Showing 63001 words to 66000 words out of 186303 words

Chapter 22 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18762

kasa ta rasa, da dan sauri ta nufi bangaren TAUFEEK tana sake gwada kiransa ama abin haushi ba'a daga ba


A nutse ta dan buga kofar sannan ta kama ta murda da salama a bakinta


Fara'a ce ta yawaita a fuskarta tana kallon Yumnah dake tsaye wajen diner, jikinta daure da rigar girki, hannayenta da safar sauke tukwane, tana sanye da wando da riga , wandon da kadan ya dan dara gwuiwarta , rigar kuwa mai siririn hannu ta juyo ta zubawa Khausar din ido ama kuma bata amsa salamar da ta mata ba


A hankali Khausar ta dan dauke dubanta gannin yannayin shigar Yumnar tana dan murmushi ta ce" Matarmu, barka da dare, dan Allah ki yi hakuri na dame ki, ko freind na kusa?"


Yumnah ta kare mata kallo, ta dago ta watsar sannan ta juya ta ci gaba da gyaran diner dinta ba tare da ta abata amsa ba


Da dan mamaki Khausar ta dan juyo dan gannin ko dai bata bata jita bane??












*ALLAH BAI SAUKAR DA CIWO BA SAI DA YA SAUKAR DA MAGANINSA*


Ni ce dai Fareeda Abdallah, na sake dawo muku da tallen magungunanmu da zuwa yanzu bazan iya ƙayyade yawan waɗanda suka dace da biyan buƙata sanadiyyar amfani da maganinmu ba. Alhamdulillah! Ƴar'uwa ki gwada, wataƙila warakarki na tattare da maganinmu.
Haihuwa ce baki taɓa yi ba ko kuwa jinkiri kike samu sanadiyyar planning ko kuma haka kawai? Muna da ingantaccen maganin rashin haihuwa ga mace da namiji, wanda za ki bada sadakar 2k ga matsalar ko wane ɓangare. In sha Allah za ki dawo da godiyarki bayan amfani da maganinmu.
Sanyi (infection) ne yayi miki yawa yake saka ki ciwon mara, zubar farin ruwa, ƙaiƙayi, ƙuraje, ɗauke ni'ima, har ma ya saka mijinki ya dinga miki gani-gani saboda bakya gamsar da shi? Da naira 3k zamu haɗa miki magungunan da za kisha ke da Oga in dai kika yi amfani da su ku da sanyi har abada in Allah ya yarda.
Muna sayar da ingantaccen haɗin sabaya, wanda zai sa nonuwanki su cicciko, hatta fatar jikinki sai ta murje sanadiyyar shan kunun sabayarmu. 2500 bokiti 1litter.
Muna da maganin wankin nono ga mai ciki da mai shayarwa, wanda indai kikai amfani da shi yaronki zaiyi tubarakallah, ba ruwanki da laulayi. Muna da ingantaccen maganin Daji (Cancer), typhoid, maleria, yaron da yayi nauyin ƙafa, da sauran cututtukan da ban ambata ba.
Muna aika maganinmu ko ina tsakanin Nijar da Nigeria, ga masu buƙatar magani da gaske su tuntuɓeni akan lambar wayata 07039080978, ko 09077591726


Noted: *MAI SON MAGANINMU IDAN BA A KADUNA YAKE BA, SHI ZAI YI KUDIN MOTARSA HAR ZUWA INDA YAKE, BABU INDA BAMA TURAWA IN SHA ALLAH.....SAI KUN ZO*


💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔




*DA CIWO A ZUCIYATA*




💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 2️⃣3️⃣



LITATAFAN MARUBUCIYAR


Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃










Da dan Mamaki Khausar ta juyo dan gannin ko dai bata jita bane?, Sai ta ga aikinta take yi bata kuma bi ta kanta ba


Da wani mamakin ta dan sake dubanta, sai ta dan koma baya ta sake yin salama wannan karron da dan karfi


Sai dai abin mamaki bata ajiye maganarta ba ta ga Yumnah ta yi wani ecpression da fuskarta sannan ta dan ja tsakin da sarai ta ji shi ta saki abin zuba abincin dake hannunta ta juyo tana cire safar hannun nata ta dangwarar a nan da wani yannayi irin na wulakancin nan dake bayane ba a boye ba ta ce" Na ji ki, ban san inda yake bane"


Daga haka ta juya da saurin tafiya ta koma kicin


Baki da hanci ke bude Khausar ta rakata da kallo har bata ji takun saukowarsa ba sai muryarsa da ta ji ya ambaci sunnanta yana idasa saukowa da mamakin ganninta dashe a nan baki bude


