Showing 51001 words to 54000 words out of 231718 words

Chapter 18 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14705

Daughter, ranar da zaki yi aure ki bar masa gidan sai yafi kowa maraici" da sauri Salman ya kalli Abbi ya ce "Aure kuma?" Abbi ya kama hannun Abra ya ce.
"E, Aure. Zata bar maka gidan ka cinye"
kasa cewa komai Salman ya yi da sauri kuma ya fice da ga cikin Parlour ya bar gidan ba ki ɗaya. Abbi kuma ya ja Hannun Abra yana faɗin
"Wallahi shi ya sa Salman ya raina ki, kece babba amma kina maida kan ki ƙarama, gashi nan shi ya zama ƙatoto ya kusa kamani ke gaki nan kamar tsinke, banda shagwaɓa ba abunda ki ka iya".

Da sauri-sauri Salman ya fito da ga cikin motar bayan driver ya yi parking a entrance ɗin gidan su Ammi. Kai tsaye ciki ya nufa hankali ta she .Granny dake zaune a parlour hannunta riƙe da ƙatoton carbi ta yi saurin runste idanunta ta ce.
"Wa'innahu sulaimanu wa'innahu bisimillahir rahim, wanne ɗan asarar ne haka ya faɗo mana gida kamar kidnapa?"

Salman ya nemi waje ya zauna, ba tare da ya kalli Granny ba, infact hankalinsa ba ya jikinsa. Granny ta miƙe tsaye jiki na rawa tace.
"A'isha! A'isha! A'isha ki fito, fito maza Allah ya yi wa Na'ima rasuwa, Allahu Akbar Na'ima sa'i ya yi" Kallonta kawai Salman ya yi jiki na rawa Ammi ta fito ta ce.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wacce Na'ima? Daman bata da lafiya ne?" Granny ta girgiza kai ta ce. "Huhu ina zan sani, bari dai muji ko mutuwar ce?" Ammi ta ce "A'a, Hajiya ba shi ne ya faɗa ba?" Granny ta haɗe fuska ta ce "A'a kawai sai gani nayi ya faɗo mana gida hankali ta she, idan ba Na'ima ce ta rasu ba Uban mene zai saka ya faɗo mana gida kamar ɗan fashi ko irin kwartayen layin nan?"

Ammi ta zauna kusa da Salman ta ce.
"Mai gida ya ya akai ne?"
Salman ya ce. "Ammi da gaske Yaya ba ƴar Mami bace?" Granny ta dafe ƙirjinta ta ce.
"Masifa ta sauka a gidan Kamalu tirrr da halin Na'ima, ban taɓa gani ko jin labarin gantalliyyar mace mara rufin asiri irin Na'ima ba, Ubangiji ka ɗai ya san yadda zai da ita"
Kasa Magana Ammi ta yi hankalinta gaba ɗaya ya tashi har wani gumi ke tsastsafo ma ta.

"Ammi wajanki na zo domin ki faɗa min gaskiya, don Allah ka da ku barni a duhu, gani na ke har yanzu dare ne ban farka ba, gani nake kamar mafarki nake, Pls Ammi ka da ku barni cikin DARE DA DUHU" Salman ya ƙare maganar yana kama hannun Ammi.

A sanyaye Ammi ta ce.
"Naima told the truth, Abra is not her daughter, You and Abra are not siblings"
Kai Salman ya shiga girgizawa Ammi ta ce.

"Khamal ne ya tsinto Abra lokacin da suka je wani jeji...." She told him everything in a nutshell. Da yadda aka samu Abra, da kuma matsalar da Na'ima ta bayar kafin ta amince da riƙe Abra!
Kasa Magana Salman ya yi a lokacin na farko ya fashe da kuka yana ɗora kansa a cinyar Ammi, yana wata irin sheshsheƙa kamar ba namiji ba, wani irin tausayin Abra na ratsa zuciyarsa, ya na ji tamkar zuciyarsa ce zata bar tsakiyar ƙirjinsa sbd tsabar tashin hankali.

