Showing 81001 words to 84000 words out of 186303 words

Chapter 28 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18747

dan rayata a hannunsa na hagu da dayan hannun nasa ya dan talafota a lokacin da ta karaso tana kokarin dane damuwarta


Fuskarta ya dan zubawa ido kadan, kasa kasa ya ce" Ki yi kokarin wuni a wajen hajia yau Yumnah...."


Cikinta sai da ya juya daga tsayan da take, ta zata ya manta da maganar cewa ta je 5 gaisar da Hajiar da ya mata, sai gashi abin ya ce za zani harda su ta wuni a cen?, Wuni? Ita da matar nan? Tap to ita ta wuni a yaya kennan? Ai ta tabata tana iya wuni ne cikin ukuba da tsoro, matar da kowa tsoronta yake a gidan? Bale ita da ta tsaneta Ζ™arara? ..... gaba daya sai ta rasa kuzari har ya fice a gidan ba tare da ta tabuka abin kirki ba


Saman kujera ta zauna tana sauke numfashi bayan ta dannawa mahaifiyarta kira
Kamr ko yaushe jajen Khausar ne suka yi, mahaifiyarta cike da mamaki ta ce" Wai a yanzunma da yarinyar nan ta fita a makarantar su ba zata rabu da shi ba?, Alakarsu ta fara bani tsoro Yumnah"


Yumnah ta share hawayen da suka tarun mata a gurbin idannuwanta a sanyaye ta ce" Mama, sai kin ga kamar ba ita a duniyar da sai kuma ki ga tana nan daram a duniyar tasa, kin ga dai an dan jima ban ji duriyarta ba, kuma bata zo gidan ba tun wancen zuwan da wancen tsohuwar ta yayabota, sai kawai dazu na ga yana ta danna mata kira da safiyar nan, Ni kam ban san wannan wace irin maya ce ba!"




Mahaifiyarta ta yi dan tsai, a dan kausashe ta ce" kema sai nake gannin harda laifinki, ta yaya zaki bari yana maki kiran wata a lokacin da kike tare da shi? Wannan fa saken ki ne ba komai ba, kuma yanzu ki zo ke hankalinki a tashe nima kina tayar min da hankali, a gaskiya wannan din saken ki ne!, ya dace ki san mace kike in ta laluma ko ta tsiya ki kwatantawa mijinki idan yana gabanki kece a gabansa ba wata banza ba koda matarsa take bata da wannan hurumin in yana gabanki naki ne ke daya!, Ama sai kina wani abu kamar wace ke jin tsoronsa, in na baki shawarwari ki nunan kin dauka ama in na tambaya sai ki nunan baki yi ba zaki yi, mazan nan na zamaninmu ma ba wani cika kiyaye hakin iyali suka yi ba bale na yanzu!, Na fada maki da kirsa zamu rabata da shi ama kuma wani abin sai mun dora doka irin tamu ta mata, ki sani mace fa sarauniya ce in ta yi wasa kuwa tana iya zama bola, kuma du namijin da yace shi karya ne babu macen da ta isa ta juya shi ko wani abin karya yake Yumnah, bai dai hadu da mai juya shin ba, kar ki yarda TAUFEEK ya fi karfinki ta yadda zaki dawo kina kuka da barin jiki idan ya yi magana Ni dai na fada maki, kuma maganar zuwa wajen kakarsa ban ce ki wuni ba, ko daya ban saka ki ba, ki je ki gaisheta sama sama ki dawo dakinki ko uwarsa ban saka ki sakin jiki da ita ba bale wata kakarsa da ba sonki take yi ba ni kin ji maganata!"
Daga haka ta kashe wayar tana ta bambaminta, ta bar Yumnah cikin wani dogon tunanin da sake daurar damarar yaki da duk wata halitar da zata iya zamtowa matsala a duniyarta da mijinta ko wacece!


Da wuri ya iso asibitin, domin yau aikin ba iya na takarda bane na aikace ne wanda yake saka tsauri sosai a cikin lamarin


A wajen ajiye motocinsa na asibitin dake gefe daban da sauran motocin manyan ma'aikatan cikin asibitin ya ajiye motarsa a hankali ya sake daukan karamar wayarsa a kasan zuciyarsa yana tunanin me kennan? Me yasa take kin daga kira harda numbar da bata sani Bama?, Bai san me yasa fushin nata ya masa katutu a cikin zuciya ba


