Showing 15001 words to 18000 words out of 186303 words
duniya bashi da damuwar da ta wuce tamu, Rukaya nima ina so na amsa shi idan ya sake mana tambayar nan dan bana so hankalinsa ya tashi a kaina, wayo Allahna ni duka kaf kowama ya tsaneni, na gaza samun tsayaye ? Ku duba ku gani yadda na gandame na gaza samun tsayaye?, Ni komai tsufan mutun ni dai a min auren hankalin su Mama ya kwonta summa, a anguwar nan fa da gangan ake yadawa mamanmu magana kunna kallo, yi take yi kamar bata gane yaren da aka haifeta cikinsa dan a zauna lafia, wai mutane dan rashin jin tsoron Allah basa gane cewa auren nan lokaci ne sai su ringa maka muguwar fasara?, Aisha Rukaya kun san Allah idan har na taba saka iskanci a raina ya hanna min kula namiji da nufin aure Allah ya hanna min dukan farin cikon duniya da kiyama, kun dai ga TAUFEEK ne kadai namiji kwal a duniya da muke kawance zumunci wanda ya gama gari yanzun ba wani abin mamaki bane hakan ko? To ku shaida ne TAUFEEK shine mai min fadan in gyara ba dai ya yarda ya batan ba, kuma a kan mutuncina TAUFEEK sai ya bata da du wani saurayin da ya so zagina dan ni ganau ce ba jiyau ba , ko baban abokinsa da ya taba ce min wai me yasa ni hijab hijab ina boye jiki kamar mai gyambo har gobe basa shiri dan a gabana a gabansa yace bai taba tunanin zai wulakantani ba, ya daukeni kanwarsa kawarsa aminiyarsa ba zai bari a wulakantani ba, kin ga shi dinma jiya na masa rashin kunya ya kyaleni irin jeki katuwar banza ki yi haukanki ko? Shikenan A'isha ni kam duniyar tai min zafi Allah ma kuwa....."
A hankali mahaifinsu ya yi baya, ya jima da dawowa anguwar daga wajen jana'izar y'ar abokin nasa, gannin bata dawo ba ya saka shi zama cen wajen mai shayi sunna taba hira yana kuma kallon hanyar da zata bilo,
Yana gannin shigowarta da yannayin fuskarta ya taho shine ya iske koke kokensu da magangannunta
Ajiyar zuciya ya sauke a soron gidansa ya daga kansa sama a hankali ya furta" Allah kaine Allah, kai kadai ka san abinda ka boye a jinkirin auren y'ata, Allah kai ka halicemu kuma ka bamu jarabawar rayuwa dan ka auna imaninmu wanda zai karra mana kusanci da kai, ya ubangijin al'arshi idanma KAUSAR bata da rabon yin aure a duniya har ta koma gareka ne ni bani da ja kuma nani da matsala a abinda ka kadartawa bawanka, Allah ina rokonka a tafiyarta da dawowarta a mu'amalarta ta yau da kulun ka karra tsareta ka kareta ka hanna dukan wani mugun abin dake iya samunta wanda zai saka mu zubar fa hawayenmu a kanta, ya ubanji ga baiwarka nan idan har tana da rabon yin auren kuwa ka fitar mata da miji mai jin tsoronka, mai ibada, wanda zai riketa dominka ya zamto malami, yaya, amini, masoyi a gareta, da yardarka ba zan kuma daga mata hankali ba, ama zan ringa tuni da maganar auren dan ta ringa kokari irin nata, Allah na gode maka da yau har ta je ta yi kitso mamanta kuma tace harda kwaliya ta yi, ka karra kare min ita a duk inda take....."
Adu'ar da ya yi kennan kafin ya fice daga gidan dan zuwa samun liman ya karra amso aduo'i kamar yadda ya saba
A cikin dakin kuwa rarashinta suke yi har sai da ta daina kukan ta dawo sauke ajiyar zuciya
A tausashe tamkar sunne yayun suka ringa nuna mata cewar kowani bawa ai da irin kadararsa, jarabawa ce ta ubangiji kuma alhamdulilah Allah ya basu iyaye masu tausasawa a dukkan rikita rikitar dake iya samunsu yau da gobe a cikin gidansu
Cikin ikon Allah suka samu ta saki jikinta sosai sai ajiyar zuciyar da take ta saukewa kafin A'isha ta dauki wayarta ta buga numbar TAUFEEK bayan tace bara a mata kiran TAUFEEK din ta bashi hakuri tunda da kanta ta gane itace da laifi tace ta masa rashin kunya
Kira na farko bai daga ba, sai a na biyu ne ya daga kuma ya yi shiru ya ki ya yi magana hakan ya sa Aisha yin murmushi dan ta san TAUFEEK ba dai zuciya ba ta ce" Yayanmu barka da warhaka, dama bamu jika ba muka ce bara mu tabo mu gaisar da kai"
Amsata ya yi jin A'isha ce sai kuma ta ba Kausar wayar tana fadin" Amshi aunty ga yayanmu nan"
Wayar ta amsa tana kallonsu sunna dariya suka fice dan yadda ta zaro ido irin kuma sai ki bani?
