Showing 135001 words to 138000 words out of 186303 words
ko a jiya fa ta san abinda zai faru kennan da bata yi yade yaden maganar nan ba, ama tunda Baba ya sanar mata mahaifin Yumnah na so a zauna sai ta saka a ranta shima zai zo ya ki sauraron kowa ne ya zubda rashin kunya, shi yasa ta zo a shirye a jiyan sai ta ga mutun mai mutunci da daraja wanda ke so y'arsa ta yi zaman aurenta cikin salama, fatanta Allah ya daidaita wannan lamari, ama bata tunanin zata iya jituwa da fitsarar Yumnah sam, kuma ta tsaya tsai a kan kaffafuwanta sai inda karfinnta ya kare a zamantakewar magidanci da Khausar, dan ita ta jima da Sannin cewa Khausar itace zuciyar jikanta, abinda bata sani ba shine menene dalilin da ya sa ya kasa neman aurenta a kulun sai dai ya je ya zube saman kujerar ta ya yi ta huci idan wani abu da ya danganci soyyayar Khausar din ya shiga kunnensa,
Khausar ta karya daidai misali, Hajia ta shake mata tsumin da ta hada da kanta ta mika mata tana fadin" Maza shanye maganin basir da maiko maikon mara ne , in kana shan wannan fa da kika gani ko al'ada zaka yi baka jin ciwo "
Khausar da mamaki ta ce" Kai Hajia? Wannan din? Kin ga kuwa nakan ji ciwon al'ada sosai magani nake sha du idan zai zo"
Hajia ta gyara zama ta wani saki murmushi ta ce" ke magungunan nan ai sai su tarun maka ciki , ya zamana ko wani wata sai ka makari magani ko zaka iya mikewa? Daga yau ga sauki Allah ya kawo sosai ki sha kawai ki kuma ajiye daf da gadonki ki ringa sha ga kuma madara sabuwar tatsa kin san magidanci na kiwo a bayan gida ana kawo min kulun da asubahi shine na yan maki"
Zuciya Na son mai kyautata mata, Hajia yada zango ta yi suke fira hankali kwonce da Khausar tamkar jikarta ta jinninta har goma ta gota sannan ta mike ta yi tafiyarta bangarenta
A bangaren TAUFEEK kuwa a fitarsa ya gana da mahaifinsa sannan ya samu Alhusain dake bangaren baki dan a nan ya kwana ya yada zango suka shiga fira kadan kadan sunna fitar abinda ya shafe su sai kuma Alhusain ya yi murmushi cike da shakiyanci ya ce" Yaya kwanan Besty dinmu?"
TAUFEEK ya zuba masa ido, sai kuma ya dauke ya masa banza
Alhusain ya ce" A jiya, da aka hanna mana Besty dinmu yaya zaka yi? "
TAUFEEK ya yi murmushi yana girgiza kansa ya ce" Rigima kake nema?"
Alhusain ya girgiza kai ya ce" wane mutun, Ni in nemi rigima da mai fuska biyu? Kai fa ka ga a wajen aiki aikinka kala biyu ne, a gaban Aba kai yannayinka biyu ne domin a gabansa salihi marar fada haka kake ama a waje idan ka samu wajen yi har tubewa kake yi, kuma ka ga haka besty dinmu ma kake mata a gabanta kai besty ne ama a zuciyarka ba hakan bane, kai kam kana fama, Ni ina zan iya , ba zan iya ba ko kadan man!"
TAUFEEK ya sauke ajiyar zuciya , a hankali ya dafe gaban goshinsa yana rintse idannuwansa da tuna irin fargabarsa da tashin hankalinsa
A hankali ya ce" Nima na kusa mutuwa Man"
Alhusain ya zarro ido yana kallonsa ya ce" Mene?, Rashin lafiya ka yi ne?"
TAUFEEK ya yi murmushi mai daci yana gyara zamansa daga kafa daya kan daya ya maida kaffafuwan a kasa yana kallonsa ya ce" Man, da ban mutu Bama da na hadu da jinya, ka san saura kiris yarinyar nan ta auri wani ko habu ko Murtala? Ni sunnan bace min yake yi dan a kulun in ta fadi sunnan sai in ga kamar wani la'antacen sunna"
Dariya Alhusain ya fashe da ita, dan walahi irin yadda TAUFEEK ya yi harda dantse lebe ya tabata da ya hadu da wannan mutumen a yanzuma sai sun raba hali
Yana dariya harda saukowa daga saman kujera yana kallonsa ya ce" Kana da akida mai tsauri abokina, tunda ka gabatar min da ita na gane nima halin da kake ciki, na rikitaka ainun ama ka ki ka fada mata, duba ka ga ranar aurenka ka yi kiranta murya a shake , burinka ta zo daf da kai, ka ga tunda na ga ka iya sakama kanka irin wannan rikicewar zuciyar na san du wanda ya taboka tsaf zaka hargitsa shi, why zaka rayu da ciwo a zuciyarka tsayin shekaru?"
