Showing 36001 words to 39000 words out of 186303 words

Chapter 13 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18760

sauri ya cire kansa yana Adu'ar neman tsari da shedan , yawancin lokuta yakan rasa me yasa idan ya tsinci kansa a irin haka sai ya ji kamar zai ji haushin ƴaƴansu kansu bama su ba, bai san yaya zai yi kwatancen ya dace a ringa kiyaye ido idan za'a yi halaya na wulakanci wa mahaifiyarsa, sai dai ba komai ya san ya zame masa wajibi ya yi biyaya ya kuma bada example wa kannensa kamar yadda mahaifinsa yake fada a kulun


Hannunta da ta rike nasa tana kukan ta ce" Yayanmu, dan Allah ka masu magana su daina, ka ga fa ba abinda aka yi suka kama wannan rigimar, me yasa suke mana haka ne?"


Fuskarta ya dan sake kafewa da ido, sai kuma ya budo bakinsa zai yi magana
Kiran da ya shigo a karamar wayarsa baka ta aikin sirrinsa wace idan kira ya same shi irin haka to urgent ne ya saka shi da dan gagawa fadin" Ki daina kukan nan, ki wuce bangarenku ki yi wanka ki yi alwallah lokacin sallar magarib ya kusa, bana son ki shiga abinda ba'a saka ki ba kin fahimta?"


Baima iya gane amsarta ba ya shiga falon na hajia da dan sauri ya dauki ky din motarsa ya fice






*Tallah2*


*ALLAH BAI SAUKAR DA CIWO BA SAI DA YA SAUKAR DA MAGANINSA*


Ni ce dai Fareeda Abdallah, na sake dawo muku da tallen magungunanmu da zuwa yanzu bazan iya ƙayyade yawan waɗanda suka dace da biyan buƙata sanadiyyar amfani da maganinmu ba. Alhamdulillah! Ƴar'uwa ki gwada, wataƙila warakarki na tattare da maganinmu.
Haihuwa ce baki taɓa yi ba ko kuwa jinkiri kike samu sanadiyyar planning ko kuma haka kawai? Muna da ingantaccen maganin rashin haihuwa ga mace da namiji, wanda za ki bada sadakar 2k ga matsalar ko wane ɓangare. In sha Allah za ki dawo da godiyarki bayan amfani da maganinmu.
Sanyi (infection) ne yayi miki yawa yake saka ki ciwon mara, zubar farin ruwa, ƙaiƙayi, ƙuraje, ɗauke ni'ima, har ma ya saka mijinki ya dinga miki gani-gani saboda bakya gamsar da shi? Da naira 3k zamu haɗa miki magungunan da za kisha ke da Oga in dai kika yi amfani da su ku da sanyi har abada in Allah ya yarda.
Muna sayar da ingantaccen haɗin sabaya, wanda zai sa nonuwanki su cicciko, hatta fatar jikinki sai ta murje sanadiyyar shan kunun sabayarmu. 2500 bokiti 1litter.
Muna da maganin wankin nono ga mai ciki da mai shayarwa, wanda indai kikai amfani da shi yaronki zaiyi tubarakallah, ba ruwanki da laulayi. Muna da ingantaccen maganin Daji (Cancer), typhoid, maleria, yaron da yayi nauyin ƙafa, da sauran cututtukan da ban ambata ba.
Muna aika maganinmu ko ina tsakanin Nijar da Nigeria, ga masu buƙatar magani da gaske su tuntuɓeni akan lambar wayata 07039080978, ko 09077591726


Noted: *MAI SON MAGANINMU IDAN BA A KADUNA YAKE BA, SHI ZAI YI KUDIN MOTARSA HAR ZUWA INDA YAKE, BABU INDA BAMA TURAWA IN SHA ALLAH.....SAI KUN ZO*




......................m💓💓💓💓💓


💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔




*DA CIWO A ZUCIYATA*




💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 1️⃣4️⃣



LITATAFAN MARUBUCIYAR


Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃






A haka sallar magariba ta shigo , harma isha'i ta shigo, ya zamto masu haramar daukan amarya har sun shirya sun tafi , ciki harda mahaifiyar su KAUSAR, Kausar din kuwa kacokam a bangaren Hajia suka wuni da yan uwanta , harma ta je amsowa hajiar maganin ciwon kai sai dai wanda ta siyo din ba shi hajiar ke so ba, hakan ya sa Hajia saka hijabinta ta sakota gaba cewar bara su koma tare tunda gidan ba mutane sosai kuma tana son mike kafarta itama ta yiwu zaman waje dayan da ta yi yau ne ya hadasa mata ciwon kan


