Showing 30001 words to 33000 words out of 231718 words
Chapter 11 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
yana faɗin "Yaya, menene? Kukan me kike?"
Abra ta riƙo hannunsa tace "Salman cikina ciwo"
"Subhanallah, sannu ciwo yake miki?" Ta jinjina masa kai tana kuka.
"To kiyi shiru, ko dai cikin ki ne ya ɓaci, ina da maganin gudawa"
Kasancewar ta shagwaɓaɓɓiya cikin shagwaɓa tace "Um, Um ni ba gudawa nake ba"
Salman yace "to bari in kira Mami"
"A'a ni karka tafi ka barni a nan"
Salman yace "to, bari in kirata a waya"
Abra ta riƙe hannun Salman gam, tana cigaba da rintse ido.
Falo yaje ya ɗakko wayar gida, ya dawo ɗakin Abra ya zauna Wayar Mami ya kira, ya sanar mata da halin da Abra ke ciki, se dai amsar da ta bashi sam be ji daɗin ta ba, na ya kira mata likita ita tana da abun yi.
Haka Salman ya nemo lambar doctor Habib, wanda yake Family doctor ɗinsu ne, kuma soja ne, doctor Habib yace gashi nan zuwa.
"Faris" ta kira sunansa.
Yace "Na'am Yaya"
"Har amai fa nake yi, da ciwon kai"
Yace "to kiyi haƙuri, doctor yana hanya"
Tace "Ina Mami?"
Salman ya ɗanyi jimm sannan yace "tana zuwa, kiyi haƙuri" yai maganar cike da kulawa.
Yana nan zaune tare da Abra, Doctor ya kira wayar gidan Salman ya ɗaga, ya ce "gani nazo, tana wani ɗakin ne?"
Salman ya kalli Abra, kayan bacci ne a jikinta, ya ɗan tsuke fuska kamar yana gaban doctor yace "jiramu a falo"
Ya kalli Abra yace "tashi muje likitan ya zo"
Abra ta yunƙura ta tashi, se dai Salman ya zare ido yace "Yaya, meye wannan a jikinki?" Da sauri ta waiwaya, jini ne duk ya ɓata mata shimfiɗa da jikinta.
Aikuwa ta fashe da kuka tace "Na shiga uku, meya sameni Faris mutuwa zanyi?"
Salman yace "Innalillahi ba zaki mutu ba, ki canza wasu kayan, semu gayawa doctor, ai normal ne"
Salman yace "to shiga ki canza kaya, bari in jiraki a falo"
Haka ya koma falo shi da likita suka jira Abra, ta fito tana ta tsantsame jikinta, likitan yai mata tambayoyi, nan ya tabattar da period ta fara, se dai ya zo mata da wahala, dan haka ya sakamta drip, tare da bata magunguna da shawarwari.
Salman yaje ya samu mahaifiyarsu kwance a ɗakinta, ta haɗa abinci ta karya, Salman yace "Mami Yaya ba lafiya fa"
"To ni na saka mata ciwon da zan cire mata?"
Salman ya girgiza kai yace "A'a, doctor yace wai idan da wannan Pad ɗin da mata ke amfani da ita wai ki bayar".
"Me za'ai da ita?" Ta tambaye shi.
" ukhty ce za tai amfani da shi"
Hajiya Na'ima ta ɗanyi jimmm, sannan tace "jeka toilet ka ɗauka"
Salman yaje ya ɗakko ya fice, dan abun kunya, Hajiya Na'ima na gidan, amma se doctor ne ya nunawa Abra yadda ake amfani da pad ɗin, hakan ba ƙaramin ciwo yai wa Salman ba, duk da yana da ƙarancin shekaru amma yana matuƙar kishin yayar ta sa, he is always protective to her, ko a Makaranta ba ya son yaga wani ya raɓeta, wanda tun suna yara sosai baya son ko baƙi sukai yaga yara sun fiye zuwa in da take, se ya dinga ganin kamar zasu cutar da Ita kasancewarta ba me hayaniya ba.
Tana nan kwance, doctor yana jiran ruwan ya ƙare ya samata wani, Salman yaje ya ɗakko bargo ya rufe Abra, yaje kitchen ya dafo mata tea ya ɗakko bread ya zo ya haɗa mata.