"A kanta ina da tsoro mai girma Man kaima ka sani, tsorona daya ne tall a wayi gari dan na kasa rike abinda ke raina in rasa zumuncinta, ka san yarinyar nan kallon sako take min?, Kuma tana iya zama ta fada min sirinta, na shaku da hakan ainun, kai bari ka ji da an aura mata wani da mun yi mutuwar kasko !"
"Abokina idan akoy boyayan mutun bayanka ne, ka dai bi min besty a hankali!" Alhusain ya fada yana sake yiwa TAUFEEK dariya
Taufeek ma ya yi yar dariya yana girgiza kai ya ce" Ya danganta , kuma ka daina ce mata besty, babu abota tsakanin namiji da mace sai Ni da ita kadai!" ( To ba kun ji ba?)
.......................im sorry people ina busy ne ga weekend
Na gode ππππ
[7/24, 10:04 AM] +234 816 049 3429: ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
*DA CIWO A ZUCIYATA*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 5οΈβ£3οΈβ£
*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*
1: Duk karyar kada
2: Yar mahaukaciya
3: Neman na kaina
4: Bani da zabi
5: Bak'a ce
6: Kutkale
7: Makauniya ce
8: Mage
9: Duk nisan jifa
10: Idan ka raina inda kake
11: Dutse
12: Alkalamin kadarata
13: Bani da zabi
14: Dakika Biyar
15:Wata kokowar
16: Aure yakin mata
17: Ni zan ladabi
18: Daga tafia daukar soja
*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicΓ©
Lait de nuit
Parfums dΓ©sodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaΙannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiππ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mataπππππ
A nutse Husaini ya yi masu takaitaciyar nasiha irin wace ya dace ace ya yin a matsayinsa na aminin kusa da TAUFEEK din
Bai wani ja dogon Zama ba ya nuna zai tafi, nan Khausar ta mike tana fadin" Ina zuwa Besty"
Ta juya ta haye sama, shi kuma ya kalli TAUFEEK yana masa murmushin shakiyanci dan Khausar ta ce masa besty
Jim kadan ta sauko hannunta rike da wata bakar leda mai sirri, ba komai bane a ciki sai yan kannanun humura masu dadin kanshi da saka nutsuwa ta bada tana fadin sakon madame ne sannan ta koma ta zauna
Har ga Allah bata yi haka dan ta birge TAUFEEK ko dan ta ba matarsa haushi ba, a ranta ta ji ya dace ta yi hakan dan tana da damar hakan, ko a da idan ya zo takan daka su kuli, su miyar Hausa da yajin dadawa ta bada a kaima madame, yanzun kuwa gannin bata da su sai ta bada humura dan ta san itama abu ce da take iya birge wanda ke kasar waje
Sai dai wannan kokari nata ya matukar birge TAUFEEK duda ba yau ta fara ba, matarsa kuwa sai ta ga kamar wace ta yi da gaya dan ta bata mata, ita dai tana zaunenta har ya mike suka tafi Yumnah sai addu'a take yi da fadin a turo mata numbar madame din sa ringa gaisawa idan ta sake waya , shi dai Husaini ya yi godiya sosai kafin ya fice TAUFEEK ya sanar masa yana zuwa dan sai ya kaishi aeroport du kuwa da irin yadda ya ki ama yace sai ya kai shi
Dawowar da ya yi ba ta komai bace sai ta tsokana da son cinma burinsa cikin ruwan sanyi
Zama ya yi a saman kujerar yana fadin" Wai yau me zan ci ne? Wifeyyyyyyy"
Har ga Allah ita ta kalle shi ne ba dan ta saka a ranta da ita yake ba, sai kuma gannin ba ita yake kallo ba ya saka ta zuba masa ido a ranta tana jin to wai wannan kamar an cin mata fuska ko ana daf da raina mata hankali
Yumnah kam wani sanyi ta ji a ranta, cike da rage murya irin karma a ji tan nan, irin maganar nan ta wasu matan idan sunna yiwa miji a gaban kishiya cike da kisisina ta munafurci ta ce" Oh sorry my hero, yau baka ci komai ba? Bari in shiga kicin in sama maka wani abin"
