Showing 96001 words to 99000 words out of 186303 words

Chapter 33 - DA CIWO A ZUCIYATA COMPLT BY SAJIDA.txt

09 Nov 2024

18783

ba, nan da nan ta sakawa ranta cewa eh lalle da gaske Salis yake bai zo da wasa ba kamar yadda ya sanar mata, ya fada mata cewa zai turo mahaifinsa da wuri a tsaida komai dan yana so a yi komai kafin tafiyarsa, a cen kasan zuciyarta babu abinda ya cika mata zuciya sai tarin farin ciki da zumudi da kuma adu'ar Allah ya nuna mata ya kuma tabbatar mata da alkhairin hakan, ta kuma tabatarwa iyayenta cewa tana kan bakanta, koda a rashin sani aka daura mata aure ya dauru dan su suke da ita ba ita take da su ba


Daga nan ta shirya ta wucewarta wajen aiki, zuciyyarta cike da tunani kala kala , abinda ya fi komai tsaye mata a rai shine farin ciki, sai dai ko TAUFEEK ba zata sanarwa ba , sai ta ga abinda yake faruwa ya tabbata kafin kowama ya ji,
Haka ta wuni aiki cike da tunani har yama ta yi ta juya gida a ranar ko haduwama basu yi ba da Taufeek dan bai shigo asibitin ba, sai dai tana ji a cen kasan zuciyarta da wahala yauma ta iya kwontawa ba tare da ta dan sanar masa abinda ke tafe ba, ta rasa ta yaya take iya wannan abin, sam bata san wani abu wai shi sirri tsakaninta da shi ba, ga yan uwanta mata dai, sai ta boye masu abu dubu bata boyewa TAUFEEK ba




_____________________________________






Firar dare suke yi su uku a saman baban filin wajen hutun Aba, watau da Aban, da HAJIA sai TAUFEEK


Kusan firar ta fi yawa tsakanin TAUFEEK da Aba, domin Hajiar zaune ne take sai kada kafa take yi abinda ke bakinta mai yawa ne ama zuwan TAUFEEK ya sa ta kame baki dan yana mata fadan irin hakan, yana hannata kawowa mahaifinsa karar matansa, bayan ita tafe take da magana mai mahimmanci ta abinda bata tunanin zai haifi ɗ'a da ido, domin ita ke gannin take taken iyalinsa a kan sarakuwa daya tak da ta fara shigowa gidan, yarinyar sam bata da wayo, in ba rashin wayo ba ta yaya zaki zo gidan da sarakuwarki a ciki ama tsakaninta da ke in ta sauko ta ganki ku gaisa shikennan, koda yaushe kina nanike jikin kishiyoyinta kina aikata me Kennan? Da ace kin tarar da wata fahimta bayananiya da sai kice ai kansu hade kika tardo su, ba'a hannaki musu biyayya ba ko yin zumunci da su da zama inda suke ba, ama ta yaya zaki fifitasu a kan mahaifiyar mijinki? Dama ita HAJIA kaka ba ta kanta take ba dan kuwa Yumnah ta gaisheta bata gaisheta ba du ita ta gano, ama mahaifiyar taufeek da ta zamto kunnu huce in shaka ba zata yarda a ringa raina mata wayo ba gaskiya, shi yasa take zaune sai sake hade baki take tana turowa cike da gundura da jin firar tasu, kuma ta tabbata da gaya Magidanci ya ki basu waje suke firar kasuwanci shi da ubansa, dan ya san mai kwanoni da son fira da shi yake takalo maganar nema, ai kam yau ko ita ko su an ga wanda zai gaji dan kuwa a harshen zanninta akoy goro daure tun dazun da ta ji alamun za'a raina mata wayo takan ciro ta kantsa sannan ta daure tana binsu da kallo da harara


Wayar Aba karama dake kuka ce HAJIA ta kawo masa, da kyar take tafia domin a dazun anma zata zata haihu ne sai kuma nakudar ta dan lafa, ama yanzu haka cikinta take shi yasa ta tahowarta bangaren mijinta dan ba wani yarda zata yi dayarsu ta ga gazawarta a wajen nakuda ko haihuwa ba bale kishiya ta yadda mata magana


Wayar ya amsa yana mikewa ya dan yi gaba, dan maganar da zai yin yana bukatar ya dan matsa


Jim kadan ya dawo yana dan murmushi gannin Hajia ta sakar masa harara tana dauke kai ta dubi TAUFEEK ta ce" Wai Ni ko meye abin munafurci a waya kuma? Salon a yi gaba a yi da ni, to ahir dinka inma aure zaka yi ba dai uwar Magidanci zaka karawa ba , ah to , ko mema yace a wayar Allah na tuba?"


