Showing 117001 words to 120000 words out of 186303 words

Chapter 40 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18787

Washe gari karfe takwas da yan mintina


Sauri take yi tamkar zata zura da gudu sakamakon yan mintinan da ta dora a yadda ta saba zuwa asibitin, a cen kasan zuciyarta kuwa fada take yi kamar zata ari baki na irin tsayar da Itan da direban ya yi da irin yadda Mama da kanta ta sakata saka wannan suturar ta jikinta kuma ta rufeta da fadan wai ta saka turare da yawa bayan yanzu matar aure take, ita abinma ya so bata dariya, ama kuma da ta duba tsantsareren kunshin hannayenta sai ta ji wani dadi dan kunshin ba karya ya zanu Allah ma kuwa


Da dan gudu kadan cike da tsoron kar sabon takalmin nata ya kayar da ita ta saka hannunta ta hanna lft din rufewa sannan ta shige da sauri tana dan haki a hankali tana duban mutanen ciki ta furta" Barka da safia"


Docter Aliyu , da sister Bahija ne suka amsa, Sister Bahijar na rike da wata yar akwati baka a hannunta tana duban Khausar sunna dan jiran ta danna wajen da zata sauka dan ya rufe su tafi ta ce" Dubiya kika zo ne? A wani etage zaki sauka ne? Yi ki danna muna tare da Sir muma bangaren dubiyar muka nufa"


A hankali ta ji gabanta na neman yankewa ya yi faduwar da bata taɓa ji ba, sakamakon mutumen dake tsaye ya bada baya ya dan juyo , ashe waya ce yake amsawa , fuskar nan tasa cike da kamilalan saje, bakinsa dan ciwat da shi, idannuwansa dauke da farin tabarau, rigar jikinsa baka ce sidik sai abin wuyansa ruwan kasa mai duhu, ama rigar da wani tsabar sabon salo da rashin jin magana boturanta uku reras a bude suke, da hannunsa daya yana dan alamun balawa yake yi, watau ya fito ya ratso doguwar tafiyar nan bai Bala ba sai a nan, hannun dake rike da wayar kuwa agogo ce shekekiya dai Wali take irin na rashin mutuncin nan Wada ke nuna wanke hannunka ka taba ne ya wani kafeta da duban da ta tabata shima bai zaci ganninta ba da bai dubeta ba dan abin kunyar da aka launa masu su , wai su din nan


Da karfi KHausar ta juya bayan ta zarro ido jikinta na rawa ta saka kafa ta fita daga lft din da gudun balaki ta saki yar wayar salular Tata a nan da rigarta ta Nurse ta karasa bakin matatakalar hawa ta zauna tana haki zuciyarta tamkar zata buga da tashin hankali


A hankali ya lumshe idannuwansa, ya dan girgiza kansa da idannuwansa ya yiwa docter alamun ya rufe su tafi, sannan ba nuna kyankyami ko wani abin ya duba ya dauki wayar nan da rigar daidai abin ya tsaya ya fice gaba sunna biye da shi ya yiwa sister Bahija shiru a lokacin da take tambayarsa ya bata kayan ta rike, dama kayansa ne a hannunta, ama ya yi kamar kurma yake ya bude dakin da Yumnah take ya shige


A bangaren Khausar kuwa hannaye ta saka ta talabe tana jin tsararen kukan dake neman zuwar mata


Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, yanzu itace take tsoron kallon besty? Ita da ta zo da kudirin su hadu ta sanar masa su fa samawa kansu mafita tun wuri? Shin yaya zata fara masa zancen nan ne? Ta tabata shima abin ya wuce tunaninsa, ina ita ina shi? Me zata ce masa ne? Kai bari ta mike ta je ta yi jiransa kofar office dinsa su zanta, ya bata takardarta ta koma ta kaima Aba, wannan magana ta Aba cewar a zauna da wahala Bama zata iya zaunawar ba gaskiya


Tana mikewa ta ji ana fadin".......


























