Showing 66001 words to 69000 words out of 231718 words

Chapter 23 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14702

a gidan ne ko gidan na arna ne? Ana ta sallama an ƙi amsawa."

Hararar ƙasan ido Suwaiba ta wurga wa Granny, cikin raini ta ce. "Me Idonki ya gane miki?" Tafa hannuwa Granny ta yi ta ce. "A'a fa, kar ki mun fitsara da farar safiyar nan, wallahi jibguwa zaki yi, kin san jikana soja ne, yanzu sai in kira shi ya turo sojoji mota-mota a tafi dake a ɗaure, don haka ki kiyaye ni. Kodayake ba laifinki ba ne, zafin zawarci ne, dan shi babu abun da ba ya sakawa." Ba ta jira cewar Suwaiba ta shige ciki tana baɓɓata fuska.

Mama ta tarɓe ta ba yabo ba fallasa, Granny ba ta damu ba ta zazzage musu abun da yake cikinta tass, sai da ta ƙare musu cin mutunci akan mugun halinsu sannan ta dubi Nai'ma dake ta banka mata harara a sace ta ce. "Kya iya kwaso jiki ki biyo ni mu tafi, ba kuma don halinki na zo bikon nan ba, don ɗanki Salman na zo, yaron kirki kar ya ƙullace ni akan abun da na yi miki." Nai'ma ba ta tanka mata ba ta miƙe ta shige ɗaki. Taɓe baki ta yi. "Ko ba komai yau an yi kwanan gidan gyatumi cikin sauro da zafi ba cikin raɓa gidan jikana da aka saba ba." Tsaki Aunty Suwaiba ta yi ta miƙe ta bi bayan Na'ima.




Around 12 na rana su Abra suka fito daga lecture, lecture biyu gare su kawai yau. Za ma ta yi a ɗaya daga cikin rumfunan department ɗinsu dan jiran Salman, shi sai 1 za su tashi. Khairat ce ta ƙaraso ta kama hannun Abra ta ce. "Zo mu je ki kira ni in duba wani abu kafin twin brother ɗin naki ya fito." Ƙin tashi Abra ta yi ta ce. "Kai khairy kin fiya yawo."

"Please ki taso mu je."

Yamutsa fuska Abra ta yi ta ce. "Ina za mu?" Khairy ta ce. "Can ne fa ba wani da nisa ba, daɗina dake ragwanta, yanzu ɗan zaman lecture ɗin nan sai ki ce kin gaji, ana ganin ki an ga fresh student." Murmurshi Abra ta yi ta miƙe suka tafi.

Office ɗin Fayyad suka je, Khairy ta duba ko za ta ƙara ganin Adnan yau ma, sai dai ta yi rashin sa'a, yana tafiya suka zo." Cikin rashin jin daɗi ta ce. "Oh My God, kar dai yau ban zo school a sa'a ba?" Abra da ba ta san akan me take magana ba ta ce. "What happened?"

"Guy ɗin da nake ba ki labari jiya na zo gani, daƙyar na iya bacci daren jiya saboda tunaninsa, na ci burin sake ganin shi yau, kuma kin san muna zuwa nan na ji ƙamshinsa." Khairy ta ba ta amsa cikin rawar jiki.

Jinjina kai Abra ta yi ta ce. "Kin gamu da wahala amma, daga ganin mutum duk kin wani burkice, har kin gane wani ƙamshinsa?"


"Ba za ki gane ba ne Abra Khamal Khamis, guy ɗin ya haɗu ƙarshe, kin san bana son baƙin Namiji, amma ganin guy ɗin nan jiya gaba-d'aya ya canza mini ra'ayi, ban yi tunani cikin baƙaƙen maza akwai masu kyau haka ba."

Taɓe baki Abra ta yi dan totally shirme ta ɗauki batun, a ganinta wannan wahala ce da ɗora wa kai jidali. Komawa gurin zamanta ta yi ta bar Khairy da dube_dube, dan ƙin haƙura ta yi ta ce ita ba za ta tafi ba sai ta gan shi.


Bayan sun koma gida suka tarar Nai'ma ta dawo, ba ta nuna musu komai ba da za su gane akwai dalilin da ya sa ta tafi gida jiya ba. Kasancewar Abbi yana nan ba ta nuna wa Abra komai na kyara ba, har girki ta yi kafin su dawo, a cewarta ƴarta ta kwaso gajiyar school ba za ta dawo ta yi girki ba. Abra tana cin abinci ta yi Sallah ta watsa ruwa ta kwanta, tunda babu abun da za ta yi.





