Showing 3001 words to 6000 words out of 186303 words

Chapter 2 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18804

gabatar da rayuwarta haka? Allah masani


Sunna nan zaune har yan matan suka gama cin abincin, cikin gagawa ta shirya ta daura alwallah ta dauki salaya ta saka a jakarta ta kuma daukan hanya domin safe da yama ne jarabawar kwana uku


Ta yamar ma bai zo ba haka ta sake shako wani takaicin harda yiwa kanta fadan in sha Allah ba ita babu shi, tunda a zamantakewarsu ba zata iya fada masa magana ya dauka ba, tunda bata isa ta nuna masa mahinmancin karatunsa ya gane me take nufi ba, ita har yanzu ta kasa gane ina ya dosa , in karatun ne baya so ai ba dole ya yi zamansa mana a gidansu? Ama sai ya wani dauko kafa ya zo makaranta ya koma har gashi yanzu ana cikin lokaci mai mahimmanci wanda idan baka samu abin kirki ba to fa ka san me ka shekare kana yi shi bama zai zauna ya yi ba? Tana matukar jin takaicin rashin maida hankalinsa a kan karatu kamar yadda zata iya ji a kan yan kannenta A'isha da Rukaya, bale dai shi da yake biyan makarantar nan mai masifar tsada, ita kanta da ta samu shiga saboda kyan sakamakon jarabawar shigar da takardunta suka yi bata wasa sai shine zai yi wasa?
Haka ta yi karatunta bayan sun ci abinci ta shige da wuri ta yi sallah ta yi kwonciyarta domin yau ko abanta ba zai sameta ido biyu ba, haka take idan ana jarabawa bata da lokacin kowa sai an gama


Bayan an yi sallar asubahi mamansu na zaune tana jan carbi abansu ya dawo daga masalaci
Datijo mai mutunci da daraja, mutun mai karamin hali ama mai wadatar zuci, mutun mai daraja iyali da iyawa talaucinsa a kan muradin iyalinsa na yau da kulun, Abansu mutun ne mai zuciyar nema , yana siyar da turare ne kama daga na feshe har zuwa na haki, yana hi kasuwanni da ma'aikatu da kayan tallarsa ya rabawa masu siya kama daga masu daukan bashi masu biya har zuwa zuwa masu dauka na bakin hanya ciniki yanzu biya yanzu
Ya kasance mai saka riba kadan ya saka albarka shi yasa rana ba zata fito dare ya yi bai samu abinda iyalinsa suka ci suka yi yan bukatun yau da gobe na rayuwa,
Tukunya dai ukun nan ana dorata a gidansa kofa kuwa ruwan koko za'a dora a yi kari sai an yi shi , basu da mandar abinci bale na ruwa ko na sabulun wanke dati......, Sai kuma Allah ya taimakeshi matarsa macece da ta iyawa talaucinsu
Bata da kwatamniyar fade faden abubuwan da suka fi karfinsu bale har ya dawo neme nemen abinda ya fi karfinsa, ta kasance mai talafa masa ce da dukkan hanyar da Allah ya bata dan su ji saukin rayuwa, domin tun daga kan awon masara, hatsi, ko yar shinkafa zuwa sabulun wanka, omo , clean da dai sauransu idan ya kawo ya ajiye har sai ya karro wani da tunanin na gidan ya kai karewa sai ya ga da saura....., Bai taba zuwa gidansa ya tarar da tari tarin abinci banzace a yashe kamar ba nema ake yi ba, bai taba gannin guntatakin sabulai na yawo a cikin gidansa a zubde ba, komai a kilace komai a adane daidai karfinsa, hakan ya sa tafiyarsu cikin rufin asiri da taimakon junna ne, zamansu kuwa bayan Adu'ar gamawa da duniya lafiya sai fatan a je a samu baban rabo gobe kiyama.......
Shi dai Abansu bashi da kiba ko kadan, domin lange lange yake kamar zai rabe biyu, mamansu ce mai jiki sosai, dan ifan har jerawa zasu yi ba zaka taba hango abansu ba in ta yi tsaye......a haka tafiyarsu take tafe cikin aminci da tsarin addinin islama, inda Allah ya azurtasu da ya'ya hudu , mata uku dai auta namiji




Da salama ya shige dakin ya karasa ya shiga fitar da kwalayan turarukansa yana ajiyewa gefe , ga dakin Mamansu ta kunna dan turaran haki ya gama dakin da kanshi masha Allah