☹️☹️☹️☹️🙃🙃🙃🙃🙃🙃🙃


💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔




*DA CIWO A ZUCIYATA*




💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 4️⃣5️⃣


*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*


1: Duk karyar kada


2: Yar mahaukaciya


3: Neman na kaina


4: Bani da zabi


5: Bak'a ce


6: Kutkale


7: Makauniya ce


8: Mage


9: Duk nisan jifa


10: Idan ka raina inda kake


11: Dutse


12: Alkalamin kadarata


13: Bani da zabi


14: Dakika Biyar


15:Wata kokowar


16: Aure yakin mata


17: Ni zan ladabi


18: Daga tafia daukar soja


*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃






Ta ce" Khausar Muktar? Alhamdulilah, zo maza kama wannan ki hau cen dakunan VIP ki jona mata wannan allurar, yi gagawa zan kai hoton cikin da akai mata ne waje Docter tana jirana, kar sai na je na jona mata ruwan kuma ran sir ya bace"


Magana take yi da dan gagawa da alamun azalzala , sai kuma ta dan dakata tana kallon KHausar din


Da dan mamaki ta ce" Ke wai lafiya? Ina rigarki da takalmin ki na aiki? Ko dubiya kika zo yau?"


Da sauri Khausar ta girgiza kanta tana kama kanta ta ce" Aa aunty kayan na bari a adaidaita sahu shine nake jira a kawo min"


Kai ta dafe, sai kuma da dan sauri ta cire Tata farar rigar tana mika mata ta ce" Saka bani abayar nan ki je ki yi aikin nan Ni inada wata a office dina in an kawo maki taki kya kawo min"


Tana fada ne tana taya Khausar cire abayar jikinta, da sauri Khausar ta dora rigar auntyn tasu ta tare kwanon silbar mai dauke da maganin ta sakarwa auntynsu abayar da ta ɗora saman riga da sket dinta sababi masu masifar kyau wa'inda suka kama jikinta dasss da su


Juyawa ta yi ta koma lft din tana adu'ar Allah ya sa har ta gama ta koma kar su hadu da shi, ta fi ganewa ta tarda shi da kanta


Lft din na tsayawa ta fito a nutse ta nufi VIP na dakunan ma'aikatan asibitin a ranta tana tunanin waye ba lafiya a cikin ma'aikatan asibitin, dan kuwa waje ne da ake saka manyansu ko ahalin manyansu


Tana daf da karasawa dakin ta dubi madubin dake ajiye sai walwali yake


Gabanta sai da ya yanke ya fadi, a dan rikice take kallon kanta tun daga sama har kasa,
Watau dama aunty ba wani tsayi ne da ita ba, kuma tana da jiki hakan ya sa rigar Tata ta shigi Khausar, sai dai ta je cen daidai da dima diman cinyoyinta ta wani hau take budewa idan tana tafiya


A raunane Khausar ta hadiye yawu mai wahala tana jin nauyin shigar Tata, da dan sauri ta karasa kofar dakin ta ayana magana kamar haka' zan shiga in yiwa marar lafiyan allurar sai in koma gida, idan na je sai in dauki wayar Baba in kirashi mu yi magana kawai, sai ya zo mu daidaita ya bani takardar kawai'


A nutse ta bude dakin bayan ta dan buga kadan sannan ta yi salama kasa kasa sosai, dan wannan din shine dabi'arta, koda tana likita tana kiyaye hakin mutane, bata cika irin shigowar nan kai tsaye fuska daure ba ta wasu likitocin, takan dan buga ta dan yi jim, sannan ta bude ta shiga da sallama a hankali duda ta san nurse zata tarar sai marar lafiyar dan kuwa yanzun ba lokacin shigowa gannin mararsa lafiya bane, sai an jima kusan sha biyu na rana ake budewa a bada damar ziyara, karfe uku kuma a rufe sai shigar sasafe karfe shida zuwa takwas rufe


A hankali ta ja ta tsaya idannuwanta suka sauka a kan fuskarsa da kuma wace ke kwonce tamkar babu rai a jikinta, ga dukkan alamu barci ne take yi mai nauyin gaske


A hankali Khausar ta lumshe idannuwanta gannin shi bashi da niyar kautar da nasa duban a kanta, kamar yadda ya saba a da cen, a kanta yakan dan jima yana kallonta , sai dai a da din bata dauki haka a bakin komai ba, yanzu kuwa sai take gannin hakan bai dace ba


A hankali ya dan yi gyaran murya ya mike daga saman kujerar da hannunsa ya mata alamun ta yi aikinta sannan ya koma bayanta sosai ya tsaya ya dauke kansa a kanta dan ya san wacece ita, bale sabon yannayin da ya ga ta ara tsaf take iya juyawa ba tare da ta yi aikin da ya kawota ba


