Showing 9001 words to 12000 words out of 186303 words
sannan ta girgiza kanta tana sakin murmushi mai ciwo ta ce" Na tsaneka kamar yadda na tsani mutuwata!, Lalle zan rayu da burin gannin bayanka! Ba mutuwarka nake so ba, ka tagayara ka zamo dan daudu, ka zamo wanda ana takamar kaine namiji daya jal da aka haifa ama kuma ba anfani, yadfa uwarka ke rayuwa da farin cikin kai daya jal ta malaka tana ji tana gani zaka salwanta ka daura zani elhaji ya tsine maka ya kore ka! Yadda ubanka ya sakar maka ragamar dukiyarsa na rantse da wanda raina ke hannunsa sai ya kuleka saboda dukiya domin sai na yi sanadiyar da zaka zamo tamkar kare a bin mata, mai kuma shaye shaye dan kuwa du wanda ya auri bin mace ba zai taba ajiye dukiya mai albarka ba komai kudinsa, a haka zaka karar da dukiyar ta yadda sai ya yi shara'a da kai sannan ya tsine maka ya koreka!, Wannan alkawarina ne!".............
Da kyar ta iya saisaita kanta sannan ta fito muryarta bata fita da kyau ta ce" Ke Hamdiya Ajiye wayar nan maza ki sauka ki ce da auntynku na shiga nafila ba zan sauko ba dan kar ta ga shiru"
Ajiye wayar Hamdiya ta yi ta dauki hijab dinta ta saka sannan ta fice, dan kuwa dokar gidan ce, ko mace dokar yayansu ne ya masu hani yawo ba hijab ko shigar da zata rufe suturarsu sosai koda a falo ne, idan dai so kake yi ka yi yawonka tsirara ko da shiga ta rashin da'a cen ka kule dakinka ka yi, in kuwa ka yarda ka fito da shigar da ba ita ba aka yi rashin dace ka hade da shi a ranar tsag zai darwaye maka fata kuma babu abinda za'a yi
Da takaici ta kule ganninta a kan Hamdiya ta karasa saman kujerar cikin dakinta na farko ta zauna tana kada kafa........., Watau du iskancin FATAHIYA baya gabanta, wani jiji da kai a kan ciki ko? Ba shine a gabanta ba, abinda yake gabanta wannan ne, ta tabata ko yan biyar maza Fatahiya zata haifa ta riga ta makaro tunda kafin su zama abin alfahari ta gama jigatuwa, ama wannan basamuden mai balagagiyar iskanci da tsiron rashin kunya ko? Ya gama yi mata kaka gida da ya'yan gidan baki daya, ita saima ISHRAT ta shigo ta ci ubanta yau, yarinya sai kunnen kashi, irin yadda take yiwa ฦดaฦดansu biyaya na ci mata tuwo a kwarya, zata daidaitata ne , dan ba zai tana yiwuwa ta zama aminiya a wajen makiyinta ba!
Murmurshi ne kwonce a saman fuskarta tunda ta buda ledar kilishin nan ta gani
Kanta ta dago dan yi masa godiyar dawainiyarsa a kanta, domin koda ta zamto mahaifiya a gareshi baya hannata yi masa godiya a duk lokacin da ya kyautata mata, sai ta ga a tsaye yake a wajen da ya mike tun bayan gaisheta da ya yi ya ajiye ya mike
Sake tsura masa ido ta yi kafin ta dauke kanta ta ce" Kai zauna mana "
Inda ta nuna masa ya kalla, sai kuma ya zauna yana sada kansa
Baki ta tabe ta ce" Ka leka Hajia ne?"
Kai ya girgiza dan rabonsa da kakar tasa tunda sasafe da ta kai masa maganin baki da na basir ta saka ya sha ta kuma tofe shi da yawu ciki da bai
Baki ta kuma tabewa ta rufe ledarta da kyau ta ajiye a gefe ta ce" Baka da lafia ne?"
Kai ya dago wannan karron ya dan kalli mahaifiyar tasa, sai ya kuma gimtsewa yana ayana yanzu zaka amshi sakamakonka a hannu TAUFEEK tunfa baka tausayin kanka
Mamansa ta tabe baki tana harararsa sama da kasa kafin ta dauke kai ta ce" Kai dilla tashi ka bani waje, bana son shashanci kuma ni ba sa'arka bace da zaka zo har dakina ka min rashin kunya!, Kai in banda iya shege ni zan ringa magana kana yarfawa? Ka kula ni ba Hajia bace kuma ni ba elhaji bace tsaf zan wanke fuskar yaro da mari, tunda dai lafiyarka kalau sarautar da baka gada bace ta motsa sai ka yi, daga nan ka je wajen ubanka yana nemanka kuma ka je wajen HAJIA ka san in bata ganka ba yanzu zata hauro nan ta bi daki daki ta barmu da Allah, ni ka rabani da rikicin da ya fi karfina ka ji na fada maka! Jeka kawai jeka walahi tun muna mu biyu!"