Shiru ya mata kamarma ya ajiye wayar, sai dai ita ta san bai ajiye din ba dan baya mata haka du fadan da zasu yi kuwa
Hanci ta ja wani hawayen ya bale mata a sanyaye ta ce"Ka yi hakuri dan Allah"
Wani irin tsinkewa gabansa ya yi ya fadi har sai da ya dakatar da rubuta code din bankinsa da yake yin transfer ya saurara yana sake tabatar da kamar kuka take yi kamar kuma mura take, sai dai to me zai sakata kuka ita ? KAUSAR fa mutun ce mai mugun hakuri da kuma juriya, har ga Allah shi yana girmama hakurinta da kawar da kanta a kan abubuwa da dama, kuma ya san dai fadansu ba shine zai saka ta yi kuka ba, shi yasa ya ce" Mura kike yi ne?"
KAUSAR ta dan yi jim, Sa kawai ta fashe masa da kuka har tana shasheka ta ce" TAUFEEK...... TAUFEEK ka gani ko?????"
Idannuwansa ya rintse a hankali ya idasa saka code din ya tura ya rufe computer sannan ya mike ya kashe kiran ya fito daga office din nasa yana lalubar aljihunsa dan jin inda ky dinsa yake ya nufi wajen dankareriyar jeep dinsa dake ajiye ya bude ya shiga yana dan lalubar gashinsa ya kunna sannan ya harbata kan titi
Silalewarya ta yi tana hawayenta, bayan ta yi tunanin gaba yake mata shima ta rintse ido tana tunanin to mema ta masa ai du laifinsa ne ta yi zuru zuru ta jiyo muryar Abansu yana fadin" Shiga mana TAUFEEK, ke Rukaya shinfida masa tabarma , nima ba zama zan ba zan koma nan na dawo"
Firgigit ta mike daga kwonciyar ta bi Rukaya da ido da ta fitar da tabarmar ta shinfidawa TAUFEEK wanda ya cire takalminsa ya zauna yana kunce agogonsa ya ajiye gefe kafin ya dago kansa ya zuba mata ido
Abinda da mai manyan idannuwa masha Allah idon yai mata zuru zuru ya yi ja , haka abin kwalin du ya zubo sai wani wiki wikitu take da idon tana kikiftawa shi kuwa yana sake kallonta har ta karaso tana kallon A'isha ta janyo masa ruwa a rijiya a zuba a tsaftatacen kwanon silba an ajiye masa
Habarta ta ringa sosawa a hankali murya shake ta ce" Da kana anguwar?"
Hannunta ya bi da kallo dake dauke da kunshi ja ya dan tabe baki ya ce" Ke kukan me kike, ke da waye?"
Kasa kasa ta yarda harara ta ce"
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
*DA CIWO A ZUCIYATA*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 7οΈβ£
LITATAFAN MARUBUCIYAR
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicΓ©
Lait de nuit
Parfums dΓ©sodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaΙannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiππ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mataπππππ
Kasa kasa ta yarda harara ta ce" Kukan me zan yi ni kuwa, ba kukan da nake yi"
Da haushi haushi ya ce" Kin ga ya isheki haka, zaki fada min kukan me kike yi ko ba zaki fada ba?"
Ido ta zarro tana kallonsa ta ce" Besty dukana zaka yi?"
Shima ya kare mata kallon da haushi ya ce" Idan ta kama a dake kin ai option ne, meye wannan a fuskarki du ya maki baki ? "
Sai a lokacin ta shafo sai kuma ta tuna ashe fa kwali ta saka itama a ido
Daria ta saka kasa kasa tana sake gogewa da kyau ta ce" Malan ya ka ga mata? Kwali na saka kuma na je na yi kitso harda kunshi....."