Shi kansa doctor yanayin gidan Khamal yana burge shi, kan yaransa a haɗe yake, suna son juna sosai, sai dai yana mamakin yadda matarsa bata bawa lamarin 'yar ta ta mahimmanci.
Da drip ɗin farko ya ƙare, Salman da kansa ya din ga bawa Abra abinci, har ta ɗan ci sosai, sannan ta kwata aka kuma saka ɗayan, ya nunawa Salman yadda zata sha magungunan ta, da yadda ze cire mata ruwan idan ya ƙare, sannan ya fita saboda yana da in da za shi.
Salman se jera mata sannu yake, ya ga ta kai hannu tana shashshafa gashin kanta, cikin kulawa yace "Ukty ya dai?"
"Ni kitson nan ne ya dameni, ƙaramin ciwon kai yake" ta faɗa har da ƙwalla.
Salman ya kalli kitson, manya guda shida, ga gashin nan baƙiƙirin, kwance a farar fatar kanta, yace "ko a tsefe ne?"
Tace "eh" ya tashi ya tafi ɗakinta, ya ɗakko comb da kibiya, ya dawo ya zauna ta ɗora kanta akan cinyarsa, ba'a jima ba ya tsefe kan nan tas, dama Salman ya saba da tsifa, shi yake tsefewa Abra kai wasu lokutan.
Ya shiga taje mata a hankali dan kar taji zafi, gashin ya baje a jikinsa, ya rufe mata fuska.
Hajiya Na'ima ce ta buɗe ƙofar part ɗinta ta fito, turus ta tsaya tana kallon Salman, "meye haka kamar wani ɗan daudu?" Mami tai maganar tana nuna su.
Salman yace "Mami ba kiga ba ta da lafiya ba, tsefe mata nake"
"Au bayan kurumtakar kuma, kuturwa ce ita da ba zata iya tsefewa ba, kai yau nina ke ganin tsiya, tsifar ma se kayi mata namamajo"
Abra tace "Faris bar shi haka, nagode sosai".
Salman yace "tsaya in sa miki ribbon ɗin, sai a mai da hular"
"Ina maka magana kana cewa seka sa mata hula, ina ga nan gaba kuma shagon kitso da lalle zaka buɗe, sai kuma suyar doya da ƙwai tunda ka zama ɗan daudu"
Shi Salman ma dariya Mamin ta bashi yace "haba Mami, in ba gashin ki kona Ukty ba, gashin wa zan iya taɓawa, Mami ki mata sannu mana ba kiga ta rame ba?"
"Ba zan mata sannun ba, a kanta aka fara haila da za ta wani langaɓe ta na numfarfashi?, dalla tashi ka bar gurin nan, in ban yi da gaske ba ina ga nan gaba maƙale hannu zaka fara irin na 'yan daudu"
Jiniya ce ta cika layin, zuwa cikin gidan, wanda hakan ke almta cewar megidan ya dawo.
Wani murmushi ne ya bayyana a fuskar Abra, tare da murna tace "Abba ya sauka a gids, se dai Wannan karon ban masa girki ba".
Kan su gama maganar Abbi ya shigo falon tare da sallama.
Yana ganin Abra a kwance a gigice ya ƙarasa yana faɗin "sweetheart what's wrong? Ya na ganki a kwance? Har da drip haka?"
Hajiya Na'ima ta hau yaƙe tace "Yallaɓai barka da sauka"
"Yawwa Madam, meya sami Abra na?"
Salman yace "Abbi ba ta da lafiya ne"
Hajiya Na'ima tace "yanzun nan doctor ya bar gidan nan, she start first period today, shine take ta shagwaɓa da koke koke"
Abbi yace "Eyya, sorry my dear, dole ta damu sosai, this is her first day is not easy for her, sannu Sweetheart".
Baƙin cikin yadda Salman da Khamal suka lalace akan Abra, kowa yana mata Sannu kamar za su maida ita ciki ya sa wani baƙin ciki ya turnuƙeta, gashi se wani shagwaɓa Abran take, har da hawaye, Hajiya Na'ima ji take Kamar ta ɗura musu Ashar su duka ta huta.
Haka Hajiya Na'ima ta shiga hidimar dole, da yaƙe ta samar musu da Abinci, kasancewar me girkin gata kwance ba lafiya.
Abba da kansa ya din ga bawa Abinci, Salman kuma yana ɓallo magani yana bata.
