Showing 216001 words to 219000 words out of 231718 words

Chapter 73 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14670

ba ni."

"Shikenan na ɗauki ƙanƙantar Yaya Faris."

Murmushi suka yi a tare cikin ƙaunar junansu. Adnan dake kallon su ya ji zuciyarsa na wari irin tafarfasa saboda kishi, a fusace ya taho zai zare hannun Abra daga cikin na Salman tare da ja masa warning, taku ɗaya ya yi tari ya sarƙe shi. Da sauri Abbi ya kama shi suka fita ganin ya fara aman jini. Taɓe baki Abra ta yi tare da shigewa ciki, Salman ya bi ta da kallo.




Ya san Yayarsa tana son shi har yanzu shi ma kuma haka, amma shi ya fi son ta koma gidan Adnan ko dan little, ba ya son yarinyar ta taso ta ga iyayenta ba sa tare. Sannan Afra tana mugun son shi, a zaman da suka yi tare shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su, idan ya ce Abra yake so ba ita ba za ta shiga mawuyacin hali.


Ɗakinta ta shiga ta tarar da Ummi da Inna a zaune. Zama ta yi a kusa da Ummi dake sakar mata murmushi.
"Allah ya yi muku albarka." Ummi ta faɗa tana shafa kanta. Cikin jin daɗin kasancewa da mahaifiya Abra ta ce. "Amin." Kwantar da kanta ta yi akan kafaɗar Ummi ta ce. "A Ina ƴan'uwan mahaifinmu suke a ƙasar nan? Ina son mu haɗu da su." Ɓata fuska Ummi ta yi alamun ba ta san zancen Bulama, amma duk da ƙin shi da take ta san ba ta isa ta raba shi da Ƴaƴansa ba. Kamar an mata dole ta ce. "Suna Adamawa, amma iyayensa duk sun rasu, sai ƙanwarsa guda ɗaya Murja da sauran relatives ɗinsu." Kafin Abra ta kuma magana Afra ta shigo da Little a hannunta. Ba tare da yi magana ta ɗora ta a kan cinyar Abra. Kawar da kanta ta yi duk da cikin ranta cike take da zumuɗin ganin fuskar ƴar tata.

"Ki ɗauki ƴarki, wannan abin da kike yi ba daidai ba ne, tunda ba ta miki laifin komai ba, bai kamata kuma laifin mahaifinta ya shafe mata ba."
Afra ta faɗa cikin sigar nasiha.

Murmushi Inna ta yi a ranta tana mamakin hankalin da ƴar Baba ta yi a zamanta a gidan Abbi. Rungume little Abra ta yi tare da sakin ajiyar zuciya, ƙaunar yarinyar na ratsa ko wane saƙo na jikinta, ta ji duk duniya babu abin da ba za ta iya yi ba saboda ita. Haɗa su Ummi ta yi ta rungume gabaɗaya tana hawayen farinciki, Afra ta zo ta zauna a ɗaya b'arin ita ma ta rungume ta, ban da ajiyar zuciya da hawaye babu abin da suke.


Haka rayuwa ta cigaba da garawa cikin farinciki ga su Abra, duk da tunanin mahaifinsu da halin da yake ciki yana damun su. Sun samu labarin har yanzu ana shari'a akan asibinsa ba a ƙare ba, kuma kotu ta ƙi bayar da belin shi yana can a tsare. Shirye-shiryen bikin Salman da Afra ya kankama, Abbi ya sa an ƙara gyara wa Salman guest house ɗinsa, a can za su tare shi da amaryarsa da suke cin soyayyar su babu tsinke. Abra ta kwantar da hankalinta, ta cigaba da kallon Salman a matsayin blood brother ɗinta. Aunty Murja ta zo tun saura kwana uku biki, Ummi ta kira ta, ta sanar da ita duk abin da yake faruwa, da yake suna shiri sosai. Amma fa ta sha ciwon bakin ƙin sanar mata Bulama ya ƙara aure da ta yi. Adnan yana can jiki ya ƙara rincaɓewa, kuma ya ƙi yarda a fitar da shi waje, ya ce maganin ciwon shi kawai Abra ce. Abba kuma ya ƙyale shi ya ce ya je jikinsa ne, shi yake shan azabar ciwo ba wani ba. Kullum sai ya kira Abra ba adadi, ita kuma ba ta ɗaukar kiran, mamakin ma inda ya samu numbernta take, saboda sabon sim ta sake. An yi biki lafiya an gama lafiya, ba a wani ja abun sosai ba, dinner kawai aka yi da ɗaurin Aure aka kai amarya gidanta. Ranar Afra ta sha kuka, na barin su Inna da kewar Baba, ta so a ce ya ga ranar aurenta kamar yadda ya ci buri, amma Allah bai yi ba. Abra ma ta taya ta kukan, don duk da ba su jima da kasancewa da juna tare ba amma ta ji ba daɗi sosai a cikin ranta, a gefe kuma ta taya ta farinciki matuƙa na auren Namiji Jarumi, Yaro da halin manya Salmanul Farisi.




