Showing 84001 words to 87000 words out of 186303 words
ya nufeka da asiri in sha Allahu zai kome masa ne, gyara da kyau mana wai meye kake cika kunci uwa balan balan"
Karra hade fuska ya yi ya ce" Kar ki saki ki turara min kaurin nan ke kuma!"
Hajia ta yi turus tana kallonsa, kasa kasa ta ce" Magidanci maganin tsarin ne ya zama kauri kuma?"
Cire kai ya yi bai bata amsa ba, hakan ya sa ta ajiye tana kallonsa ta ce" Kai ko wancen mai kai uwa na ifirutun ce ta bata maka? Ka dan yar nan dan rashin da'a da ta zo gaisheni kafada da kafada muka gaisa? Yar nan ka kuwa san in ta je cen bata zuwa bangaren Mamanka sai dai na kishiyoyi? Ka fa ja mata kunne dan Ni nan ko mai kwanoni ya yi kadan bale matar dansa, aikin banza aikin wofi "
"Ki matsa min da warin abin nan nace, kuma ki daina sako ubana a abinki kin dai ji na fada maki, da kike cewa wai tsoron Allah in tambayekima hijab umarnin Allah ne ko na mutun?"
Hajia ta yi tsuru tana gannin yadda fuskarsa ke Dada daukan ja alamun rikici ke kunne a cikinta na kirki, gaba daya sai ta bace, to waye kuma ya ki saka hijab ne? Me ya kawo maganar hijab ne? Mema aka yi da maganar hijab ne? Ita dai tana iyaa rantsewa da huwa rahamanu a shigowar magidanci bata kawo maganar hijab ba ko daya, to wa ya kawo maganar hijab?
Kaskon ta mayar gefe ta bada abin a ranta tana ayana' ai da yake fanka a kunne ta kado maka iskar, bari in ji ubanda ya taba min kai yau sai inda karfina ya kare dan ba zai yiwu ba gaskiya ina zaune a ringa kokarin dagan hankali ana kawowa magidanci farmaki!'
A fili kuwa ta dube shi ta ce" To wai wani shedanin ne yace kar a saka hijab? Ai du wanda ma ya ki hijab gaskiya shedani ne, bayan wannan ai shi lulubi dadi gareshi, me ake da gayar zirr ba auki? Na tabata wancen hure ka fadin ce bata son saka hijab ko? To ta kiyayi duniya ta kuma kiyayeni dan bata isa ta daga hankalin jikana ba tashi mu je in ji uban me take son budewa da ba zata saka hijab ba a bushe kamas, yo in bandama son duniya ke matar aure me kuma ya rage ? Tashi mu je in ci duniyar uwayenta a dakin cen yau in ban mareta ba ba Ni na haifi mai kwanoni ba!"
Tunda ta fara hayagahar kawai ya yi tsai yana tunanin duniya, shi dai ya ga abu gannin idannuwansa, to kuwa zai tabatar mata maganarta ake ita din nan ba kowa ba, dan haka ya sake hade gira ya ce" ba wani inda zamu je, kina neman wanda ya hanna saka hijab aka zo kanki an tsaya, maganar jin tsoron Allah kuwa ki yiwa kanki fada! Kina zaune sai neman fitina !"
Hajia ta yi tsuru tana kallonsa, to ita yau wani dan bakin ciki ne ya hadata fada da jikanta? Gashi dai a sanninta ba abinda ta masa ama tunda ya shigo kamar wanda yake jin haushinta
Murya a sanyaye ta ce" Wai waye ya taboka? Ni kuma wa na hanna saka hijab a duniyar nan ta malikiyau midini?"
π€π€π€π€π€ Gaskiya gaskiya dan gidan mai langa ya fara kin jin tsoron Allah, wannan hali sam ba na Musulmin kirki bane, mema Hajiar ta yi da zaka nemi dora Mata laifi? Ka ji tsoron Allah πππππ
*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*
1: Duk karyar kada
2: Yar mahaukaciya
3: Neman na kaina
4: Bani da zabi
5: Bak'a ce
6: Kutkale
7: Makauniya ce
8: Mage
9: Duk nisan jifa
10: Idan ka raina inda kake
11: Dutse
12: Alkalamin kadarata
13: Bani da zabi
14: Dakika Biyar
15:Wata kokowar
16: Aure yakin mata
17: Ni zan ladabi
18: Daga tafia daukar soja
*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*
*LITAFIN KWATENA*
π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨
*BAIWATA*
π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨
Alhamdulillah, Alhamdulillah, labarin BAIWATA labari ne da zan iya kiran sa da BAKANDAMIYA, sakamakon Ζayatuwar labarin, y yi nasarar lashe gasar Gwarazan HIKAYATA, wanda ya zo Ιaya a cikin labarai guda goma da aka zaΙesu kuma za'a bugasu a takarda (publish). Ganin wannan gagarumar nasara da muka fara hayewa yasa muke da Ζudirin rarraba littafin gidajen radio da muke da su dan su karanta da kuma bayar da kasuwarshi ga masu sana'ar siyar da littafi. Sai dai hakan ba zai faru ba sai da *gudumuwarku masoya*, Ζauna da taimakon da zaku mana shine, ku siyi littafin na takarda duk da na san dayawanku kun karantashi sannan free book ne, amma wannan zaku mana ne a matsayin gudumawarku, madadin mu ce muna roΖonku da ku taimaka ku mana karo-karo, Shiyasa muka ga Gwara ku siyi littafin ya zama guminmu ne zamu ci.