Jiki ba karfi ta ajiye kwanon, sannan ta duka ta tsayar da gudun karin ruwan, ta daidaita allurar da ruwanta ta bude wajen da aka jona karin ruwan a hankali ta rike tsintsiyar hannun Yumnar ta shiga zuba mata ruwan allurar a hankali a hankali tana dan duba yannayinta domin allura ce mai zafi ba'a zugata zuuuuuuu ta tafi, kuma tana iya taba numfashin mutun ko ta saka shi amai ko muguwar juwa shi yasa ake yi a hankali ana hankalce da motsin mutun
Sai da ta gama saka mata ruwan allurar sannan ta maida mata karin ruwan


A hankali ta juya tana dan duba dakin dan gannin abin auna bugun zuciya


Dayan nan dai na wuyansa shine, ita kuma nata yana cikin rigarta da ta yar a cikin lft


Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta karfafawa kanta gwuiwa cewar Besty ne fa, TAUFEEK ne fa, dilla menene a ciki


Ba tare da ta sake saka tsoro ba ta nufe shi tana aro jarumta tana yafawa kanta ta ce" Shin me yake damun Yumnah ne? Ban san bata da lafiya ba, dan bani abin nan na ga bugun zuciyarta"


Maimakun ya bata abinda take nuna masan sai kawai ya kama hannunta kiiiii ya fice da ita daga dakin


Jefa kafa take yi gabanta na faduwa domin bata san ina suka nufa ba, kuma irin yadda fuskarsa ta dauki ja alamun ransa a bace ko menene sai ta sake tsorata ainun har suka shiga lft suka sake hawa sama cen wajen office dinsa
Ko da lft din ya tsaya hannun nata ya cika ya yi gaba yana kunce abinda ke daure a jikin rigarsa na wuyansa dan ji yake yi tamkar zai tsaida masa numfashinsa ya dadana code din kofar office dinsa ya shige lokaci daya ya dauki commande din camarar bangarensu ya sakata a halin duhu sannan ya kurawa kofar ido yana jiran shigowar ta


KHAUSAR da ta gama summa a tsaye da kyar ta cira kafarta ta karasa office din


Rana shigowa ta ajiye farar rigar aikin domin itama du a rikice cire rigar ta yi ta tunkaro kusa da table din da yake tsaye kanta tsaye tana dubansa idannuwanta na cikowa da kwallah ta ce" Kana tunanin laifina ne?, TAUFEEK kana tunanin nice na saka su Aba aikata aikin nan?, Walahi walahi ban sani ba, nima na san ai na wani hadi, in kana tune ka min alkawarin kasancewa da Ni har a Daura aurena da .........."


"Khausar Please cn U be quiet?!" TAUFEEK ya fada a kasashen da ya saka Khausar zuba masa ido tana jin tamkar zata kifa a tsayen da take , shin yaya zata kwatanta masa cewar ba fa ita tace a daura mata aure da shi ba?


A nutse yana binta da kallo ya ce" sai yaushe zaki fara jin maganana ne? Menene wannan shigar? Ina hijab dinki? Me yasa kike son daukan dabi'ar da zata ringa bata min rai? Babu ruwanki a gaban kowa sai ki arta a guje ? Kina kallo muna tare da docter kika wani fita da gudu menene haka ne?"


Da mamaki take kallonsa, sai kuma ta kalli jikinta


A hankali ta shiga juyawa a gaban nasa har sai da ta juyo tana fuskantarsa a sanyaye ta ce" Menene laifin shigata? Me yasa kake son min fadan shigata ne bayan na san cewa harda ita a tsaikon samun mijina yanzu na kare da ......"
Ta yi shiru sakamakon zuba mata jajayen idannuwansa da ya yi yana sauraronta


Gannin ta yi shiru a hankali ya ce" Kika kare da me?"


Khausar ta dafe gaban goshinta, a hankali ta ja kujera ta zauna sannan ta mika hannunta ta kama bayan hannunsa dake jimke saman table din a tausashe dayan hannun nata kuwa ta bude abinda ke ajiye ta ciro tisu fari ta nufi gaban goshinta da shi a hankali tana share zufar da ta karyo mata kasa kasa ta ce" Dan Allah ka zauna, ka san ba son rikici nake ba, kuma baka san abinda ya faru ba ga dukkan alamu, ka zauna dan ina tsoron in na fada maka yanzu ka fadi, Taufeek its vry srius , ka zauna Please"


Hannunsa ya janye daga jikin nata, domin tunda ta dora din tana magana ne tana dan shafa bayan hannun nasa da sigar rarashi ba da wata manufa ba, wace sshi kuwa hakan ba daidai da yannayin da yake iya dauka bane