Hankali tashe Granny ta yi waje wajan gatekeeper tana faɗin. "Huhuhu idan bai kai Na'ima kotu ba Shegiya uwata ta haifan, Allah shi kaɗai ya san yadda zai da Na'ima ni da zan bawa Kamalu shawara kawai ya Aure yarinyar muga tsiya..." Sai kuma ta yi shiru tana zazzare idanu ta ce.
"A to ai ba wani abu ne, uban kowa ya san ba shi ne ya haifeta ba, wlh Na'ima za ta ga yadda ake tsiya da iya bariki idan ban saka Kamalu ya auri Babura ba a gantale a na zo duniya to"

Gatekeeper ya ce.
"Hajiya lafiya kowa?" ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Ashe matar Kamalu mahaukaciya ce?"
Shi dai Ya yi shiru, dan sun saba da wannan rikicin na ta na tsufa.

Sai Yamma Salman ya bar gidan bayan Ammi ta ba shi amanar Abra akan ya kula da ita, kada ya bari ta san Maganar ya share mata hawaye, Abbinsu baya zaman gida sosai.. ya ajjiye girmansa da Abra ta yi a gefe ya kula da kimarta.

Kaduna North.
Police station.
Ya na zaune a cikin office ɗin sa, jikinsa sanye da farar singlet sai ɗaukan idanu ta ke, ta kama faffaɗan ƙirjinsa fuskar nan tasa, a Kame kamar kullum babu alamar fara'a. Fararen idanunsa maƙale a jikin keyboard ɗin system wacce ke gabansa a saman table, cikin zafin nama yake operating system ɗin yana taune laɓɓansa. Baka ganin komai a fuskarsa sai jan laɓɓansa da farin Eyeballs ɗin sa, sumarsa tai kwance luff a kansa.

Tsaki ya ja kaɗan, sbd hayaniyar da ke ta shi da ga cikin police station ɗin zuwa office ɗin. He doesn't like noise, ciwon kai take sa shi. Tsaki ya ƙara ja a karo na biyu, cikin zafin nama kuma ya miƙe tsaye yana tura hannunsa cikin sumar kansa idanunsa ya yi jaa sosai sbd ciwon kan da ya fara.

Hannunsa zube cikin Aljihu ya nufi wajan office ɗin, da ga shi sai farar singlet da dogon wando na police uniform Wanda ya ƙara haska ɓakar fatarsa. Tsaye ya yi a bakin wajan hannunsa ɗaya cikin Aljihu ɗaya kuma ya riƙe ƙugu da shi.

Cikin tsawa S.p Adnan Aliyu Matawalle ya ce.
"Heyyy!  What's going on here?"  Wani da ga cikin police ɗin wajan ya tsarawa S.p Adnan ya ce.
"He was arrested for raping a three-year-old girl"

S.p Adnan ya ware manyan idanunsa, idan akwai abinda ya tsana a cikin  main crime that people are found with shi ne ”fyaɗe” He hates the word and doesn't like it at all. Cikin ɗaga murya S.p ya ce "What? Reped  three-years old? Police officer ɗin ya ce "Yes sir, wlh abin is so boring The girl died too"

Nan take idanun S.p Adnan ya ƙara yin jaa fiye da baya jikinsa na ɗan rawa kasancewar sa Mutum mai zafin zuciya, yana zuwa wajan Mutumin da ya yi fyaɗen ya kama hannunsa yana faɗin.

"You're mad, How can you rape a little girl like that? Ehh? you killed her!"
S.p ya faɗa yana fesar da iska da ga cikin bakinsa, idan ransa ya ɓaci bai iya controlling kansa ba, gaba ɗaya Police Officers ɗin suka shiga hankalinsu.
Cikin ɓacin rai S.p Adnan Aliyu Matawalle ya damƙi Hannun mutumin ya ce.
"An old man like you is the one who will rape her?"
Ƙass!!! Sauti Hannun tsohon ya bada ƙara sakamakon ƙarya hannunsa da S.p ya yi, wanda shi kansa bai san ya aikata ba.
Rai ɓace ya koma Officer ɗin sa ya ɗauki key car ya nufi waje.
Police Officers ɗin suka faɗawa D.o.p, abinda ya ke faruwa shi kuma D.p.o ya faɗawa presquito, presquito ya miƙa tsohon zuwa Court.

Tun da ga bakin gate ya fara danna Horn babu saurarawa, da sauri gatekeeper ya buɗe masa gate ɗin, cikin zafin nawa ya tura kan Benz ɗin sa cikin entrance ɗin babban gidan na su. Murfin motar ya buɗe ya fito kansa a ƙasa hannunsa zu be cikin Aljihu ya nufi cikin gidan da ɗan sauri domin babu abinda ya ke bashi tsoro irin hadari. Gashi garin dab ake da fara ruwan sama.