Shafa fatihar ta yi sannan ta ciciba ta mike ta karasa wajen kayan da ya zo da su jiya ta dauko ledar da bai mata bayaninta ba ta kawo ta ajiye sannan ta duka tana gaishe shi kamar yadda al'adun malan bahaushe mai nagarta yake


Da kula yake amsata da yi mata yan tambayoyin gidan da yaren, itama ta amsa shi sannan ta ce" Aban KAUSAR ledar nan baka min bayani a kanta ba"


Ledar ya dan ƙalla yana cirewa yaren turarukan daidaya masu kyau da tsada ya ce" Au na manta, na KAUSAR ne"


Dan murmushi ta yi tana kuncewa ta ce" Bara mu ga me yar gatan Abanta ta samu ne?"


Shima murmushin ya yi ya dan dakata da aikin da yake yi yana kallonta yana kuma jiyo kiciyar ya'yan nasa a tsakar gida ya san abin kari suke shiryawa da kuma shirin school ya ce" Kayan kwaliya ne jiya a shagin elhaji na ga wata mata na siyawa y'arta, y'ar yadda kika ga Kausar dina ana ta siya mata su nima nace a bani abinda aka basu kin ga takalmin nan mai dan tsayi kuwa? Zai yiwa KAUSAR kyau , harda wata shada nacewa Elhaji a yanka min yafi goma sha takwas karshen wata zan kai kufin mu ci sallah da ita in sha Allah"


Mama fuskarta bata gushe da murmurshi kawace a kai ba tana ta dagawa duda abinda take sakawa daban a zuciyarta shine addu'a da fatan gannin wata rana KHAUSARma ta fara gabatar da rayuwa irin ta yan mata, irin yadda mahaifinta ke kokarin nan yana son lalle lalle shima babar yarsa sai ta zamo kamar yan uwantan nan ta san burinsa daya ne Allah ya nuna masa ta samu miji ya aurar da ita ko ya fuskanci kannenta da suke da manema tuntuntuni...., A yanzu dai a kasar hausa shekara ashirin da hudu zuwa da shida ai an kai a shiga dakin miji, sai dai halin rayuwa da kadarar bawa idan har Allah ya yi mijin bai samu ba dole a yi hakuri a yi ta addu'a


Tana murmushin ta ce" Allah ya karra budi, ya karra rufa asiri, to ina na yan matana kayan kwaliyar ?"


Murmushin ya yi shima ya ce" yan matanki rasawa suke, inace ba'afi sati biyu da suka ce hodarsu ta kare ba har nace da Aisha ni indo hodar nan ko barci za'a shiga fai badata ake yi kau?"


Mama na daria ta ce" Kai, ai ƴaƴan nan sunna son kwaliya nu har mamakinsu nake yi, koda yake kwaliyar ai da ranarta gashi du sun samu manema , ama ita hajiar ba ga kwaliyar ba , ba ga dandasa gayun ba, ita dai barta da takarda da byro abinta"


Murmushi kawai ya yi , hakan ya sa ta sake tausasar da muryarta, domin abinda ta kwana da shi har ya saka ta kwana tana juyi kennan, maganar ya'yan nasu


A tausashe sosai ta ce" Abansu ina so mu tatauna wata magana ni kam"


Ajiyewa ya yi ya fuskanceta ya ce" Ai tunda na ga an ki fita a kamawa yayana aiki an bar min yan muleka da shara da wanke wanken asubahi na san da magana, yi bayaninki kai tsaye mamansu"


Murmushi ta yi , harshenta na yi mata nauyi kan maganar, a sanyaye ainun ta ce" Baban Muhamadu, kan maganar ya'yan nan ne yan mata...., Abansu dan Allah ina so ka dan duba lamarin nan mu samu mafita, ka ga Aisha da Rukaya sunna da masu so dan manemin auren Aisha yace idanma da hali yana so bayan babar sallah a yi bikinsu dan ya gama ginninsa...., Haka Rukaya a yadfa KAUSAR ta dabar min itama manemin aurenta ya shirya dama yake jira....."


