Showing 12001 words to 15000 words out of 186303 words
mace har namiji sai KAUSAR, shi shi????
"Ana halo halo a wayar magidanci amsa mana ka gama na ji kukan uban me take yi ita kuma? Ba dai gaba take saka ka tana maka kukan rainin hankali ba salon a raba maka hankali biyu, jigilar gidan nan ka yi ko rikicin munafurci na mata? Ni fa ka ga du macen da za'a aura maka sai na kaita kotu ta yi rantsuwar ba zata cuta maka ba dan bana son rikita rikitar yan matan zamani yan iska masu taba halitar ALLAH sunna zanna gira da kwaliyar aljannu wai su masu kyau" ta karashe tana sake gyara tsayuwa ta dauke kai daga kallon da yake yi mata kamar ya ga bakuwar halita harda zarro ido yana kallonta da mamaki
Dididif din wayar ya saka shi kallon alon wayar sannan ya sake kallon Hajia dake harare harare
Kasa kasa kamar kar wani ya ji shi ya ce" Kin kuwa san wacece kika zazage tas ?"
Hajia ta juyo tana maka masa harara ta ajiye kaskon ta watsa magungunnan da ta harhada ta yi raf da hannunsa da ya kawo zai kautar da hayakin da ya shiga binsa bududu tana gyatsine ta ce" Ko wacece uwata, nace uwata in itace mai KWANONI kuwa ni nice babarta!, Alkur'ani idan baka san ciwon kanka ba na san ciwonka babu wace zata lalata maka zaman lafiya ta maka kukan kirsa ta cuceka ina raye!"
Har ga Allah bashi da karfin rikicin yau, haka kawai yake jin karfinsa ba na rikici bane yau, ga hayakin nan juya masa kai yake kamar zai sume bayan tace na mayu ne da na aljannu, shi kuwa ba maye bane a sanninsa haka kuma shi ba aljani ba, hayakin ne kawai bai cika so ba har wani makaki yake masa a wuya, ama ta ki ganewa sai da ta gama rikita masa rayuwa ta saki tana jan tsaki ta dauka ta ringa zagaye kujerar da yake zaune tana tofe shi sannan ta yi gaba tana ta fadace fadacenta
Idannuwansa a lumshe suke ya zuba su a kan hanyar da ta bacewa ganninsa a kala ya dauki minti biyar kafin ya sauke ajiyar zuciya ya shiga bude abincin ya shiga ci dan yinwar dake cikinsa idan ya kwonta ga takaicin Kausar, ga na Yumnah, ga na Hajia ana iya tardoshi ya karkace da hawan jinni, gwara ya cencani kansa tunda rayuwar ta zama haka
Sun dan jima kafin suke shigowa kusan a tare a lokacin Aba tuni ya dawo gida ya ci abinci ya shiga karatun Alkur'ani domin shi wannan lokacin kadai yake da shi wanda yake yin ibada sosai, dan kuwa idan ya fita nema baya zama sai dare ya yi kafin yake samun zama
Bayan sun huta Aban ne ya saka aka masa kiransu su dukansu ukun,
Sun jinginu ne a jikin garu kwon fitilar da nepa sula kawo ya haske dakin, hakan ya sa yake binsu da kallo daya bayan daya harda Mamansu Auta kuwa yana cen saman katifa yana barci abinsa
Numfashi ya sake saukewa zuciyarsa a tsintsinke ya shiga bayanin abinda ya wuni da shi a saman zuciyarsa wanda bai shigo gidan nan da wuri bane saboda sai da ya je wajen manyansa ya duka ya nemi shawara kuma aka amince masa da hakan harma aka sake bashi shawarwarin da zai ji dadinsu
A tausashe sosai ya ce" KAUSAR, A'isha, RUKAYA, na tara ku a nan ne dan na ji daga bakinku dangane da maganar aure......."