Washegari da safe Afra tana baccin gajiyar da Salman ya tara mata a daren jiya ta ji ana yi mata tafiyar tsutsa a ƙafa. A hankali ta buɗe kumburarrun idonta da suka ci kuka ta sauke a kan fuskarsa. Murmushinsa mai kyau ya sakar mata tare da ranƙwafowa cikin sanyin murya ya ce. "Morning princess." Juyar da kanta ta yi gefe tare da turo baki. Kissing lips ɗinta ya yi tare da faɗin. "Tun ɗazu nake jiran ki tashi ki yi breakfast kar yunwa ta illata mini ke, kuma bana son na tashe ki kanki ya yi ciwo." Cikin shagwaɓa ta ce. "Ai dama ciwon yake." Marairaice fuska ya yi ya ce. "I'm sorry dear, mu je ki wanka sai ki sha magani, idan bai daina ciwon ba sai mu je asibiti." Riƙe duvet ɗin da yake ƙoƙarin yayewa ta yi ta ce. "To ka bar ni zan tashi da kaina." Murmushi ya yi cikin ransa yana faɗin. "Wanne dare ne jemege bai gani ba." Ƙarar da ta saka ya sa shi saurin ɗago ta yana tambayar ta lafiya? Hawaye ta fara ta ce. "Na kasa tashi, ko'ina a jikina duk ciwo yake mini, ƙafafuwana kamar ba a jikina suke ba. Cikin tausayawa ya shafa kanta tare da faɗin. "Sorry, har yanzu jikin bai bar ciwo ba?" Gyaɗa masa kai tare da taune lips ɗinta saboda zugin da take ji a ƙasanta.

"Okay bari na ga gurin ko da rauni."

Kuka ta saka masa tare da ƙanƙame jikinta ta hana shi ganin abin da yake son ganin. Numfashi ya sauke a hankali tare da saka hannu ya fara goge mata hawayen fuskarta, ture hannun ta yi tare da ƙoƙarin tashi daga jikinsa. Riƙe ta ya yi sosai cikin rarrashi ya ce. "Har yanzu fushin bai ƙare ba? Na ce fa ba zan kuma fa, jiyan ma duk ke kika ruɗani da kyawun da kika yi da daddaɗan ƙamshin da kike." Ya ƙarasa maganar tare da tusa kansa a wuyanta yana shaƙar ƙamshinta dake saukar masa da kasala. Ajiyar zuciya suka sauke a tare da lumshe ido. Jin ya fara sassauke numfashi tare da yawo da hannunsa a jikinta ya sa ta buɗe ido da sauri tare da ture kansa, don ba ta manta bak'ar azabar da ta sha ba a hannunsa jiya. Bai ce komai ba ya ɗauke ta cak ya kai ta toilet.



Littafin dare da duhu na kuɗi ne, mai so ya tuntube mu a wannan numbern. 09047871750
[11/30, 9:12 PM] Abk: Da yamma Salman na zaune a parlourn gidansa ya yi wani fresh alamar tun a daren jiya angwancin ya amshe shi, shi kaɗai sai murmushi yake lokaci zuwa lokaci yana ɗaga kansa tare da kallon ƙofar bedroom ɗin ta.
A hankali ya miƙe tare da ajjiye remote ɗin hannunsa kai tsaye bedroom ɗin ya nufa daga shi sai trousers iya giwwa jikinsa ko riga babu. Kwance ya sameta har yanzu saman gado ta rufe jikinta da duvet barci take a wahale har yanzu.