Hajiya Na'ima baƙin ciki ya sa ta koma ɗakinta tana huci, tana jin kamar ta ɗakko muciya ta saukewa Abra muƙamuƙi kowa ya huta.
Haka Abbi ya wuni ririta Abra, tare da yi mata nasiha akan yadda zata kula da kanta da Addinin ta.
Sakkowa take daga kan bene, hannunt a riƙe da waya ƙirar iPhone, se taune taune take.
"Meenal" ya kira sunanta.
Ƙarasa sakkowa tai daga kan benen, cikin siririyar muryarta tace "Daddy i miss You"
Yace "I miss You too, ya school ɗin?"
"School Alhamdilillah, mun kusa gamawa, ya aiki ya fiɗa"
Yai murmushi yace "fiɗa sekace wani mahauci?"
Tai murmushi tace "Daddy ai banbancinku ku mutane kuke fiɗewa"
Yace "Meenal kenan? Ina fatan zaki gajeni ai"
Cikin sauri Meenal tace "No, no, Daddy, ka manta Art class nake yi, ni bana son ganin jini, is so iiritating to me, ni masscom zanyi"
"Yanzu shikenan Daddy baze samu magajiya ba?"
Tai dariya tace "Daddy ba shi da magajiya"
Yai murmushi yace "To shikenan, Allah ya ida nufi".
"Aku me Magana, tun da kika dawo gidan nan kowa se yasan kin zo, se surutu kike masa ki bar shi ki huta mana" cewar matar da take sakkowa daga kan step me tsananin kama da Meenal.
Meenal tace "Mummy I have to show him how much I miss him"
Doctor yace "And i miss you too dear, yau tare ma zamu ci Abinci ma, banda ma ke kike son boarding ɗin nan, ai da ni ba in da zaki matsa daga kusa da ni".
Abra ta ji sauƙi sosai, dan har ta koma makaranta, Salman se nan nan yake da ita yana bata kulawa, duk da ita tana art class shi kuma yana science, amma buni buni se yaje ajinsu ya ga ko tana Lafiya.
Kasancewar Khamal yana nan, hakan yasa Abra ta samu sauƙin hantara da zagi daga gurin Mami.
Wani mummunan labari ne ya iske Major, kasancewar an kama manya manyan 'yan ta'adda, al'umma na ta murna, cewar ko ba komai an rage mugun iri, ku ma za'a samu sassauci dan za su bada wasu bayanan, idan aka hukunta su ko ba komai, wasu za su ɗan rage raɗaɗin rashin 'yan uwansu da 'yan ta'addan su ka kashe, da wanda aka raba da mahallansu, da wanda aka sace musu 'yan uwa, da kisan da aka din ga yiwa mutane ba dalili.
Se dai bayan zama da shugaban ƙasa yai da manyan jami'an tsaro, labari ya cika gari cewa, gwamnati za tai afuwa ga waɗan nan 'yan ta'adda, za ta mai da wasu Makaranta wasu kuma a ba su aikin yi.
Hakan ba ƙaramin cece kuce ya janyow ba, mutane na ganin ya za'ai wanda ya kashe mutum ɗaya an kama shi an ɗaure an yanke masa hukunci, amma wanda suka kashe dubban mutane, suka girgiza tattalin arzikin ƙasa, su za'ai musu afuwa har da ma samun wani tagomashi da ga gwamnati, nan mutane suka dinga sukar wannan hukunci na gwamnati.
Labari ya iske Major Khamal, shi kansa ya sa rai tare da zuba ido akan matakin da gwamnati za ta ɗauka, dan sun sha baƙar wahala tare da tsananta bincike, kan su samu nasarar kamo wasu daga cikin manya manyan mutane da ke cikin ƙungiyar ta'addanci, amma katsam ya samu labarin matakin gwamnati akan lamarin.
A hankali ya miƙe tsaye yana zagayawa yace "lokaci ya yi, da zan yi wasan kura da duk wanda suke da hannu cikin lalacewar tsaro a ƙasar nan! Sedai hakan ba ze yuwu ba se da goyom bayan manya, amma suwaye manyan? Su ne dai wanda sukewa harkar zagon ƙasa.
A hankali ya nemi guri ya zauna tare da dafe kansa, da yai masa wani irin nauyi.
Hajiya Na'ima na ta shiri da daddare, zata tafi ɗakin Yallaɓai Khamal, sai dai wayarta ta fara ringing, ta amsa wayar tare da sata a kunnenta.