Ta dan tsagaita tana sake sada kanta ta ce" Abansu na san menene damuwarka, ama idan har haka Allah ya yi gwara mu fuskanci lamarin a aurar da Wa'inda suka samu malamuncin nasu, kar a tsaya jiran har sai KAUSAR ta samu miji a hade aje Allah ya kiyaye suma su zo ana kame kame...., Ka fa san menene rayuwar y'a mace, gashi KAUSAR bata yin wani kokarin da zai nuna tana son ta samu itama mijin nan ta je ta kilace kanta, yanzu dogon karatun nan na likita dai bana an ga karshensa in sha Allah koda sakamako bai yi kyau ba ba za'a kuma zaman bence ba sai dai a yi jiran wata jarabawar....., Ka ga sai ta zo mu girka sana'a ginaniya mu yi dan karra talafa maka a cikin gidan"


Da kyar ta iya kai karshen zancen, domin ta sani ne abinda ke daga masa hankali Kennan a rayuwa irin maganar nan


Ya jima yana kallonta , shiru yana tunani


Cen ya iya budar bakinsa ya ce" In sha Allah, itama zata samu malamuncinta....., Lamarin rayuwa kowa da irin tsarin da Allah ya yiwa rayuwarsa......, Maganar ta kama sana'a aa ban lamunta ba, tunda dai da sauran karfina kuma ina yin daidai gwargwado bi izinillah zan ci gaba , ba zaku ringa fita sana'a ba, ta cikin gidanama da kike yi dan kar na hanna a ga na so kaina da yawa ne Mamansu, maganar shekarunta kuwa ni baya gabana , ko dan ni na haifa? Lalle yana damuna ama ba shi yake nufin yana gabana ba, abinda yake gabana bara ki ji , dama jira nake yi ta gama, in sha Allah dukkan hanyar da zata dan daidaita rayuwarta zan sake nema na rike, zan kaita a dan kokoya mata dan gyara irin na yan mata, ni bana yiwa y'ata kwadayin auren wane sai dan mutunci ko wanene komai tsufansa, kar ki manta a lokacin da na ganki bakida ko digon kwali a idannuwanki, ina yiwa y'ata fatan miji na gari baki dayansu, dan Allah mamansu ki daina yin magana da sarewa a ciki kin ji? Na san abu ne mai matukar hanna zuciya sukuni, ama idan har ke kika fara haka zaki yi gagawar cin mini kin ji?......, Yaran nan kuwa zan duba maganar auren Allah ya doramu a kan hanya madaidaiciya"


Ajiyar zuciya ta sauke tana amsawa da amen sannan ta ciciba ta tashi dan ya ci gana da aikinsa haka kuma yannayinsa baya mata dadi dan walwalar tasa ta ragu, ama ba zata saka damuwar haka a ranta ba, fatanta ya gane ya kuma rike wannan dama, dan idan har suka rayu da jiran babar yarsu in Allah bai yi zata samu da wurin ba sai a zauna a tauye kowa da kowa?, Su Aisha kansu yanzun sun fara gandamewa ai




Da wannan ya'yan du suka shirya, ita zata fara fita bayan ta gaisar da Abanta tana ta doka murmushin tambayoyin da yake yi mata tana bashi amsa sannan ya salameta yau har dari uku ya wanka mata hakan ya sa ta fito kanta a sama kamar sarauniya ta zo ta duka ta yiwa Mamanta salama sannan ta mikowa Maman nata watsetsiyar wayar TAUFEEK wace ta saka su Aisha zaro ido sunna kallon wayar domin su sun san cewa ba karamar waya bace, ita dai ce da ba komai ya dameta ba ba wani sannin kudin wayar ta yi bama bale har ta ji tsoron rikewa ta ce" Mama wannan wayar adanawa TAUFEEK ita kar aje ta fashe ina hadeta da kaya a jakar nan"


Maman nata ta amsa tana kallonta ta ce" KAUSAR me yasa kika amshi wayarsa har ki je ki yar bakya tsoro? Da gani wayar nan ba karama bace ba fa?"


Aisha da ta rafka tagumi ta ce" Mama, wayar nan ai sai ta sayi aunty Kausar tsaf harma a nemi kari, Aunty Kausar da wayar nan kika kwana a gidan nan a san tana nan a shigo a yi kidmashin dinmu?"


