Showing 57001 words to 60000 words out of 186303 words

Chapter 20 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18743

aika maganinmu ko ina tsakanin Nijar da Nigeria, ga masu buƙatar magani da gaske su tuntuɓeni akan lambar wayata 07039080978, ko 09077591726


Noted: *MAI SON MAGANINMU IDAN BA A KADUNA YAKE BA, SHI ZAI YI KUDIN MOTARSA HAR ZUWA INDA YAKE, BABU INDA BAMA TURAWA IN SHA ALLAH.....SAI KUN ZO*


💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔




*DA CIWO A ZUCIYATA*




💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 2️⃣1️⃣



LITATAFAN MARUBUCIYAR


Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃








A sanyaye ya ce" Yauma kin yi aiki ne?"


Fuskarta ta dago a hankali ta zubawa tasa ido, kwanakin nan da ta yi kusam biyar bata ganshi ba saboda aiki ya yi tsanani sai ta ga ya wani cika kasumba a fuska, ko idannuwanta ne ke nuna mata haka?
A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta dan girgiza kai tana kawar da dubanta a kansa ta kai wajen motar
Ido cikin ido suka yi da Yumnah
Da kallo wani kalla wanda idannuwanta suka gane mata daga idannuwan Yumnar, wani kallo daban kamar , kamar dai, kamar........


"Uffff, ya salam" ta fada a hankali tanaa dauke nata idannuwan, domin abu daya ranta ya bata shine yannayinta na son taba mata kwakwaluwa bayan zuciya


"Kina da wata damuwa ne?" Ya sake fada, domin gaba daya yannayinta ke neman taba nasa yannayin


A hankali ta girgiza kai tana kokarin daidaita yannayinta ta ce" Ba komai"


Zuba mata ido ya yi, yana gannin kwalar da ta maida karfi da yaji, naan fa ya ji hankalinsa na neman tashi
Ya san wacece wannan yarinya ciki da bai
Kasantuwarta mai tsananin rauni , mai mutunci mai mutunta kowa, mai farin cikin badawa, mai zama da zuciya daya ya saka ya shaku da ita shakurwa irin ta mamakin nan, domin yakan rikice lokuta da dama da damuwarta


"Yaushe kika fara boye min damuwarki?" Ya fada a hankali yana so lalle sai ta kalle shi


Dagowa ta yi lokaci daya idannuwanta suka ciko da kwallah mai zafin gaske ta saka idannuwanta cikin nasa


A hankali hawayenta ya shiga wanke fuskarta har ya zamto ta dan fara shasheka tana kallonsa cikin hijab dinta milk color wanda ke boye sirrin jikinta gaba daya


Ido cikin idon nan bataa dauke nata ba dan tana nitsewa ne a cikin idannuwansa idan har tana hali na kaka nakka yi, takan samu solution ne a nasa idannuwan dan takan ga tausayi, karfafa gwuiwa, fada, jajircewar sai ta yi hakuri a nasa idannuwan a kan dole


A hankali taa shiga fadin" shin menene nakasata? Har yau ka ki kaa fada min, ko da ake cewa nauyin jikina haka din ne? Shin na yi mugun nauyin da za'a riga raina min wayo ne ? Anya Mujaheed zai aureni kuwa? Yau da gobensa ya fara bani tsoro, bayan dukkan biyayar da ya dace ace na masa ina kamantawa hharda wace bai dace ba domin tun kafin na shigaa gidansa ya dora min dokoki irin masu tsaurin da idan ka ji kana iya yin fushi da ni,ama shiru kake ji bayan a da shine da kansa yace ana yin sallah zai turo, gashi yanzu an fara irgen kwanakin babar sallah,....."
Ta langwabe kai ta ci gaba da fadin" idan na yarda iyyayena suka ga hawayena a yau tanar farin ciki yaya zamu kwashe ne? Idan kuma suka ganni gani gododo Rukaya kanwata ta baya an saka mata rana yyaya zasu iya rintsawa ne? Gashi ranna ce baba, rana ce da gidanmu kaf ya dace ace muna cen muna shagali, shin na fara yiwa ahalina baakin cikin samun farin ciki komenene nake ji a nan ya tsaye min a daidau kahin zuciya? TAUFEEK inada ciwo mai girma a zuciyata wanda nake rainonsa tunda na kai shekaru goma sha bakwai a duniya, domin nan da ka ganni tun inada sha uku Mama ke dan tare tana fadin zata ga autanci idan na kai sha bakwai Aba ya mikani dakin miji, a yau shekarata ashirin da bakwai zuwa da takwas, tun tana jefa yan kofunna da kwanoni Aba na hannawa a taba cewar nawa ne har wasu suka lalace aka zubar wasun kuwa a dole aka fitar muka yi anfani da su a cikin gida, TAUFEEK yannayin jikina zai iya hannawa na auru ne ni na hakura gaba daya ko menene? Ko dai bani da lafiyane? Domin wasu na cewa ko ina fama da bakin aljani ne?????"


