Showing 48001 words to 51000 words out of 186303 words

Chapter 17 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18764

FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃






Koda ta tashi da asubahi bata ganshi a gefenta ba, duda ta ga an rufata sai ta kasa barkata wani abin kirki, a tunaninta baima kwana a cikin gidan ba ya koma inda ya kwana jiya
Wannan tunani ya karra saka mata tunanin lalle sai ta yi da gaske, banda hanya irin ta kirsa da zata ara sai ta jajirce ta fadawa Allah ya raba mijinta da wannan fitinaniyar,
In ba asiri ta masa ba ta yaya za'a yi a kalli mijinta rikaken namiji mai jini a jika a dangantashi da Khausar?, To ita bata iya bin bokaye ba, ama zata yi dukan abinda ya dace dan gannin ta rana wannan alaka mai wuyar fasara, in Khausar ta iya ruwa bata iya laka ba, da izinin ubangiji zata san tana bibiyar mata miji dan kiri kiri sai ya fi karfinta walahi!




Da wannan ta samu ta dira ta yi bayi
Ta yi wanka ta kuma dauro alwallah
Zuciyarta du bakin kirin na tunanin yau kwana har biyu cif tana matsayin matarsa aman komai bai shiga tsakaninsu ba? Ina ba haka take hango tarayarsu ba, ba haka take hango zamantakewarsu ba




Sallah ta yi du rabin hankalinta a waki wajen
Tana gamawa bata tsaya yin adu'ar ba ta yi wajen kayan kwaliyarta da sauri ta shiga kimtsa kanta
Niyartama tana gamawa ta fice ta yi bangaren manyan ta gaishe su ta yiwu yana cen, inda dai ta san ba zata saka kafarta ba bangaren Hajia ne, dan matar ta tsaneta bata san abinda ta yi mata ba




Bayan ta gama kwaliyar ta dauko wata rigarta ta ajiye doguwa ta lesh tana kokarin nemo abinda zata hada mata aka turo kofar aka shigo


Da salama ya shigo yana dan shakar kanshin dakin da ta baza na turaren jikinta da ta fesa, sai kuma ya sajke dubansa a kanta a inda take tsaye da doguwar rigar barci da ta saka dan yin sallah da safen


Idannuwansa ya dauke a kanta bayan ya ga irin kallon da take binsa da shi idannuwanta na neman kawo ruwa


Bakin gadon ya karasa ya zauna a hankali sannan ya sake dubanta a lokacin da ta nufo shi a hankali kamar wata mai jin tsoronsa
Yannayinta ya saka shi sasaura fuskarsa sannan ya miko mata hannu


A sabauce ta karasa jikinsa ta fada cikin fafadan kirjinsa hannayenta na yin rawa rawa, muryarta na rawa ainun ta ce" Fushi kake yi da ni?, Dan Allah ka yi hakuri, ka yi hakuri ba zan kuma ba, idan na bata maka, ama Yayanmu sai ina jin tsoro, kamar dai baka yi murnar kasancewata matarka ba? Du bana gannin murna a fuskarka"


A hankali ya rungumeta bck, idannuwansa a lumshe ya ce" Murna? Yumna ina murna mana, kin san shekaruna nawa ne yanzu? Na fi kowa murnar kasancewarki a rayuwana....."


A hankali ta dago tana kallon fuskarsa , hankalinta na sake karantar mata yannayinsa, alamu na farin ciki na son bayana a fuskarta


A tausashe sosai ya ce" Shin akoy wani abu da Khausar ta maki kika boye min ne?, Idan akoy shi ki fada min ni zan dauki mataki dan ba zan taba amincewa a wulakanta min ke ko a ci zarafinki ba....."


Wani dadi ne ya ringa ratsata, ita? Ashe? Wani irin luuuu ta yi tana kallon fuskarsa, bakinta na nemo laifin da ya dace ace ta fada ama tana ta kai kawo tana tsayuwa a waje daya, laifin da shine kawai take gani kuma shine bata so


A tausashe ya ce" Tell me, an yi wani abin da bannsanu bane? Ta maki wani abin da bai dace ba kika boye min ne?"


A hankali ta dan girgiza kanta, tana da niyar fadin laifin ya tsatsareta da ido , a tausashe yana dubanta ya ce" Yumnah, kina zargina ne?"


Da sauri ta zuba masa ido, ta ce" Zargi kuma?"


