Showing 177001 words to 180000 words out of 231718 words
Chapter 60 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
kyauta".
"Au Inna, in tsaya tsinto gyaɗa ya rungumeni ko? Kuma in dawo ki hau cajeni"
"A'a ni bance ba, Allah ya mayar mini da alkhairi, amma dai kin gama da ni".
"Allah sarki Baba, da yana nan da shi zai biyaki kuɗin gyaɗar nan, ki daina yi mini mita, amma yanzu ba mai biya mini sai mita ki ke yi, Allah ya jiƙan ka Baba"
Inna ta ce "Ameen, amma ai dole in yi mita, tun da asara ki ka janyo mini" Inna ta ƙarasa maganar tana ɗagowa, sai dai tuni hawaye ya wankewa 'yar Baba fuska.
"Wai ba zaki daina wannan koke koken haka ba? Kina tunanin kukan nan yana da amfani a gareki da kuma Baban ne? Ko shikenan idan kin yi laifi ba za ayi miki faɗa ba?" Cewar Yaya Musa da jikinsa ya yi san yi.
"Yaya Musa, ba ina kuka ne saboda fa₦an Inna ba, in dai wannan faɗan ne ai na saba da shi, ina kuka ne saboda rashin Baba, da kuma yadda aka yi Baba ya rasa ransa. Ka san wacece ni, kuma ka san waye Baba a wurina, na so ace ya yi tsawon rai a duniya, dan in nuna masa gata. Ina fatan Allah ya bani damar da zan yi ilimi mai zurfi, yadda wani talaka kamar Baba, ba zai ƙara rasa ransa ba, saboda shi talaka ne ba. Wallahi ba zan taɓa yafewa waɗanda suka yi sakaci a kan rayuwarsa ba, na san lokacinsa ne ya yi, amma ya mutu a wulaƙance ba kulawa, Allah ya tsinewa wa......
"A'a A'a, kar ki kuskura in ji irin wannan mummunan furicin a bakin ki, ai ko baki faɗa ba, Allah ishashe ne, kuma ya ga abin da ya faru, shi baban na ki tunda ki ke da shi, kin taɓa jin ya tsinewa wani? To kar in kuma ji, maza je ki yi alwala ki ɗau carbi, ki ta masa addu'a".
Abin duniya ya bi ya addabi zuciyar Bulama, ko wurin aiki ba ya iya zauwa, sai dai ya wuni a gida, kusan kullum cikin zarya yake tsakanin Asibitin da aka ce Adnan ya kwanta da kuma gidansa. Maƙwabcin Adnan ne ya nunawa Bulama gidan Adnan, da ya gaji da zaryar da yake masa, gidan Adnan ɗin ma idan yaje, sai mai gadi ya ce masa baya nan.
Babban abin da ya ƙara ɗagawa Bulama hankali, bai wuce yadda aka ce masa yarinyar nan ta mutu ba, saboda zuciyarsa ta azalzalu da son ya ganta, ya gano ya aka yi ta zama 'yar sa, sai dai har duniya ta gushe, ba zai fasa ɗorawa kansa da Asibitinsa laifin da sa hannunsu a kisan Abra ba.
"Yanzu kenan na bada gudunmawa wurin kashe 'yar da na haifa, idan ta tabatta 'ya ta ce?" Ya yi wa kansa wannan tambayar.
Wasu hawaye ne da bai shirya zubarsu ba, suka gangaro a kan kuncinsa, bai taɓa aikata abin da ya zo ya dame shi ba, ya hana shi sukuni ba irin wannan. Shiryawa ya yi ya kuma ɗaukar mota, ya tafi gidan Adnan.
Ya na zuwa ya tarar da maigadi suka gaisa, mai gadin ya ce "Wallahi ranka ya daɗe, yau ma baya nan, yama yi balaguro fa".
Bulama ya ce "Bulaguro zuwa ina kenan?".