TAUFEEK ya yi dan murmushi har ta mike tana layi dan ba fa karfin jikinta take ji ba ya riko hannunta yana kallonta ya ce" A'a, a haka ba zaki iya girki ba, bari idan na fita in shigo mana da shi, zan raka Husaini"
Yumnah ta dawo ta dane cinyoyinsa ta dora kanta a kirjinsa, nan ne kuma Khausar ta mike dan ta kula ana daf da aikata rashin mutunci a gabanta ta juya da dan sauri bayan ta warci kaskon turaren wutarta ta haye sama tana jin wata tafarfasa da ranta ke yi ta kai ta ajiye kaskon ta kashe wutar sannan ta ringa kai kawo cike da jin wani haushi a ranta kafin ta nemi waje ta zauna tana karkada kafa cike da jin kewar iyayenta yau har kwana na biyu bata ji su ba, bata da waya, ga wayar nan layin baya ciki, kuma babu litatafanta daga ita sai ranta dan ko Alkur'ani babu a dakin nata bata san ba kuma akoy wajen Ajiyesu a falon masu yawan gaske ma kuwa bale ta dauko ta yi karatu, sai kawai ta ringa sake sake har ta ji ranta na tafarfasa yana bacewa sosai kan irin abinda TAUFEEK ke yi mata a gidansa
Kwonciya ta yi tana ta huci har ta dauki lokacin da ita da kanta bata sani ba sai da ta ji bude kofar nata ta mike da sauri dan bata san cewa bata rufe dakin ba ta dago ta zuba masa ido
Yanzun bata da hijab din rigar ce kawai a jikinta, kuma bata da rigar mama sai kafecen pant dinta a kasan rigar wanda tsaf ya bi sawun rigar tunda ba yar a rufe asiri bace mai santsin nan ce kuma link color ya zamto harta zannen yan mulalan Mamanta ana gani tsaf ga wanda ya kalla dan ya gannin
Ledojin dake hannunsa ne suka so kubcewa daga hannun nasa
Da kyar ya iya tarewa ya rike yana dan dafe bango kadan daga makogwaronsa kuwa yana fitar da wani irin huci mai dumin gaske ya sake zuba mata ido
Da kyar ya cira tafiyarsa ya karaso inda take tsaye ta rike kugu tana sakar harare gefe da gefe
Ajiye ledojin ya yi ya dago ya sake zuba mata ido
Dukkan alamu na masifa sun bayyana a tare da ita, wa'inda sam bai so ganninsu a yanzu ba, bai san dalili ba, harma yake daf da manta abinda ya yi mata take fushi
Ledar ya juya ya kalla ya sake juyowa yana kallon yadda kannanun kitsonta suka wani yarfu abin dai ba'a cewa komai ya dan yi gyaran murya dan maza ne ai kar ya bada kansa a tausashe ya ce" taho mu ci abinci Khausar"
Ledar ta bi da kallo zuciyarta na mata wani irin tukuki
A hankali ta maida dubanta kansa, yanzun bata daga murya irin na dazu ba, ama a sanyayen sai ya ji inama Muryar ta daga yadda zasu yi ba dadin
A hankali ainun Khausar ta samu kanta da fadin" Ni acici ko? Taufeek Ni acici ko? Bana ci barci nake ji"
Daga haka ta karasa bakin bed dinta a nutsen da bata san tana da nutsuwa har haka ba ta hau gadon ta juya bayanta ta kwonta tana janyo abin rufa a hankali ta rufa jikinta da shi
Tunda ta bashi baya har ta kwonta din kallonta yake yi yana tunanin me yake faruwa ne? Me ya sameta ne? Ko bata da lafiya ne?
Dayar ledar mai dauke da kwalin wayarta wace yanzun ya ajiyewa Yumnah Tata da abincinta kafin ya mata salama ya shigo nan din ya dauka ya karasa a hankali bakin gadon yana mika hannunsa ya yaye rufar a hankali ya ce" Hey, menene? Waye ya taba ki? Taso in ji waye ya bata maki rai?"
Khausar dake boye hawayen dake neman tarun mata a idannuwanta a hankali ta girgiza kanta tana rike abin rufar ta ce" a'a babu wanda ya bata min TAUFEEK barci ne nake ji Please "
Wani irin tashin hankali yake jin zai damu zuciyarsa, har ya kasa ciro wayar tasa
Khausar ta dan juyo tana kallonsa kasa kasa ta ce" Ka tashi in rufe dakin dare ya yi "
Dakin ya bi da kallo, a hankalin shima ya samu kansa da fadin" Ni kuma fa, in kwana a ina?"