Taufeek ya hade fuska yana mata duban nan nasa idan tana abinta tana sako ubansa, hakan ya sa ta sake tabe baki ta dauke kai ta ce" Dadin abin mai kwanonn nice nan babarsa ba wancen sanyi karai din ba, ina da damar daukeshi da mari in ta raya min babu mai ce min na marar masa d'a ehe!"


Aba ya saki kawatacen murmushi yana kaiwa zaune ya ce" Allah ya huci zuciyarki HAJIA, dama maganar auren KHAUSAR ne "


A tare da ita da TAUFEEK din suka zuba masa ido, sai dai cikin ikon Allah Aban ya kame bakinsa ya shiga dan duba wayar hannunsa


Kallonta TAUFEEK ya yi a hankali gannin ta yi shiru bayan Aba dai ai d'anta ne kuma ya fara magana ya yi shiru bai gama ba? Ai Bama kyau fara zance a kyale,


HAJIA kuwa da kufula ta karɓe wayar Aba sannan ta nuna shi da wayar ta ce" Kai zaka bani magana a bude a bayyane ko sai na rotsa wayar nan ne Ni?"


Aba ya zuba mata ido, sai kuma ya saki murmushi ya ce" Au, HAJIA dangane da maganar auren KHAUSAR din ?"


HAJIA ta gyada kai ta ce" Eh mana da nawa?"


Aba ya girgiza kansa da sauri ya ce" dama maganar ce mahaifinta ya sanar min cewa nan da yan kwanaki goma haka za'a daura mata aure ta samu miji a anguwarsu"


Kusan a tare bakin HAJIA da TAUFEEK suka yi magana, TAUFEEK da subutar harshe ya ce" Khausar din?"


HAJIA kuwa lokaci daya ta shiga sallalami tana tafa hannu kafin ta debowa TAUFEEK wani duba tun daga ƙafarsa har kansa ta watsar ta rafka tagumi ta ce" ka cucemu, ka gama cutarmu, sai ka shirya tun gobe mu je kasuwa Ni da kai mu ciro anko mu maidawa kura aniyarta , daga nan ka kaini wajen masu kayan ganye in hado hade hade na tsumi mu zo in tafasa mu kai mata ta shiga sha dan tsumi iya tsumi sai na tsumata alkawari ne na yi kuma cikawa ya zame min tilassss!, Kai wannan yaro wannan yaro da kake gani ka haifi durum baki a dinke , kai yanzu wannan hali ne? Da WANCEN abar a bushe uwa karauki zaka gama rayuwa? Ama ba'a more aure ba sam, kuma ba'a gaji uba ba, kai ko koyi na zaka yi da mahaifinka ba? Siririya daya ya yi ya ga ba riba ya ajiye, yanzu idonka idon Khausara wani zai dauka? Dubata fa cinyoyin nan ko na sa albarka, bayanan kuwa tas kake ajiye faranti ya zauna......."




Idannuwansa ya lumshe a hankali sakamakon yadda amon Muryar HAJIA ke amsa masa a kwakwaluwarsa


Da kula ya sake zuba mata ido a karro na biyu yanai mata alamun ta iya bakinta ama zuba take tana fada har tana neman share hawaye, d'anta kuwa na bata hakuri cikin ikon Allah


A hankali ya iya saka takalmansa da ya cire ya dora ƙafarsa saman abinda ta shinfida ta zauna ya mike cikin kula da yannayinsa ya juya dan sai ya ji sam surutun ne baya so


"TAUFEEK?" Aba ya fada yana dubansa da dan mamakin yannayinsa, duba da yanzu yanzu suke firarsu a sake yadda suka saba


Juyowa ya yi dan amsawa sai ya ga shi din suke kallo, hakan ya sa ya sakar masu murmushi yana dan sosa goshinsa a hankali ya ce" Aba, inada wani aiki ne ashe yanzu na tuna, good night"


Aban ya amsa shi da Allah ya tashe su lafia sannan ya tafiyarsa ya bar Aban da HAJIA na tatauna wata muhimmiyar maganar




A daren nan, wani irin ciwon kai mai masifar zafi ne ya sauko masa, wanda ya danganta shi da rashin isashen barci ne kwana biyun da baya samu, dan haka ya yi iya yinsa dan ya samu hutun ama sam barcin ya ki zuwar masa