Da yamma Abra na zaune ita kaɗai a main Parlor tana duba lecture note ɗin da aka yi musu yau. Salman ya fito daga ɗakinsa cikin shigar kayan Ball. A hankali ta ɗago ta kalle shi jin ƙamshinsa, ɓata fuska ta yi tare da ɗauke kanta. Ƙarasowa ya yi ya zauna a gefenta ya ce. "Angel Sarkin karatu, ba ga bokon ba, ba ga islamiyya ba."


"Ina zaka je?" Ta tambaye shi a shagwaɓe.

Idanunsa a cikin nata ya ce. "Ball, amma bazan jima ba zan dawo."

"Ball kuma Faris? Maimakon ka zauna ka yi karatun abun da aka yi muku yau? Ko dan ka ga Abbi ba ya nan ne?"

"Idan na dawo zan yi, kar ki damu Babyn Faris da Abbi."

Turo baki ta yi ta ce. "Ni dai kar ka fita ka bar ni, ni kaɗai Please."

"Ki yi haƙuri Yaya, ba zan jima ba fa." Ya ƙarashe zancen tare da kamo hannunta. Kamar za ta yi kuka ta ce. "To zan bika."

Shafa sumar kansa ya yi ya ce. "Angel rigima, gurin ball ɗin zan tafi dake? ai ta kalle ki ana tanka ki raina yana ɓaci a banza, ban yarda ba gaskiya."

"To mene abun ɓacin ran?"

"Ke ba za ki gane ba ai." Ya faɗi haka tare da miƙewa tsaye ganin lokacin fara ball ɗin har ya wuce. Kallon shi kawai take ba ta ce komai ba, ganin yanayinta ya san yana fita za ta iya yin kuka, shi kuma ba ya son hakan. Cikin rarrashi ya ce. "Mene wai? Yanzu fa zan dawo, ki yi kallo ko chat ko game kafin na dawo, zan taho miki da favourite thing ɗinki, choculates and sweets, I promised."


"Ba na so, tunda kai always sai dai ka fice ka bar ni."

Da ƙyar ya samu ya lallab'a ta, ta bar shi zai tafi, amma sai da sharaɗin ba zai wuce one hour ba, ya ce ya amince. Har bakin gare ta raka shi, sai da ta ga fitar shi sannan ta koma cikin gida.


Kasa cigaba da karatun da take ta yi, tunanika kala-kala ne suka shiga yi mata yawo a cikin kai, tunanin rayuwarta da ƙalubalen da take fuskanta daga gurin mahaifiyarta, da kuma yanda yanzu take ƙoƙarin shiga tsakaninta da Abbinta.


Knocking ɗin ƙofar parlour'n da aka yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi. Numfashi ta sauke tare da miƙewa cikin sanyin jiki ta je ta buɗe ƙofar bayan ta tambayi waye. Gabanta ne ya yanke faɗi ganin Uncle Faisal, ba ta ƙaunar abun da zai na haɗa ta hanya da mutumin nan ko kaɗan a rayuwarta. Baya ta yi da sauri ganin irin kallon da yake bin ta da shi, cikin rawar murya ta ce. "I...ina ...kwana?"

"Lafiya ƙalau, Aunty Nai'ma fa?"

"Tana sama tana bacci, bari na kira ta."


Wani ɗan murmushi ya yi yana bin parlour'n da kallo kamar mai neman wani abu, cikin ransa kuwa faɗi yake. 'Wannan wata dama ce da ka samu Faisal, ka yi amfani da ita wajen cimma burinka na shekara da shekaru ba tare da kowa ya san kai ka aikata ba." Ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idonsa, ya tuno lokacin da ya shigo gidan yanzu bai gamu da kowa ba, dan yana ta horn mai gadi bai zo ya buɗe masa gate ba, hakan yasa ya yi parking Motar a waje ya shigo babu ita, ya yi sa'a kuma ƙaramar ƙofar gidan a buɗe take. Ya san Salman ba ya gidan yanzu, dan da yana nan dole tare zai gan su da Abra a parlour, tunda ba sa iya rabuwa idan ba lokacin bacci ba, tamkar HANTA DA JINI haka suke.