Khausar ta maida idannuwanta ta rufe tana ji kamar tace masa ka je dakin matarkan mana, sai kuma ta kwabi kanta ta ce" Ai dai ba a nan ba zaka kwana ko?"
TAUFEEK ya mike tsaye yana fadin" A ina kike so na kwana?, Bari in dauko computerna kar ki rufe min daki"
Samun kanta ta yi da bin bayansa da kallo kafin ta maida idon nata a hankali ta rufe tana jin ta kasa mikewa ta rufe dakin, ko kuma bata so ta rufe din ne? Kai kamar wace take gudun ta rufe din ya je wancen dakin ya kwanan, haka kawai take jin idan ta yarda aka yi mata haka kamar an wani wulakantata ne ai! Sai kawai ta lumshe idannuwanta tana sauraronsa har ya dawo din ta sake yin shiru tana sauraron dan motsinsa kadan kadan har ta ga ya hayo gadonta, hakan ya sa ta dan dago tana kallonsa sai ta ga sam bai dubeta ba ya dauko filo yana jerawa a tsakaninsu har kusan kafafuwa sannan ya tafi cen karshen gadon ya wani rabe da computarsa ya yi kamar bai san tana kallonsa ba ya shiga aikinsa yana waya hankalinsa a kan wayar gaba daya
A hankali ta kara komawa tsinin gadon ta makure jikinta kwakwaluwarta cike da tunanin to yaushe zai saukar mata a gado?
Tun tana hangen bayansa da jiran gannin ya saukar mata a gadon har barci ya ringa fizgarta gaba daya ya dauketa jikinta ya saki sosai idannuwanta a lumshe ta yi filow da dayan hannunta dayan kuma yana daf da abin rufar ta sake shi da barcin ya dauketa
A hankali ya ajiye computarsa sannan ya juyo ya ringa janye filo din yana sauke su gaba daya daga gadon, dan bai ga amfaninsu ba, sam basu da waje a gadon nan
Yana gamawa ya sauka ya je ya kashe fitila sannan ya hayo saman gadon ya kwonta ya haska yar karamar wayarsa ya zubawa fuskarta ido
Kasa kasa sosai ya ce" Khausar, my dream, my life, ......"
Idannuwansa ya lumshe yana jin nutsuwa na shiga zuciyarsa, a hankali ya matsa bayan ya cire rigar jikinsa ya janyota jikin nasa ya rungumeta ya zamto rabin jikinta a saman kirjinsa ya zagaye sauran jikin nata da hannunsa ya tofa mata adu'ar barci ama shi masa barcin ya ki zuwa da salama kamar yadda ita ta samu
Bukarta yake, so yake yi ya ji lebenta a saman nasa ta yadda zai iya samun nutsatsen barci
Sai dai kashhhh
Ba zai yi mata gagawa ba, ko a haka ya san ya godewa Allah ya samu wani baban abin daga ita bayan dogon jira da cire tsamani
A hankali barcin shima ya dauke shi, har ya ji karancin barcin a lokacin da kiraye kirayen asubahi suka farkar da shi ya zubawa fuskarta ido gannin yanzun itace ta masa riko irin na filo tana barcinta hankali kwonce
A hankali ta fara alamun motsawa saboda kiraye kirayen sallah, shi kuma ya ki sauketa a jikinsa dan yana so ta farka ya ga reaction dinta
Idannuwa ta fara budewa sannu sannu kafin ta laluba hannunta a inda yake ajiye daf da gemunsa
Lalubawa ta sake yi tana mai tabatarwa kanta eh lalle gemu gashi ne dan haka da sauri ta dago idannuwanta suka shiga cikin nasa
Ido ta zarro , shima ya zarro nasa ta mike da sauri tana kale kale shima ya zuba mata ido a dole sai ya ga gudun ruwanta, ai kuwa ta kawar da kai salatinta ya fito fili ta mike da sauri ta yi bayi tana wartar hularta ta ja ta rufe sai zarro ido take yi
Murmushi ya saki ya sauka a gadon ya dauki rigarsa kadai ya saka ya fice shima a dakin hankali kwonce ya nufi nasa dan zuwa Masallaci
Ko da ya dawo daga masallaci ya je dakin Yumnah 6a tarda ita ta koma barci dan bata samu barcin ba duka daren sai ya fito a hankali ya je dakin Khausar din ya bude ya shiga da salama sannan ya sauke dubansa