Iska ya fitar mai zafi daga bakinsa a hankali ya juya da niyar daukan bak'ar jakarsa dake ajiye dan ya fice zuwa ciki, domin tuni vigil biyu ke jira ya fito su amshi kayan hannunsa idan yana da su, ya dago dubansa a hankali dan bude motar ya fito nan ya dakata da sauri yana ruko idannuwansa ya zuba mata ido


A hankali ya sake dan kifta idannuwansa yana sake dubanta dan tabbatarwa ko dai ba ita bace? , Sai dai a lokacin da ta dan dakata tana laluba yar bakar dake hannunta ta ciro karamar bak'ar wayarta ta duba kiran da shine ya yi mata shi ta katse kiran ta jefa wayar a jakar ya tabatar masa lalle wannan baiwar Allahn dake tafiya zuwa cikin asibiti da shiga irin ta riga da sket daidai da jikinta, kanta da dan karamin hijab fari kal mai dan kwaliya, sai kuma dan mayafinta siriri fari kal a gefen kadarta ta yi yafe da shi, yafe jama'a ba ta bude shi ta rufe jikinta ba, harda yar agogo siririya a hannunta baka sidik wace ta kama hannun nata ya mata wani irin sassa gwanin kyau


Bai ankara da kallon da yake mata ba har sai da ta bacewa ganninsa


Da mamaki ya dan dafe goshinsa a hankali ya furta" me kike nufi ne Khausar?, Baki isa ba!, Hakan ba zai taba yiwuwa ba, dan kina fushi da ni ba zaki fito a haka ba sutura ba!"
















πŸ˜”πŸ˜• Inaga dole sai mun hadashi da Hajia ta ce igiyar uban wa ke wuyanta? Ni dai ba luwanaπŸ€£πŸšΆπŸ»β€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™€οΈ


πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”β€β€πŸ©Ήβ€β€πŸ©ΉπŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”




*DA CIWO A ZUCIYATA*




πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”β€β€πŸ©Ήβ€β€πŸ©ΉπŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 3️⃣0️⃣


*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*


1: Duk karyar kada


2: Yar mahaukaciya


3: Neman na kaina


4: Bani da zabi


5: Bak'a ce


6: Kutkale


7: Makauniya ce


8: Mage


9: Duk nisan jifa


10: Idan ka raina inda kake


11: Dutse


12: Alkalamin kadarata


13: Bani da zabi


14: Dakika Biyar


15:Wata kokowar


16: Aure yakin mata


17: Ni zan ladabi


18: Daga tafia daukar soja


*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicΓ©
Lait de nuit
Parfums dΓ©sodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaΙ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiπŸ’ƒπŸ’ƒ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙ“i wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan MataπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ








Cike da jin haushin ta ya yi kyaftu ya zauna nan ba tare da ankara da yannayin lokaci ko yannayin da yake ciki ba, shi ba aiki ba, shi ba tafia gida ba, karshema sai ya danna buton ja dake nunin idan yar fitilarsa ta bada kar a shigo office dinsa baya bukatar gannin kowa


A lokacin da Khausar ta fito sauri ta ringa yi wajen saukowa daga kasa, cikin sauri ta nufi bangaren su ta shige dakin su na mata sannan ta yi bayinsu da sauri ta shiga ta rufe kafin ta karasa ta dukar da kanta jikin abin alwallah ta ringa sakin nishi a jajere a jajere, sai kuma hawayenta suka bale tamkar an bale mata
su ne
Bata san dalilin da ya sa take jin dacin abin har haka a ranta ba
Ko ba komai ai ya nuna mata a kan aikinsa yake, kawai abinda ya sa abin ya mata ciwo ainun tunanin an wulakantata ne, an wulakanta iliminta da hankalinta
A kan abu daya ta ajiye kusancin da TAUFEEK ya kirkira tsakaninsa da ita dan ta zamto balagazar makaranta wace ta san kowa take hulda da kowa ba ruwanta da ta birgeka ko ta mata kwaskwasa dan ka sota, kana iya yin firarka a gabanta dan ba abinda ya shafeta, haka mu'amalarta da malamai du irin yadda duniya ta lalace ita dai da su ido ne domin ko kucakin malami ba birgeshi zata yi ba a yadda ta gudanar da rayuwar makarantarta


A dole abin ya mata ciwo mai zafin gaske
A dole abin nan ya taba mata zuciya
Bata san me zata ce ba, yaya zata yi, tana matukar jin ciwo mai girma a zuciyarta na irin yadda mu'alamarsu zata ruguje tana ji tana gani
Sai dai rugujewar shine alkhairi dan bata ga kuma me zasu iya cewa junna a yanzu ba, ya fi karfinta ya fi karfin ajinta shi din ba abokin yinta bane, ta kowani fani idan ta duba a yanzu sai ta ga idan har ta yarda ta sakawa ranta ci gaba da shi din kamar ta cuci kanta da kanta ne