Abra ganin yanda ya yi shiru ta san ba Alkhairi yake kitsawa a cikin ransa ba, hakan yasa ta juya da sauri don guduwa ɗakinta. Ko taku biyu ba ta yi ba ya damƙi hannunta, ƙara ta saki tare da faɗin. "Please Uncle leave me, me na yi maka kake bibiya ta da wannan mummunar manufar, na roƙe ka da girman Allah ka bar ni, kai fa ƙanin mahaifiyata ne, ni tamkar ɗiyar ka ta cikinka nake."


"Na bi ki ta lallami kin ƙi yarda, dama na faɗa miki idan ba ki yarda ta daɗin rai ba, za ki yarda ko ta halin ƙaƙa. Babu abun da zai hana ni cika burin raina a yau, ko dan na rama tijarar da Babanki ya mini akan na nemi wata alfarma a gurinsa."


Fashewa ta yi da kuka tare da ƙoƙarin ƙwace hannunta tana kiran sunan Abbi da Faris, saurin toshe mata baki Faisai ya yi da hannunsa ɗaya, ta ƙarfin tsiya ya ja ta suka fice ta ƙofar kitchen wadda za ta kai ka ga ƙofar bayan gidan, Abra tana ji tana gani ya fice da ita daga gidan ta ƙofar baya ba tare da an gan su ba. Wani irin kuka take yi tamkar za ta shiɗe, don ta gama saddaƙarwa Faisal ya ci galaba, zai tafi da ita ya ɓata mata rayuwa kamar yadda ya sha furtawa.
[10/1, 2:40 PM] Abk: Ihu Abra take yi, tana turjewa amma ya dinga janta, idanunsa gaba ɗaya sun rufe, ya manta da irin abunda ka iya biyo bayan ɗanyan aikin da yake ƙoƙarin aikatawa, ba abunda makauniyar zuciyarsa ke raya masa, illa cikar muradin sa akan Abra.

Har waje ya janyota, tana tirjewa tana kuka, amma ya cigaba da janta har waje, layin shiru babu kowa. Ba zato ba tsammani sai ga wani daga cikin masu gadin gidansu Abra, wanda ya kasance soja ne ya nufosu akan babur, take Faisal ya tsaya cak yana wuri-wuri da ido.

Cikin mamaki sojan, mai suna james yace "Hey Oga lafiya kuwa?".

Faisal yace "eh lafiya ƙalau".

James yace "to ya naga kana janta, kuma tana kuka, ga jikinta ba ko mayafi".

Faisal ya haɗe rai yace "Eh laifi tayi mini, zan je in hukunta ta".

Ɗan waro idanu Abra tayi, tana kallon Faisal.

James yace "koma me tayi maka, ai be kamata ka dinga janta haka ba, da Oga na gari kaima ka san ko me tayi maka, ba ka isa ka fitar da ita daga gidan nan ta ƙarfi haka ba, koma me tayi maka kayi haƙuri"

Wani irin baƙin ciki ne ya cunkushe zuciyar Faisal, na tarnaƙin da ya samu gurin cinmma mummunan burinsa akan Abra. Abra kuwa tana ganin Allah ya ƙwace ta, ta koma gida da sauri tana cigaba da kuka.

James bai kawo komai ba, saboda ganin Faisal ƙanin matar gidan ne, bai kawo wani abu na cutarwa yayi niyyar yi mata ba.

Ɗakinta ta koma ta cigaba da kuka, ta rasa wannan wace irin rayuwa ce, yanzu wa zata gayawa abunda Uncle Faisal yake yunƙurin yi mata, ai wannan ba abunda ma za ta iya faɗawa wani bane, ta yaya ma zata faɗi wannan mummunar magana haka.

Tana cikin kukan ta jiyo muryar Salman, yana ƙwala mata kira, nan da nan tai sauri ta ja bargo ta rufe idonta, dan ba ta son ya zo ya sakata gaba da tambayoyi.
Yana buɗe ƙofar ɗakin nata, ya hangota kwance ta juyawa ƙofa baya, dan haka sai yayi tunanin bacci take, dan haka ya rufe mata ƙofar ya koma ɗakinsa.


Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423  Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750








A duk wani motsi da zai yi, tunanin Abra yake yi, lokaci-lokaci ya kan tsinci kansa da ɗaukar ID card ɗin ta yana kallo.
Yanzu hakama zaune yake akan gado, hannunsa riƙe da ID card ɗin nata, ya zuba masa idanu, ya tattara dukkan wata nutsuwarsa a kallon ɗan ƙaramin hoton passport ɗin ta da yake jikin ID card ɗin.
  Wata irin ajiyar zuciya yayi, ya ɗan lumshe idanunsa tare da damƙe katin sosai a hannunsa a hankali ya furta "Abra Khamal Khams" sai kuma ya ajiye shi akan gadon, ya tashi yana tafiya a hankali, zuwa banɗakin da yake cikin ɗakin.

A department ɗinsu, sukayi parking ɗin motar, Abra ta kalli Salman tace "Faris"
"Yaya" ya amsa.
"ID card ɗina, ban ganshi ba"
"Kiyi haƙuri, za'a ganshi insha Allah, saura kije kiyi ta kuka dan bakiga ID card ba, rainaki za'ayi"
"Mhmm, to ka bani naka"
Ware ido Salman yayi yace "Namiji kika koma?"
"To kowa yana da nasa, amma ni bani da shi".
Salman yace "to waye yace ki ɓatar da naki?" Tura baki tayi tana ƙoƙarin fita daga motar.

Salman yace "ayi lectures lafiya My Angel ki kula da kanki Please,ba ruwanki da kowa kinji?"

Murmushi kawai tayi masa, ta nufi hall ɗinsu, duk da hijjabi ne a jikinta, da facemask a fuskarta ba'a rasa msu binta da kallo ba, saboda hatta tafiyarta cikin nutsuwa takeyi gwanin ban sha'awa.

GY BULAMA HOSPITAL AND MATERNITY.
GY Bulama ne ya haɗa gumi, yana yiwa wani matashi ɗinki, a ƙafarsa sakamakon faɗan daba, an ƙi karɓarsa a Asibitin gwamnati ance sai da 'yan sanda, shine suka taho Asibitin Bulama.
Gaba ɗaya Emergency room ɗin sai ƙarnin jini yake, dan har a lokacin jinin be fasa zuba ba , haka Bulama yayi ɗinkin nan, da taimakon Nurses.
Bayan ya kammala, ya cire safar hannunsa yace a kai mara lafiyan male ward, a biyo shi Office a karɓi takardar gwaje-gwaje da za'ayi masa.

Haka akayi, Nurse Jamila ta bishi Office, ya rubuta gwajin ya bayar yace a kai lap, suje su ɗibi jininsa ayi wannan gwajin akawo masa.
Bayan ya Sallami Nurse Jamila, wasu 'yan mata suka shigo su uku, suka samu guri ta zauna suka gaisa da Bulama.
Ya kallesu yace "'yan Makaranta ya school ɗin?".

Ɗaya daga cikin su tace "Lafiya ƙalau doctor, ya aiki?".

Ya amsa da "Alhamdilillah"

Tace"Yawwa doctor, kaga Wannan ƙawayena ne, to an samu matsala ne, nace bari in rakosu Asibitinka, ɗaya 4months, ɗaya 5Months".

Bulama ya ɗan kallesu yace "to ku ya akai kuka bari haka ta faru?"

Ɗayar tace "wallahi doctor tsautsayi, bamu san kan abun bane"

Yace "Well, gaskiya Yakamata ku dinga kulawa, iyayenku karatu suka turoku, irin wannan rayuwar ba in da zata kai ku, mussaman kasancewar ku mata, Aure ko karatu shine ya dace da ku, duk abunda Namiji zai yi ado ne, yanzu Gashi nan su suna can hankalin su a kwance, ku kuma kuna wahala, ai haka ba daɗi" su kayi shiru kamar gaske.

Yace "dubu ɗari ne kowacce, amma saboda wannan ƙawartaku patient ɗin gidan nan ce, ku bada 80k each of you".

"Masha Allah, mun gode sosai doctor, Allah ya saka da alheri".

Yace "Bakomai Allah ya kiyaye gaba,idan a shirye kuke, kuje ku biya kuɗin, za'ai aikin yanzu insha Allah" su kai tayi masa godiya, sannan suka bar Office ɗin.

Suna fita ɗayar tace "Beb amma doctor nan ɗan rainin hankali ne, shi ba aikin zunubin ze yi ba, amma yake mana nasiha ya fara yiwa kansa mana"

"Ke, nifa hankalina a tashe yake Wallahi, kar inje wani abun ya faru, tsoro nake ji". Cewar ɗaya daga cikin su.