Idannuwansa ya lumshe matsayin amsa


Da sauri ta girgiza kanta ta ce" Ba, bana zarginka, kawai dai ni abotakarku ce nake gannin bai dace ba, ba abota tsakanin mace da namiji, sam bana son tarayarku da ita, daga min hankali take yi, sai in ga ka fi sonta da ni, bayan nice matarka, sai in ga ka fi darajata a kaina"


Da mamaki yake kallon fuskarta, wannan din itace hujarta kawai?, Eh lalle a jiya Abansa ke cewa wani sain fa magidanci zaka iya tsintar kanka da rarashi a kan abinda bakama aikata ba, ka yi rarashin dan nima shi nake yi nan da ka gani, ita mace tana iya yin fushi a kan abinda baka taba zato ko tsamani ba, in ka ga hankalinta tashe yi kokari ku sasanta dan sasantawar itace zaman lafiyarka a gidanka


"Yumnah, wannan shine dalilinki?" Ya fada yana s9n sake gaskatawa


Kai ta gyafa har tana sauke ajiyar zuciya


Gefe ya kalla kadan yana ta tunanin to kennan ya shigo fagen da nanata zancen da ya san an sani zai zame masa wajibi? Ikon Allah


A tausashensa ya rike hannayenta yana kallonta ya ce" Wannan din, bai dace ya zama abinda zai saka ki bude baki ki yi furuci kamar wace ke zargina da KHausar ba, hakan ba daidai bane sam ba kuma wayo bane, KHausar na santa tun kafin na sanki, a yadda kika ganmu da akoy maganar so da na aureta tun kafin na aureki, ita din tamkar jinnin jikina ce, ina nufin kamar kanaina haka nake dubanta, mu'amalata da ita tsarkakakiya ce, zumuncina da ita mai daraja ne, ina kare mutuncinta dan mai mutunci ce, daga wannan kar ki dada kar ki rage Yumnah, bayan wannan babu wani abu mai iya gigita tunani ko ya saka shaku, na yarda cewa al'adunmu sunna da nasu tafiyar a rashin gannin ire iren haka, hausawa muke, haka adininmu, ama ki yarda tsakanina da KHausar zumunci ne, haka kuma zan iya kare hakinka a gaban kowa...."


Ya dan sasaura , a hankali ya dora da fadin" Ke iyalina ce, maganar sonki ko gannin darajarki kin san ya kai matsayin da na aminta har na saka ki dakina......., Ba zan so mu fara takalar magana irin haka ba, zan kuma so li yi zumunci da Khausar idan har kina ra'ayi, in bakya yi ba zan takuraki ba, ama kar ki wulakantata dan ita din a kulun mutuntaki take yi kin fahimta?"


Ba ainahin fahimtar ta yi ba, ama a yadda yake zaunen nan ya bata dukkan hankalinsa zata iya cewa rigimar ta lafa a irin wannan lokacin


A hankali ta koma jikinsa ta sake makalkale shi hannayenta duka a jikinsa


Idannuwansa ya dan lumshe, karfe bakwai ne duka duka na safe, yana fa niyar fitama, haka kuma wannan yannayi yana tsikararsa sosai


Kasa kasa ya rada mata maganar da ta sakata dan sake shigewa jikinsa tana sakin murmushi


Murmushi ya yi ya sake fadin" ba zaki lafawa tuzurancina bane? Kar fa ki takali dodo ki nemi kumna fitila Yumnah"


A ranta fatanta dodon nan ko mai cin dodo ne irinta ta takale shi, burinta itama ta zama matar aure a yau din nan, dan haka cikin dabara, da koyarwar da ta samu ta ringa dan shafa hannunsa zuwa wuyansa kamar da gangan take yi, bayan tana sane sarai, gashi ta idasa cimuymuye rigarsa da Hajia kakarsa ta bashi ta sallah, ta idasa rike shi iya rikewa


Tun yana sake tunawa cewar ba yanzu ba, sai da ya tsinci kansa tsamo tsamo a aiki irin na musulmai, aikin da ya zamto gagarumi a gareshi shi kansa, aikin da bai taba kwatanta aikatawa da wata y'a mace a kaf fadin rayuwarsa ba, aikin da yake wuni yana kwana da shi wanda yake tunanin idan ya tashi yi ta yiwu ya karya y'ar mutane, da safiyar gari, da yinwa a cikin y'ar mutane, da komai, haka ya riketa riko na firgici da mamaki, tun tana iya gane sarafa junna suke har ta cenza tunani ta fara tunanin sarafa ake yi, harma ta dawo tunanin ko ranta ake nema?
A hankali ta fara bambance aya da tsakuwa, a hankali ta nemi dna juyo da hankalinsa ko zai dakata tun kafin ya fara mai gaba dayan
Sai dai sani ne bata yi ba, ba sabon shiga ake yiwa fi'ili ba, ba kuma namiji mai sunna namiji ake tsokana a mike ras kamar yadda aka koyar da ita ba
Bata taba tunanin Mijinta ya fi ainahin mijinta girma ba sai da tashin hankalin ya nauje ta ya cakumeta ya nemi karta
Wahala iya wahala ta tsinci kanta a ciki a lokacin da summa ta ki zuwar mata take farke tana sauraron aikin likita
Jigatar shima ya jigata dan yau ya fara sauke nauyin nan kuma a irin lokacin nan da ya dan warci furana wajen hajia cikinsa ya dan dauka kadan


