Showing 168001 words to 171000 words out of 231718 words

Chapter 57 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

Advertisement

28 Feb 2025

14829

maganar auren 'yarka, koma menen tun da ba zaka faɗa ba kai ya dama, amma dole a san abin yi a kan Auren 'ya ta".

Miƙewa yayi ya fice ya bar mata falon gaba ɗaya.
Ƙwafa hajiya Saudat tayi, ta tashi ta koma sashinta.
Meenal ce ta tarar da Mummy a ɗakinta. "Mummy kin gaya masa ya kuka yi da shi?".
"Ni na rasa me yake damunsa, gaba ɗaya a takure yake, baya cin abinci ya daina zuwa wurin aiki, ko bacci ba ya iya yi"
"To meya same shi?"
"Ina na san masa, na tambaye shi yaƙi gaya mini".
"To ni dai da kika gaya masa zancen Usman me yace miki? Ya ce su zo ɗin?".
"Ina ya saurareni ma, balle muyi maganar"
"Innalillahi, Mummy to jira za suyi har sai ya daina damuwar tukuna? Jira suke fa ya basu lokaci su zi".
"Zan cigaba da yi masa magana, gara a san abun yi".
"Yawwa Mummy, dan Allah ki cigaba da lallaɓa shi".
"Ina jinjina abin da yake damunsa haka, na ga baya wasa da duk abin da ya shafe ki, amma naga yana cikin damuwa sosai".
"To Allah ya yaye masa damuwar ta sa".
Meenal ta amsa da "Ameen".



Salman yana zaune a kan gadon Abra, yana tuna Abubuwa da suka shuɗe, na rayuwar da suka gudanar, tun daga ƙuruciya zuwa girmansu, halayyarta na shagwaɓa, a hankali ya lumshe idanunsa, yana tuna yadda ya dinga wasa da hankalinta a matsayin unkown ɗinta suna hira, lokaci ɗaya rabon Aishatul Humaira ya sanya Adnan ya kutso rayuwarsu, ya rabasu cikin gaggawa ashe rabon ajali ne ya sanya, da shigowar Adnan rayuwarta da Aurensu ba a ɗau lokaci mai tsawo ba.
Hawaye yake sosai, yana ƙanƙame filonta a ƙirjinsa, yana juyi a kan gadonta, kansa har wani irin sarawa yake yi, saboda kuka.


Sai da Abra ta kwana goma da rasuwa sannan aka sallami Adnan daga Asibiti, shima bisa sharuɗa da dokokin da likitoci suka shimfiɗa, saboda har yanzu baya hayyacinsa, da allurai sun sake shi, yake fara zabure-zabure da kuka shi wurin Abra zai je, a bashi matarsa su tafi. Idan ya ɗan watstsake, sai ya dinga tuna cewar rabon da ya ga Abbansa a kansa, tun lokacin da aka kawo Abra Asibiti.
Hajiya Mama ce ke ta cigaba da rarrashinsa da bashi haƙuri, amma ya kasa yarda da cewar Abra ta mutu, lokuta da dama sai ya birkice yace mafarki yake yi.
Kafin su tafi gida, Mama ta ce Adnan suje ya ga 'yar sa, dan bai ganta ba tun da aka haifeta.

Tafiya yake tamkar wanda ya zare, jan ƙafarsa kawai yake yi, Mama na riƙe da hannunsa, wani Cousin ɗin Adnan Aminu na gefensa, jefa ƙafarsa kawai yake, yana kallon Asibitin.

Haka suka je suka nemi izinin shiga wurin da jaririyar take, Adnan ya zubawa jaririyar idanu, Abra ba ta ga abin da ta haifa ba, gashi a hankali kamanninta juyewa suke zuwa na Abra, likitoci suka tabbatar da an kusa cireta da ga kwalba, a ɗorata a kan madara, ko kuma idan an samu mai shayar da ita a kafa masa dokokin kula da ita.

"Mama ɗaukar mini ita a hoto" Adnan ya faɗa idanunsa na zub da hawaye.

Mama ta ɗau hoton jaririyar, suka fito daga cikin wurin, zuwa cikin mota.

Tun da Aminu yake bai taɓa ganin abin da ya sanya Adnan kuka ba irin mutuwar Abra, dan mutum ne mai dakakkiyar zuciya, ba komai ne ma yake ba shi tausayi ba, balle a sa ran zai yi kuka.