"Wani aiki aka tura shi ƙauye, ka san jami'in tsaro ne".
"Amm, ko zaka iya gaya mini cikakken sunansa?".
"Wallahi ban sani ba, kawai dai Adnan na sani, amma ban san cikakken sunansa ba, da yake ban daɗe da fara yi masa gadi ba. Tun da dai matar nan ta sa ta rasu, gaba ɗaya ya zama sai a hankali".
Bulama ya yi ajiyar zuciya, ya ce "Wane ƙauye aka tura shi aiki?"
"Yo ni ina zan sani?".
"Dan Allah idan ba damuwa, ka bani lambar wayarsa".
Mai gadi ya ce "Babu damuwa, bari in baka" ya bawa Bulama lambar Adnan, ya yi masa sallama ya tafi.
Ko da Adnan ya ƙarasa gidan maigari, aka yi masa iso, ya shiga suka gaisa, ya ce musu "Ni baƙo ne daga cikin garin Kano, ga takarda da aka bani na taho da ita zan yi wasu 'yan kwanaki a nan, kan in wuce".
Mai gari ya nuna farin cikinsa da jin batun Adnan, suka karɓe shi hannu bibbiyu aka ba shi masauki, a wani gida, wanda galibi a nan suke saukar baƙin su, sai dai hankalin Adnan, sam ba ya kan aikin da aka turo shi, yana kan a ina zai sake ganin yarinyar nan? Ko kuma dai kamar yadda yayi tsammani, tsabar sanya Abra a ransa ne ya sanya ya ke ganin fuskarta na yi masa gizo a fuskar mutane?.
Yayi alwala ya yi sallolin da suke kansa, bai nemi Abinci ba ya zauna ya cigaba da aikin na sa na tunani.
Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba wayar amma ya ga baƙuwar lamba, kawai sai ya share, ya cigaba da tunaninsa.
Jin an cigaba da kiran ba ƙaƙƙautawa ne ya sanya, ya ɗau wayar zai sanya a silent, amma ya fasa ya ɗaga ya kai kunnensa tare da yin sallama.
"Wa'alaikum salam, barka da yamma".
"Yauwa wake magana?" Adnan ya faɗa cike da ƙosawa.
"Doctor G.Y Bulama ne"
Wani uban tsaki Adnan ya ja, "Me zan yi maka? Me ka kirani ka gaya mini?".
Bulama ya kwantar da muryarsa ya ce "Dan Allah ka yi ka haƙuri ka tsaya mu fahimci juna".
"Babu wata fahimta tsakani na da kai, ka jiraye ni zuwa lokacin da zan kai ka kotu, a kan kisan mata ta".
"Kana da right ɗin da zaka yi haka, amma dan Allah ina son ka mini bayani yadda zan fahimta, ya aka yi yarinyar nan ta zama 'ya ta?".
"Au mamaki ma ka ke yi? Bayan har gidanka na kai maka envelope da hotunan ta a ciki da wasiƙa watannin baya? Meyasa tun a lokacin ba ka yi ƙoƙarin neman 'yar ta ka ba, sai yanzu da ka kasheta?".
"Adnan ka daina faɗan haka, ban kasheta ba, amma dan Allah ina son mu haɗu".
"Mu haɗu ka yi mini me? Da fari ka kashe mahaifiyata shekaru Ashirin da uku da suka gabata, cike da zalunci ka sayar da jinin da za a sa mata, ka yi mata gurɓatacciyar allura, wadda ta yi ajalinta, katsam Allah ya haɗani da 'yar ka wadda ita kanta ba ta sanka ba, da yake Allah ba Azzalimin sarki ba ne, sai gashi irin halin da ka ke wa mutane na wasa da rayuwarsu, ka yiwa 'yar ka har ta rasa ranta. Haƙƙin rayukan mutane ba zai barka ba, kuma daga kan matata ba zaka ƙara wasa da lafiyar wani ba" Bulama zai yi magana, Adnan ya katse wayar, ya cillar da ita gefe, ya dafe kansa yana wani irin huci tare da haɗa gumi.
