a


Sai da suka gama ajiye mata kayayakinta sannan suka wuce bangaren Hajia, Hajiar cike da mamakin Yumnah ko a leke ko kafarta ba'a gani ba a yanzunma ? Uhum....




Fira suka sha , KHausar cike da jin kunya domin HAJIA gyara zama ta yi ta saka Mama a gaba wai du abinda ya dace na yi a rubuta masu su fara zuwa kasuwa, ita saima da ta sha mamakin Kennan dai maganar aurenta dai da gaske ne? Mahaifinta yace mata da izinin ubangiji ya yanke aurenta nan da kwana goma, kai sai take ji wani iri, wai ita KHausar? Ashe dama mijin nata a bayan gidansu yake bata sani ba?, Allah mai hikima bata da abin fada sai hamdallah


Bata tashi tafia gida ba sai da yama ta yi sosai domin har sai da ta haษ—awa HAJIA yar tsala ta toya suka ci abinsu harda Mama sannan maman ta saka direba ya kaita har gida sai godiya take mata, HAJIA kuwa fadi take in sha Allahu gobe zasu je su ciro anko ita da TAUFEEK, ita kuwa daria kawai ta yi abinta tana tunanin HAJIA da rigima ina ita ina tisa Taufeek cirar anko? Cap itafa tunda ta san waye shi take wani kiyaye wasu abubuwan da a da kai tsaye take masa


Koda ta huta sosai wayarsa ta gwada kira dan ta sanar masa da kanta domin ta san in HAJIA ta ji yanzu zai ji, ita kuma haka kawai bata so ya ji daga bakin wani, tana so ta ji irin murnar da zai yi, tana matukar so ta ji irin farin cikin da zai nuna , hakan nema ya sa har ta kusa shiga barci tana neman layinsa , sai dai cikin ikon Allah Sweet off ake fada mata, karshe dai haka ta hakura ta nemi na Salis , sai dai shi kuma tana ta ringin har ta katse bai daga ba , a dole ta yi kwonciyarta da nufin gobe asabar in sha ALLAH tana da isashen lokacin hutu da gyaran jikinta da kuma neman wayar TAUFEEK din , Salis kuwa ta sani ne a yau din sai ya nemeta dan haka ta kashe wayar ko zata samu isasshen hutu dan ta san in dai ya ga miss call DINTA zai kirayeta ne ya tsareta da firar dare




Wasa wasa lokaci matsowa yake yi, lokaci da wuyar zuwansa saka shi ne dama, haka kuma cikin ikon Allah Mama ce da kanta mahaifiyar TAUFEEK ta yi kiran KHAUSAR cewar ta dakata da zuwa wajen aiki har a daura auren nata wanda dududu abinda ya rage kwana uku ne kawai, sai take ji kamar fa wannan din da gaske zai tabbata ne


A kulun zata tashi ne cikin tarin fargaba da tsoro da faduwar gaba, bale a yanzu wayarta da Salis ta rage sosai ya zamtoma itace zata yi kiransa kulun idan ya daga kamar wanda yake cikin ษ“aci ko busy kulun yana da uzurin da zai gabatar mata da nuna mata zai tabota ya katse kiransa hakan ya sa zuciyyarta ke cikin tarin zulumi da tsoro har take tashi tsakiyar dare tana fadawa Allah take kuma daukan azumi kan koma menene ke damunsa Allah ya sa ba na daina aurenta bane tunda dai zuwansa da farko farko ba haka yake ba


Ana saura kwana biyu Hajiya ta yi wani zuwanta gidan suka dinke da Mama a daka , sai da yama sosai ta juya gida da tarin kyaututtukan da suka saka KHausar fashewa da kuka cike da gannin kokarin mutanen ta ringa yi masu Adu'a da tunanin koda bayan aurenta ne rabasu zumunci da mutanen nan da ita ba zai taba katsewa ba, abinda ya karra daga mata hankali kwana biyu saura a daura mata aure ama bata da labarin Taufeek, ta yi kiran, ta bar msg ama shiru, ko yanzu ta tambayi HAJIA sai take ce mata aiki ne ya mukemuke shi dan suma rabonsu da shi a yi fira ta gwa da gwa har sun manta, sam basa samun lokacinsa , duda haka dai ta so ta sake damun kanta da tunanin duba da bai taba share sati cirrr bai zo gidan nan ba, ama gashi har yau kwana takwas ba shi ba labarinsa? Gashi an kusa fara tafia HAJI , ta yiwuma har ya tafi bata da labari