A hankali suke tafe, wajen siyar da maganin ba wani nisa da gidan, layi na biyu ne kawai kemis din mai maganin yake


Maganin KAUSAR ta kalla a karro na ba adadi ta ce" Hajia, maganin da kike son mu amso fa bai dace kina shansa yanzu ba, kin ga da kin sha zai rabaki da ciwon ne na dan lokaci, ba'a son shan ire iren magungunnan nan, ni kam da wannan din kika sha ya fi wancen anfani"


Hajia ta dan kalleta shekeke ta dauke kai ta ce" Ke kuwa, ko kece Magidanci kya shafa min lafiya, shima sai iya yin tsiya idan bani da lafia na je asibitinsa ya kama min iya yi kennan, shi yasa na samu mai kemis din nan ya zama abokin sirrina, ya zamto idan dai bani da lafia to yana gefe zai bani magani na hadiya an gama, ba sai na je wajen Magidanci an sosoke ni da allurai ba ana min iya yi"


Murmushi kawai KAUSAR ta yi tana tunanin to magidantan na Hajia har nawa ne? Ita dai daya ta san tana cewa Magidanci TAUFEEK, kennan ba shi kadai bane take fadawa hakan?, Abinda dai ta sani shine ba TAUFEEK bane Hajiar ke nufi, domin TAUFEEK dai TAUFEEK karatunma ai bana ne suka gama tare da shi


Dale su da hasken mota ta yi ya saka su ja suka tsaya
Da sauri Hajia ta riko hannun KAUSAR kasa kasa tana fadin" Ke mu juya kar a sace mu Y'ar nan"


KAUSAR din kanta haske sun ya dan tsorata ta, dan yanzu yannayin insecurity din da ake fama da shi dole idan ka ga wani abin ka kiyaye


Bude motar aka yi aka fito, a kusan tare suka sauke ajiyar zuciya gannin TAUFEEK ne da abokinsa, sai dai kafin ya karaso inda suke tsaye wata motar ta zo ta makunma tasu daga baya har sai da motar ta yi gaba kadan sannan ta tsaya


Da sauri ya juyo ya zubawa wanda ya karrun masun ido, da kuma abokinsa da ya nufi wajen a fusace yana dauko wani ashar irin na an bata makan nan ya lailayawa wanda ya zo da a kori kurarsa ya bugun masun bayan ba wani a kan hanya suka tsaya ba


Juyowa ya yi yana kallon yadda Hajia ta makalkale masa hannu jikinta na rawa tana zarro ido ta ce" Nu kam kamar wace ban yi addu'ar fitowa ba?mene wannan din kuma"


A hankali ya dauke dubansa daga kanta ya sake dorawa kan Kausar dake tsaye fuskarta a cure waje waje daya alamun har yanzu fushin take yi da shi , kuma yanzunma wani hijab ne da yake iya kiransa a tsokali adini domin sam ba irin hijab din da ta saba sakawa mai rufe suturarta bane , ta wani kebe baki uwa an mata laifi
A nutse ya ce" Ku kuma daga ina kuke da daren nan?"


KAUSAR zata bashi amsa, Hajia ta rafka wani irin salati da karfi tana dafe fuskarta tamkar ita ce aka wankawa mari ta ce" Aan kafta masa mari, an kaftawa abokinka mari, ka ga ya yi kashangar kar aje ya summa, kamo shi mu tafi gida mema ya hada shi biyewa mutumen da ya tardo mota ajiye ya make? Ai da gani a maken yake shima"


Da mamaki ya sake zuba idannuwansa, ai kuwa abokinsa ne dai abokinsa Adahir da ya hadu da shi yanzun a asibiti ya biyo da shi dan gidansu bayan layi ne motarsa ta samu matsala aka shekawa marin da ya saka shi zama ya dafe kuncin ya shiga tunanin rayuwa da abubuwan al'ajabinta, daga zuwa jin ba'asin an yiwa motar makocinsa barna ya samu hannun kato a gefen haba har yana jin bakon yawu a bakinsa ga dukan alamu an sabauta masa matauna


Hannunsa ya janye ya karasa wajen bayan da hannunsa na hagu ya masu alamun su juya gida , ya karasa wajen da har ya fara daukan tsirarkun mutane yan taya bera bari ana ta kokarin rike mutumen da shine ya zo ya yi barnar ama sai warce hannu yake yana fadin a barshi ya sabautawa Adahir fuska in yana takamar shi mai kudi ne shi ba abinda ya shafe shi da kudinsa , gidan horon hali ne ba yau ya saba shiga ba


A tausashe ya ce" Soubahannalh" bayan ya yi ido hudu da Adahir dake tsugune uwa an girgiza bera a kwano, ya cire dubansa yana saukewa kan Mutaka mai Shago ya ce" Soubahannalh, ku sake shi mana me ya yi zafi haka ne malan?, Ko dai a hanya ne muka tsayar da motar ne ni ban gane ba"


Hannunsa ya warce rai bace ya ce" a hanya ne mana, in ba a hanya ba a gidan uwar mutun ne?, Zaku zo ku ajiye mota a hanya dan an karu ba'a gani ba ku zagi mutane, idan rama masa ka zo yi ai sai ka matso in kai namiji ne na ci uban baba............"