Hajiya Mama dake zaune a Parlour tana kallon News ta ce. "Wlcm My son"  wajanta ya Ƙarasa yana ɗora kansa a cinyarta idanunsa ya rufe, kalmar fyaɗe na yi masa yawo a cikin kansa. Hajiya Mama ta ce "what happened? as if you are worried"
Mirginawa ya yi a saman cinyarta ta tare da yin shiru, a hankali ya ke saukewa numfashi a nan cinyarta barci ya ɗauke sa tana shafa masa kai. Da idanu Hajiya Mama ta ke bin Adnan har tsoron zafin ransa ta ke, ga taurin kai. Tana jinjinawa matar da zata iya zama da shi matsayin miji. Burinta a yanzu bai shige ta ga aurensa ba.

Washegari ya kama weekend. Driving ya ke kamar zai tashi sama, Usman dake gefensa ya ce. "Wlh ka zubar damu Allah ya isa" S.p ya ja tsaki ransa a ɓace Usman ya ce "ka daɗe ba kayi tsaki ba, zance ne dole ka rakani kayi ta zama a haka mu soyayya yanzu muka fara" Adnan dai yaƙi cewa komai, kuma babu alamun zai ce Usman ya gyara zama ya ce.

"You don't understand, but love is love, it changes a person, ban taɓa tunanin zan so farar mace ba, burina na auri baƙar mace, When I saw Meenal for the first time, I couldn't help myself, yarinyar classic ce very educated ƙyakƙyawa ce sosai, A beauty I have never seen before" Usman ya wani lumshe idanunsa ya ce. "Kuma a photo kawai na kanta,  ina ta imagine yadda zan ganta reality, Uhm anya zan iya controlling kai na?

Ƙiiiiii!! S.p Adnan Aliyu Matawalle ya ja burki cikin zafin zuciya ya damƙo Usman ya ce.
"Banza, lion mayen mata zaka fice min da ga mota" Usman ya zare idanu ya ce "Goodness, zaka yiwa Meenal asarata let go of me pls my dear friend" hankaɗasa gefe S.p ya yi cikin ɓacin rai yaci gaba da driving har suka isa unguwar su Meenal wacce take da ɗan nisa da tasu sosai.

Kaf unguwar babu gida mai kyau da girma irin gidan Dr G.y Bulama, mai gadi ya buɗe musu ƙofa kasancewar Meenal ta sanar masa da zuwan guests ɗin ta. S.p ya gama parking Usman ya fara fita Adnan ƙin fita ya yi sai ma ƙira'ar Mishary Rashid Alafasy. A hankali ya ke bin ƙira'ar idanunsa rufe, cikin jin haushi Usman ya ce "Wannan dai wulaƙanci ne, ka ga idan zaka wulaƙantani a gaban Yarinyar nan ka koma kawai Nagode"

Adnan ya yiwa motar key, ganin da gaske tafiya zai Usman ya ce "Amma da ga ɗan iska sai kai S.p kaga ni wasa nake Please get down ga yarinyar nan" kashe motar ya yi tare da fitowa yana ƙare haɗe fuska nan na tasa, jikinsa sanye da maroon ɗin voyel mai kyau idanunsa maƙale da glasses mai kyau sai sumar kansa kwance da ita. Idanunsa ya ɗauke lokacin da Meenal ta ƙaraso wajan Usman ya shafa kai ya rasa me zance tayi musu Welcome ta ce "shall we...?" Ta faɗa ta nayin gaba. Usman ya kama Hannun S.p suka nufi guest Room ɗin da Meenal tayi.

Few minutes ta cika musu gabansu da kayan motsa baki, S.p ko amsa gaisuwarta bai ba, saboda rsai zufa data yanko masa, ganin yanayin S.p yasa Usman faɗin "Are You Okay Adnan?" A karo na farko Meenal ta ji Muryar Adnan mai tsananin daɗi ya ce "Headache.. i think I'm going now" ya faɗi hakan yana ɗauke idanunsa daga kan photon dake maƙale a jikin bango, Waje ya yi yana dafe kansa, yana fita Usman ya ɗan tattauna da Meenal ya na jin kamar ya ɗauke ta su tafi kawai tun yaushe, a nan tayi inviting na su zuwa birthday party ɗin ta, kana sukai sallama.