_Da wannan muke roΖon da ku siyi littafin BAIWATA na takarda, nasan dayawa kun san labarin, sannan kun san ingancinsa da kuma cncantarsa, ga duk wacce ta shirya siya ta tuntuΙi wannan lambar ta WhatsApp *+227-93-81-16-18* ko kuma *+227-82-21-91-74*, farashin *1000k* ne ga mutanen mu na Nijeriya, namu na Niger kuma *1000f*.
π *MUNA DA YAΖINI A KANKU.*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
*DA CIWO A ZUCIYATA*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 3οΈβ£1οΈβ£
*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*
1: Duk karyar kada
2: Yar mahaukaciya
3: Neman na kaina
4: Bani da zabi
5: Bak'a ce
6: Kutkale
7: Makauniya ce
8: Mage
9: Duk nisan jifa
10: Idan ka raina inda kake
11: Dutse
12: Alkalamin kadarata
13: Bani da zabi
14: Dakika Biyar
15:Wata kokowar
16: Aure yakin mata
17: Ni zan ladabi
18: Daga tafia daukar soja
*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicΓ©
Lait de nuit
Parfums dΓ©sodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaΙannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiππ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mataπππππ
Da jin haushi ya ce" Au kin manta wace kika dage sai ta daina saka hijab ko? Wace kika kama hijabinta a filin Allah zaki masa diban albarka wai ki ga kumarinta? Wace kika ringa fadin zantuka mararsa dadi dan ta yi kwaliya maimakun ki mata fada? Bari ki ji, kika yarda Aba ya hadani tafia Haji da ke dama a cen zan maki aure na dawo dan kin isheni!"
Daga haka ya mike ya yi gaba yana jin sam bai huce ba in ya tsaya iya haka, kamar wanda bai mata komai ba yake ji, ji yake a cikin ransa ya zama wajibi ya sake wanke babar mai kwanoni ko zata dawo hayacinta ta daina aikata aiyuka mararsa kyau
A wannan dare kwata kwata Yumna bata gane kansa ba
Irin dan janyota jikinsa da yake yi wani lokacin har ta dan fuskanci yanada bukatarta sosai a wannan daren bata ga haka ba
Karshema a dole ta fito ta Bara masa dakinsa dan daure fuskar na hadasa mata faduwar gaba ta zo ta kwana a nata dakin idannuwanta biyu tana hawaye
Ba za'a gane irin radadi da tashin hankalin da take tsintar kanta a duk lokacin da ta ga fuskarsa ta cenza ba
Ko a lokacin da take da dama irin na budurwarsa ba matarsa ba bata cika iya hadiye ganninsa rai bace ba bale a yanzu da shine mai sarautar ita kuma bafadiya (a ganninki ba)
Sosai ta ringa neman mafita a zaune ba a saman salaya ba
So take yi ta gane meye a lalle sai ta je ta zauna da kakarsa? Ta ki ta fahimci yarensa bale har ta yiwa tufkar hanci tun ba'a je ko'ina ba, gaba daya ta kasa gane Yaren shima mutun ne mai zuciya a kirjinsa da kuma ahalinsa a cikinta, tashin farkoma bata yiwa kanta shinfida mai kyau ba da take tunanin sonsa ama kuma ta ki danginsa wannan shine wahalarta har kiraye kirayen sallar asubahi ya tasheta daga zaunen da take jiki ba karfi ta saurara ko zata ji ya tasheta kamar yadda ya saba, kanta kuwa ciwo yake kamar zai fashe mata tsabar sakawa kai damuwa
A lokacin da ya bude kofarta salama a bakinsa kasa kasa idannuwansu suka shiga junna a lokacin ne ya dan zuba mata ido kadan ya ce" Ki tashi ki yi sallah.........."
