Showing 21001 words to 24000 words out of 186303 words

Chapter 8 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18798

suka tsinke mata a lokacin da Aba cike da wani yannayi na son ta daga wayar ya ce" KAUSAR ba kiranki ake yi ba?"


Kai ta girgiza da sauri tana share hawayen dake sake zubo mata murya a kurya ta ce" Ba kira bane Aba"


Aba ya kafeta da duba kadan yana fadin" Aa, kamarya ba kira bane, daga mana wannan na uku ne fa, kukan meyema kike ni ba an kusa shan ruwan ba? Ko yau juwar da karfi ne?"


Kai ta sake gyadawa , ta dauki wayar ta mike da kyar ta shige ciki ta je cen bayan katifar Mama ta duka ta labe sosai murya a shake ta amsa wayar tana cicijewa da son sannin wani bakon munafurci ne wai wannan kiran nata ba lokaci?


Murmushi Mujaheed ya yi , da yannayinsa na sanyi sosai ya ce" Wai kina jin kishirwar nan ta yau kuwa Kausar?"


KAUSAR sai ta so ta ce da shi Ina ruwanka da kishirwata? Ni fa bana son neman fitina ban iya fada ba gaskiya, sai dai jin yana dan murmushi ya sake cewa" To ko dai aikin mamana kike ne na dameki?" Ya sakata jin ba zata iya fada masa hakan ba, hasalima sanyin da muryarsa ke yi in zai mata magana na damunta lokuta da dama, sai ta ji kamar ta dauke shi ta goya ta bashi hakuri kar ya yi kuka, kamar wani maraya gaba da baya, koda yake Mujaheed ai bashi da alamun karfima bawan Allah, jiki ne da shi sosai kuma bashi da tsayi, ga yannayi irin na yayan madara dai tare da shi dan ko a shagonsu a zaune yake abinsa yana yan ciye ciyensa yana kai karshen yayan banki, watau shi ke amsa ya ja gaban table ya zuba ya dadana abin irge ya watsa , su kuwa yaran shago na zubawa a leda da kuma kaima mutun waje, sai dai ba zata yi karya ba a dan tsanin zuwa da dawowa sun kula shegen kyauta ne da shi sosai, bayan ribarsu ta atampa da ake ware masu a shagon du wanda ya je siya wace aka basu damar dorawa, sai kuma ya karra masu da na adaidaita sahu du idan sun je , ita tana kyautata zatonma Aisha ko Rukaya yake so, ai kuwa zata fada masa gaskiya ya yi hakuri an masu miji dan har an zauna da manema aurensu an basu su har an saka lokacin biki da babar sallah ne in sha Allah


Dan gyaran murya ta yi ta ce" Ina yini Elhaji?"


Murmushi ya sake yi ya ce" Lafiya Hajia , yaya gajiya?"


Yanzun kam bata amsa ba sai dan uhum kawai da ta ce tana dan murja yan yatsunta, haka kuma wayar na dan tsut tsut tsut alamun wani kiran na shigo mata ne


A hankali ta ce" Dama , dama babu mai son atampa fa"


Dan tsai ya yi ya ce " Wace atampa fa HAJIA?"


KAUSAR ta yatsine gaban goshinta ta ce" Na zata dan ka ji ko na tara kudaden masu son atampa ne?"


Har ga Allah abin sai ya bashi dariya, ama sai ya ki nuna mata dan kar ta ji ba dadi, a sanyayensa shima ya ce" Aa, ba wannan bane, dama ji na yi ina matukar son jin muryarki da kuma jin ko kina lafiya? Bale yau kin ga ana rana sosai ga zafi ina jin kishirwa sai na damu da son jin kar aje kema haka kike ji?"


KAUSAR ta yi tsuru tsuru, wannan wani irin bakon balagagen tashin hankali ne? Tana zaman zamanta yace wani dan ya ji ko tana lafiya ne? To ita ina hadinta ina shi dan Allah? Mema ta masa da zafi?


Da sauri ta samu kanta da kashe wayar tana ta zazaro ido cike da tsoro da fargaba, sai kuma ta ji alamun motsi hakan ya sa ta juyo da sauri


Ido hudu suka yi da A'isha, wace tun shigowarta take tsaye tana kallonta da sauraronta


Cikin dabara Aisha ta wayance ta ce" Aunty, baki ji kiran sallah bane? Aba yace ace maki an sha ruwa"


Sai a lokacin kunnayenta suka ringa jiyo mata alamun dake nuni da an sha ruwa


Jiki ba karfi ta mike ta fito ta samu waje ta rakube ta dauki kayan shan ruwanta ta shiga sha tana sauke ajiyar zuciya, baki daya ahalinta sai suka yi tamkar basu ga komai ba suka ci gaba da shan ruwansu suka tayar da sallar magariba


Da dare bayan an dawo daga masalaci yau yan matan kaf dinsu sunna daki, tunda yayarsu ta shige ta labe suka tatara abincinsu suka bita, hakan ya sa Abansu dan damuwa yana tambayar wai ina suke ne?