Wayar Mama ya karɓa, yayi zooming ɗin fuskar Aishatul Humaira, wadda yake yiwa laƙabi da little Abra.

Babban abin takaici shi ne da ka kalli jaririyar ka san jinin Bulama ce, dan a hankali kammaninta suke juyewa irin na Abra, ya tuna lokacin da ya ɗauko Abra daga Asibitin Bulama, tana zubar da jini, saboda halin ko in kula da wasa da rayuwarta da aka yi a Asibitin. Sakin wayar Adnan yayi ya ƙanƙame Mama yana kiran sunan Abra.
Lamarin Adnan ya fara bawa Mama tsoro, amma tai shiru ta cigaba da yi masa Addu'a, har suka je gida yana kuka.
"Mama ku fara kai ni kabarin Abra dan Allah"
Mama ta ce "Adnan ni da ba dani aka kaita ba, ina na san kanarinta, muje gida Abbanka ya kai ka".
"Mama Abba ya san Abra ta mutu ta barni kuwa?".
Mama ta ɗan yi jimm, dan ba ta san ta ina zata fara yi masa bayani ba, amma ta basar ta ce "Eh ya sani mana, da shi aka kai ta gidanta na gaskiya ma"
"Mama shi ne bai zo ya ganni ko sau ɗaya ba, shine bai bari na ganta ba yaje ya binne ta? Dan ba matarsa ba ce, shi lokacin da matarsa ta mutu haka aka yi masa? Ai shikenan idan na tashi daga baccin na san zan ganta a kusa da ni, ai tare muka kwanta jiya da daddare, har Abincin dare ta yi mana. Idan kuma muna Dubai ne sai inje gidan Abincin Hilal in sayo mana gasashen nama".

Aminu ya ce "Anya Hajiya Adnan ba za a kai shi wurin likitocin ƙwaƙwalwa ba, kar fa abin ya zarce".

Mama ta ce "Bari muje gidan tukuna, idan bai ware ba sai a san abun yi".

Har suka je gida, Adnan surutai yake yi, yayi zancen hankali idan aka jima kuma, ya fara shirme da surutai.


Haka suka isa gida, suna shiga cikin babban falon gidan suka tarar da Abba a zaune, yana duba system ɗin sa, Adnan na ganin Abba ya nufi wurin Abba, ya zube a kan gwiwowinsa ya riƙe ƙafar Abba yana faɗin "Abba, wai da gaske i loose my Abra, Abba ka sa aka binneta ban ganta ba, Abba ka nuna mini kabarinta in ganta kafin in tashi daga baccin" hankaɗe Adnan Abba yayi, ya zame ƙafarsa, ya kalli Adnan cikin tsananin takaici ya ce "Am disappointed on you Adnan, ban san a inda ka kwaso baƙin hali ba, ashe zamanka da yarinyar nan zalintar ta ka dinga yi? Na gode Allah da ba wani ne ya gaya mini ba, da bakinka Allah ya sa ka dinga faɗa, ba wani ne ya gaya mini ba balle in ce ƙarya ne, to kanka ka yiwa, kuma komai aka yi maka a rayuwar nan idan ka barwa Allah, ya gani zai saka maka, amma ina ruwan baiwar Allah da bata san laifin da aka yi maka ba, kai laifi nawa kake wa Ubangiji ya yafe maka? Ka samu yarinya 'yar mutunci mai haƙuri amma ka zalunceta, to ka sani har abada ba zaka taɓa samun yarinya mai haƙuri da kirki kamar Abra ba, Allah yayi mata rahama amma na yi dana sanin shigewa gaba wurin nemawa mutumin banza irinka Aure".

Jiki a sanyeye Mama ta ce "Dan Allah Yallaɓai kayi haƙuri, ka tausaywa halin da yake ciki, likita ya kafa masa dokoki kar ya rasa hankalinsa".

"I don't care, komai ya same shi shiya janyowa kansa, bai shafeni ba, na jinjinawa haƙurin yarinyar duk wannan zaman naku bata tona maka asiri ba, kaji kunya Adnan, kuma ka tattara ka bar mini gida ka koma gidanka kar ka sa in gaya maka wata muguwar Maganar" ƙurawa Abba Idanu Adnan yayi, ko ƙyaftawa ba yayi, kamar mai shirin aiwatar da wani abu.


Bulama kuwa lambar maƙwabcin su Abra, ta jikin File ɗin Asibitinsu ya kira, yai sa'a mutumin ya ɗaga, suka yi arranging zasu haɗu da Bulama.