Ta karashe tana wani basarwa ta wani hade fuska irin ta kankaro wulakancin nan
Murmushi yake yiwa dariyar su Rukaya dake mata tsokanar wa ya ga ba saban ba
A tausashe ya ce" Rukaya kukan me take yi wannan matar? "
Rukaya ta kalli auntynsu, ta kalle shi sai ta samu kanta da kasa sanar masa, tunda bata san ko auntynsu zata so hakan ba
Itama da basarwa ta ce" Ba fa abinda nake yiwa kuka, ra'ayi ne ai shi kuma kuka kamawa ne"
Shiru ya mata dan ya kula banda tashin balagar rashin kunya harda neman fitina a wajen yar nan yau
Hira suka shiga yi tsakanin su hudun, duda su Aisha hirarsu ta fi karfi, su hirarsu a kan abinda ya shafi karatun fa ta kirta ba dadi a kai ne da kuma hira irin ta gidansu haka wace dai yawanci abokanai ke yi idan sun hade ne kawai suke yi, yan matan na aikinsu su kuwa sunna zaune har dai hirar ta yi nisa sosai sannan ya tunna abinda yake son fada mata da kula ya sanar mata abinda Abansa ya yanke kan maganar aurensa da YUMNAH wace ta san da zancen dama kuma ta san da an yi zaman ba'a dai yanke bane
Farin cikin da ya wanzu a fuskarta sai da ya saka A'isha wace jikinta haka kawai ya yi sanyi tana kallonta dakatawa ta zuba mata ido sosai tana kallonta a lokacin da KAUSAR ke ta murna tana ainahin fitar da murnarta kafin ta ce" Allah na gode maka zan aurar da besty, tsayama wai kennan kwana nawa ya rage? Bai fi arba'in da uku ba fa, gaskiya aiki ja a gabana, kuma tun yanzu zan fitarwa da yan mata da samari anko, ta yan mata daban ta samarin daban du wanda bai min ba ya cira bata nuna ba, ka ga fa azumin da za'a fara jibi da sati saya zamu shiga aji mu yi jarabawar ai ni komai ya zo min daidai ba tunanin jarabawa bale na kasa kwaso shoki dan kuwa sai na kwaso shoki"
Ido ya zarro ya ce" KAUSAR shoki? Dama kina rawa?"
KAUSAR ta yi dariya tana sakar masa harara ta ce" Komai ai da mafari, a aurenka rawa zan har kafafuwana su yi ciwo, me kake tunani?"
Daria ya yi yana girgiza kai dama ya san farin cikin da zata nuna idan ta ji mai yawa ne, gashi ko YUMNAH dinma bai hadu da ita ba bata san maganar ba , domin da ta sani ya tabata da Yumnah ta neme shi ta fada masa
Haka dai ya cika dare domin sai bayan magariba ya tafi har Mama ta zo nan fa ta sanarwa Mama maganar auren sai murna take inda mahaifiyarta itama ta tayasu murna har tana fadin" Lalle daga yau ganninki sai an shirya , watau kirjin biki ba dama, kema Allah ya nuna mana naki KAUSAR na tabata har TAUFEEK sai ya gayato mutanen da ba yan gari ba"
Daria suka yi gaba dayansu, suka sake cika dare sunna hira kowa ya je ya kwonta
A daren ne Aba ya zauna da mamansu ya sanar matta abinda ya yanke, ya fada mata ba zai tayarwa da Kausar hankali ba, zai ci gaba da addu'a, ama yan uwanta a ba manema aurensu damar su turo dan ba za'a ce sai ta samu ba tukunnan a hade
Karshe dai da tsokana suka kwonta domin ya shigo da wani katon asusu ya bata kudade yana fadin a zuba a adana masa shi yanzu kuma a dole ya kule ciki ko ya yiwa yan mata gado da gara............