"Ke uban wanene ya dake ki iyi?" Muryar Hajia ta katse mata hawayen da take yi da kuma maganar da take masa mai kamada rada wace take fitarwa daga zuciyarta tana sanarwa mutun daya tak da take iya sanarwa a duniya


*KAF DUNIYA BATA DA SIRRI SAMA DA TAUFEEK* , kaf duniya bata da da sirrin da take gannin bai sani ba, komai ya sani nata, kamar wani wanda sukaa girma tarr bayan ya bata tazarar shekaru , asalima bai fi shekara hudu da suka san junna ba


Da kyar ya iya sauke dubansa a kan Hajia, wace ta kamo kumatun Khausar tana gyatsine ta ce" Ke dilla kalle ni nan, nace uban wanene ya dake ki? Ke yanzu a haka zaki zauna ki yiwa wani kuka? To na cire maki mutun biyu, ita ko shi wa'inda suka kawo ki duniyar, bayansu du wanda ya san ya dake ki fada min sai inda karfina ya kare, aikin banza aikin wofi ni du sai na ga kamar kin rage kumari daga gannin karshe da na maki, kumatun nan naki kamar sun rage auki, dan mu ga dagen hijabin mu gani....."


Da sauri ya rike hannun Hajiar, har idannuwansa na yin waje, jasa kasa ya ce" Cire mata hijab zaki yi a waje ?"


"Igiyar uban wani ke kanta da zan ki gannin kumarinta a waje?" Ta bashi amsa tana maka masa harara sannan ta kama hannun KHausar ta ce" Ke maka maka share hawayen maka, wuce mu je"


Da ido ya iya binsu, jiki a sanyaye ya juya ya nufi motar ya bude ya shiga sannan ya saka hannunsa a hankali ya dafe wajen gemunsa yana hangen kofar gidan inda Hajia ke magana da Aba wanda zuwansa kennan ya dan zagaya dan amso ruwan piyawata don su yi anfani da shi a gidan


Hajia kuwa abinda ta fadawa Aba ya saka shi yin murmushi yana bada hanya ya ce" Kai Hajia ni kam ai bani da ta cewa Khausar ai taki ce"


Ta sake sakin wani murmushi ta ce" Mamuda ko, kai dai an yi dan mutunci walahi bara na karbo completinta ko ashirin ne mu je, yar nan sai na tashi tsaye a kanta inaga sam ba'a san ciwonta ba"


Shi dai hanya ya bata ta shige, kafin ya sauke ajiyar zuciya, godiyarsa ga Allah da take da wajaje na jin sanyi a zuciya, ya sani zata dan sake tare da hajia kuma har cikin ransa ya yarda da Hajiar bashi da damuwa da tafiyar Khausar din gidanta na kwana biyu


Sunna shiga Hajia ta kirayi Mama gefe ta rage murya sosai ta ce" Kayan yar nan zaki bani mu je tare, wai kin kula kamar ta rage kumari kuwa? Yadda na ci burin auren yar nan harta gado nice nan zan mata bana son na ga tana rage kumari, wai kina bata yan jiko da su yusufa dan karro farin jinni kuwa? Sai fa da yan jiko da turare turare saboda makiya, yau ko dan yannayinta sai fa ta tsole ido, dan dauko min ko kala ashirin ne mu je kin gane?"


Mama ta amsa da to,sannan ya yi dakinsu da dan sauri


Jim kadan ta fito dauke da yar akwati dauke da kayan na Khausar, dan a shigarta sai da ta tabo Aba , yaba dagawa ya sanar mata su tafi dan haka ta sauke ajiyar zuciya ita dinma ta hado mata harda yan baby hijab dinta da hijabinta baba da kalolin kaya uku


Hajia ta amsa tana washe baki ta yi gaba ta bar Khausar tsaye wace ido ya cikowa da kwallah takasa bin hajiar ta kuma kasa cewa komai


A sanyaye tana kallon mamanta ta ce" Mama"


Mama ta sakar mata murmushi a hankali ta dan shafa gefen fuskarta ta ce" Ki je Khausar din Aba kin ji? hajia ce ai , kin ga tana sonki ki yi kokari ki kiyaye abinda zaki batawa kowa rai kin ji? Idan kina so gobena sai ki dawo ko?"