Da dare bayan Aba ya dawo da auta an dan taba fira Aban ke sanar mata wani sabon cenji cewar ba zata dauki dogon lokaci zata tare ba wai mahaifin mijin nata ya nemi alfarmar ta tafi gidanta da wuri , wannan ya sakata shiga hali irin na kimtsatsun amare, ba irin amarenmu na zamani ba da za'a masu auren sai dai su maka kiba su yi bulbul da su, maimakun su ringa zugewa saboda zulumin rabuwa da iyaye da tunanin sabuwar rayuwar da za'a je a tarar a gidan mijin, wanda in dai yarinya budurwar take dole tana cikin zulumin abubuwa da yawa masu firgita zuciyyarta


Tarin fargaba da tsoro ya sakata da safe neman izinin zuwa gidan yan uwanta, wanda tunda aka yi auren
kannen nata bata taษ“a zuwa gidajensu ba dan kuwa takan ce in dai ba halin rashin lafiya ba ita din bana ce na zata je gotai gotai yin komai gidansu ba, sai dai su su zo gida lokaci zuwa lokaci dan su dinma Aba ya Hanna zuwansu koda yaushe yace su yi zamansu a dakunnansu su yi ibada


Mama ta hanna mata tafiyar, karshema ta sakata zaman dakin dole, domin a yau din baki Mama ta ringa samu yan anguwa ne da sako ya je masu ta wajen auta cewar daurin auren KHAUSAR din gobe da safe a masalacin anguwar, sai kuma daidaikun dangi dake nesa da sukan zo da nufin kwana


A yau din du sai ta idasa firgicewa, Bama idan aka daga labule dan a ga wai barci take ne? Har Kannenta suka iso ta ringa binsu da kallo irin murnar da suke a ranta tana tunanin shin ina madafa ta rasa Salis din tun jiya ta rasa da wa zata zanta tarin tsoro da fargabar dake zuciyyarta har dare ya tsala sawaye suka dauke sai daidaikun da zasu kwana a gidan a dakin Mama hakan ya sa ta labe ta ringa kuka ko abinci ta kasa ci ta kasa motsin kirki du ta haukace burinta daya ne a yanzu ta samu wayar TAUFEEK, ama amsa daya ce wayarsa a kashe? Shin ina zata saka ranta da tashin hankalin nan?.......




๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”โคโ€๐Ÿฉนโคโ€๐Ÿฉน๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”




*DA CIWO A ZUCIYATA*




๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”โคโ€๐Ÿฉนโคโ€๐Ÿฉน๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 3๏ธโƒฃ8๏ธโƒฃ


*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*


1: Duk karyar kada


2: Yar mahaukaciya


3: Neman na kaina


4: Bani da zabi


5: Bak'a ce


6: Kutkale


7: Makauniya ce


8: Mage


9: Duk nisan jifa


10: Idan ka raina inda kake


11: Dutse


12: Alkalamin kadarata


13: Bani da zabi


14: Dakika Biyar


15:Wata kokowar


16: Aure yakin mata


17: Ni zan ladabi


18: Daga tafia daukar soja


*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicรฉ
Lait de nuit
Parfums dรฉsodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waษ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuษ“i wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ






Karshe wayar HAJIA ta shiga kira, tana ji a ranta in dai yana gidan Hajiar zata bata shi, zata masa kuka ya sanar masa ya rarasheta ya kuma tayata da addu'ar Allah ya sa a yin in ALKHAIRI ne