Bayan haɗuwar ta su ne, Bulama ya sanar masa cewa yana son ya gaya masa alaƙarsa da matar da suka kai Asibiti ranar.

"Matar maƙwabcina ce".

"Yanzu ina maƙwabcin naka yake?".

"Ai matar tasa ta rasu, shi kuma yana Asibiti babu lafiya".

Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce ta ziyarci Bulama, wani irin gumi ya shiga tsatstsafowa a goshinsa, wata irin nadama da tashin hankali suka mamaye shi.

A saɓule ya ce "Ko zaka kwatanta mini Asibitin da yake?". Nan ya kwatanta masa Asibitin nan dai da yabi Adnan amma ya ɓace masa. Ya gaya masa har room ɗin, Bulama yayi masa godiya ya tafi.


Adnan fa sai abin da ya ƙaru, gaba ɗaya ya ƙara birkicewa, dan an haɗasu da likitan ƙwaƙwalwa, saboda kar a rasa hankalinsa, Mama kuma nata rarrashin Abba a kan, ya sassauta fushin da yake da Adnan, kar abun yayi masa yawa. Ba ya cin komai sai ruwa sai kuka, wasu lokutan idan ya birkice sai dai ayi ta masa allurar bacci.


Abbi da Mami tare da Salman, suka zo garin Kaduna domin karɓar jaririyar Abra, dan lokacin cirota daga kwalba yayi, Mami ta dage a kan cewar ita za'a bawa Little Abra ta riƙe.


Abban Adnan ya koma wurin aikinsa, Adnan kuwa ba shi da lafiya da cikakken hankalin da za'a tambayi ra'ayinsa a kan riƙon Aisha.

Tare da Hajiya Mama suka tafi Asibitin, suna nan tsaye suna ƙoƙarin shiga, Bulama ya fito daga cikin Asibitin, neman Adnan amma ya tarar an sallame shi.
Salman ne yabi Bulama da ido, ko ƙyaftawa ba yayi amma ya kasa Magana.


Na kuɗi ne a biya mu kan a karanta dan Allah
07063065680
[11/3, 6:09 PM] Abk: Har Bulama ya fice daga asibitin Salman bai daina kallon shi ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya bi bayan su Abbi da suka wuce cikin kasala, kamar mutumin da Angel ɗinsa ta ɓaci, banbanci su kawai shi Namiji ne ita mace. Bai ɗauki hakan a matsayin wani abu ba, saboda yadda Abra take masa gizo akan duk abin da zai ɗora idonsa a kai sai ya ga fuskar Abra tana yi masa murmushi. Wasu hawaye masu ɗumi ne suka zubo akan kuncinsa. Cikin raunin murya ya furta. "Allah ya ji ƙan ki Yayata ya gafarta miki."


Karɓar A'isha Humairah sai ya zamto fami a kan mikin dake kwance a zuciyar su Mami, tunda aka miƙo mata yarinyar take kuka, Hajiya Mama na taya ta da hawaye. Abbi kuwa ya yi shiru kawai sai numfashi yake saukewa. A haka Salman ya shiga inda suke ya same su, bai ce komai ba bayan sallamar da ya yi ya karɓi A'isha ya riƙe tare da zuba mata ido. Bacci take cikin kwanciyar hankali, ta ƙara girma da kyau da fari, a hankali ya kai hannu cikin ƙaunar ta ya shafa gashin girgarta zuwa kuncinta, idanunsa taf da hawaye ya ce. "Allah ya ji ƙan mahaifiyarki, ya raya mana ke, ya ba ki haƙuri da sanyin hali irin nata."

"Amin ya Allah." Abbi ya amsa idanunsa a kansu.

Kuka Nai'ma ta ƙara fashewa da shi tare da faɗin. "Da gaske dai ba zan farka daga wannan mummunan mafarkin da nake ba, ta tabbata Abra ta rasu, innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, na kasa sabawa da rashin ki ƴata, kodayaushe kewar ki ƙaruwa take a cikin zuciyata."

"Sai haƙuri Hajiya, dukkan mai rai mamaci ne, mu ma duk zaman jiran ta muke, fatanmu kawai Allah ya sa mu cika da kyau da imani." Cewar Likitan da suka karɓi A'isha Humairah a hannunsa. Haka suka baro asibitin zuciyoyinsu babu daɗi, Salman dai na riƙe gam da Baby ya ƙi bawa kowa ita. A ranar suka juya Kano ba su kwana ba, duk kuwa da yadda Hajiya Mama ta so hakan, har suka taho ba su haɗu da Adnan ba, yana baccin allurar da aka yi masa.