"Oh sweetheart barci har yanzu?" Ya faɗa yana saka hannu tare da zame duvet ɗin, firgigit ta farka tana buɗe idanunta wanda hawaye ya gama cika su. Hucin zazzaɓi na fita a jikinta Salman ya haura gadon baki ɗaya suna haɗa ido ta fashe da kuka sosai, domin gani take kamar yana sane yake mata komai haushin shi duk ya kamata.
Cikin rarrashi yana jawota jikinsa baki ɗaya tare da shafa kanta ya ce.

"Sorry wife double sorry ni ne ko?" Kai ta ɗaga masa alamar "eh" tana ƙara shigewa jikinsa saboda daɗi ɗumin jikin da take ji. Ya ya yi kissing lips ɗinta yana zame mata hannun duguwar jikinta a ƙoƙarin shi na son sake haɗa jikin nasu waje guda da kyau! Yadda za tafi jin daɗi domin ya lura da yanayin nata..
Gaba ɗaya ta juya tare da rungome shi sosai sbd bayyanar jikinta hannunta a ƙirji shi tana duka tare da ƙananun kuke ta ce.

"Uhm Uhm zan faɗawa Abbi da Mami mugunta kake mini"
Ya kwaikwayi muryarta yana sake riƙeta a jikin nashi tare da ƙoƙarin lalubar bakin da ya yi maganar ya ce.

"Uhm to ai haka shi ne auren sweetheart wife"

"Sure?" Ta tambaye shi tana kafe shi da maraitattun idanunta wanda suke ƙara kashewa Salman jiki da zuciya. Ya tarairayota baki ɗaya saman sa sun jima suna kallon juna cikin ƙasa da murya ya ce.

"I love You Afra Yusuf Garba Bulama, ban san adadin son da nake miki ba, bani kuma da bakin yi miki godiya a bisa kyautar da kika bani,
I am immensely thankful to you for deciding to marry such a stubborn person like me and for going forth numerous times just to assure I was happy. Wallahi Afra ina son ki so mai yawa, son da baki ba zai taɓa iya faɗa ba sai dai gangar jikina tayi aikin ta,
The best part of my day is your smile. Being with you is the easiest choice I have ever made, and I'm so lucky I get to make it every day. I love you more every day. I love your honesty, your passion, your resilience, your courage, your partnership, and your smile"

Manyan kalaman da suke fita daga cikin bakin Salman sukai wa Afra nauyi a zuciya da sauri ta juya ta rungome Salmanun-faris a jikinta tana shassheƙar kuka wanda babu tantama na farin ciki ne.
"I love You Amore Mio, love you to the rest of my life"

"Amore Mio?" Salman ya tambaya yana ɗago ta daga jikinsa, taƙi yarda ta kalle shi sbd Kunya a hankali tana ɓoye kanta ta ce.

"My love" yana kashe mata ido ya ce "da wanne yare?" ta rufe idanu ta ce "French" ya ɗago ta zuwa jikinsa yana sauka kan bed ɗin tare da nufar parlour da ita ya ce.
"Oh, ashe matar tawa ta iya speech shi ne take pretending" yana faɗin hakan yana kissing nata.

Abra dake zaune a parlour shigowar ta kenan tai gyaran murya kunya ta kama Salman da ita kanta Afra, Abra tai murmushi hannunta riƙe da Little ta ce.
"I'll pretend I didn't see anything".
Salman ya shafa kai yana sauke Afra data kasa kallon Abra ya ce "Yaya" ta watsa masa harara ba tare data ƙara kallon shi ba, ba sabon au bane gare ta ganin Salman ba riga shi ya sa ba taji komai ba.
Ya juya da sauri zuwa bedroom ɗinsa Afra kuma ta taka a hankali tana cije baki ta zauna tana faɗin.
"Daughter mai kama da Maman ta" Abra ta gyara zama domin Adnan ta guduwa tun ɗazo yake gidan ya hanata sakat da naci.
Kuma ba tai niyyar zuwa gidan nasu ba kawai bata da zaɓi ne.