"Barka da dare Hajiya Na'ima, mrs Khamal"
Cike da rashin fahimta ta amsa da "yawwa barka wake magana?"
"Garajen me kike? Zaki ji ne, ya 'yata take ina fatan tana lafiya?"
"Wace 'yar kenan?"
"Abra Khamal Khamis, na kiraki ne dan jin ya 'yata take, fatan kina riƙemin ita da amana, sannan ina miki albishir da cewa daga yanzu zuwa kowane lokaci zan iya shigowa gidanki, domin cigaba da rainon 'ya ta da kaina!.
LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
[9/30, 8:55 PM] Abk: *DARE DA DUHU*
_Brigh pens✍️_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee Kumurya
P9
Domin samun complete litattafanmu, ku yi following ɗin wannan accounts ɗin a Arewabooks
https://arewabooks.com/chapter?id=6316f4af434cfeb9e7fe2949
https://arewabooks.com/u/nimcyluv
Elegant online writers
LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
Wata irin bugawa zuciyar Na'ima ta yi, cikin ƙaraji ta ce. "What? Wacece ke?"
Dariyar rainin hankali wadda ta kira wayar ta yi ta ce. "Ko ba ki ji abun da na faɗa dai-dai ba ne in ƙara maimaita miki?"
Wata Uwar ashariya Na'ima ta ƙunduma ta ce. "Wallahi k'arya kike matsiya, Shegiya karuwa, Khamal nawa ne ni kaɗai babu wacce ta isa ko da rab'ar shi ne ta yi balle har ta aure shi, ba'a halicci mace ba wallahi."
Cikin murmurshi ta ce. "Za kuwa ki gani, ganin idonki, ki cigaba da kular mun da my Daughter yanda ya kamata." Sannan ta ja tsaki ta kashe wayar.
A haukace Na'ima ta sauke wayar daga kunnenta ta shiga bin screen ɗin wayar da kallo, tamkar za ta ga matar da ta kira ta a cikinsa, babban baƙin cikinta sai da aka b'oye numbern sannan a kira ta.
Wani irin tuƙuƙwin baƙin ciki zuciyarta take mata, cikin takaici ta cillar da wayar, Allah ya taimaka ta faɗa kan gado. Hannunta ta ɗora akan goshinta tana bubbuga kanta ta fara magana ita kaɗai.
"Impossible! Wallahi ba zai yiwu ba, sai na gano ko wace ce ke na kashe ki, sai dai ki auri Khamal a lahira ba dai a duniya ba, matuƙar ina numfashi babu macen da ta isa ta shigo cikin gidana a matsayin matar Mijina.
Wayarta da ta cillar ta ɗauka ta fice daga ɗakin a matuƙar fusace ta nufi part ɗin Khamal.
Salman dake zaune a parlour yana kallon Ball ya bi ta da kallo cikin mamakin ganin yanayin da ta fito kamar wadda ba ta cikin hayyacinta.
"To Macuci, mayaudari, azzalumi, mugu, yau Allah ya toni asinka, dama an ce rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tal ta mai kaya."
Abun da Na'ima ta faɗa kenan bayan ta tura ƙofar ɗakin Khamal da ƙarfi ta shiga.
Da mugun mamaki Khamal dake zaune yana operating system yake kallon ta, kasa cewa komai ya yi saboda tsananin mamaki.
Cikin kuka ta ce. "Ka cuce ni, na yarda da kai Khamal, amma ban san me ya rud'e ka, ka ci amanata ba."
"Na'ima, wannan maganar banzan da kike yi duk na mene ne?"
"Na cikin shegen da kika yi aka haifi waccan shegiyar yarinyar ne."
Fauu! Fauu!
Khamal da ya miƙe cikin sauri kamar wanda aka hankad'a ya saukewa Na'ima tagwayen maruka a fuska.
Cikin tsananin ɓacin rai ya fara magana.
"I told you Na'ima, duk abun da zaki yi ki yi amma kar ki ƙara danganta mun ƴa da Shegiya, na faɗa miki ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba."
Na'ima dake riƙe da kuncinta wanda take jin kamar ba ya jikinta saboda tsananin azaba, idanunta na zubar da hawaye ta ce. "Ni ka mara Khamal akan waccan yarinyar mara asali?"
