Showing 129001 words to 132000 words out of 186303 words

Chapter 44 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18791

yi saman wando irin mai likewa a jikin nan da riga mai dogon hannu sai ta rufa mata alkyaba fara kall , ya zamto kanwar Mama rike da Khausar, su Rukaya sunna rike da wasu yan abubuwanta, Hajia Fusam na fesa turare a dukan tafiyarta, abin sai wanda ya gani daukaka Allah ya daukaka y'ar gidan Aba


A hannun Hajia aka damka KHAUSAR, bayan an dukar da ita ta gaishe da Hajiar
A nutse Hajiar ta bude alkyabar Khausar tana murmushi ta ce" Masha ALLAH khausara masha ALLAH"


A hankali Khausar ta fashe da kukan da take rikewa lebe har yana yi mata rawa a hankali ta dora kanta a cinyar Hajia wace ta kwashi salalami tana kallonta ta ce" Ke dan kaniya nan din ba gida bane? Ni kar ki sakani kuka bayan na dinka ba takashin kowa ba na buga daurin bando na rangada kwali abina kin ji ko?"


Mama ta saki murmushi, a hankali ta karaso daf da Hajiar ta zauna, a nutse ta saka hannunta ta dago Khausar ta saka tissu tana share hawayenta , da kula ainun ta ce" Ya isa haka mana, na san kukan ne kike ta yi tun safe ko? Tashi ku je ki huta, Allah ya maku albarka ya yiwa rayuwar aurenku albarka"


"Kai na Annabi yace amen!" Hajia ta fada tana kallon jama'ar dake daukan vidio ne, hoto ne, da masu amsa adu'ar, kai abu dai masha ALLAH, haka Hajia ta ja Khausar sauran na biye da ita suka karasa bangaren TAUFEEK kasa kasa tana fada mata magana kamar haka" ke yi shiru abinki, abinda an daina yayin kuka? Kuma yau din da na kawo ki nan dan gudun yan uba ne, gobe cen bangaren nawa zaki kaura fa kin ji ? Share hawayen kar ciwon kai ya hannaki rawar gaban hantsi!"
Da haka har suka karasa suka shigar da ita da addu'a aka haura da ita rantsatsen dakinta dake daf da na Yumnah aka zaunar da ita a gefen gadonta


Sosai danginta da yan rakiya suka yaba mutunci da karamcin ahalin mai kwanoni sannan suka tafi da addu'ar alkhairi suka bar Khausar na sauke ajiyar zuciya tana jin abin wani iri tamkar a mafarki


Ta dauki lokaci a zaunen nan har ta kage,
A hankali ta mike ta sauke alkyabar da aka naษ—a mata ta nufi wajen madubin dakin mai girma wanda gabansa ke cike da tarin turaruka na alfarma kala kala ta ja ta tsaya tana kallon abin hannunta da su zoben da aka saka mata


A nutse ta sabule alkyabar gaba daya ta ninke ta ja kujerar ta ajiye sannan ta zubawa fuskarta ido har zuwa tsarin halitar da Allah ya yi mata


Da kunya ta kauda dubanta, dan a kulun takan ji kunyar kirarta sosai, bata son tsarewa kanta ido dan abin na bata kunya, bale yau da aka yi mata kwaliya irin ta mata masu aji sai ta zama tamkar ba ita ba


Wandon ne na ciki baki mai santsin nan da kama jiki wanda ke rike cinyoyi taf, sai farar rigar mai dogon hannu itama a jikin take, sai bakin dan kwalin da aka yiwa dauri irin na zara Buhari daurin da ya hau kan kitsonta das ya kawata fuskarta da dan wajen gefe da gefen nan na mata mai kyau ya yi mata luf masha ALLAH, du kuwa irin kukan da ta sha hakan sai bai boye tsararan kyan da ta zuba ba a yau


Idannuwanta ta rintse sakamakon jin karar bude kofar dakin gabanta na dokawa, dan ko wanene a yanzu ya shigo bata raba dayan biyu ko matar gidan ko mijin matar gidan ne


Ta madubi ta dan bude idannuwanta jin ba'a yi mata salama ba, kuma kamar an shigo ta zuba dubanta a kan fuskarsa


Da sauri ta dauke duban nata, hannayenta suka dan fara rawa


Gaba daya yau tamkar an karra masa cika ido da girma a idannuwanta
Shigarsa ta ษ—inkin shada ne ruwan maroon , kansa dauke da hula
A tsayen da yake jinginuwa ne ya yi da garun dakin ya zuba mata ido da irin kallon nan da ba kyau ana yinsa wa mutun fa ai ko?