Murmushi kawai Mamansu ta yi tana sada kanta, domin har ga Allah ita din da kanta sai ta ji tana iya jin kunyar maganar nan da Abansu, KAUSAR fa itace yarsu ta fari, sai ta ji tana iya jin nauyin maganar sosai da sosai


Daria Aba ya yi, har cikin zuciyarsa wani farin cikin na sake ratsa shi, a hankali ya daga hannayensa ya ce " Allah kai ke badawa, kai ke hannawa, ko waye yake son shiga rayuwar y'ata idan da alkhairi ya zo ya ubangijina ka tabatar mana, in ba alkhairi ya zo ba ka rabata da shi cikin aminci, domin irin wahalar zaman da ta sha ina fata idan ta shiga gidan aure ta yi zama na farin ciki"


Mama ta amsa da amen a hankali, a zuciyarta kuwa tana tunanin lalle lalle sai ta bada gudunmuwarta itama a matsayinta na uwa, domin ฦดaฦดanta ita ta haifa babu wace bata san halinta ba, a cikinsu tsaf zata iya zana halayar kowace, ta sani ne bakon lamari ne wannan din a duniyar yarinyarta, idan aka yi wasa tana iya kabe shi ta kore dan tana tsoro, a dole za'a jata a jiki cikin dabara a ringa kwatanta mata har ta gane ta kuma dauka da hannayenta bibiyu ta rike, dole za'a tayata idan ya so in har abin ya tabata gaba sai ta kwaci kanta, sam sam KAUSAR bata da wayon iya zancema bale wai har a kai ga fahimtar junna ita da namiji, zata iya cewa maza biyun nan kwarara sunne suke da mu'amala ta fahimta a tsakaninsu da halayan KAUSAR, daga Abanta sai amininta


Da wannan farin cikin suka yi zama a ranar


Yan matan kuwa a ciki kowace dariya ke neman halakata
Kiri kiri auntynsu ta kashe waya ta nemi mutsukets tana ta hada rai, ta ki kowama ya kawo mata wata maganar ta raini ta hade ta tsare tana ta basarwa, abincin kansa yau ba damka ta sako da sako akai masa ba, sai da aka raba shi biyu sannan aka samu ya shiga a hankali, daga karshema ta yi kwonciyarta da wuri wuri bayan ta kawo dalilinta na kwonciyar da wuri cewa tana so idan Alllah ya wayi gari lafiya su fita da wuri dan kaiwa mace daya da ta rage, tana kuma yarda da maganar Rukaya da tace da ita ya dace su malaki wayar android koda daya tak ce, domin da da ita da ta wayar zasu raba ankon ba tare da sun sha wannan uban yawon ba, abinda ya fi bata takaici da shi kiri kiri ya ki ya rabawa abokanansa maza, sai da ta ga ba fa zai yi ba ta kaiwa amininsa daya da suke jin maganar junna ta bashi ta yi tafiyarta, ta tabata shi kam ya raraba, TAUFEEK kuwa dole ya shafa mata lafiya domin biki sai ta warwasa yadda ake yi a ko'ina ehe!










Tsakanin wannan lokacin zuwa karshen wata mai albarka, watau watan azumi a hankali shakuwarsu ta fito fili har ya zamto babu wanda bai san cewa Kausar itama ta samu masoyi ba, ciki kuwa Harda TAUFEEK


A hankali yan uwanta suka fi karfinta suka saka mata ra'ayin amsa kiran da kuma ra'ayin kulashi har ya zamto ita da kanta tana jin dadin hakan har ta iya rike lokutan da yakan kirayeta su zanta, sannan ta sanar masa ya yi hakuri nacin yana son zuwa gidansu ya bari a salace baki ya bude sai ta sanar a gida , a lokacin kuwa tuni Mamansu ta sani itacema ta ce sai baki ya bude dan a yanzu cikin ibada ake ba ji ba gani du wani mai neman duniya da kiyama zai maida hankali in dai yana da hankali kuma yana da rabo


๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”โคโ€๐Ÿฉนโคโ€๐Ÿฉน๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”




*DA CIWO A ZUCIYATA*




๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”โคโ€๐Ÿฉนโคโ€๐Ÿฉน๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 9๏ธโƒฃ



LITATAFAN MARUBUCIYAR


Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicรฉ
Lait de nuit
Parfums dรฉsodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waษ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuษ“i wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ






Sanu sanu azumi ya zo karshe, aka wayi garin sallah, sallar musulmai, baki daya musulmai kwonsu da kwarkwatarsu a wannan rana sunna cikin yannayi na farin cikin gannin sun samu gabatar da ibadarsu har Allah ya nuna masu ranar sallah


Hakan ya sa a ranar da yawa sunna gida wasu kuwa sun fita ziyara...., Ranaku a kalla sun kai biyar da ake gabatar da bikin sallah kennan a kasarmu ta hausawa, ziyara ne gidajen yan uwa da aminan arziki, zuwa wajen wasan sallah ne da sauransu har kwanakin kaiwa samari kwarya kwaryar sallah ta zo, ya kama daidai da ranar da KAUSAR zata amshi nata bakon, watau goma ga watan sallah


Ita dai du gannin abun take yi wani iri, bama da ta ga mahaifinta ya shigo da kankana da yan kayan hadin da ya saka Mama ta zana masa ya ba su Aisha kan su yiwa bakon ruwan tarba wanda hakan ya matukar sakata sake jin kunya da nauyin mahaifanta harma ta kashe wayar ta boye a daki ta wuni cikin tunanin ta inama zata fara ? Yaya zata dubi abin? Ta ina zata bi da abin? Haka dai ta har magariba ta kawo kai Mama ta shigo ta tasheta tana fadan me take haka bata kimtsa ba bayan ta san tanada bako?


Aisha ce ke dan murmushi tana kallonsu Maman na tsaye kofar bayi tana fadin maza ta yi wankan nan da kyau ta fito Rukaya kuwa ta idasa kimtsa kayan tarbar bakon ta saka a dakin Mama ta kilace bayan sun fitar da na gidan


Shirin ya zo mata wani iri, riga da sket dinta sai hijab wanda da kadan ya zarce gwuiwarta aka bata kan su zata saka domin tarban bakon


Ta saka sket da rigar ama ta kasa saka hijab din har Rukaya ta sanar da ita cewa bakonta fa na waje kusan minti ashirin kennan


Jiki ba karfi ta mike ta dauko wani hijab din sabo wanda suka saka ranar sallah ta zumbula abinta sannan ta dauki carbi kamar wace zata he bayar ta wa'azi ta fito tana rakubewa wayarta a kunnenta tana amsa kiran TAUFEEK dake sanar mata zai biyo ya bata katinta da zata bayar dan ta nace sai da ta buga mata kati na gayata ta samu ta wuce a gidan da kyar tana sauke ajiyar zuciya


Motar ta kurawa ido bayan ta ja ta tsaya a kofar gida, ance ta je ta shigo da shi ne, sai dai bata tunanin in har zata iya karasawa wajen motar cen dake tsaye ko ba zata iya karasawa ba, uwa uba yau anguwar dinke take tak da jama'a yan matan ne da samarinsu, tsofafin ne ana firar dare dai haka, kuma a hasken farin watan da ya haske anguwar tarin bolar dake zube ko'ina ta hasku tarrr haka itama ta hasku cikin farin hijabinta harma aka fara dan tsunguri tsoman ana raraba maganar cewa ta yiwu wanda ya saba zuwa ne ko kuwa menene wannan? Ciki harda yan matan da suka sha kwaliya suke kannan bayanta sosai sunna zaune a nasu gefen sun zubo ido sunna son gannin ya fito ya shiga cikin shigarsa ta kamala da tarin kwarjininsa kamar yadda ya saba, sai dai yau har yanzu babu fito daga motar ba


Tana kokarin neman layinsa ta ga ya bude motar ya fito, hakan ya sa ta dan sake matsawa kadan jikin garun ta sada kanta


"Barka da warhaka Hajia Kausar" ya fada da muryarsa mai sanyi kamar yadda ya saba yi mata magana


Cike da kunya ta dan dube shi, sai ta ji inama zata iya rage tsayinta koda basu zo daya ba ta dan gota shi kadan? Sai dai har ga Allah bashida tsayi ko kadan Mujaheed, dan dai yanada dan fadinsa ga tumbinsa kuwa a cikin manyan dinkinma ana gannin yadda ya yi gefe abinsa