A cikinsu su biyun nan wani irin salama ne ya sauka a kahon zukatansu, ita kuwa wani irin firgici da tashin hankali ne ya dirar mata bayan fushin fadanta da yaron cen da ya raina mata hankali
Kanta a kasa yake, ama mahaifinta yana iya gane halin da take ciki domin ta kama hannunta sai murzar yar yatsarta take yi haka kuma kaffafuwanta dake hade daya kan daya sai murzasu take yi tamkar tana jin fitsari ya matsotan nan
Idannuwansa ya dauke cike da rauni ya sauke kan fuskar matarsa
Irin kallon da take masa mai dauke da girmamawa da mutuntawa da nuna alamu na tana tare da shi ya saka shi jin dan kwarin gwuiwa a hankali ya ce" In sha Allah gobe da safe ina jiran amsarku, kowace ta yi kokarin gannin ta bani amsar da ta dace mai kyau wace zan yi bincike a kai dan mu samu matsaya daya mai kyau, domin bi'izinillah shekarar nan idan har ta wuce ku babu aure to zan samo maku Wa'inda suka dace na hadaku na aurar, ku tashi maza a je a kwonta a huta, du wace bata yi shafa'i da wuturi ba ta tabatar ta yi kafin ta kwonta"
Amsawa suka yi su biyun, ita kuwa kai kawai ta iya gyadawa tana jin hankalinta na karra tashi
A hankali ta mike dan bin bayan yan uwanta , mahaifinta ya yi kiran sunnanta yana dauke dubansa daga kan mamanta dake masa alamun kar fa ya nuna gazawarsa
Juyawa ya yi ya ciro yar karamar wayarta da ta bashi ajiya tunda zasu fara jarabawa ya miko mata yana dan murmushi ya ce" Dama ga wayarki nan ai na san za'a samu kira yau ko?"
Wayar ta kalla, sannan ta kalli mahaifinta.....
Za'a samu kira?, To daga wajen wa?
Sai dai bata da amsa, hakan ya sa ta yi godiya ta juya ta fice ta karasa dakin itama ta kwonta saman katifarsu ta juya tana fuskantar garu
Tun tana jin maganar yan uwanta sama sama sunna waya da albishir wa masoyansu cewa Abansu ya yi tambaya kan abinda ya shafi zumuntarsu da sake jadadawa zumuncinsu da karra yarda in har alkarsu da burinsu na nan? har shiru ya wanzu a dakin a hankali minsharin Rukaya ya fara tashi hakan ya tabatar mata cewa sun yi barci ne
Idannuwanta kekyashe suke ba alamun zasu risina ko su aro barawon da aka sheda kwarewarsa a sata dan ya saceta ko dan wuni da ta yi a kai kawo da jigila kala kala na auren da aka yi yau, ama shi sarkin baiwa bawa kunya shiru bai dauketa ba, bai yi alamun zai dauketa ba
A hankali ta dago hannunta da ya sage ta dafa ta mike zaune sannan ta jinginar da bayanta a jikin garun ta kurawa waje daya ido
Wani irin hawaye ne mai dumi ya shiga kokarin saukowa daga cikin kurmin idannuwanta dan zubowa saman fuskarta a lokacin da ta shiga tambayar kanta shin menene laifinta ? Menene laifi dan ta zamto mai rufe jikinta?, Menene laifi dan Allah ya haliceta a yadda ya haliceta? Ita dai ba mai munin da za'a ce kai wance kuwa akoy muni ba, dan har fadi ake yi ta fi yan uwanta dorinar kyau kawai dan bata fitar da kyan ne......, Sha nawa ake cewa da ace zata yi kyale kyale irin na yan mata ta yada wannan hijabin da ta ga maza na biniyarta kamar kuda, mutun nawa suka ce idannuwanta, girarta, karan hancinta, bakinta abin kyau ne a idon mai kallo koda kuwa baya so.............., Fatar jikinta mai haske ce domin ta yi hasken mahaifiyarta ne, yannayin jikinta ba dati ba wari, shin wannan bai isa namiji nagartace ya nuna yana yinta ba?....., A yanzu dududu idan ta ajiye rayuwar nata a fili ta duba ba zata ce ga tsayaye nan da ya nuna mata aure yake so ba, ita fa kunyar yin zancema take ji, haka kuma kunyar yin saurayinma take ji, ita baban abinda ya fi bata kunya ace za'a mata aure itama, duda ta dade da yarda cewa auren nan ka so shi ko ka ki shi akoy lokacin da jiki ke amsawa hankali ya damu da bukatar abokin halita sai dai idan ka ki bada hankali ka yi watsi da lamarin a samu sasauci ba wai a daina jin bukata irin ta hannun bawa a jikin baiwa ba!