A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ringa takowa har inda take tsayen nan tana ta kiciniyar kunce agogon da aka daura mata ta gaza ya tsaya daf da bayanta bayan ya zubawa bayan nata ido a hankali ya sauke dubansa a wajen kugunta daidai inda ya lotsa saboda tudun mazaunanta da fadinsu sai ya zamto nan daidai tsatsonta kamar tana masa da gangan ko dan ta nuna kirarta bayan haka Allah ya haliceta kwatuwar wajen ne ya sa nan din karyewa da fitar da shap dinta sosai


A hankali ya sako hannayensa ta bayan nata ya dora hannayen nasa saman nata ya rike agogon yana kunce mata a nutse hakan ya sa ta dago a tsorace ta zarro idannuwa tana kallonsa ta madubin


Shima dagowar ya yi ya saka nasa idannuwan a cikin nata
Wa'inda a yau ya kasa boye dukkan nau'in abinda ke zuciyarsa a cikinsu, suka bayyanar da shi suka tona shi
A cikin makoshi ya budi bakinsa kadan ya ce" Barka da zuwa gidanki *MY WIFE*"
A rikice ta sake zuba masa ido, sai kuma ta buda hannayensa ta juyo da sauri dan son fita daga wannan mugun tashin hankalin da yake son sakata gabanta na dokawa, sai dai tana juyowar ya zamto yanzu ido cikin idon ba ta madubi bane suke yi, ta gar da gar ce


Da sauri ta sada kanta, lebenta sai son kiran sunnansa yake yi ama ta gaza fitar da amon


Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya dan matsa baya kadan sannan ya kamo hannunta kasa kasan ya ce" Zo mu je"


Kasa hanna kanta binsa ta yi, du kuwa da irin yadda jikinta ya mata nauyi har suka karasa kofar dakin Yumnah ya dakata ita a gefensa kadan yana kallonta ya dan buga kofar ta sake zuba mata ido


Basu wani dauki lokaci ba suka ringa jin nishinta da kyar


Da sauri Khausar ta dago kanta daidai lokacin da Yumnar ta bude kofar da kyar , sai luuuuuu ta fado jikinsa tana sakin hannayenta gaba daya tamkar wace ta tafi duniyar summa


Ba wai shi ba da bai shiryawa haka ba, ita kanta Khausar sai da ta kwala ihu a tsorace tamkar ba likita ba tana ja baya kadan sannan ta yiwo gaba tana kama masa da taya shi ambaton sunnan Yumnar


A rikice ta mike tsaye tana fadin" Ina valise dinka? (Wato ta likitocin nan ta duba marar lafiya)"


Rudewarsa bata kai Tata ba sam, shi dai ya talabi Yumnah ne yana kiran sunnanta da dan buga gefen kuncinta


A nutse ya mike da ita tsaye ya juya yana sauka Khausar na biye da shi ya ce" Tana part din Hajia"


Bata tsaya jiransa ba ta wuce da gudu, abinka da likita kamar masu wani boyeyen tsumi idan suka hadu da marar lafiya a waje, ta je bangaren Hajia wace ke sauraron wa'azin karfe goma ta fada da gudu gudu bayan ta yi salama ta ce" Hajia, ina akwatin TAUFEEK ta asibiti?"


Hajia kiris ya rage bata fado ta kai ba ta mike jiki na bari ta ce" Me ya samu magidancin? Innalilahi na shiga uku, gatacen a kasan gadona "


Kafin Khausar ta fito ta sanar mata Yumnah ce ba lafiya tuni ta nufi bangaren TAUFEEK din sai salalami take yi hawaye kuwa tuni ya bale mata


Khausar ta dauko da saurinta tana jin abin nan kiris ya rage ya tadeta dan sai da ta rike abu da ya dabaibayeta ta rasa yaya zata yi sai kawai ta karasa kofar falon da kyar ta tsaya ta warware nadin kaf dinsa ta yarfa a gefen kafada ba tare da tunanin komai ba ta shigo da akwatin da dan sauri ta kawo daf da shi sannan ta zauna ta bude tana kallonsa ta ce" Me zan miko?"


Sai a lokacin Hajia da ta turo baki ta juyo ta kalleta da niyar kai nata rankwashi ta kuma sileta tasss dan ta kusa hadasa mata hawan jini ashe wannan ce take marmarmartu kamar ta summa bayan ita sai ta rantse da huwan rahamanu karya ne dan ta hanna magidanci rawar gaban hantsi ne, ita kuma ta wani je a guje kamar mai kwanoni ne ba lafiya mai malan muntari tsabar rashin Sannin ciwon kai sai kuma ta yi arba da Khausar din a Khausar dinta


Ido ta fara fitarwa, sai kuma ta tafa hannunta ta ce" lah lah jama'a astagfrullah ke y'ar nan ke ce?"