Kasa driving S.p ya yi, hakan yasa Usman ya amshi driving ɗin suka nufi gida.

A nan garin Kano. Salman ne ke biye da Abra cikin Ado Bayero mall, bayan ya rakata Saloon suka biyo yin shopping tare da shan ice cream. Bill ɗin kuɗin kayan akai masu Salman ya bada a.t.m aka cira, shi kuma ya ɗauki kayan ya ce "Angel muje" Abra ta bi bayan Salman cikin sanyin jiki, musamman da wani mutum ya kafeta da idanu. "Yaya idan ki kai aure ba'a gidanki zan tare ba, sbd na dinga tayaki aiki,  wannan sanyin jikin naki ya yi wa, kalleki wata rana dai zan goyaki naji nauyinki, dan na tabbatar jariri sai ya fiki" Abra tai Murmushi ta ce "Allah ya shiryaka Faris" da sauri ya ce "Amin Yayata, ina buƙatar shirin Ubangiji kiyi min addu'a kwana nan bana gane kai na"

Da sauri ta ce
"Meke damunka Faris? Gaya min Pls" ya girgiza ma ta kai ya ce "Wlh ban sani ba Angel" suna ƙoƙarin fita daga cikin wajan mutumin dake kallon Abra ya yi saurin riƙe ma ta hannu. A razane Abra ta juya sukai idanu biyu da saurayin mai kyan gaske, fari tas ƙyakƙyawa ajin farko. Jiki na rawa ta fara ƙoƙarin  ƙwace hannunta.

Saurayin mai suna Abdullah ya ƙara riƙe hannun Abra gashi Salman ya yi mata nisa yana can yana surutu ya ɗauka suna tare, cikin razani Abdullah ya ja numfashi ya ce "Who are you?" Ya faɗa yana ƙoƙarin shafa fuskarta, kafin ya Ƙarasa ɗora hannunsa akan fuskarta ya ji an sauke masa wani irin mari, da sauri ya dubi Salman dake tsaye yana huci kamar zaki ya ce "How dare you slap me like that?"  Salman ya ce "An marake, kasan jikin waka taɓa? Wlh kamar an soka min  ma shi a zuciya,  mutum ɗaya keda mallakin jikin Angel wlh na ƙara ganin ka shiga harkata sai nayi maka illa"

A wannan lokacin Salman har Abra ya ji haushi,  ko inda take bai kalla ba ya juya tare da yin waje, yana ƙoƙarin ficewa Abra ta ƙwala masa kira
"Faris...!!!" Zubewa ta yi a waje jikinta na rawa numfashinta na ɗaukewa ƙirjinta na ɗagawa kamar mai Asthma, hannunta riƙe da cikinta, a kiɗeme Abdullah dake tsaye ya durƙusa zai kama Abra Salman daya ƙaraso wajan ya hankaɗe Abdullah yana zubewa gaban Abra yana faɗin "Yaya mene ya sameki? Yaya menene I'm here ga ƙaninki a wajanki, Angel open your eyes" ya ƙare maganar yana jijjigata amma tuni numfashinta ya yi sama yana ƙoƙarin ɗaukewa. Cikin tashin hankali Salman ya jawo Abra jikinsa yana ƙanƙameta kamar wani zai ƙwace masa ita.

Ganin numfashi na ƙoƙarin ɗaukewa, ga shi duk mutane sun zagaye su yasa Salman warware rolling ɗin kan Abra ya rufe mata fuska can kuma ya tuna da maganar wani malamin su daya faɗa musu a lap, cikin sauri jikinsa na rawa da ɓari ya ɗaga mayafin nata tare da zura ƙansa ciki, a hankali ya tallafo fuskarta a hannunsa tare da ɗora bakinsa akan nata...


LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
[9/30, 8:55 PM] Abk: *DARE DA DUHU*

_Brigh pens✍️_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee Kumurya

                               P14

Domin samun complete litattafanmu, ku yi following ɗin wannan accounts ɗinkin a Arewabooks

https://arewabooks.com/chapter?id=6316f4af434cfeb9e7fe2949

https://arewabooks.com/u/nimcyluv
https://arewabooks.com/book?id=

Elegant online writers

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.