Cikin ikon Allah sauran zagin da ya dibo daga bakinsa yake tunanin ya gama amayarwa dai hadiye shi ya yi a zuciyarsa a lokacin da gefen fuskarsa ya amshi naushi irin na kato dan uwansa , Naushin da yake tunanin da katon itace ne aka mauza masa shi, sai dai idannuwansa suka sheda masa mutum ne ya yiwa fuskarsa shima barin mahaukaciyar da ya gaza tantance zuwanda da sauke masa shi a fuskar


Ihu ya sake , lokaci daya ya kama hannun Mutaka mai shago da yale salalamin gannin abinda bai taba ganni ba MAGIDANCI na fada , da karfi ya warce hannun ya janye Mutakan ya durfafi wanda ya buga masu mota idannuwansa na rintsewa ya kamo wuyan rigarsa ya hade da makogwaronsa ya rike da riko irin na gaskiya da gaskiyar nan sannan ya aniya jijiga shi a tsayen da suke kafin ya sake shi kasa


Da sauri ya shiga nade hannayen rigarsa, sai dai gannin kamar zasu tsayar da shi mutane na kokarin hannawa ya saka shi dauke rigar gaba daya ya cire daga jikinsa ya yi ciki da wannan mai akori kura da ya shiga hali na dana sani da tunanin inama hannun agogo zai koma baya da sun zanta sun sulhunta kansu cikin salama ba tare da hankalin kowa ya tashi ba


Da gudu KAUSAR ta sakarwa Hajia maganinta a lokacin da Hajia ta fashe da kuka hannaye saman kai tana ihun a raba fadan cen jikanta ne Magidanci ne kuma yau yake ango kar a zane shi ko a raunata mata shi ta rasa tudun dafawa, a lokacin ne ita kuma KAUSAR ta karasa muryarta na rawa , jikinta na rawa ta duka ta dauki rigarsa da yar karamar wayarsa da ya yar a nan dan masifar dake cin zuciyarsa wadda yake neman wajen amayarwa wunin yau cirrr bai samu ba sai yanzu a rikice ta ce" Freind, Freind, innalilahi wa inna ilaihi raj'une, Bawan Allah ka hanna shi mana wayo Allahna"


Lokaci daya ta fada tana riko hannun Atahir da ya samu kansa gannin su ke cin wasan ya mike yana aukin fadan ci ubansa kar ka barshi Docter ci UBANSA ta rike tana dan jijigawa dan ya bata hankalinsa


Da kyar su Mutaka suka kwaci mai akori kura da hancinsa ke zubar da jinni har ya bata gaban rigar TAUFEEK dan matse masa kai ya yi a hamata ya rike taf ta yadda zai ji jiki ko bai summa ba ya yi kannin sumar, danma hamatar ba hamami ai da ya garda rana ya kuma shanye hanyar a kansa kamar sunnansa


Kamar ana tura mota baya haka suka masa suka samu ya yi baya sannan aka shiga bashi baki, ciki harda daidaikun datawan anguwan da suka sanshi suka kuma san wannan din ba halinsa bane tabo shi aka yi, kuma abin ya mugun masa zafi har yau aka ga Magidanci da haka, Shi da kansa sai ya samu kansa da jin matsananciyar kunya, dan a cikin mutanen harda abokan mutuncin mahaifinsa da datawa masu daraja


Maimaitawa yake ba komai , ba komai har ya karaso kusa da motarsa inda Hajia ke tsaye sai sharbar kuka take yi su KAUSAR na kusa da ita har yanzu KAUSAR rike tsaf da hannun Atahir hawaye na bin gefen kumatunta tana bin TAUFEEK da kallo tamkar bakonta


A hankali ya dan shafa sumar kansa yana dauke dubansa daga fuskar Kausar ya karasa inda suke tsaye ya tausasa muryarsa ainun da nufin sake basu umarnin su shiga motar ya mayar da su gida idannuwansa suka sauka a hannunta rike da na Attahir shi kuma zuru zuru kamar sabon kamu sai kallon TAUFEEK din suke su duka


Takaici ya nemi sake shaka, haushi haushi ya nemi kume shi, bai san lokacin da ya saka hannunsa ya raba hannayen nasu ba sannan ya jaa hannunta kiiii ya bude motar da hannunsa ya mata alamun ta shiga fuskarsa tamkar hadarin gabas


Da sauri ta shiga tana matsawa tana sake zubawa fuskarsa ido Hajiama ta zo ta shiga tana rungume maganinta hadi da hannayenta a kirji ta yi tsuru tana hangensa sunna magana da Attahir


Ajiyar zuciya Hajia ta sauke kasa kasa ta ce" Ko dai aljannu suka shafe shi yau?"