Wadda ta yi musu rakiyar ta kwaɓe baki tace "kina jin tsoro, amma kin iya kwanciya da namiji, mu biya kuɗi a cire cikin, mu koma in ci uban gayen nan, dan daga nan Abuja zan wuce, dan baze tonan Asiri ba, sai ya biya kuɗin aikin nan da zan biya, tijara zamu yi masa, kuma kar ki mana wannan sakacin naki Ke Ihsan, ki buɗe baki ki tatse shi".

Wadda aka kira da Ihsan tace "Baby to ta yaya?".

Baby tace "Au tambayata ma kike? Waye be sanshi a ƙasar nan ba, babban sojane da ƙasa take ji da shi, idan ya musa biyan kuɗin, vidoen tsiraicinsa zakiyi mana, mu saka a YouTube wallahi"

Jannah ta kwashe da dariya tace "kai Baby baki da dama".

Ihsan kamar za tayi kuka tace "Baby soja ne fa, idan ya harbeni fa?".

Baby tace "Sojan me? Ina ruwan wani da aikinsa? Ya san sojan ne amma yayi iskanci, Wallahi kika ƙyaleshi, ya cuceki a banza"

Da wannan hirarrakin nasu, suka ƙarasa reception dan biyan kuɗin.

Nurse Jamila ce ta koma ofishin MD, hannunta riƙe da file, ta shigo Office ɗin, taje gaban teburin Bulama tace "doctor ga file ɗin nasa, an yi masa gwajin sakamakon yana ciki".

Ya karɓa ya duba sannan yace "Ki turomin 'yan uwan patient ɗin"
Ta amsa da to, sannan ta fita suka dawo tare da wasu maza guda biyu.

Suka sake gaisawa sannan yace "yawwa duba da yadda mara lafiyan ya rasa jini sosai, akwai buƙatar mu ƙara masa jini, kamar leda uku haka, kuma muna buƙatar jinin da gaggawa kar ya rasa ransa".

Sai da mamaki ya kama 'yan uwan nasa, ganin mara lafiyan nasu yana hayyacinsa, kuma ana ta hira da shi, amma ance wai sai an ƙara masa jini, kar ya rasa ransa, amma suka ɓoye manakin nasu, duba da aikinsa me ba nasu ba, ɗaya yace "to nawa ne jinin?"

Bulama yace "eh to, duba da yadda kuka kashe kuɗaɗe sosai, zakuje lap a duba wanda jininsa zai yi, a ɗiba a saka masa, zaku biya dubu Arba'in, idan muma ba'a samu wanda jininsa yayi ba, zaku biya dubu saba'in, jini leda uku".

Ɗayan yace "doctor babu ragi, naga baku karɓe mu bama, sai da muka ajiye dubu hamsin?".

Bulama yace "Amma da bamu karɓeku ba kamar yadda Asibitin gwamnati sukayi, ai da wani zancen ake ba wannan ba, nan fa ba Asibitin gwamnati bane".

Ɗayan yace "shikenan, bari muje mu biya".

Bayan fitarsu, cikin damuwa Nurse Jamila tace "doctor, PCV ɗinsa fa 31%, meye amfanin jinin da za'a ƙara masa?"

"Jamila ban hanaki yi mini shishshigi a aikina ba? Shekarata nawa ina aiki? Dan kinyi Nursing shekara uku shine zaki dinga min shishshigi a aikina, banda ina duba wani abu, da tuni na salamemeki, get out from my sight" yayi Maganar yana nuna mata hanyar fita.
Tabbas Jamila akwai aiki, kamar jaka sam bata da son jiki, aiki take tsakani da Allah, yana jin daɗin aikin da ita, shikuma yana kyautata mata, dan Bulama akwai kyauta, mussaman ga ma'aikatansa masu ƙwazo, idan ya bushi iska, sai yasa a dire katan-katan na taliya da makaroni a raba musu, ko haka nan tsakiyar wata ya bisu me dubu ɗaya mai ɗari biyar ya raba musu, shiyasa ya samu masu goyon bayansa a harƙallar da yake a Asibitin nasa, kuma Asirinsa yake a rufe.

Sai ƙarfe biyu sannan su Abra suka samu sukunin fitowa daga lectures, dan yin salla suci Abinci, su koma ta 2_4.
A gajiye take sosai, sam Abra ba ta son takura, ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login