A hankali ta dafe kanta hawaye take yi sosai sannan ta dafe gaban kirjinta a sanyaye ta ce" Ama da wa zan yi fira? Wa zan SANARWA damuwata?, Wa zai rarasheni? Waye zai min fada? Wanene zai ringa sakani ko hannani bayan su Mama?, Me yasa ka saka na sakankance da kai haka? Me yasa ka shiga jikina haka?, TAUFEEK baka min adalci ba, baka min adalci ba TAUFEEK, shin yaya zan ci gaba da walwala ba farin cikinka a tare da Ni? Ya Allah ka bani mafita mai sauki a cikin lamarina.........."
Surutu take yi irin na zafi da ciwo a cen kasan zuciyarta....... Ta shagala sosai yar karamar wayarta ta shiga kuka a cikin aljihun rigarta


Da sauri ta lalubo tana tunanin ko dan sahunta ne da ya ga shiru bata tabo shi ba har yanzu?


Numbar ta zubawa ido tana kallo, domin bakuwar lamba ce a wayar Tata


A hankali ta daga tana dan gyara muryarta hadi da yin salama sannan ta yi shiru
"Amincin Allah ya tabata a gareki kema Likitana....."


Shiru ta yi, jin Muryar namiji ne, da kuma abinda aka fada din


A hankali ta dan budi bakinta ta ce" Ban gane mai maganar ba?"


Dan murmushi ya yi shima ya ce" Allah sarki dama nace akoy sanyin murya matata to be in sha Allah, jiya na turo kanwata Salma ta amsar min numbar dan na yi na yi na tareki na amsa na kula da wahala fa ki saurareni a hanya, karma aje ki ce min bakya so na na suma dan firgici"


A hankali Khausar ke dan sauke numfashinta, lokaci daya ta afka wata sabuwar duniya ta tunani da tarin mamaki


Yayan Salma?, To wane? Salma dai Salma? Kai, anya kuwa? Har yake kiranta da matarsa? Ko dai ya yi batan numba ne?, Da wahala in ba batan numba ya yi ba, ya rab.........,
Sai dai du rikicewar ta wannan karron sai ta ki kashe kiran haka kuma ta kasa yin wata magana da zai iya jin ba dadi


Ko ba komai tana kan gaba ne ta nema irin wannan


A hankali ta dan sauke numfashi jin yana ta afkin fadin ta amsa shi plz


A sanyaye sosai ta dan ja numfashi ta ce" Zan je gida ne na ga dan sahuna na kira"


Shima a sanyayen ya ce" Ba damuwa, sai kin zo, plz ki kular min da kanki, sannan zan yi kira idan kin huta dan ina so ki amsheni, ki dubeni ki bani dama kin ji kanwata????"


Murmushi ta samu kanta da saki a hankali ta furta" Na gode"
Sannan ta kashe kiran tana dan samun kanta da sake sakin murmushi


Yayan Salma? Yayunta maza biyu ta sani.....shin wanene a cikinsu?................haka kawai ta tsinci zuciyarta da jin nutsuwa da farin ciki harma ta wanke fuskarta ta fito ta cire rigarta ta nade ta saka a jaka sannan ta dauki kayanta da mayafin nan nata ta kade ta dora a kafadarta tana turo baki cike da jin haushin furucinsa wai wani bata yi kyau ba, kar ta yin, karma ta yin! Ai dama ba cewa ta yi ita mai kyau bace, kwaliya ne yace itama ta aura irin na yan mata!...........
Haka ta yi ta fadanta a zuciyarta har ta samu ta fada adaidaitar, domin ba wani a sake take ba da mayafin nan, kawai rikici ne rigima ce, kuma tunda ta yafa shi mamama da mamaki tace a haka zata tafi ne? Tace eh, mama ta ce da ta bude shi ta dan yafa jikinta duka sai tace ai ba komai , ita dai Mama kallonta ta yi tana jira ta ga da gaske? Sai kuwa ta ga da gasken ta tafi da yafen, jirantama tane yi a gidan ta dawo su zauna dan ba dabiar kirki bane hakan sam