Kira na biyu Hajia dake falonta zaune shiru, TV a kashe, rediyo a kashe, hankalinta a kansa ta kori yar gidan HAJIA tunda ya shigo falon suka zauna sunna zaman kurumci ta yi tambayar shin a kawo abinci ya kyaleta ta yi tambayar bashi da lafiya ne? Ya kyaleta, a kwonce yake saman sabuwar kujerarta da aka cenza mata ko kwana biyar basu yi ba, idannuwansa lumshe, gashin girarsa sun karra yin lumbuk sun yi sidik a goshinsa, hakama na idamnuwansa, jan lebensa jajajir ya bushe sosai sai hasken fatarsa da ya karru ya yi fayau da shi yana kwoncen bai ce mata ci kanki ba, itama kuma a zaunen da take kunshi ne ta kunsa a kaffafuwanta ta saka Safa saboda gobe idan Allah ya tashemu lafiya karfe shiga zuwa bakwai tana gidan su KHausar ai dan haka take gama komanta da wuri danma ta jima bangaren Mama sunna shirye shiryen abubuwan yi a goben ita da ita, da tunima kunshin nata ai ya jima a kafarta


Tana daga kiran ta Muryar ta gane mai kiran, ta saki wani murmuahi tana dan gyara zama ta ce" Amarya ce? Khausara ya gidan ya shirye shirye ? Ai Ni dinma abinda ya sa baki ganni ba yau din shirin nake, kin dai ganni nan an kusan kunshi , kuma so nake sai an daura mu wuce kasuwa da yan matan gidanku mu ciro bayanin ankon, har ina cewa MAGIDANCI kala biyar cir zan ciro mu wuni muna rakashewa ranar tarewar ko?"


KHausar ta ja hanci da kyar tana sake boyewa a jikin katifarta muryarta a raunane ainun ta ce" HAJIA, ina yini? HAJIA wai ko dai TAUFEEK ya yi tafia ne?"


HAJIA ta yi shiru, ta yi kiskirin tana sauraron yannayin na khausar din, kasa kasa ta ce" Waye wai Magidanci? Gaya a falona ai ya min jikaka a kujera, bara in baki shi "


Daga haka HAJIA ta dafa ta mike ta kai ta kanga masa wayar dan kamar wanda ya yi barci tana fadin" Amarya ce amsata"


Idamnuwansa ya bude a hankali ya sauke dubansa a fuskar Hajiar, idannuwansa sun yi jajajir hakama hannunsa ya dauki zafi sosai


HAJIA ta dauke kanta daga fuskarsa tana jin kamar zuciyyarta na neman gazawa ta mike ta yi gaba dan sai ta ji kamar zuciyyarta zata gaza daukan yannayinsa


Shashekar da take yi da jan hanci yake sauraro, da kyar ya iya budar bakinsa da har ya fara sabawa da shiru shirun da ya aura kasa kasa sosai ya ce" Are u crying?"


Kamar jira KHausar take ta bude idannuwanta da kyar da suka mata nauyi ta fashe da kuka muryarta a kurya tana yi ba ji ba gani har shasheka take yi


A hankali ya lumshe idannuwansa yana jin kamar ba kukan nan yake da bukatar ji a irin wannan lokacin ba, sai dai cikin ikon Allah tana daya daga cikin mutanen da suke da alfarma a duniyarsa, ko me take so takan yi kanta tsaye ne ba ruwanta, shi kuma yana iya dauka koda a wani irin lokaci ne, dan haka yana sauraronta har ta ringa jan numfashi da kyar kafin ya iya budar bakinsa ya ce" ke fa likita ce, kin san irin daga hankali haka bashi da kyau ko?"


"TAUFEEK na maka laifi ne?" Ta yi gagawar tare numfashinsa


Shiru ya yi dan bai san me zai ce mata ba, laifin me kuma ?


KHausar ta dora da fadi " TAUFEEK wayarka a kashe, gaba dayama Ni ka cenza min, me na maka ne? Ka san halin da ake ciki kuwa? Ance wai gobe za'a daura min aure da Salis kuma ka ga Salis yana neman ya min irin abinda Mujaheed ya min ko?, TAUFEEK bayan wannan aure fa nima wai aure, TAUFEEK kuma ka ga in shima ya guje min fa? TAUFEEK bashi da matsala Salis ya nuna yana sona nima kuma ina sonsa fa, TAUFEEK ka ga tsoro nake ji, hankalina du a tashe yake, na rasa me zan yi tunani, in fa aka fasa????? TAUFEEK ka ga.............