Bulama ma ajiye wayar ya yi, ya dafe kansa yana tunanin, wace envelope aka kai masa? Shi ba wanda ya kai masa wata envelope.
Ta da motarsa ya yi, ya ja ta a guje, ya nufi gida, yana parking ya fito, ya nufi wurin maigadi a sukwane.
Ganin da mai gadi yayi Bulama ya nufo shi, ya sanya ya taso da sauri ya taho, tare da risinawa a gaban Bulama.
Bulama ya kalleshi ya ce "Kwanakin baya, ko ma in ce watannin baya, an kawo wata envelope an ce a ajiye mini?".
Mai gadi ya yi shiru, can ya ce "Tabbas Yallaɓai an yi haka, an kawo saƙo an ce a ajiye maka watannin baya".
"Ina takaddar?".
"Yallaɓai ban duba ba, ban san ko takadda ce a ciki ba, na kaiwa Hajiya ta karɓa ta ce zata ajiye maka".
Jinjina kai ya yi ya tafi da sauri, Hajiya Saudat na ɗakinta, tana kwalliya a gaban mudubi, Bulama ya faɗa ɗakin ba bu ko sallama.
"Doctor lafiya kuwa?".
"Watannin baya an kawo saƙo a envelope, an bawa maigadi, shi kuma ya ce mini ya baki ki ajiye mini, ina saƙon?".
"Wane saƙo kuma? Ni ba wani saƙo da ya bani".
"Kar ki mini wasa da hankali, envelope aka kawo mini, da takadda a ciki da hotuna suna ina?".
Gabanta ya yi mummunar faɗuwa, amma ta dake ta ce "Ni babu wata envelope da aka kawo mini, ka dai tambaye shi wanda ya bawa".
"Shut up Saudat, Mutumin nan ba zai miki ƙarya ba, ki bani saƙon nan".
"An ya ba ciwon damuwa ne ya kama ka ba, ya ke neman ya taɓa maka ƙwaƙwalwa ba?".
"Ni ki ke gayawa ƙwaƙwalwata ta taɓu? Kin kyauta amma na fara tunanin wani abu, akwai abin da nake tunani, idan har ya tabbata zaki ga abin da ba ki tsammani ba".
Ya juya fuuuu, ya tarar da Meenal a ƙofa a tsaye, jin hayaniya ya sanya ta fito, bai ko kalleta ba ya wuce yana huci.
Meenal ta ƙarasa shiga ɗakin ta kalli Mummy ta ce "Mummy me ke faruwa ne? Wace takadda da hotuna Daddy ya ke magana a kai?".
"Ke kar ki dameni dan Allah, koma ɗakinki"
Ƙurawa Mummy Ido ta yi, ta ga gaba ɗaya gumi ya rufeta, alamun tsoro da rashin gaskiya suka bayyana ƙarara a fuskarta.
"Mummy dan Allah ki gaya mini".
"Get out from my sight, ki koma ɗakin ki na ce" ba shiri Meenal ta bar wurin, tana tunanin meke faruwa haka?
Sintiri Hajiya Sauda ta shiga yi a ɗakin, tana jinjina kai tamkar ƙadangaruwa. "Kafin ka binciko komai, zan sake bunneka doctor, ba bu abin da zaka iya ganowa!' ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya.
Hajiya Mama ta kira Adnan a waya, ta ji ko ya sauka lafiya, suka taɓa hira, har ta tura masa hotunan Aishatul Humaira ta waya, kamar yadda Mami kan tura mata.
Adnan ya ƙura mata izanu, ji yayi zuciyarsa na son ganin Aishatul Humaira, rabon da ya ganta tun tana kwalba, tun da aka tafi da ita bai sake zuwa ya ganta ba, wata irin soyayyar yarinyar ta mamaye zuciyarsa, musamman yadda kammaninta suka juue zuwa na Abra sak, wanda kyakykyawan hanci Bulama irinsa ne ɗoɗar a fuskar Aishatul Humaira.