Murmushi ne ya subuce masa a hankali ya sake dago dubbansa yana kallon mamansa, watau ba zai tana yin tsufa da a dura masa ba dadi ba a gaban mahaifiyarsa.........har ga Allah sai ya ji wani sanyi sanyi da farin ciki, hakan ya sa ya dan sake kureta fa kallo ta fitar da kilishinta ta fara ci ya ce" Yanzu Mama dama sarauta ta fi kudi ne?, Ai asalim mulkin kudi ne Hajiar Babanmu"
Dan kwalinta ta turo gaba ta nemi ajiye ledarta,
Yana gannin hakan ya mike da dauri ya fice yana sakin murmushi harda rike hularsa dake son faduwa dan fitowar da ya yi ta dan makalu da kofa
Dakatawa ta yi itama tana yar dariya kafin ta girgiza kai ta karasa wajen wayarta ta daga ta amsa mijinta fa fadin eh ya shigo gayanan zuwa bangaren nasa
Wayar ta kife a hankali tana lumshe idannuwanta hadi da ambaton sunnan Allah...., Sai kuma ta yi shiru a zuciyarta ta shiga yi masa addu'a, duka kaf aduo'in da ta saba ta yi masa kafin ta mike ta karasa kusa da kilishinta, ta janyo ta zauna tana murmushi ta shiga ci
A bangaren mahaifinsama zama suka yi da bakin nan harda shi suka dan sake zantawa kan abinda ya shafi ci gana na harkar kasuwanci sannan bakin suka yi masu salama mahaifinsa ya masu rakiya shi kuwa ya zauna yana dan shan tea din da aka dafawa abansa
Dawowa MAI KWANONI ya yi yana murmushi ya zauna yana ta amsa wayar abokinsa
Yana gamawa ya maida hankali kan ฦan nasa ya ce" Elhaji karami yau ina aka wuni ne?, Tun safe rabona da kai"
Yar dariya ya yi yana shafa gaban goshinsa ya ce" Aba ka manta da maganar dilolin gwonjon da suka sauka yau? , Sai dazu na gama daga cen kuma na leka wajen KAUSAR"
Murmushi mahaifin nasa ya yi yana rage amon TV dake watso labarai..........
Da kula ya ce" Masha Allah, an yi zumunci kennan, fatan du sunna lafiya"
Shima da kula sosai da ladabi ya amsa mahaifinsa sai kuma shiru ya dan ratsa
Shi mahaifin nasa tunanin da yake yi shine har yanzu da ace za'a bi ta tasa da ya kawo maganar wannan zumunci na yaronsa da KAUSAR, sai dai zamani ya zo da salo kala daban daban, shi din kansa ya yarda cewa kawance ne kawai dan kuwa an yi abubuwa kala kala da da ace ba kawancen bane da ya gane , sai abin ya nuna kawancen ne kawai
A hankali ya ce" Damgane da maganar YUMNAH, bana so maganar ta wuce bayan sallar nan, mun tsayar da mahaifinta bayan sallah da sati daya kawai a yi, yaya ka gani?"
TAUFEEK ya sake sada kansa kasa sosai...., Yumnah dai na daya daga cikin yan matan da ya tsaya ya karanta har ya ga eh ta cencenci zamowa iyali a wajensa, domin ta fito daga gidan datijai na kwarai haka kuma tana da tarbiya, uwa uba idan ya yi magana ko wace iri ce YUMNAH na yi masa biyaya domin tun daga lokacin da ya kai mata hijabai yace daga yau su yake da bukatar ta saka ta amsa take kuma sakawar......zai iya cewa eh yana iya auren YUMNAH harma ya rayu da ita a matsayin matarsa idan har alkhairi ce ita din a rayuwarsa......, Sai dai ya so ace bayan an gama exam dinsu an jima sosai ne, dan kuwa bayan sallah da sati daya koda an fitar da result din ba zai fi da kwana goma ba, ga ginnin clinik da yake kai, abin kamar zai dan cakule masa ne ko menene
Dan murmushi mahaifinsa ya yi, sada kan yaron nasa ya saka shi jin dadin hakan, TAUFEEK bai taba barin nagartatun halaya ba, shi yasa bashi da darr da yaron nasa, bashi da wani darrr a kan lamarin TAUFEEK
Abansa ya dora da fadin" ka yi magana hakan ya yi ko yaya?"