"KHausar Please........." Ya fada muryarsa a cen ciki yana dan son bude idannuwansa ama sun kasa buduwa


Da wata Muryar da bai san yana da ita ba mai daci da kaushi sosai ya ce" In ya fasa aurenki sai me?, Ya dace ki daina daga min hankali haka, saboda shi ne zaki zauna kina kuka kamar an kashe ki?, Why a kulun burinki ki Hanna min kwonciyar hankali? KHausar! Idan ya fasa aurenki a gobe kina iya daukan matakin da kike so ok?, Ba zan rarasheki saboda wani ya ki aurenki ba, Ni kuma halin da nake ciki wa zai rarasheni? I'm tired KHausar, na gaji plz!"


TAUFEEK ya karashe fada yana sauke amon muryarsa a hankali, sai kuma ya katse kiran ya ajiye wayar nan ya mayar da idannuwansa ya lumshe


Kamar an tsikare shi ya bude su da dan sauri yana duban wayar


Hannunsa ya mika ya dauki wayar a hankali ya shiga kiran layin nata


Ya yi kira ya kai sau biyar kafin ta daga, har saima da ya nemi waje ya zauna sannan ta daga kiran, kuma tana dagawa alamun kukan take kawai yake ji


A hankali ya furta" I'm sorry KHausar"


KHausar da abin ya nemi girmamar tunaninta a hankali ta ce" Na tambayeka na maka laifi ne? Ka ki bani amsa, ama me yasa ka cenza min?"


Kasa kasa sosai ya furta " Kukan ne bana so"


KHausar ta ja numfashi tana sauraron Sa, cen ciki ta ce" Ama wa zan yiwa kukan bayan kai kadai nake yi ma?"


Wani irin sarawa da kansa ya yi sai da ya ji kamar ya rotsa wayar da kasa


Da kyar ya iya saisaita kansa a hankali ya ce" A yanzu, kina da wanda zaki yiwa kuka KHausar....nd ya saurareki dolensa, domin idan bai yi ba ba zan iya kyale shi ba, ki daina kukan haka kin ji? Zai zo za'a daura in sha Allah, nima zan zo gidan da safe, ko yanzu kike so na zo?"


KHausar ta ringa sauke ajiyar zuciya, tana jin wata salama na ziyartar zuciyyarta


A hankali ta ce" A'a, dare ya yi, da safen sasafe zaka zo ko?"


TAUFEEK a hankali ya furta" In sha Allah "


KHausar ta sauke numfashi ta ce" Sai goben, thank you besty am"


"By" ya furta cen cikin makoshinsa sannan ya kashe kiran


A hankali HAJIA ta ja baya ta koma dakinta ta saka ky ta haye gadonta tana dan kada kafarta ita dai bata san fitarsa ba dan bata san yaushe ya fitan ba




Tunda safe ya wayi gari da mamakin Yumnah, domin Yumnah ce da kanta ta ciro masa wani danyen yadi irin jikaken yadin nan na manya da hula da takalmi da su agogo komai dai sannan sai wani irin annuri take saki wanda ya jima bai ga irinsa a fuskarta ba taba sake fadin Bara ya je bangaren su Mama ta masu a dawo lafiya, shi ya zatama zata je ne itama, sai kuma ya kade ya ci gaba da shan lipton dinsa hankalinsa a rarabe yana jin kamar ya koma ya kwonta sai dai Aba ya jaddada masa kar ya ya dawo nemansa bangarensa dan karfe tara za'a daura auren KHAUSAR


Takwas Saura HAJIA ta dawo zuwanta na uku Kennan ta masa tsaye ta ce" Wai ina direbobin gidan nan ne? Ya haka ina so in je a yi yan share share da Ni in mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login