A dan tsorace ta juyo da madaukakakin mamakin da bai barta ba ta zuba masa ido, sai kuma ta dauke dubanta a kansa na tsarewa da kallo, domin farar riga ce a jikinsa ama botiranta a bale sai ash color din snglt a ciki mai siraran hannu , hakan ya dan bayana wasu sashe na sirrin jikinsa wanda bata taba ganni haka kai tsaye ba


Hannunta na dama ta saka tana dan murza goshinta cike da shiga rudu da kuma yar kunyar yannayinsa ta dan juya ta ce" Am, barka da yanzu, dama ina kiranka ne baka daga ba sai na zo , Mujaheed ne ke cen kofa nake so idan ba damuwa a shigo da shi ko a fada masu na leka ......???"


Ta idasa maganar tana dan ajiye zancen da dan sake duban hanyar kicin din nan


"Ok" kadai ta iya ji daga bakinsa, sai kuma ta ji yana magana da waya cewar a bar bako ya shigo a nan kofar gidan


A hankali ta dan juyo dan yi masa salama, sai ta ga ya bala boturan, hakan ya sa ta samu sakewa ta dan dube shi ta bi wayar dake hannunsa da kallo, wace ta tabata itace mai dauke da numbar da ta yi ta kira tun dazun bai daga ba, ta so kwari yi masa korafin hakan, sai dai wani abu da ya dan tsaye mata a kahin zuci na yannayin da matarsa ta yi yanzun ya dauke hankalinta, a hankali ta juya ta ce" Thank you" sannan ta yi waje




Kansa ya mayar a zaunen da yake jikin kujerar ya lumshe idnanuwansa


Shin ta ina zai bi ya raba wannan alaka? Barin wannan alaka dan ta ji dadi anya daidai ne?
Idan ya yi duba da tarin abinda ya sani shi a kan manemin auren aminiyarsa kuma kanwarsa in ya yi shiru ya yi mata adalci daga ita har iyayenta kuwa? Shi dai ba abikin yin Mujaheed bane, abinda ke iya sab hanyarsa da tasa daya ce tak idan shagonsu na son sari a kampani, bayan wannan babu ta inda wani abu zai iya hada su, da ya dan kwatanta ganninsa sun zanta a kan lamarin......, A gaskiya baya tunanin in har zai iya yin hakuri ya zuba ido KHAUSAR ta auri mutun irin wannan bayan du irin wahalar da ta sha ta rayuwa a kan wannan subjet na mijin aure ba
Kwata kwata shi din ba mijin mace irinta bane
Ba dan aljihunsa ba ko yannayinsa ba, sai dan Halayarsa da suke boye wajen yan mata ama suke bayane wajen wa'inda suke iya sani


"Honey, na kawo abincin nan ne?" Yumnah ta katse tunaninsa da sanyayar muryarta da yannayi irin na macen dake gabar son birge abin birgewarta


Idannuwansa ya lumshe a kanta , sai kuma ya mike yana dubanta ya ce" Ina zuwa Yumnah"
Daga haka ya nufi hanyar fita a falon


Da ido ta bi shi, kirjinta na dokawa da tunanin ta yiwu wancen abar zai bi?
A hankali ta silale saman kujera ta dafe gaban goshinta da hannayenta bibiyu tana tunani, tunani take yi anya kuwa tana cikin hanyyar da zata kubuta daga wannan mugun abin dake faruwa a aurenta? Duka duka yaushe aka yi auren ama ita ta hadu da kalubalan zaman auren fiye da tunanin mai karatu, babu lokaci idan wannan mata ta nemi layin mijinta yana iya amsawa, babu lokaci idan ka ganshi kana iya ganninsu tare, ba dangin iya ba na Aba an kwaso katuwar mace an kawo gidan da mijinta yake da ta dan nuna sai ya nuna tamkar yar uwarsa yake kallonta? Anya ba zata yi tashi irin na kirki dan gannin ta samarwa kanta mafita daga wannan abin ba? .....da wannan bacin ran ta yi zamanta a nan tana neman mafita da tunaninta


Fitar da ya yi shi kuwa bangaren iyayensa ya nufa , domin tunda ya zo bai shiga ba, ashe rabon ya tarda abinda yake faruwa ne, rikici tsakanin iyayen nasu , Hajia na zaune tana ta kashe wuta tana fada domin mahaifinsa baya nan