Abra na zaune bayan ta shirya cikin kayan barci ta ƙara fresh ƙirjinta ya cika sosai, tayi wani irin kyau kamar wacce batai jinya ba, fatar jikinta sai glowing take. A hankali ta zauna tana buɗe datar wayarta sbd littafin da take karantawa na IDAN BA KE ya gama tafiya da tunaninta, ita ba gwanar karatun hausa novels bace tafi ƙarfi a English. Kamar da wasa taga littafin a wattpad ta fara karantawa.
"Ikon Allah Surry muguwa ce, wannan ai muguwar shawara ce take bawa Zahrah, ta ya ya mijinta zai amshi budurcin wata a matsayin nata?" Tsaki taci gaba dayi ganin littafin yaje ending na free pages, kuma tana son taji ƙarshen labari ta ya ya Aljani zai auri mutum harda haihuwa a tsakani. Da sauri ta duba number da akai dropping 08119237616 tai adding number a WhatsApp tare da yin payment ganin marubuciyar bata Online yasa ta kashe network ɗin wayar.

A hankali idanunta ya sauka akan photon Sp Adnan Aliyu Matawalle ta sauke numfashi ta kasa tantance hukumcin da zuciyarta ke son ɗauka game da Adnan, duk da wulaƙancin da Adnan ya yi mata but till now yana da gurbi a zuciyarta tana jin tausayin shi.
Tana tuna makomar Aishatul-humaira. "You're the reason behind anything Adnan, ka rusa zuciyoyinmu"

"Uhm kafin ai ɗaran akai kwanɗi, kafin kace uhm ake taɗi" Abra ta juya da sauri ta kalli Mami ta ce "Me nayi Mami?"

"Nace wani abu? Waƙa nayi, ZUCIYAR MUTUM, SIRRIN SA." Abra ta kwaɓe fuska ta ce "Kai Mami"
"Ba wani kai Mami, kije Abbinki na kira" zuciyar Abra ta buga ta miƙe da sauri kamar zatai kuka abinka da shagwaɓɓiyya ta ce.

"Mami me nayi, wayyo Allah" Mami ta saka hannu ta ɗauki Little tana faɗin "Zonan Mamana, wannan rigimar tafi ƙarfin ki muje ki yi barci" tana faɗin hakan tai waje domin ta lura da sauyawar Abra khamal Khamis ɗin.

Jiki a sanyaye ta saka hijabi tare da saka Hermes slippers a ƙafarta ta fita zuwa Main parlour. A zaune ta samu Abbi da Mami, Sai Ummi da Abdullah da kuma Salima. Tare da Adnan dake durƙushe ya saka dakakkiyar shadda amy colour wacce ta ƙara haska baƙar fatarsa, sai baza ƙamshin Pur oud yake,
Iya kyau ya zuba kyau sai ramar dake maƙale a jikinsa na azabtuwa da soyayyar Abra. Jikinta na rawa ta nemi waje ta zauna ta ce.
"Gani Abbi"
Ya gyara zama yana ɗan sakin murmushi ya ce.
"Abra Daughter ga mijinki ada ya kawo abin da kike buƙata"
Ta ɗaga kai da sauri ta kalli Abbi zuciyarta na harbawa tsoro da fargaba suka cika mata zuciya. Ta kasa magana sai sunkuyar da kai da tayi tana wasa da yatsun hannunta.

"Allahamdulillah Adnan ya yarda da ƙaddara ya amince da abin da kike buƙata, ya kawo takardar saki i mean divorce papers, kuma zai tafi da yarinyar shi kamar yadda kika ce,
dashi da ita bakya buƙatar su, ina miki addu'ar samun miji wanda ya fi shi, shi ma Allah ya bashi wacce ta fiki"
Bata san mai ya faru da ita ba, amma tuni hawaye ya gama wanke mata fuska ta shiga gogewa ba tare da kowa ya lura ba.
Abbi ya yi murmushi ya ce "ina tunanin ke kike son haka ko?baki da idda san haka na baki sati guda ki fito da miji ko na zaɓa miki wanda naga dama"
Mami ta ce
"Kayi mata haƙurin wata ina za taga wani saurayin yanzu?" Abbi ya ɗaga hannu ya ce. "Tunda ta ce mijinta ya saketa ai ta shirya fito da wani, ba wani wata da zan bata" ya juya kan Adnan ya ce "Allah ya yi maka Albarka Adnan da umarnin mahaifin ka da kabi, maza ɗauki Mamana Aishatul-humaira ku tafi"