Daga wannan ranar KAUSAR ta daina gannin magana makamanciyar haka,
Sai dai tana gannin yan shirye shirye na auren kannenta
Haka kuma gefe guda Aisha da Rukaya sun sakota a gaba ga karatu ga jarabawar karshen shekara su a dole sai ta ringa kwaliya tana gyagyarawa irin nasu bayan ita ta san ba zata taba yin irin nasu ba, za dai ta kamanta
Wannan jarabawar kaf dinta da TAUFEEK aka yi har karshe, kuma cikin ikon Allah idan aka shiga aka fito suka zauna sunna dudubawa ba laifi ya amsa tambayoyi masu yawa harma ya bata mamaki domin bata yake ta rike ya ringa fada mata amsoshin da ya bayar itama sai ta ga hakan ne ta bayar hakan na nufin ya leka karatun ya duba sosai, sai ta ji nutsuwa a zuciyarta harma ana gama jarabawar da sati daya ta je ita da su Rukaya suka fitar da anko ta maza shada ruwan sararin samaniya , ta mata atampa mai tsada mai kyan gaske mai sirkin ruwan sararin samaniyar da baki baki wace ke iya yiwa kowace fata kyau
Daga kasuwar direct gidansu TAUFEEK suka wuce domin sun sanar da Mama cewar idan sun cire zasu kaima mamansa dan sun yi waya tace tana jira idan KAUSAR din ta ciro anko din ta kawo mata kalar da sunnan shagon da aka fitar dan a sayo na jama'ar gidan
Kasancewar Azumi ne basu samu matan gidan a falo ba, kuma yau girkin Maman ne sai kawai suka samu Maman suka nuna mata ta yaba sosai sannan ta nemi da su zauna su sha ruwa kafin su tafi, ama suka nuna sun baro Mama da aiki a gida, a dole ta salamesu da kyauta kamar yadda ta saba duda sai da ta kusan kaiwa Kausar rankwashi a kan ta nuna na zasu amshi kudi ba ga wata leda mai dauke da kaya nauyi jikit wai ankon safensu ne, atampar da suka fitar ta rana ce , da jin ledar ta yi nauyi ba iya ankon kadai bane
Haka suka fito sunna ta godiya ISHRAT na biye da su tana labari suka nufi bangaren Hajia, domin ko giyar wake ta sha ba zata shigo ta fita bata je ta gaisar da hajiar ba
Hajia na zaune saman kafet tana kallon gabas sai musmus take da baki ga dukan alamu carbi take ja dan kuwa tana ta ja tana motsa bakinta ne, dakinta dauke da kanshin turaran wuta ya game ko'ina sai dai yau ba hayakin nan bane mai yawa babuma hayakin kamar yannayin dakin ne da ya saba da kama turare idan bako ya shigo zai ji kanshin ama ita dake ciki ba lale bane kanshin ta ji shi
Da murmushi take amsa gaisuwar KAUSAR har KAUSAR ta gama gaisheta a duke sannan ta mike ta zauna kusa da ita kadan tana ciro ankon da hannu biyu ta mika mata ta ce" Hajia, dama daga ciro ankon muke, kin ganshi nan, wannan ne na mata ga kuma na maza nan"
Hajia ta saki murmurshi ta karbi atampar, tana daf da yin magana aka daga labulen kuryarta aka leko kadan , hakan ya sa ta dago ta zuba idannuwanta tana kallo hadi da kankance dubanta
Baki ta tabe ta cire kai kasa kasa ta ce" Munafurci dai ba abun yi bane, aikin mata du sai kaura yake yi yana sarkafar maza, in ba tsohon munafurci ba ai da na tsaya ina maka magana shiru ka min irin ka yi barci, ama yanzu kana jin maganar ita wannan ka wani leko, uhum zamani mai abin mamaki ku duka bakwa jin tsoron Allah, ace wai iyayenku na kallo ita wannan din itace kawarka kai kuma abokinta, a gaban mai kwanonima sai a zanta, ai tunda yanzu na yarda eh kawancen ne abu daya nake jira na ga na mika ka dakin Yamaniya ita kuma itama dakin miji in ga iya shege, ai nasara ba kowa ya samu galaba a kansa ba, na tabata in kai ka fi karfin Yamaniya ita wannan mijin da za'a aura mata zai fi karfinta, ni abinda na kasa ganewa wai me kike jira har yanzu ba'ai maki aure ba?"
A'isha ta turo baki tana ji uwa ta mike ta bar auntynta a dakin nan ta yi tafiyarta, itafa dama tsoron tsohuwar nan take yi sosai, babu wanda ta bari, da ta ji maganar kawancen auntynsu da jikanta shigarta gidan ya fi a irga, har cewa take yi a dai ringa saka ido kar a ringa barinsu su kadai lau a haifo masu dan besty
Da kyar ta hakura da zumuncinsu sannu a hankali har take kaunar Kausar, ama hakan baya hana ta ringa yanko zance marar tsari haka kawai
Fuska ya daure ya fito gaba dayansa ya kai zaune yan duban Kausar ya ce" Daga ina kike ke?"
Hajia ta sake zuba masa ido tana kankancewa ta ce" Daga inda ka aiketa ubanta!"
KAUSAR ta zarro ido sai kuma ta dauke kanta tana murmushi ta nuna masa atampar dake hannun hajia ta ce" Ankon muka ciro ka manta ne na