Da wannan suka sasaba har Amarya Yumnah ta samu abinda take nema, sai dai wa ya sani tana kan bakanta na mikewa ta kabe ta kile ?......... (😂 han)


_______________________________


Karfe bakwai na safe ta shirya , shiryawa mai tsafta da tsari daidai da kwaliyarta


Hijab dinta na sallah sabo fil fari kal ta saka sannan ta saka takalmin auren TAUFEEK ta aniya kai kawo sai sakin murmushi take yi


Zazafe da aka zubo ta karewa kallo ta cire kai tana murza dari biyar din da Aba ya wanka mata mari da ita da asubahin Allah, ita ta san yau zata shiga cikin tarihin rayuwarta domin zata ci kwan kifi iya ci a kofar asibiti sannan ta ci dambun nan na kofar asibiti mai dadin balaki, ita kam yau me zai hadata da zazafen Mama? Aa gaskiya, to mema ya hada likitama da zazafe fisabililahi?


Sintirin da take yi yan uwan ke bi da kallo har Mama ta fito daga gyaran dakin abansu domin ita ke gyaran abinta har yanzun bata barwa yayanta wannan ba, ta mikawa Khausar sharar ta kai ta zubar ta dawo ta yi wani kikam ta ki zama sam sai aukin duba agogon da ta daura a hannunta take yi baka yar siririya tun ta sallarsu ta bara da Aba ya siya masu


Mama dake zama saman tabarma ta janyo kwanon abincinta ta sake kallon KHausar ta ce" Ke wai ya hala, ki nemi waje ki zauna mana, ya baki karya ba kuma?"


Khausar ta kalli abincin ta girgiza kai a hankali ta ce" Mama ai yau ba zan ci tuwon laushi ba, kin ga dari biyar Aba ya bani, kuma shiry TAUFEEK din bai zo ba har yanzu kar fa na yi lati, Aisha ke dan bani wayarki na yi kiransa?"


Mama da mamaki take kallonta ta ce" Ke zo nan zauna"


Khausar ta karaso inda Mama ta nuna mata ta zauna tana kallon maman gannin ta sha kunu


Mama ta ce" Dari biyar din duka zaki je ki juyewa ciki sai kace baiwar ciki? Bayan ga abinci a gida? Karma mu fara haka da ke maza ki cire dari biyi ki saka a cikin asusunki, sannan maganar TAUFEEK, Khausar zuwa yanzu fa sai kin kiyaye wasu abubuwan, kamar su yawan kiranshi, kiranshi kowani lokaci, ke harta yawan ganninki tare da shi, dan kin ga yanzun sunnansa mai mace, ba daya bane da da, ita zuciya bata da kashi matarsa na iya jin ba dadi, kuma tana da gaskiya dan ko ba komai hausawa muke ai ba yaren yahudu ba, ke kin san yaya aka yi muka yarda da tarenku sai da muka yarda cewa eh ta zumunci ce, ama duda haka ba wani sakankancewa muka yi da ku ba, dan haka ba zamu yarda yanzu tarenku ya hadasa fitina da matarsa kin gane?"


Khausar kallon Mama take yi da mamaki


Ta rage kiran TAUFEEK? Ta rage karfin mu'amalarsu dan ya yi aure? To ita me hadinta da aurensa? Ita ai itacema zata gyara aurensa ba ta hada rikici ba, ama irin yadda Mama ta daure fuska a dole ta amsa da to ta kuma kai dari biyu ta saka a asusu sai cika kunci take ta zo ta zauna ta shiga shakar zazafe bayan ita ta san cewa ba girman likitoci bane daukan tuwo da safiyar gari ( ki rufawa kanki asiri autar Aba, ki ci ki yi nak, aikin asibiti ba'a yi da yinwa bale din nan kar ki je ki baje kina hailala😌)


Wasa wasa sai da ta ba karfe goma sha daya baya na rana tana jiran tsamani, ta ki ko hijab din ta cire a zaunen da take, dan shi yace za'a kaita kar ta je kai tsaye, gashi Mama ta yada dokar kar ta saki ta ringa kiransa yanzun, sai kawai ta ji kamar ta yi ta ihu a zaune


Sai kusan sha biyu aka yi salama aka sanar da ita direba ne daga gidan mai kwanoni ta fito a kaita asibiti