Da sauri ta riko hannunsa tana mai fashewa da kuka ta ce" ka yi hakuri in na bata maka dan Allah, ba wani abu ya hannani wuni ba ciwon kai mai tsanani nake fama da shi, ka ji? Taba kaina ka ji yanzu haka yadda yake sarawa.....plz ka yi hakuri"
Har ga Allah sai ya ji tausayinta sosai ya shiga zuciyarsa
A hankali ya taba gaban goshinta sannan ya bita da kallo
Yannayinta na masa kama da wace ke dauke da karuwa a matsayinsa na baban likita gane hakan ba zai masa wahala ba bale macen da shine ya santa ya cireta daga sahun budurwa zuwa Mace cikakiya
Da kula ya ce" Sorry, ban sani ba ai, ki je ki yi sallah ina zuwa"
Da wannan ta samu nutsuwarta ta dawo jikinta, dama a kwanan da ta yi mafitar da ta samarwa kanta kennan, ta san mijinta ba jahili bane, ba kuma wanda baya jin tausayin mace bane, ta tabata zai sauko shi yasa ta sake riΖe damarta har ta isar da sakonta
Ko da ta gama sallah a nan ta yi kwonciyarta tana kudurtawa ranta cewa a kan wancen tsohuwar ce har zai iya fushi da ita? Lalle dolema ta tsani matar!
Bai wani jima ba ya dawo daga masallacin sannan ya wuce dakinsa ya wuce wajen ajiyarsa ya dauko maganin da ya san koda da wani abin ba zai mata ila ba ya nufi dakinta yana dan duba agogo da tunanin ko abansa ya fito daga masallacin ne, domin cikin dare ya shigo garin basu gana ba
Dakin ya shiga, cikin kula ya bata maganin da kansa sannan ya sakata fitowa dan ta ci wani abin
A lokacin da suka dan fara karyawa kiran Aba ya same shi a wayarsa cewar ya same shi bangarensa
Gamawa ya yi da dan gaggawa ya mike ya tafi sanye da jalabiya maroon mai haske kafarta da takalmi plate baki sai dan carbin dake hannunsa yana tafe yana shaΖar sansanyar iskar safiya har ya karasa bangaren Mai kwanoni
Tunda ya bude falon ya gansu su duka zaune , watau matan Elhajin da Elhajin da kuma Hajia a zaune ta yi wani dauri gayanan dai kamar jirgi a saman kai hijab din ya tafi tsakiyar kanta sai wani MUSMUS take da baki ya ayana' To fa, na yi wani abin kau?'
Karasawa ya yi ya shiga gaisar da iyayensa bayan ya gaishe da Abansa cikin mutuntawa kamar yadda ya saba
Yana gamawa Aba ya ce" Kai, dan matso daga nan ka turaru, kai yanzu tsakani da Allah magidanci turaran tsarin ne ka dauki kwana uku cir baka yi ba? Kuma ka saka min uwata a gaba ka wanketa tasss?, Ta maka kyau, nace ta maka kyau sai ka matso ka turaru sosai ka kuma dage rigar ta shafa maka na shafawar idan kuwa baka yarda ba to ka sanar min na ji"
Murmushi kawai mahaifiyarsa ke yi kanta a kasa, tana matukar mamakin irin soyyayar da Hajia ke yiwa TAUFEEK, a kashedin da ta kawo har tana haki Elhaji ya kwashi ya fada yana fadin lalle yau zai sasabawa TAUFEEK din, sai cewa ta yi ita bata fada dan a masa fadace fadace ba, ta fada ne dan a saka shi ya zauna ta masa turare turarensa...., Watau irin yadda Hajia ke saka TAUFEEK a gaba ko Elhajin bata cika damuwa da ya yi turare tutarenta ba
Hajia harda sauke ajiyar zuciya ta saki murmushi ta ce" Dawo daga nan magidanci, ku kuwa ku tashi ku dan bamu wuri ai ba a gabanku zan masa shafen danyen man ba ko?"
Matansa dama sun san da su ake, a zaunen da suke kowace tamkar zata fashe dan jin haushi, ita dayar har ji ta yi alamun nakuda na tsikararta dan bacin rai, su dai har ga Allah matar nan da jikanta da kishiyarsu sun gama tsaye masu a wuya, ta yaya za'a ce mijinsu ya zo sun zo a zauna a yi fira ya ji yaya ya bar iyalinsa ama ta zo ta yi bake bake? Shi jikan nata ai yana da hankali domin da shine dan radin kansa ba zaka ganshi nan ba har sai uban ya kirayeshi, duda shima uban baya iya zama sai yana kiransa bini bini ka ga ya daga waya yana tambayar yana ina ne
Baki ta tabe a ranta tana ayana' in dai namiji ne? Ina ji a jikina nima shine a cikina, zan haifo shi na ga tsiya nan kusa ba da jimawa ba!'