Dan murmurshi kawai ya yi a hankali ya gyada kansa
Mai KWANONI ya ce" Masha Allah, sai kuma maganar umarar Hajia, ka ga na so ta yi hakuri su tafi da su ISHRAT, ama ta kiya, bafa zata je da kowa ba sai da wanda ta saba zuwa, na dan so kwatanta mata abubuwa kamar zasu maka yawa ama firr Hajia ta ki Maganar dan da na nuna mata kana Dubai idan ka dawo ka gaji sai cewa ta yi to shikenan a bari badi idan ranta ya kai sai ku je"
Baki ya dan tabe yana ayana irin cazar tsohuwar cen da zai yi, ita me yasa ba zata barshi ya dan ji da abubuwan dake gabansa bane? A gidan nan bai isa ya yi barcin safe ba yanzu zata zo ta ringa taba masa wuya tana faman fadin bashi da lafiya ina manemi da barcin safe?, Idan ya ki yi mata abu sai ta hada shi da wace ta isa da shi ta koma gefe abinta, HAJIA sai ya yi maganinta saboda maganar zuwa umurar nan, zata yi bayani ne
Ama sai ya ce da mahaifinsa" Ba komai Aba, in sha Allah zamu tafi harda su Ishart dinma"
Murmushi mahaifinsa ya yi ya ringa saka masa albarka, shi dai idan har TAUFEEK na duniya baya tunanin zai hadu da damuwa ko ta mecece, idan ta shigo kuwa da yardar Allah TAUFEEK zai gushe masa ita ko ta wanene, shi yasa a duniya bayan mahaifiyarsa baya hada soyayar yaron nan da kowa, kuma baya jin akoy abinda zai iya malaka ya masa shamaki da shi a nan gidan duniya, babu shi
Dan hira suka taba sannan ya mike ya karasa bangarenta yana jin gajiya sosai
Dan dage labule ya yi , ai kuwa karaf suka yi ido hudu da ita tana faman auka turaran wuta na jiji a wani makeke kasko dauke da rabshi tari guda
Murmushi ta saki hadi da fan bangalar da dariya tana dan matse ido dan ta ganshi da kyau ta ce" Shigo mana magidanci zo ka sha kanshi, ka san shi turaren jiji bayan kanshi da dadi kuma maganin mayu ne da aljanu"
Harara ya sakar mata yana jin zai kware, dan har ga Allah turaren nata kauri ne yake yi na tashin hankali ama sai faman fadi take wai kanshi, wai wani maganin aljanu, ai itace aljanar ba kowa ba!
Sakin labulen ya yi ya yi tafiyarsa hakan ya sa ta sake zuba idannuwanta tana kallon kofar kafin ta kallo Hamdiya da ta yi kamar ta suma zuciyarta na bugawa tana kallon hanyar da ya yi tafiyarsa yau ko shigowa ya dan zaunan bai yi ba bale har ta kare masa kallo ta ce" Ke Hamatu yaron nan ya tafi hala?"
Hamdiya ta dan sauke ajiyar zuciya ta ce"
๐๐๐๐โคโ๐ฉนโคโ๐ฉน๐๐๐๐
*DA CIWO A ZUCIYATA*
๐๐๐๐โคโ๐ฉนโคโ๐ฉน๐๐๐๐
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 5๏ธโฃ
LITATAFAN MARUBUCIYAR
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicรฉ
Lait de nuit
Parfums dรฉsodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waษannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai๐๐
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuษi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata๐๐๐๐๐
Hamdiya ta hadiye yawu da kyar tana sauke ajiyar zuciya ta ce" Eh HAJIA ya tafi"
Hajia ta shiga kiciniyar tashi tana fadin" Kai, to me yake damunsa? Nifa bana son na ga magidanci a haka, yaro yana tafe ana harararsa kar aje an shiga gaban jikana ina nan zaune, ke Hamata bani lawurjena na bi bayansa, cikin jakata kuma akoy dan damaso hado min da shi da kulin kaka ka yi ka fito na je na turara masa, aniyar kowa ta bi shi in sha Allahu yaron nan sai ya zama shugaban kasa sai dai maki gani ya mutu!"