Rai bace Taufeek ya dawo gida, domin kowa bai je nema ba dan a sama sama yake ba zai iya jure wani neman fitinan ba, direct bangarensa ya nufa yana mai kokarin kawar da dukkan wani bacin rai dake taso masa ko dan kar ya shiga hakkin abokiyar zamansa, domin ba ita ta hasala shi ba idan ya sauke mata fushinsa bai yi mata adalci ba


Sai da ya yi wanka ya sauko sakamakon irin yadda ta yi ta kai kawo cewar abincinsa na jiransa


Zama ya yi saman cafet a hankali ya mika hannu ya kashe tv dake yi, domin baya son hayaniya ne sam, kansa na dan masa ciwo, gaba daya ransa a dagule yake, sai dai abu daya da ya sani shine ba damuwa ya kyaleta, zumunci ne tunda ta katse babu yadda zai yi, ba zai saka mata wuka a wuyanta ba kan dole sai ta yi zumunci da shi tunda bata ra'ayi, yaya zata kasa yi masa uzuri a kan abinda yake aiki ne nasa? Idan ta ji cewa Yumnahma bata san komai game da aikinsa ba a matsayin dan kasuwa kuma matashin dan makaranta ta san shi ta ce me kennan? Ya dace ta masa uzuri, yaya take tunanin zai fito ya ringa yayata mata maganar sirrin aikin da yake da girma da daraja irin ta taimakon rayuwar dan adam?, Itama da gangan ta kasa gane cewa ya jima da samun takarda irin tata take tafe a makance, da gangan ta ki fahimta dan kawai ta daga masa hankali, kuma ta taki Sa'a ta daga masan domin ta fado a daidai lokacin da ta riga ta gama zamtowa tamkar jinnin jikinsa, yar uwarsa ta jinni, ama kuma ba komai dan uwankama yana iya kinka ka rayu kuwa !


Abincin ya ba hankalinsa bayan ya budi baki da kula ya ce da ita" Thank you" sannan ya yi bismillah ya dan fara tsakura


Ya koro da tabawar ya ji du ya koshi, a dole ya mayar gefe ya dan dauki jus din kwalba da ta zuba zai kai bakinsa yace" kin je kin wuni a bangaren na Hajia?"


Sai da gabanta ya fadi jin tambayar da ya yi mata, sai dai ta Basar cikin kisarta ta ce" na je , eh na je"


Yannayin da ta dan sosa gaban goshi ya bi da kallo , kasa kasa ya ce" ina nufin kin wuni a cen din ne?"


"Aa ban wuni ba, ama a kalla na kai minti ashirin......." Ta fada cike da tabbatarwa kanta ai ba zai yi fushi ba tunda ta je din


Jus din ya ajiye yana binta da kallon mamaki


A tsanake ya ce" kina so ki ce min umarnin da na baki ki je ki wuni da Hajia baki cika ba?"


Da sauri ta dago dan jin yannayin amon muryarsa ya cenza daga laushi laushi zuwa yannayi mai zafi zafi


Rai bace ya dan sake dubanta ido cikin ido ya ce" Wannan din ya zamto na farko kuma na karshe, da zaki take umarnina, idan nace kaza za'a yi shi za'a yi! Sannan ki kula ki kiyaye mutuncin dangina ta haka ne zan iya mutunta naki, Hajia kakata ce, ki kula, ki bata girman da take da shi idan ba haka ba bana tunanin in har zamu iya fahimtar junna!"


Daga haka ya mike ya bara mata jus din gaba dayama ya fice a falon


Hankalinta sosai ya nemi barin jikinta, lokaci daya jikinta ya dauki rawa ta rasa yaya zata yi, ya fi a irga tana gwada bin bayansa tana komawa dan ta ga ya nufi bangaren Hajia, karshe dai nan ta zauna ta zuba uban tagumi tana gadin dawowarsa dan ta bashi hakuri, in dai wajen hajia ne zata je zata je ta labe har yama ta yi ta dawo dan ba zata iya zama su shaki iska daya da hajiar nan ta kasheta a banza a wofi ba




Tunda ya shigo bangaren Hajia ya nemi waje ya zauna ya hade gabas da yama bai ce da ita ufan ba har ta zo da kaskon turare turaranta ta ce" Gaba daya ka fara aiki irin na wa'inda basu cika jin tsoron Allah ba magidanci, yanzu yau kwana biyu fa ban maka turare ba, Ni kuma ba zan ba wancen muciya da zanin kayan tsarinka ta je ta cenza da yan barbade barbade na matan zamani a malake min jika a sakani uku, gyara zamanka dan dage rigar nan na shafa maka a bayan cikinka wannan akace sunnansa kaikayi koma kan mashekiya, du wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login