A hankali ya fice a falon, ba dan komai ba sai dan gannin halin da suke ciki, ya tabata in dai yace zai zauna to yana iya haduwa da bacin ran da zai saka ya kasa hakuri
Sometimes, yakan ji kamar ya dauki mahaifiyarsa ya kaita nesa da wannan rayuwa, ama idan sun kadaice sai ta ringa kwatanta masa cewa wannan din ba damuwarsa bane tsakaninta ne da matan mahaifinsa, ya barta zata iya kwatar kanta tunda ita ba yarinya bace, kuma zaman aure take yi dole zatana haduwa da kalubale na yau da gobe, shi dai ya ci gaba da addu'a ya kuma kiyaye huldarsa ta yai da gobe da kowama




A bangaren Khausar


Tunda ta shiga motar bayan ya nuna mata cewa in bata shigo ba a ina zasu zanta? Duba da bata kawo masa kujera ba kuma bai ga wajen zama ba, kanta ke kasa tana sauraron irin tarin mitar dake bakinsa da kuma rikicin dake cikin bakinsa


Gaba daya rigimarsa idan ya jema ya dawo a kan TAUFEEK take sauka, hakan sai yake bata mamaki, ama ta nutsar da tunanintaa tunawa da wasu kalaman da ta ringa haduwa da su cewa dole fa zata iya haduwa da haka, ba kowaki namiji bane zai yi hakuri da mu'amala irin wannan dan haka a sanyaye yau ta budi baki bayan ta dago ta masa duba kamar sau biyu ta ce" Na san ba zaka taba yarda cewa mu'amalata da TAUFEEK zumunci ne kawai ba Elhaji, ka sani zumuncina da shi ya hada zumunci da iyayenmu, ko yanzu da ka ganni a gidansu Hajia ce ta zo da ni, a bangarenta nake kwana ina tashi, bayan wannan Elhaji maganar mu'amalata da TAUFEEK a yanzu da nake budurwa take da karfi, idan na yi aure du abinda mijina ya shinfida min ai dole zan yi biyaya in dai hakan bai sabawa adinina ba, dan Allah ka yi hakuri ka cire wannan magana daga ranka kwata kwata"


Har ga Allah, bai taba jin salama a maganarsu kan TAUFEEK ba irin nna furucinta na yau, ko dan ya kasance mutun mai son a girmama shi? A yanzu yana jin zai iya tunakarar wannan masifafiyar matar da ya kakabowa kansa take neman hanna masa rawar gaban hantsi, mace sai fitina, mace sai neman fitina, yanzu abinda ya fi jin tsoro maganar nan, da ya kwatanta ashariyar da ta dura a kan yarsa sai da cikinsa ya juya, ama abu daya ya sani ita din mayar kudi ce, zai kwatanta lasa mata zuma ya san da wahala ta iya kin amincewa da maganar auren nan, shi fa har mafarkin Khausar yake gashi ga ita matsayin matar aure, kuma ya tabata da wahala matarsa ta fi karfin Khausar dan kuwa in me take takama a jikinta Khausar ta damata ta shanye


"Mun yi magana da Aba, Aba ya nunan bacin ransa dan na je jiya da jus, yace baya son haka kar na kuma, sannan ya min maganar na fito idan da gaske nake" Ya fada yana dubanta


Khausar ta dan dago ta dubeshi sau daya ta sake dauke dubanta a kansa, a ranta tana tunanin yauwa ga abinda ya hasala Aba, dan ya masa magana ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ama shi kamar baya jin me ake nufi da kar ya yi


Ya dan sake muzgutawa irin rikakun mazan nan da suka isa da gidansu ya ce" in sha Allah karshen watan nan za'a kawo sadakina, shikenan zaki zama tawa ko Khausar?"


Khausar ta sake sada kanta, tana jin wani abu na dan ratsa zuciyarta mai shige da salama


A hankali ta ringa jin kamar wani abu mai kama da kwonciyar hankali da nutsuwa na game zuciyarta, har dan murmushi ya wanzu a saman fuskarta ta yi gagawar rufe fuskar cike da jin kunya
Hakan ya sa ya sakota a gaba da zolaya dan ya riga ya sani Khausar akoy kunya kamar me


Da wannan ta masa salama ta koma ciki, shi kuwa ya juya ya tafi daga gidan yana sake kallon gidan da gyada kai, shi da kansa ya san nan ana magana ne ta babansa ba wai yayansa bama a dukiyar, zai yi gagawar dauke matar nan ko dan ya ringa fada a cikin maza cewa ya yiwa ELHAJ TAUFEEK kwacen mace.....


Da Khausar ta koma bangaren Hajia ta tarda ita zaune saman kujera da waya a kange a kunnenta


Zama ta yi bayan ta cire hijabin na Hajiar a kasa daf da Kafar Hajiar ta dan kamo kafar tata ta shiga matsa mata a hankali a hankali


Jim kadan Hajia ta gama wayar ta dubeta da murmushi tana amsa gaisuwarta kafin ta ce" Kin zo bana nan, da na dawo kuma sai wancen yar tace kin yi bako, wanene ne ?"