Da ƙafarsa ya dan tura kujerar baya ya zauna yana kallonta , a hankalin da sam bata so yana mata magana ya ce" Kika kare da me? Tl me"


"Na kare da auren aminina, abokina, freind dina, TAUFEEK basu fada maka aurena da aka daura da kai bane ko menene na ga ba maganar kake min yanzu ba?, TAUFEEK ka san cewa wai ashe Ni aka aura maka.....?" Ta fada tana watsa hannayenta hadi da dan zarro idannuwanta alamun ta fada masa tashin hankalin nan


Bakinsa ya dan tabe yana kauda dubansa ya ce" Eh haka na ji"


Khausar ta girgiza kai ta ce" Ka ji? Kennan ka ji? Ya Allah, da ka san irin yadda na yi ɓaci a kwana biyun nan da ka sha mamaki, TAUFEEK aminina?"


TAUFEEK ya zuba mata ido, ya dora hannayensa duka biyu yana dubanta ya ce" Eh, sai aka yi yaya?"




"ka kuwa ji me nace ne?" Khausar ta fada tana dubansa


TAUFEEK ya dan dantse lebensa da dan jin yana daf da kowa a wannan dogon maganar da tarin raini ke jagoranta tsakaninsa da Khausar ya ce" Eh na ji me kika ce, an daura maki aure da Ni, Ni amininki, nace eh sai mene kuma?"


Baki da ido da hanci ta bude tana kallonsa har ya mike ya nufi wajen frij din office din nasa ya ciro faro ya bude ya sha ya ajiye sauran cikin abin zuba shara dan bai shanye ba wanda ya rage din kuma kadan ne
Ya karasa ya dauki suturarsa kala blu mai haske wando da riga irin na likitoci wa'inda yake shiga dakin tiyata da su ya bale boturan rigar jikinsa ya cire rigar


A zabure Khausar ta mike tana kawar da kanta, sai kuma ta koma ta zauna ta sada kan nata tana dadana yatsunta tana addu'a kunnayenta na jiyo mata motsinsa alamun harta wandon a nan TAUFEEK ya saka har ta daina ji idannuwanta a rintse zufa na neman karyo mata sai kuma ta ji maganarsa daf da ita , a kamilance harufan bakinsa ke fitowa yana dubanta ya ce" igiyoyin aurena uku ke wuyanki, ina fatan zaki kula ba tare da kin takura min tabatuwarsu a kanki ba!, Ki kula na kasance mai jinkiri sosai, inada hakuri sosai, ama a kanki babu abinda bai sameni ba......Please Khausar ki dan sanyaya mana tafiyar , ko ba komai kin ce auren hadi ne, shi kuma ai sai an zauna shi ko? Kin dai san Ni ba marar kunyar da zan cewa su Aba wai yanzu yanzu zan bijire masu bane, in ke wuyanki ya rika ki je ki fada masu kawai sai a duba a ga abinda ya dace a yi......., Khausar My wife.........


A dan zabure ta dago ta zuba masa ido
TAUFEEK ya dan dantse lebensa kadan ya ce" my wife bata da lafiya, kin san ciki ne da ita, kuma ina tsoron laifinki ne....... ki dan yi zamanki a nan har a tashi kin ji?"


Yana gama fada ya saka hular a kansa ya dauki glasss dinsa ya mayar ya ajiye mata iphone dinsa a gabanta sannan ya wuce a office din, du a kokarinsa kar a fahimci irin takaicin da ta shaka masa, da kuma tunanin mema take nufi ne yarinyar nan da shi har ya karasa dakin tiyatar da ake daf da yiwa marar lafiyan allurar kashe jiki gaba daya a saka shi a duniyar barci dan aiki ne zasu masa su ciro masa ciwon kansar dake kansa




Bayan fitarsa Khausar ta jima tana kallon hanyar da TAUFEEK ya fice, dan yana fita ya mayar da kofar ya rufe wanda ke tabatar mata cewar sai kuma ya bude da kansa koda zata iya fita


A tsorace ta maido dubanta kan hotonsa da yake matsayin zane a jikin garu ta zuba masa ido kirjinta na sama yana kasa


A birkice take tambayar kanta *ME KENNAN?*
















OHO☹️












*Promotion dinmu dai ana Tata yi, ana ta karba, ana ta yi, yauwa da 1k dinki za'a baki baki daya nvls DINA yar uwa, garzayo ki amshi naki ki more in sha Allah,😍😍😍😍😍😍😍💓💓💓💓💓💓💓🙃🙃🙃*


💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔




*DA CIWO A ZUCIYATA*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login