Lokaci kankani ya samu kansa cikin yannayi na mugu mugun bacin rai kan abubuwa da dama, domin yana dawowa daga sallar asubahi fadan da ya rike bai juyewa Yumnah ba ya sameta har dakinta tana shafa manta ya sauke mata kwondon balakin da ya tayar mata da hankali, domin tsohuwar maganar da take jin salama a ranta cewar ya manta ce ya taso mata ya sakata gaba ya mata wankin baban bargo da jan dogon kashedi a kan ko da wasa ta kuma gigin wannan banzan tunanin a kansa zata sha mamakinsa, kuma ta kiyayeshi ba auren zobe ya yi da ita ba bale tace zata ringa yanka masa kashedi a kan irin mu'amalarsa da koma waye, bai kuma aureta da alkawarin zama da ita kadai ba dan ko yanzu aure ya kama shi yana iya yi babu yarjejeniyar zama da ita kadai a duniyarsa!


Daga nan ya fice ya shige dakinsa ya shiga wanka yana jin wani balaki na Kunno shi


Yana fitowa a wankan ya saka fara kal din jalabiyyarsa da dogon wandonta yana fesa turare dan ba zai fita da wuri ba aka shiga buga baban falon


Bai tsaya wani bata lokaci ba ya shiga saukowa dan budewa


Yana budewa ya saukewa HAJIA idannuwansa da suke rine cike da gajiya da abin barci


Kicin kicin ya yi da fuskarsa ya dubeta tsaf ya ce" Meye ? Zuwa kika yi ki kaini ciro anko da menema? Sai ki daukeni, nace ki daukeni , kin ga ki fita hanyata ki bani lafiya in kina so ba anko ba ki ciro Chaina ki laka ama ni ki bani lafiya!"


HAJIA ta hangame baki tana kallonsa hadi da gyara tsayuwarta ta ce" Ka ga wani ikon Allah ranar juma'a du Musulmin kirki ai ya farka da fara'a ama banda kai?"


Taufeek har zai juya ya juyo ya sake tsareta da harara yana tunanin inama ace wannan din nan dai in ya mata wani abu mai kwanoni ba zai tsine masa ba ?
Kwafa ya yi zai juya HAJIA ta sake gyara tsayuwa ta ce" Sai ka daukeni da mari in gane tabata ta sameka, Magidanci Ni din nan da kake gani kadangaren bakin tulu nake, a karni a kar tulu a barni in bata ruwan tulu!, Maganar anko kuma ai ka san dole ne mu fitar Ni da kai dan a ramawa kura aniyarta, YANZUN dai ubanka yace ka zo ga cen wancen tana nakuda mu je mu ajiye masu ita mu wuce kasuwa, kai in ba sai na nuna maka Ni na haifi mai kwanoni ba kace min ba Ni bace HAJIA!"


Daga haka ta juya har kamar iska zata dauketa ta nufi bangaren matan gidan sai bambami take tana ambaton ita Magidanci zai gwadawa danyen kai




A hankali ya lumshe idannuwansa yana jin harda juwa ke son maka shi a kasss, a Nutse ya koma saman ya gama abinda zai yi ya sanar masu a kaisu asibitin sannan ya kimtsa ya sauko ya shige mota ya bi bayansu yana jin kawai zazabi ne ke damunsa shi yasa yake jinsa wani iri, sai tarin bacin ran da yake kyautata zaton tarawa ne ya yi yake neman yi masa yawa a ransa,




Yana fitowa daga motar ya nufi bangaren amsar haihuwar
Bai shiga ba domin likitoci ne rufe kanta dan haka ya karasa wajen mahaifiyarsa dake zaune wace rabonsa da ita tun jiya da yama ya gaisheta da kula sosai sannan ya nemi kam su mike su karasa office dinsa idan ta sauka sai su sauko


Tun kafin ta bashi amsa HAJIA dake zaune ranta a matukar nace tana sake bin asibitin da kallo zuciyyarta tamkar zata kama da wuta ta dubi bangaren da HAJIA kaka ke zaune tana jan carbi ta sake hade rai ta ce" Ni kam ina nan ai ba za'a barta ita kadai ba"


Mama ta yi murmushi ta ce" Ka je kawai ka kama aikinka ai ka ga ba zamu je cen mu zauna ba mu da muka kawo mai haihuwa, nama yi kiran KHAUSAR tace min yanzu zata karaso asibitin ko?"