Daf da Magriba ya farka daga baccin a firgice yana kiran sunan Abra. Aminu dake ɗakin ya yi hanzarin yin kansa ya riƙe shi.


"Abra! Tana Ina? Yanzu fa muke tare ta kawo mini ruwa mai sanyi ina sha tana ta mini murmushi, ashe ba ta mutu ba duk mafarki nake yi." Ya faɗa cikin son kwace jikinsa daga riƙon da Aminu yay masa tare da waige-waigen inda zai ga Abra."


Cikin son kwantar masa da hankali Aminu ya ce. "Ta fita ne, amma yanzu za ta dawo." Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi tare da yin murmurshi ya ce. "Ina ta je? Raka ni gurin ta, bana son tana yin nesa da ni, kar na je mummunan mafarkin da na yi ya tabbata."

"To zan raka ka, amma ka fara yin wanka ka ci abinci ka yi sallolin dake kanka?"

"Me ya sa?"

"Saboda ta ce idan ba ka yi ba kar na raka ka gurin ta."

Zabura ya yi cikin ƙoƙarin saukowa daga kan gadon yana faɗin. "Zan yi yanzu."

Taimaka masa Aminu ya yi ya raka shi toilet zuciyarsa cike da tausayin shi, idan ba dabara ake masa irin haka ba, ba za a samu kansa cikin sauƙi ba. Bayan ya fito ya yi Sallah ya fita parlour. Hajiya Mama da Abba ya tarar a parlour'n, cikin sauri ya ce. "Ina Abra? Where is my wife?" Dafe kai Hajiya Mama ta yi ta ce. "Oh My God! Adnan wai sai yaushe za ka yarda Abra ta rasu ne?"

"Ba zan taɓa yarda ba, saboda in dai hakan ya tabbata ni ma bin ta zan yi." Ya yi maganar cikin hawaye.

Kallon sama da ƙasa Abba ya yi masa, duk da yadda ya lalace ya yi baƙi amma bai ji tausayin shi ba ko kaɗan, taɓe baki ya yi tare da ɗauke kansa daga kallon shi. Kuka sosai Adnan ya saka tare da faɗin. "Abra me ya sa za ki tafi a lokacin da nake cikin tsananin ɓukatar ki a cikin rayuwata, ina son ki wallahi, na yi nadamar duk abubuwan da na aikata miki, don Allah ki dawo gare ni."


"Haba Adnan, yaushe za ka daina wannan kukan da surutun ne? Sai ka ce ba musulmi ba, Ubangijin da ya ba mu Abra ya fi mu son ta shi ya sa ya ɗauke ta, addu'a kawai za ka yi mata, shi ne soyayyar da za ka nuna mata."


"Shikenan Mama, na yarda na haƙura, na rasa masoyiyata." Ya yi maganar cikin wani irin yanayi tare da kwanciya a ƙasa.

Girgiza kai Aminu da ya biyo bayan shi ya yi zuciyarsa cike da ɗimbin mamakin dama akwai abin da zai mayar da Adnan haka? Mutum mai tsananin zuciya da zafin rai gami da dakiya, lallai ya tabbatar ba ƙaramar k'auna yake yi wa matar nan tasa ba.



Hajiya Saudat ce zaune a bakin gado ta yi tagumi tana kallon Bulama dake kai kawo a ɗakinsa kamar wani sabon soja.

"Wai don girman Allah Doctor me yake damun ka ne kwana biyu? Ka daina walwala, ka daina cin abinci, office ma an ce ka daina zuwa, ka faɗa mini me yake damun ka."

"Ba zan faɗa ba Saudat, na ce ki ƙyale ni ki daina biyo ni kina mini waɗannan tambayoyin amma ƙin ki ko? Wallahi zan saɓar miki!" Ya yi maganar cikin ɗaga murya.

Cikin tsantsar mamaki ta ce. "Ni ce fa Saudat matarka Doctor kake mini magana cikin tsawa? Ko ka manta ne?"

"Get out from My room, kafin na wurga ki ta window!"