TAUFEEK dake kallon yannayin Yumnah yana tunanin to mema zai yiwa Yumnar domin ba jinnin ne ya dawo ba, yana daf da cewa Khausar ta bashi abin auna hawan jinni maganar Hajia ta saka shi dagowa shima ya kalli Khausar din, daidai ta rikice tana son warware lafayar da bata san ta inda zata maidata ta daura ba, kawai sai ta mike da gudu ta nufi haurawa sama tana mai fashewa da kukan takaici har ta bacewa ganninsu dan kuwa TAUFEEK da Hajia da suka daga kai suka bi mata da kallo sai da ta bacewa ganninsu sai kuma suka juyo a tare suka yi ido hudu shi da Itan


TAUFEEK ya daka fuska yana hade girar sama da ta kasa ya ce" MEYE!?"


HAJIA ta tabe baki ta dauko akwatin ta turo masa daf da shi da gunguni tana gyara daurin kalabinta ta ce"




























Hi PEOPLE ๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜
















Maganar adabi ce muke:


A tafiyar labarin *AZAL* ina dauke da *ADABI* ne kamar haka Zamantakewa
Yaki a soyaya
Kauranci
Bariki




Ya rab ka nuna min ranar fara shi lafiya idan har alkhairi ne




[7/21, 8:25 PM] +234 708 653 0343: ๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”โคโ€๐Ÿฉนโคโ€๐Ÿฉน๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”




*DA CIWO A ZUCIYATA*




๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”โคโ€๐Ÿฉนโคโ€๐Ÿฉน๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 5๏ธโƒฃ0๏ธโƒฃ


*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*


1: Duk karyar kada


2: Yar mahaukaciya


3: Neman na kaina


4: Bani da zabi


5: Bak'a ce


6: Kutkale


7: Makauniya ce


8: Mage


9: Duk nisan jifa


10: Idan ka raina inda kake


11: Dutse


12: Alkalamin kadarata


13: Bani da zabi


14: Dakika Biyar


15:Wata kokowar


16: Aure yakin mata


17: Ni zan ladabi


18: Daga tafia daukar soja


*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicรฉ
Lait de nuit
Parfums dรฉsodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waษ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuษ“i wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ






Hajia ta tabe baki ta dauko akwatin aikin ta turo masa daf da shi tana guna guni ta ce" Miya ce, ai yau ka ga me nake nufi da ana gudu abu ba motsi, sai ka yarda a maka sakiyar da ba ruwa malan!"


Shi dai bai kuma bi ta kan Hajiar ba, Yumnah dake kwonce jikinsa tamkar wace ba rai a jikinta ya zubawa ido , kallonta yake yi zufa zufa na tsatsafowa a gaban goshinsa


A hankali ya sauke ajiyar zuciya a tausashe ya ce" Yumnah, ki buda idannuwanki"


Sosai gabanta ya fadi jin maganarsa, kar dai ya gane lafiyarta kalau? Sosai kirjinta ya ringa dokawa da tsoron kar aje ya gane cewa lafiyarta kalau ne


A nutse ya mike da ita ya haura saman dakinta da ita
Ruwa ya haษ—a a dan karamin bokici da farin tawul ya zauna daf da ita, a nutse ya ringa dan matsewa yana dan goge mata goshinta sannan ya kunna mata kira'a
Bayan ya gama still yana zaune ne rike da hannunta dan ba zai iya tafia ya barta a wannan halin ba, duda babu abinda ya fito filin da a matsayinsa na likita ya gani na daga hankali, tana numfashinta normal, ama tunda ta yi haka sai ya bita a hankali ko dan abinda ke cikinta


Tun tana summan gangan har barci ya fara fizgarta a hankali barcin ya dauketa ama a kala ta kai karfe biyu da wani abu na dare


Mikewa ya yi bayan ya gyara mata kwonciyarta ya fice a dakin
Wani irin abu yake ji mai kama da bacin rai a kasan zuciyarsa, ama ya dane ya karasa kofar dakin Khausar a hankali ya dan murda kofar
Jin a rufe ya saka shi sauke ajiyar zuciya ya nufi nasa dakin


Da kyar ya samu barci ya dauke shi, cike da bege da tarin kuncin abinda yake tunanin na nema ya fara zama rainin hankali




A bangaren Khausar kuwa, tarin kunyarsa ya saka tana shigewarta ta saka sakata ta karaci kukanta sannan ta je bayi bayan ta gama karewa bayin kallo ta yi wanka ta fito ta bude bangaren tufafinta ta dauki riga marar nauyi ta saka ta fesa turare a jikinta sannan ta saka hula fara ta je ta yi addu'a ta kwonta tana ta shaฦ™ar sansanyan kanshin sababin kaya da turaren dakin har barci ya dauketa cike da jin kewar iyayenta