A yanzu shekara ashirin da shida kennan tana rayuwa, tunda ta yi ashirin da uku ta ga haila, a hankali ta shiga saka rigar mama duda ba wadatatun maman ne da ita ba ama mamansu bata yarda dan baiwa Maman kariya da zubewa ko lalacewa, ....sannu a hankali take fuskantar kaikayi irin na jiki mai zuwa ba dole sai an gayato shi ba, a hankali ta koyi korarshi harma ta dawo ta koyi rayuwa a haka,...............ita baban abinda ya fi tsaye mata a rai shine shin me ta yiwa maza da zafi haka ne? Me suke nufi to da ita ne? , Shin a matsayinta idan ta dauki dabi'a irin marar kyau yawo da dan gyale hakan zai zamto alkhairi a gareta da ahalinta da al'umar annabi kuwa?, Me yasa ita ta kasa samun wanda zai fito magana ta tsaya tsayin daka har ya kilaceta matsayin mata ba?, Sau biyu magana na yin kwari da ita har Aba ya sani sai dai shuuuuuu kamar an yi tsatsafa an dauke dan kuwa ko yarfin ruwan kafin a fito ya gushe a ido ne, dan mahaifiyar daya tsaf ta nuna ina hadinta da danta? Wannan jiki haka ai ba na zaman karamin yaro bane sai dai tsoho
Wani hawaye ne mai zafi ya ringa bin kumatunta, a hankali ta dora hannunta daidai kahon zuciyarta ta shiga ayana kalamai kamar haka' Shin laifin duka nawa ne? Nice ko? Nice na kasa maida hankali nima na yi kwaliya ko an aureni ko?, Nice na kasa tsayawa na yi dinki irin na yan mata ko a kulani ko? Du laifina ne nice nan bana sakewa mazan fuska ko?, Dan Allah Allah ka san nima na samu mai sona ko na samu ciwon dake zuciyata ya bace, domin *DA CIWO A ZUCIYATA* mai karfi ubangijina......'
Gannin tana neman kamuwa da cutar cuwon barin kai saboda tunani ya sakata mikewa a hankali ta je ta dauro alwallah sannan ta dawo ta kabarta sallah ta shiga yin nafila
Sosai takw hawaye a cikin sujadarta tana ambaton sunnan Allah kamar yadda ta saba, fatanta Allah ya bata miji na gari itama wanda zaya *YANTATA*, Burinta ta samu miji na gari wanda zai sota domin Allah ya riketa domin Allah, ta tabata Allah zai bata itama , a da damuwar bata gigitata har haka, a yanzu da mahaifinta ya yi maganar nan sai ta ji duka kaf hankalinta ya gama tashi
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
*DA CIWO A ZUCIYATA*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 6οΈβ£
LITATAFAN MARUBUCIYAR
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicΓ©
Lait de nuit
Parfums dΓ©sodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaΙannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiππ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mataπππππ
A yanzu da mahaifinta ya yi maganar nan sai ta ji duka kaf hankalinta ya gama tashi, bata da wani sukuni, da kyar ta ji sasauci a zuciyarta har barci ya yi awon gaba da ita
Dukkan abinda suka saba yi da sanyin safiya yauma suka gabatar, sai dai babu wanda bai kula da yannayin sanyin jikinta ba har suka zauna dan karyawa
Sunna tsaka da karyawar ne aka yi kiran mahaifinsu cewa yar abokinsa ta rasu magidanciya, wannan dalili ya saka shi mikewa ya shirya da gagawa ya fice ba tare da sun samu sun yi zaman na safia ba
A sanyaye ta sanar da mahaifiyarta yau ake kafa masu result na exam dinsu da an jima zata je, maman nata ta amince ko dan ta samu ta je ta dan sake, domin itama karfin hali ne take yi bata da karfin jure yannayin KAUSAR
Du a nan tsakar gidan suke zaune KAUSAR ta yi wanka ta shige
Da kiciniya dai su suke ji, ama babu wanda ya kawowa ransa abinda yake faruwa, haka kuma ta dan dauki lokaci a cikin dakin bayan ba sabonta bane jimawa ana shiryawa har ta fito tana ta sisine kai dan har ga Allah kunya take ji kwalin da ta saka da girarta da ta caje da dan jan bakin nan kar mahaifiyarta da yan uwanta su gane, sai dai ta makaro domin ko kanshin turaran da take bazawa ya fi wanda ta saba dan gigawa hamatarta, na yau mai girma ne, haka da ta duka dan amsar kudin da mamanta ke bata dole suka yi ido hudu har maman nata ta ga kwalin dake saka idon nata hawaye dan bata saba ba, hakan ya sale karyar mata da zuciya ta dauke kai da sauri ta laluba yar karamar jakarta ta ciro dari biyu ta karra mata sannan ta suri bokici ta ce" Idan kin fito daga leka sakamakon ki tsaya gidan Laria ta maki kitso "