Dan rage tsayi ta yi ta gaishe shi sannan ta sanar masa ance ya shiga ciki


Kwarai ya ji dadin haka, dan hakan ya nuna masa yana iya samun karbuwa wajen iyayenta, domin in har aka baka dama ka shiga cikin gida to fa ana da niyar dubanka ne


Har kasa ya duka ya gaisar da Mama dake labe daga daki sannan ya zauna saman tabarmar da aka shinfida masa, ita kuma ta labe daga fan lungun dakin su Mama tana ta aukin murza hannayenta


Su aisha sun gaishe shi sun kuma kawo masa ruwa sannan suka basu waje


Shiru wajen ya dauka, tamkar bata taba magana da shi a waya ba, kanta a kasa sai zufa take yi, haka yannayin da take ta motsa jikinta na alamun rashin sabo da zama irin haka da namiji ya bashi mamaki


Murmushi ya yi ya ce" KAUSAR, alhamdulilah, na godewa Allah da ya nuna min wannan rana, ina ta fata na ganta da raina da lafiyata, sai gashi na ganta, KAUSAR ni di ba yaro bane, inada mata biyu da Y'ayana bakwai, kamar yadda kika ganni a shagon gidanmu shagon mahaifina wannan itace sana'ata, watau ni dan kasuwa ne, a gaskiya ban cika jan neman aure ba dan in har na nuna ina so din nakan fito a mutun a bani na kilace, ni dai na ga kin min kuma ina sonki da aure, dan haka me kika ce ne ke KAUSAR?"




Magangannunsa ba da tashin hankali yake fadarsu ba, hasalima a sanyaye harufansa suka fi fita sunna shiga cikin kunnayenta, sai dai mamaki mai karfin gaske da ya kamata shine dama yanada iyali? Fuskarsa kamar bata nuna ya kwana biyu ba, bama wannan ba irin lokutan da ya ware yake kiranta bata taba sannin cewa shi din mai iyali bane da bata ringa amsawa a lokuta irin wadannan ba, domin yana kiranta kafin a yi sahur fa, haka kuma bayan an fito daga sallar asham yana kiranta su dauki lokaci mai tsayi sunna magana, magidanci? A irin wannan lokacin ai ko yayane yana tare da iyalinsa, in ta yi duba da lokutan da Abanta yake gida kennan, sunna tare baki dayansu a gida fa? Ina laifin ya ware lokacin da yake kasuwa ? Sai ta ji wani iri, ama kuma maganar wai ko dan yanada iyali zata iya kasa amsa masa ko daya, to mem ake tunani ne? Ita dama abinda take tunani kennan da rayuwarta cewa lalle ba zata taba aurwn saurayi ba, to ita a haka din nan ta auri saurayi ta ce me ta yi kennan? Tap ai da kunyama wani abin , ita aurensa da ya'yansa saima tace adu'arta ALLAH ya amsa sai ta je su yi zamansu


MUJAHEED ya dan sake muzgutawa ya ce" Hajia KAUSAR kar dai a saka na sare an min shiru?"


KAUSAR ta sake sinne kanta ta boye fuskarta cike da nauyi da jin kunya ta ce" In sha Allah zan sanarwa su Mama, abinda suka yanke sai na sanar maka"


Murmushi ya yi yana gyada kansa ya ce" Masha Allah, haka ake so, ya zamto ana tambayar amanar iyaye , to ama ke yaya kika ganni na maki ko?"


Ta kofar hijab din take dan kallon nasa, yadda ya wani kanne ido sai ta ji kamar ta kwala kiran Mama dan ta zo ta tayata gannin wani makararan rashin da'a, ama kuma sai ta kwabi kanta ta sake sade kai har dai ya gaji da surutunsa shi kadai ya gaza samun yadda yake so ya hakura ya mike cike da mamakinta, kwarai ya yi mamakinta, domin halayarta sai suka so bambanta da wasu yanmatan da yake kulawa , yan matan da kamar jira suke a taya su? In ka je inda suke kuwa sai in Allah ne ya tsare maka amaninka, in ba haka ba tsaf za'a iya lalata da y'a a gidan iyayenta, ama ita tabarmar da ya zaunama bata hau ba kuma kanta da ta sada har ya mike ya ajiye alherin da ya ajiye wanda sam bata kula ba bata dago ba sai da ta ji yana yiwa su Mama salama ne sannan ta dan ciciba ta mike murya a fan sanyaye ta ce" A gaida gida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login