KAUSAR ta mayar da bayanta jikin motar a hankali ta jinginar tana lumshe idannuwanta zuciyarta na ci gaba da dokawa cike da tsoron abubuwan da suka faru yau, dan a yau ta ga abubuwa da yawa da suka wahalar da ita ciki harfa fadan nan na TAUFEEK
Bata sanshi da haka ba
Bata san yana iya yin fada haka ba
Tsoron da ta ji a lokacin da mai akori kurar ke zage zage ta kusan summa, dan tsoron da ya kama zuciyarta kar ya daki TAUFEEK din


A hankali ta share hawayenta tana sake lafewa har ya shigo ya tada motar ya ja bai masu magana ba ya nufi gidan da su


Sunna karasawa maimakun ya shige ciki kamar yadda kofar ke bude motocin daukan amarya sun dawo sai bai shiga da motar ba ya bude ya fita haka da farar singiletin dake jikinsa ya nufi wajen mai gadi dake tsaye da wasu mutane biyu


Zurru Hajia ta kuma yi tana kallon sabon badala a wajen magidanci, ita sai ta rantse da huwa rahamanu yau gaba daya kamar an cenza mata jika, ku ga fa damatsuna a fili yana tafe a wajen da kila wa kala yana iya hadewa da sirikansa tunda an kawo masa mata yau, tana murnar bayan dogon lokaci dogon jira, dogon cece kuce da saka ido daga mutane daban daban yau Allah ya yi jikanta ya wanku sai gashi yana dambe?


Dan jim kadan bayan mai gadi ya shige ciki shi kuma ya dawo bangaren da Hajia take


Bude wajen ya yi a hankali ya zuba mata ido kamar yadda take kallonsa
Murmushi ya kakaro kasa kasa ya ce" Wai kallon fa?"


Hajia ta cire idannuwanta ta dubi gabanta , sai kuma ta dawo da dubanta kasa kasa ta ce" Ka tabata baka hadu da shafar aljannu ba yau?"


Murmushi ya yi mata a bayane, sai kuma ya dan leka inda Kausar take zaune, a hankali ya ce" Ki bani rigar kar su Mama su tardoni a haka Freind"


"Au wato mune ka rainawa wayo magidanci? Yanzu ace da girmanka ka tsaya dambe da jiki a fili? Kai fa likita ne, likitanma baba , sai ka bata lafiyarka ta hanyar gwada gwonji ?" Hajia ta fada tana janyo rigar tasa ta mika masa, sai dai bata janyo da wayar tasa ba, shima sam a wannan lokacin ya sha'afa da du wani tunanin waya har ya saka rigar ya gyara da kyau sannan ya fadawa Hajia ta fito zai kai su Maman gida ne dare ya yi


Ta so ta nuna to ama shi ango yanzun kuma wani yawo zai shiga? Sai dai tunawa da ta yi waye zai kai gidan sai ta kame bakinta ta fito tana mika masa maganin da fadin ya cenzo mata ba zata yi asarar kudinta ba




Yana tsayen har su Mama suka fito
Kasancewar da aminiyar Maman su Kausar din aka wuni gidan bikin a dole Kausar ta fito daga bayan ta shiga gaba su kuwa su hudu suka shige baya Mama sai aukin fadin take da ya barsu su shige adaidaita ai kar ya wahalar da kansa, shi kuwa bai ce komai ba saima wani dan murmushi da yake saki fuskarsa na fitar da annuri da kuma wani girma na daban tamkar ba Taufeek dinta ba.......................




















*ALLAH BAI SAUKAR DA CIWO BA SAI DA YA SAUKAR DA MAGANINSA*


Ni ce dai Fareeda Abdallah, na sake dawo muku da tallen magungunanmu da zuwa yanzu bazan iya ƙayyade yawan waɗanda suka dace da biyan buƙata sanadiyyar amfani da maganinmu ba. Alhamdulillah! Ƴar'uwa ki gwada, wataƙila warakarki na tattare da maganinmu.
Haihuwa ce baki taɓa yi ba ko kuwa jinkiri kike samu sanadiyyar planning ko kuma haka kawai? Muna da ingantaccen maganin rashin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login