Kudin ta cure a hannunta ta yi wufff ta fice a gidan cike da tarin kunyar hijab din dake jikinta bai kai mata har idon kafa ba kamar yadda ta saba sakawa, tsayinsa daya da tufafinta
Tun tana tunanin zata iya jurewa ta dago kanta har ta sadakas gaba daya ta ja hijabin ta rufe jan bakin tana jin nauyi a ranta kamar ta aikata wani abin kunya
Haka ta je ta duba result dinta sannan ta fito ta karasa gidan Laria ta shige suka shiga hirar yaushe gamo aka kwonce kan aka shiga wankeshi bayan ya bushe aka dasa mata kitso wanda zai hau da yannayin gashinta
Ita da kanta sai ta ringa jin wani dadi dadi a kan nata, bama da ta je ta yi alwalar sallar azahar haka ta jita sakai ruwa na ratsa dukan kofofin kanta
Sai kusan la'asar ta fito daga gidan, haka kawai ta dasa tafiyar kafa, tafia a hankali ba kamar yadda ta saba ba, tana tafe tana tunanin dacewa a cen kasan zuciyarta, a ganninta yanzun kam ga kunshi a hannunta, ga kitso, idonta da kwali daidai gwargwado dai ai kwaliya ta kare ya dace ta samu mashinshinin da zata yiwa Abansu maganar itama ta samo fa, sai dai abin mamaki har ta cinye dogon layin kasuwa ta shiga na gidansu shiru kake ji wai maye ya ci shirwa, a lokacin da ta kawo kan kwana nema ta kusan hadewa da wani dan garuwa kana ganninsa ka san ba yaro bane ya wani ce da ita yi hakuri Mama ban kula ba
Ita da abin ya wani daketa ko ci kanka bata ce da shi ba ta ci gaba da tafia zuciyarta na zafi har ta shige gida
Ko da ta shiga gidan kasa cin abinci ta yi,mahaifiyarta dama sunna cen kai gara, sai kannenta Rukaya na kicin Aisha na wanke wanke ya wuce dakinsu ta tsuguna cen wata loko ta hade kanta da gwuiwa ta fashe da kukan da take ta rikewa tun a hanya
Da sauri Aisha ta dago daga wanke wankenta ta kallo kofar dakinsu, hakama Rukaya dake kada miya da sauri ta kallo wajen
Rige rigen shiga dakin suka yi dan kukan na KAUSAR har tsakar gida
Gaba na Faduwa Aisha ta duka tana kokarin kama KAUSAR ta ce" Auntynmu lafia? Waye ya saka ki kuka?"
Rukaya da tuni ta fara gargadar murya zata fashe da kukan itama ta ce" Auntynmu wani abu ya same ki? Ke da waye kike kuka?"
KAUSAR ta yi iya yinta dan ta yi kukanta ita kadai ama abin ya faskara, a dole ta dora kanta a gefen kafadar A'isha tana kukan ta ce" Aisha, na shiga uku, wayo Allahna, A'isha shin menene cutar da maza basa so a jikina? Na zama katuwar budurwa a cikin gida na kasa matsawa da tuntuni kuma kun samu kun matsa?, Aisha ku bar gannin na mayar da hankalina kan karatu ba dare ba rana ni dai karatu nima fa mutun ce kuma abinda kowa ke so ina so, Aisha samuwa ne bai yi ba a dole na hakura na rungumi karatun dan shi baya min tawaye, Rukaya kunna gani in dai aka ce ana sona dan tsokana ne ko dan a batan lokaci, dududu yan matancina bai fi a irga da na hadu da su ba suka nuna na masu, To ni yaya zan yi da raina ne?, Ni babu ruwana da sana'arka in dai na halal kake nema, nagartace mai halin datako nake nema wanda zai rikeni da mutunci nima, Aisha kunna gani habaice habaicen dangi har bana so a yi taron da dole sai mun je dan ta yannayin kallon da ake bina da shi kadai sai in ji du na tsani kaina, domin wasu basu zageni ba ama kallon da ake bina da shi yana fasara abinda aka kule a zuciya a kaina, shin ba za'a fahimci y'ar sunna nake du rashin hankalina ina son raya sunna ba?, Kun ga dai yanzu Abanmu shima hankalinsa ya karkato kanmu, kuma yana fa gaskiya shekaruna nawa bale ku?, Ina matukar jin tsoron na kasa farantawa Abanmu bayan shi rayuwarsa kulun a cikin faranta mana yake , bawan Allahn nan a