Showing 72001 words to 75000 words out of 186303 words

Chapter 25 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18776

ta ja numfashi ta ce" suka kakama tasa da kawarta suka hanata dukana...."


A hankali ya bude idannuwansa dake dan lumshe kasa kasa ya ce" uhum, shine kike kuka ? Khausar tsoro gareki ko? "


"Ni ba kukan dukan nawa bama nake yi, yanzun kukan kuma yaya zan yi naa samo wanin nake yi ai TAUFEEK " ta fada a sanyaye tana rafka tagumi hadi da zubawa kofar dakinta ido


Ya dan dauki lokaci bai yi magana, daga bisani ya ce" Khausar duka dukanki shekarunki nawa ne da zaki takurawa kanki haka? Kin cika saka damuwa a lamarinki Khausar bayan kin san komai lokaci ne ko?"


"A hausa? A shekaruna, a yannayin jikina kaima ka san ai na tsufa ban amsa kiran mai aure ba, duka duka tserayata da kai nawa ne? Kaima ka yi auren nan fa kai namiji bale ni?, Dole na damu Taufeek ""


" Ban ki ki damu ba, ko ba komai shekarunki da kike ikirari sun kai ki damun, ama kar ki manta Allah keda komai, ke kamar wace ta haife duniya in kika tashi zanen namijinmaa da kike so sai ki ce mai mace biyu ko uku haka, mai ya'ya ke ga wace ta gama zama uwar duniya ko?" Ya fada a dan kausashen da ya sakata jin kamar zata saki murmushi du kuwa da halin da take ciki


A hankali ya ci gaba da fadin" ki ci gaba da yin abunda zai fisheki, ki kwontar da hankalinki, idan kika gama wannan aikin daga cen zasu baki takardar asibitin da zata dauke ki, ba zama zaki yi ba aikinki zaki ci gaba da yi domin ko hutun kwana daya ba za'a baki ba......, Ki sani kowani bawa da irin kadarar rayuwarsa, Mujaheed bai kai ya sakaki kuka ba besty......"


A hankali ta ce" ka ce idan na gama za'a bani takardar daukan aiki? Kana nufin daga nan zan samu aiki?????"


Tabatar mata ya yi ba tare da ya ja maganar ba


Da sauri ta mike tana fadin" TAUFEEK kar ka min wasa mana, aiki fa kace? Aiki aiki dai? ....."


Amon muryarta na nuni da zumudin dake cikin zuciyarta, hakan ya sa ya dan rage bada tabacin dake harshensa ya ce" komai ai na Allah ne, akoy kyakyawar fahimta tsakaninsu da Aba, kuma tunda ya sama maki stage din nan yace min kina gamawa za'a kaiki asibitin da taa daukeki, ko nan din ko wani wajen"


"Wayo allahna, INNALAHA MA'ASABEREEN...." Ta furta a sanyaye tana sauke zazafan murmushi mai gauraye da tarin farin ciki


A hankali ta ce" Hakan na nufin, zan samu aikin yi nima, na zo ina taimakawa su Mama ko????????"


πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”β€β€πŸ©Ήβ€β€πŸ©ΉπŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”




*DA CIWO A ZUCIYATA*




πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”β€β€πŸ©Ήβ€β€πŸ©ΉπŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 2️⃣6️⃣



LITATAFAN MARUBUCIYAR


Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicΓ©
Lait de nuit
Parfums dΓ©sodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaΙ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiπŸ’ƒπŸ’ƒ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙ“i wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan MataπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ








Wannan karron bai bata amsa ba ta ci gaba da fadin" TAUFEEK, ban san harshen da zan yi anfani da shi dan yi maka godiya ba, TAUFEEK haduwata da kai alkhairi nake ta gani a koda yaushe, ina jinka a raina tamkar dan uwana na jinni, sanadiyarka nna hadu da haske kala kala, TAUFEEK duba ka gani yadda Hajia ta daukeni, yadda Mama ta daukeni, uwa uba gashi yanzu Aba ya sama min aiki, ka ga ko nawa nake samu a wata fa hakan na nufin zan iya kawo baban talafi wa ahalina harma nima na yi kyauta na yi sadaka ko? Irin nima ma'aikaciyar nan har na siyo kaji birjik a yi washa washa a gidan nan ko..?????"


"Khausar" ya fada a cen kasan makoshinsa


Khausar ta dakata daga share hawayen ta amsa itama a cen kasan makoshin nata


TAUFEEK ya yi dan murmushi ya ce" ki daina kukan mana, baki san bana so ba?"