Tunda asubahi ta mike ta yi sallarta sannan ta shiga dan kai kawonta tana ta duba tufafinta da tunanin abin sakawa dan zuwa wajen aiki


Karfe takwas saura ta gama shiryawa cikin shiga ta leshi da abaya mai shara shara ta dauki jaka yar madaidaiciya da takalmi mai hawa da abayar sannan ta fito ta rufe dakin nata ta dan dakata da tunanin ina zata ga Yumnah dan ta tambayeta jikinta? Domin a tunaninta idan har ta tafi ba tare da ta tambayeta jikinta ba, bata kyauta ba


Dakin nata ta nufa hankali kwonce ta kwonkwasa sannan ta dakata tana jira a bata damar shiga


A kalla ta kusa minti uku tana sake neman izini harda salama dan a tunaninta ko ba'a jita bane? Sai cen ta ji an bata damar shigowa ta hanyar fadin" Cm in!" Aka yi shiru


Dan jim ta yi sai kuma ta tura tana sake yin salama idannuwanta a kan Yumnar dake zaune fess da ita cikin rigar barcin dake dan bayyanar da wasu sassa na jikinta kamar cinyoyinta da hannayenta


Kanta ta kawar kadan tana nuna alamun zata juya ta ce" Barka da safia Yumnah, yaya saukin jikin? Dama wajen aiki zan je nace bari na ga jikinki"


Bata da niyar tsayawa bayan tambayar da ta yiwa Yumnah dan yannayinta bai dace ta tsaya din ba, tunda shiga ce da iya mijinta ya dace ya gani a nata tunanin, dan haka tana maganar ne tana kokarin juyawa ta ji Yumnah cikin muryarta tamkar ba zata fadi mai zafi ba ta yi murmushi ta ce" Bani da lafiya ne dama?"


Khausar ta dan dakata , a hankali ta juyo tana kallonta, sai kuma ta dauke dubanta ta ce" baki da lafiya mana, ba summa kika yi jiya da dare ba?"


"A'a, lafiyana kalau"
Yumnah ta fada tana sake sakin wani murmushi


Sai kuma ta sake kallon KHausar ta ce" Mamaki nake yi, amarya da zuwa aiki washe garin tarewarta? To wai budurcin ne ba'a kawo ba ko kuwa jarumina ne ba zai iya kallon guzuma ba?"


Sosai Khausar ta ji nauyin maganar nan, ko dan bata riga ta bi ta hanyar ba, ko kuwa har yanzu a wai take kallon abin? Maganar dai ta matukar bata kunya da mamaki daga bakin yarinya karama Kamar Yumnah
Shin wai me ta yiwa Yumnah ne?
A tunaninta koda wani zai kulaceta banda Yumnah, dan ta san wacece ita a taka rawar aurenta da TAUFEEK, ta kuma san da ace da wata alaฦ™a a tsakaninsu ba zata taba aikata haka ba


Kai ta girgiza ta kuma juyawa da nufin tafiyarta, a ranta tana yiwa kanta alkawarin wannan ne na karshe, ita ta kawo kanta , da bata zo ba, da bata ga haka ba


"Ji mana ai ban gama da ke ba aunty Hajia Khausar!" Yumna ta kuma katse mata hanzari


Juyowa ta yi ta sake zuba mata ido, dan kwarai tana so ta ga me kuma marar kunyar zata ce mata?


Yumnah ta dubeta ido cikin ido ta ce" Bari ki ji, shigowar ki gidana na nufin yankar tikitin bacin ranki da tashin hankalinki ne, dan a shirye nake tsaf na ja da du wani mai burin ja da Ni, zaki zauna in kin kasance nataciya mai burin son abin duniya, ama a gidan nan sai dai ki min sannu idan ina jinyar ciki in na haihu kuma ku wanken jinnin haihuwa, tsakaninki da wanda yake takamata sai gani sai hange, dama du matsiyaci ya iya kawo kansa inda zai sha wahala, zamu zuba ne, ke kin san kalmar so aka furta min, ke kuwa shishigi ne na keme da masifar son......................................................................




Ido rufe Khausar ta matsewa Yumnah magana ta hanyar dauke gefen fuskarta da mari


Wani irin ihu ta saki wanda ya saka TAUFEEK da ya fito daga wajen Khausar din ya ga a rufe karasowa da sauri ya tura dakin dake dan bude ya shigo yana kallon ikon Allah


Khausar da har idannuwanta ke neman rufewa ta nunata da yatsa ta ce" Ki kula, harshe mugun nama ne a jikin dan adam, kar tunanin shirmenki ya saka ki kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login