Kamar wanda aka tsikara ya yi saurin janye fuskarsa ya fasa yin abun da ya yi niyya, gyara mata mayafin jikinta ya yi ya ciccib'e ta ya miƙe tsaye da ita a jikinsa. Mutumin nan da Salman ya hankaɗe shi bai daddara ba ya ƙara matsowa da niyyar ya taimaka masa su riƙe Abra tare, a matuƙar kufule Salman ya kai masa duka da ƙafa, saurin ja baya ya yi cikin mamakin ƙarfin halin yaron da taurin zuciyarsa. Wata muguwar harara Salman ya cilla masa tare da yin ƙwafa sannan ya yi gaba da sauri ya nufi Motarsu.


Driver na hango su ya fito daga mota da sauri, cikin al'ajabi ya fara tambayar Salman abun da ya faru.

"Please buɗe mun baya na saka ta mu tafi asibiti."

Salman ya faɗa masa haka cikin damuwa da ɓacin rai.

A hanzarce Driver'n ya buɗe masa Motar, kwantar da Abra dake sume tamkar babu numfashi a jikinta ya yi, sannan shi ma ya shiga bayan, akan cinyarsa ya ɗora kanta ya ƙurawa fuskarta ido cikin tsananin damuwa da fargabar kar ya rasa ta, a hankali ya ɗora hannunsa akan fuskarta yana shafawa cikin rashin sanin abun yi, addu'a kawai yake a cikin ransa akan Allah ya tashi ƙafaɗun Yayarsa.


Cikin mutunen da suka biyo su suna musu Allah ya kiyaye gaba, wani ya miƙa masa handbag ɗin Abra da ledar siyayyar da suka yi. Ko kallan shi bai yi ba dan ba ta su yake ba, sai driver ne ya karɓa ya saka a front seat.

Matashin saurayin nan kuwa (Abdallah) ya kasa ɗauke idonsa daga kansu, sai da Motarsu ta bar gurin sannan ya sauke numfashi ya shiga tasa motar cikin sanyin jiki, zuciyarsa cike da tsananin mamakin wani al'amari.


Asibitin Isyaka Rabi'u nan Driver'n ya kai su, saboda yanda Salman yake azalzalar shi akan ya yi sauri, asibitin kuma shine asibiti mafi kusa daga nan Ado Bayero mall ɗin.

Ko gama daidaita parking driver bai yi ba Salman ya buɗe Motar tare da fitowa ya nufi cikin asibitin cikin sassarfa. After some minutes suka fito tare da wasu Nurses dake ɗauke da kujerar ɗora marasa lafiya.

Cikin sauri Salman ya fito da Abra daga cikin motar aka ɗora ta akan wheel chair, Nurses ɗin suka tura ta zuwa ciki Salman na biye da su.

Emergency suka nufa da ita. Har ɗakin da aka shigar da ita Salman ya so bin su, amma aka dakatar da shi aka ce ya jira waje.

Numfashi ya sauke mai zafin gaske saboda yanda zuciyarsa take yi masa ƙuna, hoton saurayin nan a lokacin da ya riƙe hannun Abra tare da ƙoƙarin kai hannunsa fuskarta ya kasa b'acewa daga cikin zuciyarsa, ganin abun yake tamkar yanzu yake faruwa. Ga kuma damuwar halin da Abra ta shiga lokaci ɗaya, zuciyarsa sai bugawa take saboda fargaba da tashin hankali.



Dafe kansa da gumi ke kwance akai ya yi, innalillahiwa'inna'ilaihirra'un kawai yake maimaitawa a cikin zuciyarsa.

"Allah ka tashi ƙafaɗun Yaya ka ba ta lafiya."

Ya faɗi hakan a fili cikin tsananin damuwa.

"Me ya same ta ne wai ƙaramin Alhaji?"

Driver da ya biyo bayansu ya tambaye shi a rud'e.

"I don't know, ƙara kawai na ji ta yi, shikenan sai ta faɗi."

"Subhanallahi, to Allah Ubangiji ya ba ta lafiya."

"Ameen."
Ya amsa a ƙasan maƙoshi.

Zarya ya shiga yi a reception ɗin cikin tashin hankali, dan ya rasa a ina ma zai saka ransa ya ji daɗi, sai kallon ɗakin da aka shigar da Abra yake, ji yake kamar ya tafi ya faɗa cikin ɗakin ya ga halin da take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login