Khausar ta sada kanta tana dan murmushi ta ce" Hajia, wanda yake zuwa wajena ne "


Hajia ta dan yi shiru tana kallonta, a hankali ta ce" A ina yake, menene sana'arsa? Saurayi ne ko magidanci?"


Khausar ta dan sauke numfashi a ranta ta ayana' To Fa Allah ya sa kar a koreni dan haushina'


A nutse ta sanarwa Hajia amsar Tambayoyinta


Hajia ta dan tabe baki tana fadin" Ni fa ban cika son namiji mai kai kawo ba kamar mace, to me yake jira da bai fito ba? In fa baya yi karma ya nemi bata maki lokaci a banza a wofi, gwara ya gusa wani ya shigo!"


Khausar dai kasa cewa komai ta yi, Hajia ta janye kafarta da kula ta ce" Tashi ki je bangaren iyayenki, in kin samu wani a falo ki gaishe shi ki haye sama wajen Mamanku tana kiranki"


Mikewa Khausar ta yi ta dauki hijabin ta saka sannan ta tafi


Da kallo Hajia ta rakata kafin ta dauke dubanta ta dan sake lumshe idannuwanta tana ci gaba da jan carbinta
Sai dai a kasam zuciyyarta wani abu ke damunta ainun dangane da matan yaron nata, akoy wasu furuci da ta tsinta a yau din da suka tsaye mata a kahon zuka, sun mata bake bake har sunna son hannata wani abin cikin walwala,
Ita dai yar hausa ce bata cika daukan magana a shantakai ba, magana kuwa irin ta gannin baya bata cika sonta ba, shi yasa ta shiga a hali na tunanin shin zafin kishi ke damun matar ko harda matsala wata daban?......
(Wannan kennan)


Khausar jiki ba laka ta karasa dakin Maman TAUFEEK , sakamakon irin amsa gaisuwarta da mutanen nan suka yi a lokacin da ta shigo da yar fara'arta


Ta samu Maman TAUFEEK din saman salaya ama kuma ba sallah take yi ba, tana dai jan carbi ne


Da fara'a sosai a saman fuskarta take amsa gaisuwarta sannnan ta mata nuni da wajen zama ta karasa adu'arta ta shafa ta juyo fuskarta a sake ainun ta ce" Khausar yaya bakunta ya fama da kakar taki?"


Khausar ta yi yar dariya ta ce" Alhamdulilah Mama"


Mama ta mike tana nufar wajen wrdrb dinta ta bude tana fitar da wasu manya manyan ledoji masu dauke da sunnan wani rantsatsan kampani da ake yayi a garin masu kawo lesuka da atampa da shada da kuma abayoyi ne su mayafai dai da sauransu


Ajiye su ta yi nan bakin gado d taimakon Khausar sannan ta shuga fitar da su da kula ta ce" Na cewa aminin naki gobe ba zaki je asibiti ba dan ina so mu fita, ya so ma ya kiya dai na fada masa ba fa zaki je ba ya sanar masu dan zamu je wajen mai dinki da kuma shagon Hajia FUSAM mai turaren wuta"


Maganar cewa ya sanar ba zata je ba ta so ta dan sakata a tunani, sai dai maganar sako sunnan FUSAM ya cire mata tunanin da dan mamaki tana bin rantsatsun atampopi da lesukan da Maman ke fitarwa da kallo ta ce" Lah Mama kin san Fusam kennan?"


Mama ta yi murmushi ta ce" na san Fusam Daughter ai wajenta nake siyan turarukana, yaya kika ga lesukan nan sun birgeki kuwa?"


Nan fa ta ringa shafawa tana fadin cewa babu na yarwa baki daya sun tafi da ita tun daga yannayinsu da color dinsu a kalla sun kai goma ko fi dan ba irgawa ta yi ba ama kuma sun rikitata
Itama Maman ta ji dadin haka, dan haka ta umarceta kan ta je da su bangaren Hajiar gobe sai su kai dinki in sha Allah, harda dorawa da fadin a ciki abinda bai mata ba sai a cenzo mata dan a online ne ne ta yi siyayar


Mamaki, tsoro, rasa abin cewa ya saka Khausar sake tambayar Mama wai tana nufin nata ne?


Mama ta gyada kai tana mayar da su ciki harda mayafan yan yololuwai da su domin shara shara ne ama rantsatsu irin na yan gayun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login