Har gudu gudu take yi wajen saka takalma Mama na yi mata addu'a har ta shige motar tana tambayar ko TAUFEEK ya yi tafia ne? Shi dai direban bai san amsar bata ba ya dai kaita har inda akace ya kaita sannan ya juya


A darare take kale kale a baban filin bangaren Emergency, bata san inda zata nufa ba, bata taba tunanin zata iya tsintar kanta da tsoro da shayi ba sai a yau, kallon mutanen dake kai kawo yake yi zuciyarta cike da tunanin me ya hannata dauko wayarta ne? Tunda suka yi waya da Elhaji jiya ta kashe wayar bata kunnata ba dan yace shi zai kawota asibitin yau, ita kuma bata son takura


Ajiyar zuciya ta sauke ta nufi hanyar shiga emgncy din


Mutumen dake gadin wajen yana tsaye kikam fuskar nan ba annuri ne ya sakata dakatawa tana kallonsa da tunanin anyama bahaushe ne?


So ta yi ta rabe ta shige salim alim, ama kuma ta san waye shi, dan ko kana zuwa dubiya ka san su waye masu tsaron kofofin asibitin, basa sasauci dan bada tsaro a hanyar


Murya na rawa ta ce" Ina yini Baba"


Kallonta ya yi kallo daya sannan ya dauke kai, wai Baba? Shi baban da tace masa ne ya bata masa raima ba kallon kure muninsa da ta tsaya yi ba
Shi bai ce mata Mama ba dan tsohon raini zata wani ce masa Baba?


Takardar ta fitar tana dan matsowa ta ce" Ka ga yau akace na zo na fara aiki, ga takardar nan"


Yanzun kam a wawure ya wawura mata kallon ta mutu ta lalace, aiki? To ko mau mukami ce dai? Ko babar docter ce ai ba haka ake zuwa ba, bale ta yiwu karamar likita ce, ta rasa lokacin zuwa sai yanzu? Lalle tana da tashin hankali a gabanta bale yau gidan a dinke yake da dakarun masu saita ire irensu


Hanya ya bata ta shiga ko ci kanki bai ce mata ba, ya san za'a rama masa kiransa baba da ta yi in dai ta shigan, ba sai ya rama da kansa ba gaskiya












😂😂😂😂😂😂😂😂 Wayo mu, Khausara Allah ya bada Sa'a yar gidan Aba






*ALLAH BAI SAUKAR DA CIWO BA SAI DA YA SAUKAR DA MAGANINSA*


Ni ce dai Fareeda Abdallah, na sake dawo muku da tallen magungunanmu da zuwa yanzu bazan iya ƙayyade yawan waɗanda suka dace da biyan buƙata sanadiyyar amfani da maganinmu ba. Alhamdulillah! Ƴar'uwa ki gwada, wataƙila warakarki na tattare da maganinmu.
Haihuwa ce baki taɓa yi ba ko kuwa jinkiri kike samu sanadiyyar planning ko kuma haka kawai? Muna da ingantaccen maganin rashin haihuwa ga mace da namiji, wanda za ki bada sadakar 2k ga matsalar ko wane ɓangare. In sha Allah za ki dawo da godiyarki bayan amfani da maganinmu.
Sanyi (infection) ne yayi miki yawa yake saka ki ciwon mara, zubar farin ruwa, ƙaiƙayi, ƙuraje, ɗauke ni'ima, har ma ya saka mijinki ya dinga miki gani-gani saboda bakya gamsar da shi? Da naira 3k zamu haɗa miki magungunan da za kisha ke da Oga in dai kika yi amfani da su ku da sanyi har abada in Allah ya yarda.
Muna sayar da ingantaccen haɗin sabaya, wanda zai sa nonuwanki su cicciko, hatta fatar jikinki sai ta murje sanadiyyar shan kunun sabayarmu. 2500


bokiti 1litter.
Muna da maganin wankin nono ga mai ciki da mai shayarwa, wanda indai kikai amfani da shi yaronki zaiyi tubarakallah, ba ruwanki da laulayi. Muna da ingantaccen maganin Daji (Cancer), typhoid, maleria, yaron da yayi nauyin ƙafa, da sauran cututtukan da ban ambata ba.
Muna aika maganinmu ko ina tsakanin Nijar da Nigeria, ga masu buƙatar magani da gaske su tuntuɓeni akan lambar wayata 07039080978, ko 09077591726


Noted: *MAI SON MAGANINMU IDAN BA A KADUNA YAKE BA, SHI ZAI YI KUDIN MOTARSA HAR ZUWA INDA YAKE, BABU INDA BAMA TURAWA IN SHA ALLAH.....SAI KUN ZO*


💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔




*DA CIWO A ZUCIYATA*




💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 1️⃣9️⃣



LITATAFAN MARUBUCIYAR


Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login