Khausar ta gyada kai a hankali sannan ta juya, tana ji wani irri, dan tunda take bata taba kwana ba a gidansu ba, komai nisan waje tana dawowa ne ta kwana a gida


Da ta fito bata ga Aba ba, a dole ta karasa wajen motar ta bude baya ta shiga dan Hajiar da TAUFEEK ne a gaba, Yumnah kuwa a baya


Dan murmushi ta so sakarwa Yumnah, sai ta ga gaba daya ba bangarenta take kallo ba


A hankali ya dan saita madubin motar ya kalli fuskarta, ba dan komai ba sai dan ya ga shin zata iya zuwa gidansu ta kwana da son ranta ko karfa karfa hajia ke son yi mata


Yannayinta bai kare shi da komai ba sai karin wani tunanin da damuwa, dan kasa take kallo da dara daran idannuwan nan nata sai busasun hawaye da suka kwonta a saman kumatunta


A nutse ya tuka su har suka karasa gidan


Sunna zuwa Hajia ta bude , sannan ta bude bayan ta janyo hannun KHausar tana fadin" Mu je , yi maza ba fara saka ki a ruwan kaka ka yi ka fito, sai an samo maki ki bugo wannan hawaye haka, ina ba zai yiwu ba!"


Da ido suka bi su har Hajiar ta shige bangaren su Maman TAUFEEK, wa ya san me zata yi a cen din


Motar ya rufe ya zagaya inda hajia ta bara masa jakar shi dan aikenta ya ciro jakar sannan ya rufe da nufin mika masu jakar


Da sauri Yumnah ta riko hannunsa, hakan ya sa ya juyo yana kallonta da dan mamaki, domin a sanninsa rabonta da ta kai hannunta da kanta jikinsa tun wayewar garin nan kafin komai ya shiga tsakaninsu


Fuskarta a marairaice sosai ta ce" Ama, ina zaka je ne?"


Dan tsai ya yi yana kallonta, ya san a yanzun kamar ba wata jituwa tsakaninta da Khausar, dan haka a hankali ya ce" Jakar zan ajiye masu"


Jakar ta kalla, da sauri ta miko hannayenta ta ce" Aa gani kuma zaka kai, kawo na je na kai masu ka shige ciki na dawo na zuba mana abinci ka ji yayanmu?"


Bai kawo komai ransa ba ya bara mata jakar, duda ya so ya dan zanta da Khausar sai dai ya san abu ne da kamar wuya dan a yadda hajia ta yi raf da ita din cen da wahala ta saketa


Ciki ya shige, ita kuma ta ja tsaki ta riko jakar kamar ta rike kashi ta kai cen bangaren hajiar ta yar da jakar a kofar falon Hajia sannan ta juya ta yi tafiyarta, dan ita tunda ta zo gidan nan kafarta bata taba shiga bama cikin falon Hajia saboda karara ta gane ba wani sonta take yi ba, ba zata ringa kai kanta inda ba'a sonta ba gaskiya, haka ta koma ranta cike da jin zafin hajiar na wannan sabuwar fitinar, a kan wani dalili zata dauko katuwar mace tana wani kama kumatunta tana share mata hawaye tana masifar da bata san dalili ba ta kawo mata gida inda mijinta ke nan? Bi izinillah daidai take da uban kowa a kan TAUFEEK, ta gama yarda cewa ya isa ta yi kuma idan ta yin ba laifi ta yi ba shi yasa ta sake daukar damarar bashi dukkan kulawar da ta dace, ciki kuwa harda mayar da shi baban waje du kuwa da tsoron da take , zata bashi hadin kai dari bisa dari ta yadda zai manta da wata jibgaga abin haushi gidan tsami kawai!