Rukaya ta yi dariya tana dungure kan Aisha ta ce" Ke haba dai wayar zata wani sayi mutun, ama fa Mama wayar nan ba karamin kudi ne da ita ba gaskiya, koda yake su a gidansu yar autarsuma mai shekara goma sha uku iphone ce a hannunta ranar da muka je din nan amsar books din aunty kamar na kifa kallonsu kawai nake yi, Mamansu wata yar gayu da ita bakinta turanci ya amshe hausar"


KAUSAR ta girgiza kai ta ce" Ku dai kula sani, Mama wayar yau kwananta biyu a wajena, ba kin ga irin fadan da na masa da wayar Aba kan karatu ba? To Mama za'a shiga aji na amshe wayar dan karma ya zauna yana dane dane, har an shiga aji kawai ya tashi ya tafi har yau dai da ban ganshi ba, gatanan wayar a hannunki idan ya ga dama ya zo ya amsa, ni ba ni ba shi ko a hanya ya ganni ba zan nuna na sanshi ba, tunda haka ya zabarwa kansa sai ya yi"


Ta gama fada da takaici ta mike ta tafi tana fadin ta tafi


Aisha a a sake tafa hannu tana rakata da ido kafin ta dawo dubanta kan mamansu ta ce" Iko sai Allah, ni wani lokacin sai su rikitani da tunani, wani lokacin kuma sai kawai in ga kawancen ne kawai, ama yanzun kamar wata budurwarsa????"


Rukaya ta ja numfashi ta ce" Ke da ke kadai ce sai a maki maganin haka, ama kuma idan har kika yi duba da yannayin abin nan bayan zumuncin babu komai, aunty fa babu wannan maganar tsakaninta da shi, shima haka, inaga fa shekara hudu ce kawai ya batama, kuma bayan wannan yarinyar da zai aura fa in fada maki komai a hannun Aunty yake, kawai haɗuwar jinni ce mai wuyar fasara, ni abinda ke bani dariya da Aunty idan suka yi fadansu ta ringa rantse rantsen ba ita ba shi, ita dole sai ta sa ya mayar da hankali kan karatun da ya je ko bai je ba takardunsa tuni a hannunsa, kuma ya yi ko bai yi ba sunnansa mai kudi, ama haka ta yi ta fushi shima ya biye mata"


Mamansu dai da ta kai wayar ta boye dan ita tsoroma wayar ke bata ta dawo tana fadin" kai maza ku tashi ku yi da jiki ku kama hanyar makaranta ba sai kun yi lati ba ku ce sai an baku na sahu!"


💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔




*DA CIWO A ZUCIYATA*




💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 3️⃣



LITATAFAN MARUBUCIYAR


Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃




Haka suka mike kowace ta shirya suka fice makaranta, Aisha na ajin karshe a secondary domin ita akoy wasa da karatu, Rukaya kuwa tana karantar malamar makaranta




Kwonci tashi har suka gama jarabawa kwana bakwai cif suka shiga hutun sati daya , hakan ya sa hankalinta ta tarkato shi ta mayar hanyar islamiya sai yan shige da fice kasuwa lokaci zuwa lokaci na shorye shiryen auren y'ar makociyarsu da kusan komai ke hannun mahaifiyarsu domin akoy zumunci sosai sannan sun sani ne Mama akoy amana, in dai ka sakata a lamarinka da izinin Allah ba zaka ga ha'inci ba, ƴaƴanta yan mata suka zamto kawayen amarya , ama KAUSAR bata wani yawan shigewa cikinsu, domin haka kawai take jin kanta ba yadda take so a cikinsu ba, hankalinta baya taba kwonciya waje daya idan tana cikinsu, sai ta ga duniyarsu ba daya bane, hangensu ba daya ba, kai komaima sai ta ga ba daya bane da ita da su, hala suma irin lokaci zuwa lokaci da zaka ga sun hade da itan basu da wata sakewar a zo a gani, idanma tana wajen du wani abu na yan mata basa sakata, dan tun daga yannayin jikinta har kafarta bai nuna tana da muradin hakan ba, sai ana gobe daurin auren nema ta yi kunshi a gida, shima Mama ce ta kunsa mata kunshi na hausa hannayenta da kaffaguwanta ta kwana da shi, ya zamto tunda ta tashi sallar asubah ta wanke ta daura alwallah ta shige dakinsu, yau ita daya ne domin kannenta sunna gidan su amaryar cen suka kwana , hakan ya sa da jiki tana gama sallar ta saka doguwar riga kawai ta saka hula ta fito ta shiga aiki ka'in da na'in dan tsaftace gidan domin nan amaryar zata wuni da kawayenta


Tana tsakiya da wanke balbalin gidan suka yi salama suka shigo da amaryar da babarsu yayar mahaifinta sai kannenta aka rako amaryar, hakan ya sa ta dakata tana gaishe su da murmushi shinfide a saman fuskarta ta masu jagora har dakinsu inda ta shinfida katifar mamansu ta shinfida zannin gado sabo mai kyau dakin sai kanshin turaren haki yake haka kuma kasan an shinfida tabarma biyu an malale ko'ina, tsaftsaf dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login