Khausar ta saki murmushi hadi da sakin hawayenta ya gangaro ta ce" To, na daina TAUFEEK....."


Ya yi murmushi ya ce" Bana so na ji wani kukan a kan wancen kin ji?, Sannan a koma aiki gobe bana son wasa da aiki fa"


Khausar ta yi yar dariya tana fadin" in ji wanda baya tsayawa ya yi jarabawa, TAUFEEK jira nake a koma makaranta zaka sha matsi dan ba zan taba barinkaa ka sarara ba sai ka ciyo min takardar nan in sha Allah "


Shima murmushin ya yi yana jin dan sanyi a ransa jin zata dawo normal, watau besty dinsa mai rigimarsa wace shi kadai ne bata tsoro ama sauran al'uma du tsoronsu take


Da wannan suka yi salama, itama har ta je ta samu iyayenta ta sanar masu wani abun farin cikin, wanda ya dan sanyaya zukatansu baki dayansu


Washe gari da sasafe ta yi tafiyarta wajen aikinta, anguwarsu kuwa a ranar wuni aka yi ana shafa wannan labari, guri guri har bayan layinsu sai da zancen ya kai , yawancin mutane fadi suke madallah dama da ta ki aure ai ba wani abu bane dogon buri ne ita likita sai mai kudi zata aura, wasun su ce yawace yawacenta da ya yi yawa ai dama da wahala ta auru, wasu suce sa dai ga karyar boki ita yar boko uba da uwa sun daure mata, daidaiku ke jimamin lamarin da fatan Allah shi kyauta domin irin anguwar nan ce da daidaya ne suka tsira da boko su dinma maza ne, ita din ce kawai ta yi dogon karatu irin na asibiti da bashi da lokaci har ta kai warhaka, a yanzunma da take aiki irin na gadi wanda take kwana a cen an sha ceece kuce, mahaifinta ne kawai mutun mai ra'ayin kansa, ya kuma yarda da yarsa, da ba wannan ba da tunima an saka ya cireta a harkar karatun




Sannu a hankali Khausar ta gama watani ukunta da ta dauka a babar asibiti bangaren emrgency


A wadinnan watanin uku da ta yi tun daga kan mai gadin kofar asibitin har zuwa manyan ma'aikatan babu wanda zai ce ga abinda ta masa marar dadi ko na raini ko aka kamata da wasa da aikinta ko kula samari ko dai wasu halayan mararsa dadi, ko gadi Khausar take yi ba zaka ga saurayi ya zo wajenta ba, haka kuma manyan doctors dake aiki maza wa'inda suke da dabi'un kula mata babu wanda ya matsewa Khausar waje dan sun san da sunnan wanda ta shigo wajen, watau ubansu ne idan suka yi wasa komai na iya faruwa, mutumen da yake abin wasa a wajenta su dodonsu ne




A ranar da ta gama harda dan hawayenta , a lokacin ne aka tabatar mata kwana daya tak take da shi na lahadi ba zata je aiki ba, likiti ta tabatar ta tafi tunda sasafe babar asibiti mai sunna *LAFIYA* wace aka ce nan ne zata je ta yi aiki a matsayin ma'aikaciya


A ranar farin ciki a gidansu ba'a magana, ta nemi layin TAUFEEK har ta gaji da nema bata same shi ba, ta so tafiya gidan a washe gari sai dai kitso da wankin kafar da ta je da kuma wajen Fusam dan amsar wasu yan kayayakin gyara a dole ta yi dare bata biya gidan ba, ama ta ci gaba da neman layinsa cike da mamakin rashin samunsa , sai da dare ya yi ta hakura dan yanzun in dai ba shi ya yi kiranta da dare ba to fa bata kiransa dan har yanzu bata gane manufar matarsa a kanta ba


Shi kuwa a irin lokacin da take nemansa wayarsa sam baima san inda take ba, aikin da ya gagabo masu shi da manyan ma'aikata suke kai, watau tantancewa da fitar da kwararu masu son aikinsu da kyma ware maus shiririta ciki harda asibitinsa clinik dinsa privet mai sunna *LAFIYA!* wace a gobe litinin yake da niyar shigarta da karfinsa dan ba zai taba lamunce abubuwan nan ba, manya manyan abubuwan dake hargitsa shi a aikinsa shine likitan da bai iya aiki ba, yana iya yin komai a kan haka, shi yasa yake da taka tsantsan da tsauri, dan a ganninsa du ma'aikacin jinya ko na dabobi ne ya dace ace kwarare ne a fannin aikinsa ba haure ba, dogon aikin da ya saka shi bada kamar shekara da shekaru kennan kuma bai ga alamun zai daina yanzu yanzu ba