Mikewar ta yi domin idan har bata yi gagawa ba HAJIA na iya wanka mata mari, a kan lamarin Yayansu bata ji bsta gani, harta mahaifiyarsa na kiyayewa dan kuwa a kan TAUFEEK ko Aba sai ta batawa bale su
Yana kokarin zama a luntsumemiyar kujerar falonsa, wayarsa a kunnensa dan kiran da YUMNAH ke yi idan bai daga ba har ta yi kuka ya santa sarai ya kai dubansa wajen hanyar shigowa dan jin motsi
Abubakar ne ya shiga shigo masa da kayan abinci
Kansa ya dauke daga dubansa a hankali ya ce" Sorry YUMNAH ba zan samu zuwa ba yau na gaji"
Har ga Allah sai da ta ji wani irin hawaye na neman tsinke mata, da wani irin daci a cen kasan zuciyarta na tunanin abu dayan biyu
Itafa idan har ba gani ta yi an daura aurenta da TAUFEEK ba da wahala hankalinta ya kwonta da wannan KAUSAR din
Ita ta rasa a wani bigiri zata ajiye wannan shirmen, kana zaune kalau da mutumen da ake kira miji a gareka nan da kwana kusa ama kiri kiri kana fuskantar kusanci da shi da wata macen cen da yake kira da kawarsa fiye da kai? Sau biyu sunna samun matsalar da TAUFEEK ya dauke mata kafa kwata kwata na tsayin lokaci, ta ringa bibiyarsa itace nan , itace cen ya ki sauraronta, har gidansu ta zo fir ya ki kulata, tana samun KAUSAR ta mata bayani ta mata fadan itama laifinta ne ta daina kula kowa tunda bata so ta kuma mata alkawarin ya wuce a washe gari TAUFEEK din ya amsa kiranta?, Bayanshi kayan sallah wannan idan za'a yi mata ta sha gannin an mata wani abun iri daya da KAUSAR bayan wannan kyauta ce ta mahaifiyarsa bama tasa ba, abubuwa ire iren haka idan har irgawa zata yi sunna da yawan gaske, sai gashi yauma an maimaita abinda aka saba yi mata sai ance mata za'a zo a fasa dan an je an zauna a wajen KAUSAR an cika dare ana hira, itafa zata iya rantsewa da Allah ko yan matan da suke amsa matsayin yan matansa a gari basa yi mata katutu a wuya irin na wannan baiwar Allahn, sam bata da nutsuwa da ita, bata son lamarinta, ama ba komai in sha Allah lokaci dai idan har ta amsa sunnan matarsa kuma zata maida hankali ta fara haihuwa du taurin kaan TAUFEEK ai dole zai daina mu'amalantar mace a matsayin kawa ko dan tarbiyar ya'yansa.....ita abinda ya fi bata mamaki mahaifinsa fa ya san da maganar KAUSAR ama bai hanna ba, ba'a maganar mahaifiyarsa dan ta kula sonsa take sosai , ama ba komai a juri zuwa rafi wata rana tulun zai fashe ne!
Hajia yake kallo da kaskon hannunta hakan ya sa bai gane jimawar da YUMNAH ta yi bata yi magana ba har sai da Hajiar ta saki murmushi tana sakace hakorinta da tsinke ta ce" Kun gama maganar ne?"
Idannuwansa ya lumshe a hankali ya ce" YUMNAH?"
YUMNAH ta ja hanci tana share hawayenta kasa kasa sosai ta amsa
TAUFEEK ya ce" Kuka kike yi ne?"
YUMNAH ta ta fashe da kukan da ta kasa hanna kanta tana sauraronshi, hakan ya sa ya dan sake lumshe idannuwannsa da suka dauki launin ja a hankali ya ce" Zan fa zo gobe in sha Allah, menene na kukan kuma?"
YUMNAH ta ringa jan hanci tana hanna kantaa kukan, a hankali ta ce" ka tabata gobemaa ba zaka tafiyarka wajen KAUSAR ba?"
KAUSAR........sunnan da ta ambata ya saka shi jin wani takaicin da ya dan barshi ya sake kule masa wuya
Yanzu KAUSAR ba zata taba girma ta yi hankali ba Fisabililahi? Inama abinda ya yi mata, bata tsaya ta ji aiken Aba bane, bata tsaya ta ji bama ya kasar Dubai ya tafi shigowarsa jiya , yau yana fama ya gama da wasu kayan ya je ya sameta ama shine ta watsa shi? Shi KAUSAR ke hanna Auta gaisarwa? Shi KAUSAR ke cema in ta haihu yar halak ba ita ba maganar ya gyara kayansa? Wai shi ya gama menema tace? Itace mene? Lalle KAUSAR ta kirta masa rashin hankali wanda ba zai taba mantawa ba, kuma shi da ita su zuna za'a ga maganar da ta yi wa zata komewa, ba tace in ta kuma masa maganar ya yi karatu ba meye meye? Zai ki yin karatun za'a gani waye zai cika dare yana fadim ya yi karatu, ita in bama ta raina shi ba shi sa'anta ne zata wanke shi soso da sabulu kamar wani danta?, Har ga Allah a gari kaf ya zagaya da kwakwaluwarsa bai ga dan jagaliyan da zai yi wannan gagancin ba bale mai hankali, kama daga kan