A hankali ya dan dago idannuwansa dake dauke da launin ja, zai bata amsa KHausar ta karaso da salama a bakinta ta karasa wajen HAJIA ta fara gaisheta sai wani washe mata baki take sannan ta karasa wajen su Maman ta duka har kasa tana gaishe su lokaci daya tana ajiyewa Maman dangin su ruwa ne ta dan kalli TAUFEEK dake gefen Mama ta ce" Morning besty, Mama kin ga ruwa kawai na tsaya cen na amso dan ban san da me zaku karya ba, bari in amshi katinsa in koma me da me zan kawo ne na kari na tabbata safiyar nan ba'a karya ba aka fito"


HAJIA kaka aka wani saki murmushi aka cira kai kasa kasa ta ce" Aikin banza, ga mace mai mutunci kana rainan hankali yarinya ta san darajar mahaifiyarka kana shirme, mu zuba mu gani dan mai Kwanoni!"
















😭 Ina tsoron HAJIA, HAJIA akoy rigima da neman mutun da balaki, sai wasu abu na neman fitina take yi🥹🥹🥹🥹 bayan mu oho sai mema wai☹️🙄


💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔




*DA CIWO A ZUCIYATA*




💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔


_MALLAKIN_


*SAJIDA NIJAR*


*FREE BOOK NE* 3️⃣7️⃣


*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*


1: Duk karyar kada


2: Yar mahaukaciya


3: Neman na kaina


4: Bani da zabi


5: Bak'a ce


6: Kutkale


7: Makauniya ce


8: Mage


9: Duk nisan jifa


10: Idan ka raina inda kake


11: Dutse


12: Alkalamin kadarata


13: Bani da zabi


14: Dakika Biyar


15:Wata kokowar


16: Aure yakin mata


17: Ni zan ladabi


18: Daga tafia daukar soja


*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*


Now


*Da CIWO A ZUCIYATA*






*Tallah, tallah, tallah*


*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*


_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_


Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes


*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata


Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃






Ita kam Khausar bata san komai ba, Mama kuwa murmushi ke kawace a fuskarta, cike da kular da ta saba ba KHausar in tana kusa da ita take dubanta bayan ta buda ledojin ta ce" A'a, ke da kika zo aiki kuma Khausar ma tsareki a nan? "


KHausar ta ce" A'a mama, yau din ai bani da wani aiki dama saloon zan je da wuri na koma gida na samu kiranki, gashi Maman ta fita itama da ta sama min wani abin na zo da shi sai kawai na sayo faro, bari dai in amso abincin"


Daga haka ta karasa kusa da shi sosai ta ce" Bani katin"


Tunda ya dinke bakinsa kasa kasa Hajia ce yake makawa harara tana maka masa, sai yanzu da ta wani tsaya masa a gaba


Aljihunsa ya laluba ya ciro katin ya mika mata da dan mamaki ya bi hannunta da kallo wanda ke dauke da kunshin da bai san da shi shekaran jiya ba
Kai kawai ya girgiza a ransa yana ayana' amare Kennan, dole a ringa kwaliya, dole ki tsirarwa kanki abubuwan da ba zasu fisheki ba, wai nine kike boyewa aurenki dan kawai na boye maki aikina???'


Zancen zuci yake yi, tsakaninsa da Allah sam bai san a me ya dora idannuwansa ba har wajen sai ido hudun da HAJIA ta juyo suka yi bayan ta raka bayan Khausar da ido ta wani dage gira saya sannan ta saki wani murmushi ta ci gaba da jan carbin da sam bai yarda da addu'a take yi ba wannan tsohuwar mai kwanonin


Kai ya dauke yana girgiza kai sannan ya mike ya bi umarnin Maman da tace ya tafiyarsa office dinsa hakan zai fi alkhairi dan baya so yana zaune gefen uwar mutane tana nemansa da fitina gaskiya ga ma'aikatansa ma ko sun durfafo da karfi karfi in suka ganshi sai ka ga sun shiga kame kame kamar wani dodo, KOWAMA haushi yake bashi yau din dan haka ya yi tafiyarsa


A kadan sai kusan goma matar Mai kwanoni ta sauka, ta samu baby girl dinta
Sai a lokacin Khausar ta nufi office dinsa dauke da ledar abincinsa da bata samu ta mika masa ba tunda ta zo da na su Mama


Knoking ta yi ta kama abin ta bude ta shigewarta da salama da kuma sakin fuska sosai ta karasa wajen office din ta ajiye masa abincin da katinsa tana kallonsa ta ce" Hajiar fa ta sauka kana office TAUFEEK ka sauko ka ga baby girl mai kyau da ita Masha Allah"


Yi ya yi kamar bai ji mai take fada ba yana ta rubuce rubuce a baban litafin dake gabansa


Dan dage ta yi ta ga aiki ne yake sosai, dan haka ta ajiye ta masa salama ta fice


Sai da ta fita ya dakatar da rubutun da yake yi a hankali ya jinginar da bayansa jikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login