Tun karfe bakwai Khausar ta gama shiri mai sunna shiri, shirin da Mama ke binta da kallo cike da mamakinta da kuma addu'a a kasam zuciyarta, domin bata taba gannin yarinyar ta yi shiri haka ba,


Ba wai makup ta makawa fuska ba, ama ta saka kwali daidai misali ta kuma saka dan jan baki mai ruwan kasa dan daidai da lebenta na kasa
Girarta cajeta ta yi sosai, kitson da kai mata kuwa sai ta daura ribom mai kyau ta daura dan kwalin atampar da ta saka doguwar riga wace Mama ta dinka mata sannan ta dora hijab mai ruwan sararin samaniya mai yar walwali a jikinsa sai jaka ruwan hijab din da takalmi plate ruwan hijab din sai dan mayafi da ta yafa wanda yake shara shara ne du girmansa dan ba abinda ya rufe a tsarin halitar jikinta wace zuwa yanzu tumbin nan gana dayansa ya sasabe ya mugin zube sakamakon wahalhalun da ya shiga da kuma dan hadin da take masa na bawan albasa da lemun tsami da cita tana sha wanda sosai ya sake sabe tumbin ama bayan tumbin babu abinda ya ragu kama daga duwawunta da cinyoyinta, sai gayu da ta fara koya na mamaki a wajen uwar gidanta docter Rauda da kuma hajiyarta Fusam, ga wani tsararen kanshi da take fitarwa mai sanyi ba mai hayaniya ba


Tsuru ta yiwa Mama cike da jin kamar a takure take ta juya tana fadin" Mama bari dai in dauko hijab, ga jakata da rigar aikina a ciki Mama"


Mama da dan sauri ta ce" Ke Khausar zo, me wannan din ya yi?"
Sai kuma ta yi shiru tana dauke kanta a ranta tana mamakin yau itace da cema khausar kar ta fita ba hijab????


Tana shirin ce mata ta dauko hijab din Aba ya shigo yana fadin" Ina Khausar din maza zo ga dan sahunki nan, shi zai ringa kaiki yana dauko ki, ki tabata wayarki da caji ga wannan katin ki loda dan kiransa in kina so ya dauko ki, ga kuma kudin abinci, a kula sosai yar albarka a kula bana son biye biye, bana son ka je aiki ka ringa abinda ba shi ya kaika ba kin ji? Ki kama mutuncin kanki kin ji ko?" Ya idasa fada yana riko jakarta dake gefen mamanta ya Sakkata gaba suka fita


Mama ta yi murmushi bayan ta rakata da addu'a ta mike ta shiga fitar da kayan abincin da aka kawo tana dubawa, harda su kwai da doya da su waken suya da madara, tunda ta kawo albashinta harda su kuka da mahaifinta ya raba biyu ya bata rabi wai ita bata son ko sisi, da kyar shima uban ya amshi duka, ama gaba daya kudin a hidinar gidan ya zuba su, ya siyo matta wata waya yar madaidaiciya da hijabai sababi har biyar, ya masu siyaya suma sannan ya daukar nata dan adaidaita sahu ya kuma ware kudin abincinta.....lalle a wata ukun nan sun mori albashinta sosai, ama na watan nan sun fi morarsa domin na watanin da suka shige a hidinar kannenta ta saka kudin kafff


Tunda aka ajiyeta a bakin makeken get din asibitin ya ringa taslima a zuciyarta, lalle a yadda ake kwatanta masu asibitin nan ba'a fadin ainahin yadda yake


Tafe take tana tambayar baban wajen reception har ta karasa tana karra bin komai da kallo tamkar wace ta fita daga kasar ta je kasar turai


Madubai ne, shukoki ne, ma'aikata ne sunna ta aiki sai sake gogewa ake yi bayan ba wani dati da wajen ya yi , haka kuma komai a tsare ga kanshi dake tashi ta ko'ina


Ajiyar zuciya ta sauke cike da samun kanta a rudu, yanzu a nan ne zata yi aiki? Ma'aikatar da akace gagaruman likitoci ke cikinta, du wani likita mai ji da kansa kana samunsa a nan cikin sauki, to ita a matsayin yar goge goge ta zo nan ko
Da ido take bin masu aikin, sai ta samu kanta da jin sanyi sanyi da ta saka sabuwar atampar nan, yau da ta rasa wajen buya da bata dan kimtsa kanta ba


Wata mata mai riga ruwan goro ce ta kula da yadda Khausar ke bin mutane da kallo ta dasu a waje daya tunda ta shigo baban filin dake rarabe da mutane daban daban kowane a bangaren da yake nasa aiki ta tunkarota tana tambayarta ko ta bata ne?


