Showing 6001 words to 9000 words out of 186303 words

Chapter 3 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18802

ba dati


Tunda ta dage labulen babarsu amaryar ta kama baki tana kare mata kallo, har ta gama ta janyo hijabinta zumbulele ta maka tana sake gaishe su da fada masu su shige ta ci gaba da aikinta har matar ta gama ta fito ta tafi gidan bikin zuciyarta fal mamaki ne ke neman kasheta


Lalle Allah ke halita, lalle ta yi mamakin wannan sankacecen sanwon dake bayan Kausar mai sunna duwawu
Ashe yarinyar nan hijabin da take sakawa abinda take boyewa a karkashin sa kennan? A kulun sai a rinha cewa KAUSAR balaluwa mai hijab, Kausar bata son kwaliya, bata son meye meye ta ki kama jiki ina zata samu mijin aure wannan zamani na yanzu da mazan suka zamto kyale kyalim shine abinda suke so, gashi Allah ya yankota mai baban jiki sai nuku nuku da hijab kamar zai makata da kasa, ashe ashe rufin asiri ne saka hijab din nan? To da ace Kausar bata lulube jikinta lalle da an ga kudan zumu a tare da ita, domin mazan fa zasu zo ne ko ana ha maza ha mata, tabas da dubu sun mayar da ita doki koda kuwa bata so, kai ita a yau sai ta ga gaskiya gwara da yarinyar ke rufewar, sai dai rufewar ba damuwa bane, damuwar KAUSAR bata damu da gyaran ba, ba wai wari take yi ko wani abin ba, ama a shekarunta bai dace ace tana fita haka ba kwata kwata, yan mashinshinan nan ko na anguwa sun gagara?
Da kyar ta kade tunanin a ranta ta shiga harkokin kaye kaye na shagalin biki


A ranar an wuni shagulgulan biki, domin anguwarsu anguwa ce ta talakawa ama fa akoy kara, dan ina ana sabga zaka ga kwansu da kwarkwatarsu an hadu ana ta murnar abin, ba wai zaka raba su da tsegumce tsegumcen anguwa ba, ama kuma hakan bai fi karfin zumuncinsu ba, dan kuwa koda irin hakan ya faru akoy Hajia datijuwa wace ta kasance mai tsawatarwa yaren matan , kuma sunna jin maganarta sosai da sosai


Kowace budurwa ta sha kwaliyarta ana shan hotuna ama KAUSAR tana fama da rabe raben abinci da sauransu, harta Ankonta bata wani saka ba tana ta kai kawo ne bata zauna ba har yama ta yi aka raka amarya gidansu dan shiryata kafin dare a yi mata rakiya


Bayan sallar magariba Mamansu ta shigo tana dan sauri ta shige ciki tana kiran sunnan Kausar


Fitowa ta yi tana amsawa hijab dinta a hannunta domin bata jima da gama sallah ba zaune dai take tana karatu


Mamansu ta miko mata jakarta ta ce" Ke ba zaki je rakiyar amaryar bane?"


KAUSAR ta girgiza kanta tana murmushi ta ce" Mama to wa zai tsare gidan? Yau auta kansa ba dama ba'a ko ganninsa yana cen wajen su Kabir"


Mamansu ta yi murmushin itama ta cenza hijab dinta ta fesa dan turare ta ce" Ai kam, to bara na je kin ga sai mun kaita dakinta, ga wayar nan ta wajen Taufik fa kar na fita na barta haka a daki duniya ta rikice ni kuwa su Aisha sun tsoratar da ni da tsadar wayar"


Wayar ta dalawa harara tana jin wani takaici nasa ya taso mata ta amsa ta kai ta ajiye dakinsu tana tsaye har mamanta ta tafi sannan ta koma ta ci gaba da karatunta hankali kwonce


Bayan sallar isha'i da kamar minti talatin da daya ta fito tana rufe gifan dan zuwa ta kamo Auta, domin ya cika dare haka a waje dan kawai ana taron nan ne da ba haka ba da tuni yana gida sallah kawai yake fita , gashi mamansa bata nan , hakama Babansa gwara ta kamo shi ya dawo gida ya ci abinci ya kwonta ko dan islamiyar safe


Dakatawa ta yi ta zubawa galeliyar motar dake parker gaban gidan kadan ido


Gane mai motar ya sakata sake bude gidan ta shige, shi kuwa daga zaunen da yake sake zubawa kofar ido ya yi a hankali ya shiga dan lumshe idannuwansa dan maganar sai ta so zame masa biyu a cikin kwonyarsa dan kuwa budurwarsa na magana ne ta wayar da ta yi kiransa da kuma tunanin me nufin komawar aminiyarsa cikin gida bayan ya tabbata ta san motar nan?