Jijjiga kai ta yi ba ta ce komai ba ta tashi ta fice. Da wani mugun kallo ya raka ta, bayan ta fice ya rufe ƙofarsa tare da faɗin. "Idiot, abu yana damun mutum za ta ishe shi da wasu mahaukatan tambayoyinta."


"Me ya faru Mom na gan ki a haka?" Meenal ta tambayi Hajiya Saudat.

"Akwai matsala Daughter, mahaifinki ya burkice gabaɗaya, har da yi mini tsawa yau."

"Ni dai ba wannan ne damuwata ba, kin ƙara masa maganar Usman?"

"Ki shiga ki yi masa da kanki." Hajiya Saudat ta faɗa cikin harararar Meenal.

Baki ta tura gaba ta fara ƙunƙuni tare da magana ƙasa-ƙasa, ƙwafa Hajiya Saudat ta yi ta shige ɗakinta.




"Maman Rahama har yanzu kin kasa cire damuwar mutuwar yarinyar nan daga ranki, ta riga ta tafi fa, ba za ta dawo ba."

Tagumin da ta yi ta sauke ta ce. "Dole na damu Baban Rahama, ranar da muka kai ta asibiti kawai nake tunawa, ashe mutuwa za ta yi ma, Allah Sarki baiwar Allah."

"Addu'armu kawai take buƙata a halin yanzu."

"To Allah ya ji ƙan ta, ya gafar ta mata, amma mutuwar ta ta duke ni ba kaɗan ba."

"Haka rayuwar take, ni sai damu na da kira Doctor Bulama yake, wai dole sai na haɗa shi da mijinta."

Tsaki Maman Rahama ta yi ta ce. "Rabu da shi, bayan wulaƙancin da suka yi mana a asibitinsa, ana ta fadar rashin mutuncin mutumin nan, amma ban zata ya kai haka ba."

"Shi ya sa na ce masa ban san inda zai same shi ba, don ni ma ranar ya ɓata mini rai."

"Allah ya kyauta."



Hajiya Nai'ma na zaune a main parlour tana jijjiga A'isha Humairah dake kuka. Abbi dake parlour'n yana karatun Alqur'ani ya ce. "Kukan little Abra ya yi yawa yau, ko wani abun ke damun ta?" Cikin damuwa Nai'ma ta ce. "Ban sani ba ni ma, amma ina jin ko cikinta ne ya ɗan kumbura, don kafin ka ji kukanta ana daɗewa, na ba ta abincinta ma ta ƙi shan na kirki."

"To, ko sai mun ga likita ne?"

Kafin Nai'ma ta yi magana Salman ya shigo parlour'n, bin shi suka yi da kallo ganin yanayin shi, kullum Salman ƙara lalacewa yake saboda damuwar rashin Abra. Jiki a sanyaye ya zauna a kan carpet bayan ya karɓi A'isha tare da gaishe da iyayensa. Jijjiga ta ya shiga yi a hankali, babu jimawa ta yi shiru bacci ya ɗauke ta.

"Lalle ma yarinyar nan, saboda kina hannun Ubanki sai kika yi shiru ko?"

Murmushi ya yi a saman leɓɓensa bai ce komai ba, karɓar ta Mami ta yi ta kwantar a kan kujera tare da faɗin. "Ga abinci can a dinning ka je ka ci."


"Na ƙoshi Mami."

Gyara zama Abbi ya yi ya ce. "Rayuwa ba za ta yiyu babu cin abinci ba Salman, ina lura da kai tunda Abra ta rasu ba ka wani cin abincin kirki. Haƙuri za ka yi ka daure, mu ma duk ƙarfin hali kawai muke."


Cikin hawaye Salman ya ce. "Na kasa Abbi, na kasa daurewa, lokaci ɗaya a ce babu Yaya babu Granny."

"Haƙuri za mu yi Salman, haka Ubangiji ya ƙadarto mana, Please my son ka rage wannan damuwar, We are all Muslim, yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau ya zama dole a gare mu, Abra ta tafi, amma ta bar mana wata, wadda muke fatan ta samu zuri'a daga gurin ta."

Share hawaye Nai'ma ta yi ta ɗauki A'isha ta bar parlour'n, cikin ƙoƙarin mayar da kukan da ya taho mata.

"Insha Allahu Abbi zan rage, sannan dama na zo ne in maka maganar komawa ta China a cikin week ɗin nan insha Allahu."

"A yadda kake za ka fahimci wani karatu kuwa Salman?"

"Zan fahimta Abbi, kar ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login