A bangaren Khausar kuwa ta ga abin mamaki gannin idonta


Wanka dai mai sunnan wanka sai da Hajia ta sakata ta yi sau uku na magunguna Maman TAUFEEK na tsaye tana rike da kwaryar, Hajiar kuwa tana hadawa tana bata tana fadin idan fa bata yi ba shiga zaki yi ki darzar min ita dan na kula shashanci na damun yar nan banza sai sakin hawaye take ta ki fada min ubanda ya daketa, danma na san shi Magidanci ba zai daketa ba ai da tuni na samu mai kwanoni a waya ya min tsakani da shi, har ga Allah yar nan ta gama sacen zuciyata sai yadda hali ya yi kuma, ji nake uwa in janyo nesa ta zo kusa in samo mata gagarumi rikaken dan arziki ya kwasheta mu tafi"


Ita dai Mama tana tsaye har ta gama ta fito da katon hijabi nan kuma aka kuma saka mata kaskon hayaki
Khausar kifta ido kawai take tana kallon Mama dake murmushin hajia tana fadan Magidanci yau bai zo ya yi hayaki ba yana cen shi mai mata abu kamar a karye ana fama da katon hanci da feleke da waya ƙatuwa
Kai magidanci ya dauko da zafi mace ba mamora da ramin kashi


Ana gama mata turaren Hajia ta wuce cikin kicin wai zata zubo mata abinci, nan Mama ta zauna bayan ta ciro mata kaya cikin kayanta tana kallonsu da kula ta ce" Daughter me yake damunki ne? Hajia sai fadi take kina kuka?"


Khausar ta sada kanta a hankali ta girgiza kanta ta ce" Mama, ba komai fa, kawai dai abin bama wani bane Hajia dai ta yi tunanin ko wani ne ya sakani kukan"


Mama ta yi murmushi tana sake kallon Atampar, sam atampar bata wani yi mata ba, ama kumaa bata nuna ba ta bar abinta a ranta da kudurin dake ranta ta ce" Ai kam kema kin ji jiki tunda Hajiata ke kaunarki, ke da Magidancin zaku ji jiki iya jin jiki"


Dariya Khausar ta yi itama kadan tana amsar atamparta ta mike ta shige ciki ta saka tana ta jan rigar gannin tana neman fado mata , gaba daya rigar ta mata yawa yanzun bayan a da har da kyar take numfashi a cikinta, zanin dai ne daidai ta daura ta sake zumbulo hijabinta ta fito


Tana shirin zama Hajia ta watsa mata harara taa ce" Ke dilla cire hijabin, haka fa take yawo yadda kika san yar aike da hijabin nan,, ba dole a yi shiru ba wannan zamani da ya zama na dan kyale kyali, ni hijabinma haushi yake bani in ba dan kar a min wata fasara ba sai nace ina dalili ne wai? Cire ko sai na tashi?"


Mama ta zarro ido tana kallon Hajia da kokarinta, Khausar kuwa ta cire din ama kuma ta kasa ajiyewa bale ta zauna, bama kamar yadda kitsonta ya tsufa kuma kan ba hula, ga yadda rigar ta mata sai a hankali


Da ido Hajia ke nunawa Mama bayan Khausar, Mama kuwa ta ki kallo kawai ta cije abinta dan Allah kadai ya san dariyar dake cinye mata zuciya na lamarin Hajia, haka kawai ki dauko yar a gaban iyayenta kice basa sonta ke zaki kulata? Ga yarinya mai kunya sai sinne kai take ama Hajia ta ki fahimta, karshe dai haka ta sa Khausar cin abincin nan sosai sannan ta sakkata shiga daki ta kwonta suka ci gaba da tataunawa da Mama kafin ta mike ta koma itama


Tana shiga falonsu ta samu abokiyar zamanta zaune tana fira a waya
Da hannu ta gaisheta ta shige ciki dan ta ga tana waya, ita kuwa ta rakata da matsiyacin kall9, duda tsohon cikin dake jikinta bata rasa fitintinnu a tare da ita, a rayuwa taren Hajia mahaifiyar mijinsu da matar mijin nasu uwar TAUFEEK na matukar ci masu tuwo a kwarya, hajiar nan basu taba gannin fitinaniya irinta ba, gashi idan bata yinka bata yinka ne babu wanda zai sakata ta yika dan dole ko waye shi, shi yasa lokuta da dama su da ita a je a gaisheta ne a tashi dan idan ka zauna yanzu wani abin zai faru ta balo maka ruwa, sun yi sun yi su lalata taren nan abin ya faskara, ko yanzu da ta zo ta jata suka wuce ya sa dayar mikewa ta shige dan haushi, ita ta zauna dan so take ta ga abinda aka yi


___________________________________


"Idan baki saka pankeken nan ba babu inda zaki je Khausara, kin ji dan uwan rahamanu babu inda zaki je, yau ga aikin banza aikin wofi, hakaa kike son fita ki je wajen aikin? Ai ba kabari za'a saka ki ba, kina abu kamar wata ni? Ko ni kajal nake radawa in fuske bale ke yarinya danya shirat budurci a leda!" Ta ajiye maganar tana sake gogo mata hodar da ta je wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login