Da dan barin baki Khausar ta mika mata ambulop din da aka bata tana binta da kallo, ita kanta mai wanke dakin masu haihuwar nan sai ta dauketa aiki jama'a, kwas kwas da ita harda farin gilas na yan gayu


Dubawa ta yi sai ta kalleta da sauri ta ce" Kai, to zo maza na raka ki sunna sama yau oga na tantancewa bakinma du sunna sama maza ciro rigarki saka mu je wajen chef sai ya saka ki bangaren da kike, Allah dai ya sa ki samu karbuwa dan baki taki Sa'a ba gaskiya a hasale oga yake kuma yau yake fara tantancewa , Allah ya da kin iya aiki yar nan, dan kuwa daya bayan daya sai kun saka ruwa ne da sauransu aikinku dai na likitoci....."


Cikin Khausar sai da ya amsa, nan take ta ji wani shaka da tsoro na neman aurar zuciyarta
Tantancewa, dama a makaranta ana cewa itafa asibitin nan ba'a wata ba'a yi tantancewar nan ba, tsaf ake iya cireka a maye gurbinka da wani ba wasa, shi yasa likitocin kowa ke aikinsa ba ji ba gani domin ko dan albashin wajen ba zaka yi sake a yi maka sakiyar da ba ruwa ba


Biye take da ita har suka karasa wani tankamemen hl wanda sunna shiga kanshin wajen da sanyin wajen ya sake sakata a hali na tsoro da tunanin lalle yau zata samu baban abu da ake kira ta leko ta koma, dan bata idasa fita a hayacinta ta ringa kallon mutane tamkar ba yan adam ba da irin tarin kayan aikin wajen sai da suka karasa aka amshi ambulop dinta aka duba aka yi mata tambayar ina kit dinta na kayan aiki irin su abin auna zuciya abin daukan zafin jiki dai da sauransu ta nuna shi hannunta na dan rawa aka umarceta kan ta fitar da su ta je ta layu wani bangare gefen hagu inda wasu bayin Allah ke laye kamar an masu mutuwa kowane na nazari da addu'a a zuciyarsa domin su kusan bakwai ne kuma dukansu baki ne yau suka fara zuwa asibitin


A kala sun dauki minti sama da arba'in ana ta karra gyare gyaren wajen
Ba wasa a lamarin
Kowa kai kawo yake cikin manyan har ta ga an dana wata katuwar tv ta nuna shigowar wasu motoci uku balbalin asibitin sannan aka kashe tv din aka sake tsatsaresu da duba kamar wa'inda suka aikata katon laifi duba irin na to fa ga maza bisa kanku, ya zamto harta manyan likitocin sun shiga taitayinsu sunna sake bin dukkan abinda suka san na iya zame masu matsala sunna tabatar da sun daidaita komai da komai


Minti kusan sha biyar kofar mai dauke da madubi ta wangale,


Shine a gaba, yana sanye da bakin wando dogo na sweet, sai farar riga kal a ciki sai cravate mai ruwan maroon da dan fari fari jikinta, sai rigar likitoci fara kal wace ta dan sauka har kusan gwuiwarsa kadan, sai abin awon bugun zuciya dake rataye a wuyansa, hannunsa na hagu daure da agogo kirar kampanin ROLEX na daman kuwa ya dan tatare rigar har zuwa kaurin hannun nasa wanda ya bayanar da jijiyoyin hannun rado rado da tarin kwarjini da fuzga irin ta cikaken gamsheken namiji ta tafi da tafia har ya karasa kusa da baban teburin kwalbar da chef ke biye da shi da sauran likitoci biyar mata biyu maza uku manya manyan likitocin da ake ji da su a kasan nasara biyu sai hausawa uku kowane cikin shiga tasa shima irin ta likitoci ya karasa nan suka dan zanta kasa kasa inda baka jin komai sai dan abin AC dake watsa sanyi domin ko numfashinsu ba fita yake yi da karfi ba


A hankali ya ajiye farar takardar da aka bashi mai dauke da bangare bangare na du wani ma'aikacinsa na asibitin nan harda baki ba tare da ya karanta ba ya mike tsayinsa a gabansu ya dauko dubansa tun daga cen kurua kurya ya ringa binsu da kallo a hankali har ya dawo bangaren da ake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login