Abinda ya birge Aba , Hajia na fadin su tashi harda Mama ta mike itama ta bi yan uwanta, irin karar nan da take yi idan mahaifiyarsa na wasu abubuwan na saka shi jin nutsuwa a zuciyarsa, domin har ga Allah wani abin ya san bai dace ba sai su ga dan ba su suka haifa ba, ama in ya ga Mahaifiyar TAUFEEK ta shige ayarin sauran sai ya samu kansa da sakin murmushi, watau matar nan itace ake kira matar rufin asiri mai kwontar da hankalin mai gida, ya tabata kuma suma zasu ji sanyin a ransu in suka ga fadan na Hajia ba iya su ya tsaya ba harda uwar TAUFEEK din
Duka kaf abinda ya dace ta masa ta masa sai sakin murmushi take tana masa magana kasa kasa tana aukin fadin" Allah ya baka hakuri ka ji magidanci? Ni na san koma waye ya taba min kai ba da gangan ya yi ba, khausara ai ba halinta bane bale nace itace ko? To koma waye ya je dan kansa Ni ba zai rikita min kai ba ka ji? Gama ganawa da MAHAIFINKA ka zo na dama maka fura da kindirmo haka take laudi ka sha abinka ka ji?"
Shi dai bai ce mata komai ba har ta dauke kaskonta ta yi gaba, dama abinda ya dameta kennan ta kuma yi, sauran rikicin a yi mana sai me
Tana tafiya Aba ya sauke murmushi a bayane yana duban TAUFEEK dake gaishe shi da yi masa Barka da zuwa gida lafiya
Bai bi ta kan gaisuwar ba ya ce" Yanzu Ιan mai Kwanoni uwata zaka yiwa aure a Saudiya???"
Shima abin sai ya bashi dariya har ya murmusa sosai yana murza gaban goshinsa
Elhaji ya sauke ajiyar zuciya da kula ya ce" Kai da waye wai? Nake gannin fara'arka du ta ragu?"
TAUFEEK ya dago dubansa ya zubawa mahaifinsa shi
A hankali ya sauke ajiyar zuciya yana Basar da zancen a harshensa ya ce" Ba komai Aba, shirmen Khausar ne kawai, ta gama service dinta a hospital din nan sai nace a kaita clinik, docteur bai fahimci tashi nake nufi ba sai kawai ya turata Lafiya, kuma a ranar ina gabatar da aikin nan na binciken ma'aikatana.....shine inaga abin ya bata mata rai sosai wai ko na boye mata, harda su cewa zumuncina da ita ba gaskiya bane ta soke komai........" Ya karashe maganar yana dan girgiza kansa da dan fitar da wani murmushi mai ciwo wanda kana gani zaka gane ba murmushin bane ya yi na kirki, a'a irin murmushin nan ne mai zafin nan
Kallonsa mahaifinsa yake yi, kallo irin mai tarin ma'anonin nan
A hankali ya sauke ajiyar zuciya yana sake duban Ιan nasa......... , Yakan tambayi kansa shin yaron nasa tsabar nauyin baki ne ke hadasa masa wannan abin ko kin gane gaskiya ne? Shin me yasa yake nan yana jira yana sakawa kansa ciwo a banza da wofi?
A hankali ya ce" kana nufin a yadda kuka shaku, shekara ta hudu zuwa biyar, baka kwatanta mata wanene kai ba MAGIDANCI?"
A hankali ya dan zubawa fuskar mahaifinsa ido, sai yake tunanin kamar shima ganni zai yi bai kyauta ba? Ko menene?
Ajiyar zuciya mahaifin nasa ya sake saukewa yana dan juyar da dubansa ya rage sanyin acn dake busawa
Da kula sosai ya gyara zamansa yana fuskantarsa ya ce" ka gane, In shekarun ka ajiye hudu nema ka jima da kaiwa , in halin kula da bukatunsu ne inaga kana iya rike wani gidanma ba naka ba, ko lafiyarka ne ba zata baka damar ajiyeta a gefenka ba? Ko ...........," Ya dan sasauta ya sake dubansa gannin ya yi wani tsuru yana kallonsa ya karasa maganarsa kai tsaye tunda dai shi din ai shine mai kwanoni uba a wajensa ba zai batar da shi a Saudiya ba ko?, A nutse ya ce" Ko tsoro take baka yannayinta ne?"""
Da sauri ya cire