Muryar Adnan a sarƙe ya ya miƙe tare da faɗin "Na gode Abbi, Allah ya ƙara girma" ya faɗa idanunsa akan Abra wacce ta kasa motsi.
Yana miƙawa Little hannu kamar mai jira ta ɗaga hannunta tana sakin dariya ya yi murmushi kaɗan tare da rungome ta.
Da sauri Abra ta miƙe ta ce.
"Ka bani ƴata ai ba kai ka haifar mini ita ba" Ummi dai kallon komai take hukuncin Abbi ɗin ya yi mata daɗi domin yanzu tausayin zaryar da Adnan ɗin yake take.

Adnan ya kalli Abra wani abu na fisgar shi yana jin kamar ya rungome ta ya yi ta kuka ko zata sassauta masa, zuciyarsa har wani dunƙule masa take.
"Ka bani ƴata Malam, ka fita daga cikin rayuwarmu, ka saki uwa me ƴa zatai maka kuma?"
Mami zatai magana Abbi ya dakatar da ita, tare da nuna mata ta zuba idanu zuwa inda dramar zata ƙare. Adnan ya sassauta murya mai nuna ki tauyasa mini komai nayi kuskure ne ba son raina bane.
"Na rasa abin da kike nufi? Kince na sake ki? Kuma kince na ɗauki ƴata dani da ita bakya buƙatarmu, mene laifina saki ke kika nema fa? Ƴa kuma ta wace" a fusace Abra ta wani lailayo zagi zatai komai ta tuna kuma Ohu! Taja baki tare da yin shiru.
Idanunta ya yi jaa sosai ta juya wajen Abbi ta ce
"Abbi kace ya bani ƴata? Tunda ya yi abin da zuciyar shi take so nima zan yi abin da nai niyya"

"A'a ba ruwana Daughter,bana son rashin gaskiya ke kika bashi zaɓi kuma yabi, Son kada dare ya yi maka" Abra ta fashe da kuka sosai tare da shigewa part ɗin ta, ta shiga kiran number Abba da Hajiya Mama amma duk basu ɗauka ba kamar haɗin baki.
Ta shiga rera kuka a yanzu babu abin da zuciyarta ke muradi da son kasancewa da ita irin Aishatul-humaira gashi Adnan ya yi amfani da maganar da tayi wajan rabata da gudan jikinta. MAGANA ZARAR BUNU.

Tun daga lokacin Abra ta shiga gaba da kowa ta yini kuka ta kwana kuka, Salman da kansa ya bawa Abbi haƙuri akan a bawa Abra ƴarta. Amma Abbi ya yi masa korar kare.
Ummi taja Abra jikinta ta shiga yi mata nasiha akan ta koma gidan mijinta daga nan ta ƙwato ƴarta ko kuma ta koma sbd yarinyar badan halin Adnan ba.
Hajiya Mama ta ci-gaba da kula da Little yarinya mai shiga rai. Ɓangaren Salman da Afra soyayya mai zafi ake tun tana jin kunyar shi har ta daina ya shagwaɓata da tarin soyayyar shi da kalar nasa salon mai mantar da duk wanda ƴa mace duniyar da take ciki. Har ta kai idan ba shi sam ba zata iya bacci ba ta sama da rayuwar auren kamar yadda yake buri tattali take samu sosai cikin sati guda daga Salman har Afra suka ƙara wani haske da ƙima Masha Allah.

Ummi da Abdullah suka koma Dubai bayan an mata al'ƙawarin zuwan twins ɗin nata, burinta na son tafiya dasu bai cika ba, Dr Bulama har yanzu yana tsare domin an gano manya-manyan laifukan daya aikata a asibitin shi da ɗaukan ma'aikatan wanda sam basu dace ba, uwa uba kuma Ummi ta ƙara sawa akai masa sammacin cinye mata dukiya da ya yi, domin har yanzu wasu kuɗin basu fita ba, tare da cewa ya bata takardar sakin ta.
Wannan abu ya zaga ko'ina har kunan gwamna, aka shiga binciken ko wanne asibiti tare da tabbatar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login