"Yes, kuma idan kika ƙara maimaita abun da kika faɗa, abun da ya fi mari ma zan miki wallahi!"
Yana gama faɗar haka ya fice ya bar mata ɗakin ya tafi other room dake part ɗin ransa a matuƙar b'ace.
Da wani irin kallo ta bi shi har ya fice, wani irin ɗaci take ji tun daga zuciyarta har zuwa bakinta.
Zama ta yi a bakin gado tare da fashewa da kuka, a ranta tana faɗin, 'Komai zai faru sai dai ya faru, amma wannan karon ba za ta hak'ura ba, ba za ta cigaba da zama da Shegiya a gidanta ba, sai a yi duk wacce za'a yi.'
Sai da ta ci kukanta ta ƙoshi sannan ta lalubo wayarta dake gefenta, dan ko gani ba ta yi sosai saboda masifar ciwon da kanta yake mata. Numbern Aunty Suwaiba ta kira, ringing biyu ta ɗaga tare da ambatar sunanta.
Kuka Na'ima ta sakar mata cikin rashin abun yi.
"A'a, Lafiya? Me ya faru? Wani abun ne ya samu Khamal ko Salman zaki kira ni a daren nan ki saka mun kuka?"
Aunty Suwaiba ta tambaye ta cikin kid'ima.
Cikin kukan ta ce. "Na shiga uku na lalace Aunty, ta tabbata Abra ƴar Khamal ce ta cikinsa, duk abubuwan da ya faɗa mun a baya ashe duk k'arya ne, shashasha wadda ba ta san abun da take yi ba kawai ya mayar da ni."
"Ke wa ya faɗa miki? Mene hujjar ki na cewa hakan?"
"Wadda ya yiwa cikin ta haifa masa ita ce ta kira ni ta tabbatar mun da zargina."
Kwashe duk yanda suka yi da wadda ta kira ta, da yanda suka yi da Khamal ta yi ta faɗawa Aunty, ta ƙara faɗin. "Ni kam yarinyar nan ta zame mun bala'i da masifa a gidan Aurena, da ina rayuwata da mijina hankali kwance amma yanzu ta shigo duk ta wargaza mana farincikinmu."
"Na rasa yaushe zaki yi hankali Na'ima, shegen kishi ya rufe miki ido kin kasa ganin dai_dai, idan ma ta tabbata mahaifiyar Abran ce ta kira ki sai ki yi masa wannan haukan? Ke sai ka ce ba jinin Mama ba? Yaushe zaki ko yi kissa ne.
"Aunty wannan abun fa ba zancen wata kissa ba ne, ba za ki gane yanda nake ji ba ne a cikin zuciyata, kamar ana rura garwashi haka nake ji, ni yanzu kawai ki faɗa mun yanda zan yi Yarinyar nan ta bar gidan nan, dan wallahi ba zan cigaba da zama da ita ba."
Numfashi Aunty Suwaiba ta sauke ta ce. "Na ji zan faɗa miki, amma sai kin mun alƙawari zaki je ki bawa Khamal hak'urin maganganun da kika faffaɗa masa."
"A saboda me zan ba shi hak'uri? Shi fa ya mun laifi, har da mari fa, abun da tunda nake da Khamal bai taɓa mun ba. Ki bar ma wannan maganar, kawai ki faɗa mun yanda zan yi, abun fa bana sanyi ba ne, na ga baki ɗauki abun serious ba, ko dan bake aka yiwa haka ba?"
Ta yi maganar fuskarta na nuna tsantsar ɓacin ran da damuwar da take ciki.
Aunty Suwaiba ta ce. "Ba haka ba ne Na'ima, kin san bayan ke babu wanda ya kai ni baƙin cikin zaman Yarinyar nan a gidanki, amma bana son ki yi abun da zaki zo kina da na sani ne."
"Babu wani da na sanin da zan yi, wallahi sai dai mu rabu da Khamal, matuƙar ya zaɓi cigaba da zaman yarinyar nan a gidan nan, haba abun ya ishe ni haka, hak'urina ya ƙare."
Ta ƙarashe maganar cikin kuka, wani irin kishi na nuƙurƙusar zuciyarta.
Daƙyar Aunty Suwaiba ta rarrashi Na'ima ta yarda za ta je ta bawa Khamal haƙuri, shi ma dan ta ce idan ba ta