Jim kadan ta fito tana sake kulle gidan ta karaso hankali kwonce ta bude gaban motar gefen da ba kowa ta shiga ta zauna ta mika hannunta ta dan matso kofar dan a bakin hanya ne ga anguwarsa da yan acaba


......ba komai ya saka ta shiga motarsa ba sai dan ta fada masa abinda ta kulo a zuciyarta!
Tarin abinda zata juye masa ne a zuciyarta!
Kuma ta rantse sai ta fadawa Taufik duka kaf abinda ta shaka


Kasa kasa sosai Taufik dake kallon wayarsa da ta ajiye gaban motar ya ce" Zan yi kiranki *YUMNAH*"


YUMNAH dake son sannin wai yaushe zai karaso gidansu ta ce" To shikenan, ama baka fada min karfe nawa zaka karaso ba?"


Agogon ya dan kalla, sai kuma kasa kasa ya ce" Zan dai taboki"
Wannan karron bai tsaya ta bashi amsa ba ya katse kiran sannan ya juyo yana dan sake rage girman idannuwansa dan ya ga ta gyara zama ta cika fuska tamkar zata fashe ya bata hankalinsa


A takaice dai kamar yadda ta saba ne idan ta kwaso masifa sai ta zo juyewa ta rasa ta inda zata fara da kowama hakan ne yanzuma yake neman samunta


Da kyar, da kyar ta iya sake cije lebenta sannan ta saka hannunta zata bude motar ta fice


Da sauri ya ce" KAUSAR "


Dakatawa ta yi ta juyo da wani tuwon takaicin mai hadasa ciwon kai ta sake zuba masa idannuwanta tana sauraronsa


Kai ya dan sinne kasa kasa ya ce" Sorry besty "


Rai bace ta ce" Taufik, ka rike sorry dinka, nace ka rike Sorry dinka Taufik, bari ka ji in dai ni yar halak ce an haifeni a hanyar halaci ba zan kuma........................."


Idon da ya tsura mata da wani irin kallo mai kama da kashedi ya saka ta shiga wani inda inda kamar tana gaban Aba, har sai da ta tuna irin haushin da ya shaka mata sannan ta jure ta yi watsi da wani wasi wasin tunani ta ce" Ba zan kuma yi maka magana a kan harkar karatun nan naka ba, ai da ake fada min nice nale rintse ido dan tunanina na isa ko ina iya gyarawa ne? Ban san cewa nice nake lalube kai karatu ya maka rana ko kar ya yi kansa ne, sai dai na kasa gane a kan me ka zabi zama likita bayan ka san shine aiki mafi hatsari a duniya, domin da allura daya kana iya kashe bawa, na san kana da ilimi, hakan ba yana nufin kai aljani bane, likitanci ba'a cenkarsa sai dai a karanta du ilimin mutun!, Ka ki ka gane ko ka ki ka mayar da hankali zan ce? Duka wannan yanzun kam babu ruwana ka yi yadda kake so Taufik, ka ga tafiata"


Watau da ake cewa babu abinda ya fi ciwo a duniya irin ka shako fadanka ka rikoshi da hannu bibiyu irin na rashin mutuncin nan, ka zo dan ka juye shi a kan mai rabo ama ka yi ka yi a maka shiru hakane, watau a ki biye maka hakane, yau ta karra yarda da maganar


Du wannan babatun da ta yiwa Taufik, duka kaf wannan fadan da ta saukewa TAUFEEK ita TAUFEEK ya karewa kallo ya mata banza tamkar wata shashasha wace bata san ciwon kanta ba? Ita TAUFEEK ya kyale ta ringa hayaniya kamar zata ari baki? Lallema!


Da bacin rai ta maki masa marfin motar , tana juyowa ta ga Auta a tsaye yana bangalar baki shi da abokinsa har yana dage ya ce" Auntynmu, yayanmu ne a motar?"


Wani takaici ya kuleta, wai ฦดaฦดansu, to yau du wani mai kiran TAUFEEK yaya dan yana dan uwanta ta soke!, Da bacin rai ta janyo shi ta ingiza keyarshi gaba bata bashi amsa ba suka karasa kofar gidan ta saka dan makulin ta bude suka shige ko gaishe da Malan Barau bata yi ba domin ya wani kura mata ido har lekawa yake yi motar da ta fito, ta tabata yau sai an dora dandalinta a anguwar




Ajiyar zuciya ya sauke ya sake duban wayarsa dake haskawa


Bai daga ba kawai ya tayar da motar ya juya ya nufi gidansu, dan ba zai je wajen abokanan nasa ba, haka kawai yake ji idan ya je yana iya sauke fushin da ba nasu ba a kansu


Mikewa malam Barau ya yi yana lekawa kafin ua juyo yana kama haba ya gyada kai ya ce" Ikon Allah, ni ban taba gannin gida irin na bawan Allahn cen ba, ka ga fa malan Saidu sai ya je ya dawo daga kasuwa da ledoji na kayan kwalam da makulashe ya shige ciki ya sake tirke kartin yan matan cen ya ciyar ya yi barci harda minshari safiya na yi ka ganshi kalau abinsa....., To ni Allah na tuba ko daya na girke irin ya'yansa ai ba ni ba rintsa ido kalau kamar wanda bani da damuwa a duniya, ba zan taba iya rintsa idannuwana ba dan ya'ya mata ai fitina ne, ka ga du sun kamo shi a tsayi biyu jikaka biyu mudil mudil ama baya ko yar suman nan ta badi? A gaban idannuwansa a shiga a fita ana rawar nanaye wai yan mata ne? Ka ga yanzun itama wace ake cewa bakin aljani ne ya sa bata da mashinshina ta fara shiga motocin karti!"


Malan Agali ya zubo shayi ya juyo yama miko masa ya ce" Kai wani bakin aljani, malan ai wannan y'a ta Malan Saidu garke ce ciyar da ita sai makiyayi, sau nawa ana kwatanta tunkararta sai ace tsoronta ake ji?, Wannan y'a da ka gani ina fatan gannin namijin da zai dauka, kuma motar cen da kake gani inaga ta wannan elhajin ce da yake shiga gidan nasu, ni na rasa a ina suka samo shi, mutun mai kudi yana shiga gidan motar cen tasa ce ni na santa"


Na Awa ya fyace abin raken dake bakinsa ya fuskanci Barau da Agali ya ce" Ni ka ga da za'a bani y'ar nan, tsaf zan aura, Allah na tuba Malan Saiduma ya iya da mace irinta bale ni? Kai dai abu daya nake tsoro da shi da ka ganshi a nan lange lange sai masifar karfi, bana son na shiga lamrinsa ya kwasheni ya watsar a anguwa da yan jikoki da sirikai fita ta gagareni, dan tsaf tasalah zata ajiye min dandali a bayan layi ta tsigeni , ita har yanzu bata hakura da ni ba ni kuwa na gama aure da kazama, tasalah fa ko jini ta gama bata wankan kirki sai shafe wai yawan zubawa fata ruwa na raurautar da ita, ji fa masifa?......."
Hakane, wannan zamani ya zo mana da abin mamaki, maza sun dauri aniyar yiwa mata shiga hanci da kudundune harta dan tsegumin da ake kira na mata nema suke su mana fin karfi, kiri kiri yanzun idan namiji ya dara biyu basa jajen nema da turbisa sai su aro kalabi su yafa su nemi yin shige cikin shingen nazaru.....zamani kennan babu ruwanka da wani ama kana fama da tunaninsa.... Allah shi kyauta


















TAUFEEK direct gidansu ya nufa, Baban gidan fitacen dan kasuwa nagartacen mutun mai kyauta da kari, mutun mai sadaka da tausayin talakawa, wanda aka fi yiwa lakabi da *MAI KWANONI*


Kasancewar get din a bude sakamakon bakin da aka yi daga cikin gari na mahaifinsa ya sa ya bi bayan motocinsu kafin ya yi baya ya ganganra cen gefen da ake ajiye motocin gidan ya dakatar da motar a hankali ya kashe ya sake duban wayarsa da yanzunma ake kiransa kiran kuwa ya tabata idan har ya yarda ya shige bangarensa ba tare da ya daga ba yanzu zai ga wace ta isa da shi ta tardo shi ta kuma wanke shi soso da sabulu, a dole ya juya baya ya dauko ledar kilishinta da kuma embulop ta maganinta da ya siyo sannan ya rufe motar bai ko dauki wayar ta wajen KAUSAR da ta dawo masa da abinsa ba






A nutse ya nufi bangaren Matan gidan, watau matan Elhaji
๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”โคโ€๐Ÿฉนโคโ€๐Ÿฉน๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”




*DA CIWO A ZUCIYATA*




๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”โคโ€๐Ÿฉนโคโ€๐Ÿฉน๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 4๏ธโƒฃ



LITATAFAN MARUBUCIYAR


Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicรฉ
Lait de nuit
Parfums dรฉsodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waษ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuษ“i wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ










A nutse ya nufi bangaren Matan gidan, watau matan Elhaji yana sauke idannuwansa a kan kannensa uku dake zaune a baban filin kofar dakin mai dauke da farin tiles da shukokin da duka zagaye wajen sunna bitar karatun islamiya, ya tabata malaminsu bai jima fa tafia ba ya kuma basu assignment na yi


Amsa gaisuwarsu ya yi da kula, sai kuma ya dakata dan a lokacin ne kanwarsa mai sunna ISHRAT ta taso da ladabi ta ce" Yayanmu, Aba yace idan ka shigo ko wani lokaci ne ka je baya samunka a wayarka"


Jim ya sake yi a dole yana dan kallonta kamar itace ta kar zomon, dan maganar sai ta so dauke masa a harshensa domin ya so ne yace da ita Aban na nan? Sai ya ji ya kasa ciro kalmar a dole ya juya kawai ya shige tankamemen falon gidan nasu mai dauke da bangare bangare na falo uku dauke da kujeru saiti uku kala daban daban da kwaliya irin ta manyan mata masu maiko a baki




Takalminsa ya cire , sai farar safar kafarsa ya idasa shiga


Matan mahaifinsa su biyu dake zaune a falon Hajia FATAHEEYA sunna hira ya karasa da kula sosai da kuma ladabi ya gaisar da su kafin ya mike ya shiga haurawa sama bayan sun gama gaisawar dan nufa bangaren mahaifiyarsa hankali kwonce ya bacewa ganninsu




Shiru ne ya ratsa wajen nasu bayan tafiyar tasa, shirun har na dan lokaci domin kowace shirun da ta yi a cikin zuciyarta tana tunanin abinda ya tsaye mata a rai ne wanda yake damuwarta ko jin dadinta, sai dai a irin yannayin fuskarsu ba sai an tambaya ba abin tsaye masu ne ya yi , ba damar amayarwa, dan ko a tsakaninsu babu wace ta yarda da y'ar uwarta, zama ne ake yi na bugun ciki da munafurci, kowace na boye kalar wasanta ne dan sun yi wayon da ba zasu hada kai da kishiya ba, komai dadin dan miji ai ba d'ana bane...in ji Hajia NUWAIRAH


Wannan d'an daya cilo namiji ya zame masu wani baban gibi mai wuyar fasara
Shi din nan shine baban damuwar cikin kuryar zuciyarsu


Idan suka yi tsai suka duba irin girma da darajar da yake da ita aa cikin gari kadai sai su ji inama ace da wani gagarumin ciwo suke fama da wannan faduwar gaban


Irin daukakar da yake da ita a aikinsa, wanda yake matsayin baban likita aka nuna masu kuma ua dawo karatu,karatun wani munafurci? Kuma mahaifinsa ya ja maganar idan suka fitar da sirrin yaronsa daidai suke da fita a gidansa ya sake hadasa masu wutar kiyaya boyayiwa fiye da ta kishi




Juyowa Hajia NUWAIRAH ta yi bayan ta saisaita yannayin fuskarta sukai ido hudu da hajia FATAHIYA


Murmushin yake da ya fi kuka ciwo suka sakarwa junna , cike da isa irin ta isasun mata Hajia NUWAIRAH ta ce" Muna da shagali baba a gidan nan idan auren Elhaji karami ya tashi"


Da dan yanga da basarwa Hajia FATAHIYA ta dan yarfe hannu da cikinta a gaba wanda duka duka watansa biyu a jikinta ama idan tashi zata yi tana turo shi in zama haka dan abin nema ne ya samu ta ce" Ai kam, na san ranar ke uwar ango har kya yi kari da zinari dan farin ciki, Allah ya nuna mana"


Murmushin ta yi itama , ama bata bada amsar Adu'ar ba, karshema sai ta mike tana nufar sama bangarenta dan abinda ke ranta lalle lalle sai ta amayeshi zata ji dadi




Tana bude dakin nata ta ga yarinyar wajen yayanta da take riko wace tun tana karama aka bata zaune tana waya a saman kujera


Direct ta karasa inda take ta karbi wayar gana duba da wanda suke wayar, gannin sunnan kawarta ya sa ta mika mata wayar sannan ta nufi bayi tana ta dane abinda yake tukarta, dan kuwa ba kowa ne ya san me take ciki da asalin d'an mijin nata ba




Tana shiga ta rufe ta karasa ta kunna ruwa sannan ta cire dan kwalin kanta ta kama kanta da hannayenta bibiyu dake sara mata
Ta jima a haka sannan ta dago kanta idannuwanta na sake yin ja ta kalli madubin da idannuwanta da suka yi kamar sun rine na bacin rai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login