Nan ya barwa zuciyarsa cewar zai je Kano ya ga Little Abra.
Kwanansa biyu a garin, ya je ofishin 'yan sanda na yankin, ya ga DPO, domin fara gabatar da aikin da ya kawo shi, daga nan kuma ya tafi Kano.
Ba ƙaramin mamaki Mami ta yi ba da ganin Adnan, sam bai sanar da zuwansa ba, ita abin har mamaki yake bata, yadda ko ta waya baya neman ya 'yar ta sa take ciki, sai dai ta yi masa uzuri, kasancewar tun da Abra ta rasu, yake kwance ba lafiya, dan a yanzu ma ya rame da yawa, ya ƙara duhu sai idanu.
Mami ta yi masa kyakywar tarba, tare da yi masa ya jiki.
"Jiki da sauƙi Mami, ya Mamana?".
Mami ta ce "Ai na ɗauka ka bar mini ita gaba ɗaya ne, baka sonta?"
Adnan ya sunkuyar da kai ya ce "Mami ya za ayi in ce bana sonta, ina gujewa abin da zai sa in dinga tuna Abra ne kawai, yanzu haka ina cikin wani ƙauye a katsina, na tafi aiki, Mama ce ta turo mini hoton ta,naji lallai ina son in zo in ganta".
Mami ta ce "Allah sarki, ai sai haƙuri mu cigaba da yi mata addu'a,bari in ɗauko maka ita".
Ta shiga ɗaki ta ɗauko masa Little Abra, wadda ta ke ta bacci, ya ƙura mata idanu kamar zai cinyeta, tayi girma yanzu kamar ba wadda aka ciro a kwalba ba.
Ya ɗagata yana cigaba da kallonta, amma sai lanƙwashe wuyanta ta ke tana tura baki, alamar bacci bai isheta ba.
"Like Mother like daughter" ya furta yana tuna Abra, tuni idanunsa suka cika da hawaye.
Mami ta ce "Ayi haƙuri dai, Ai mata Addu'a".
Adnan ya jinjina kai sannan ya ce "Abbi ba ya gari ne?".
Mami ta ɗan kwaɓe baki ta ce "Eh".
"To, ga siyayya can na mata, kuma ina ganin tun da ta ƙara girma, ai mata hakika".
Mami ta ce "Tun yaushe aka yi mata hakika, ai kana wannan rashin lafiyar aka mata komai, taron suna ne da bai yiwu ba, tunda ga abin da Allah ya saukar"
Adnan ya ce "Haka ne, Allah Ya rayata ya jiƙan mamanta".
Mami ta amsa da Ameen.
Adnan ya kwaso uban kayan da ya sayowa Aishatul Humaira.
Mami ta ce "Da ka yi shawara da ni ba zaka sayo wannan kayan ba, ta na da kaya da duk wani abun buƙata, da ga can ɓangaren ku sun kawo, nan ma duk an mata komai, madara kawai tana da gwangwani kusan Ashirin, diapers da komai duk akwai".
"Lallai wannan 'ya 'yar gata ce, bakoma Mami ai alhakina ne nima na yi mata".
Sai bayan azahar sannan Adnan ya yi haramar tafiya, kamar kar ya tafi, ji yake kamar ya ce a bashi 'yar sa ya tafi da ita.
Ba yadda ya iya haka ya yi sallama, ya tafi, sai dai ko da ya wuce ta ƙofar sitting room ɗin da yake zama su yi hira da Abra, sai da gabansa ya faɗi, ya tuna yadda ta dinga nuna masa soyayya a wannan lokacin.
Jiki a sanyaye haka ya baro gidan su Abra.
Bai isa katsina ba sai dare, tun a hanya ya sai 'yan kayan da zai buƙata, da abin da zai ci ya kwana a wani Hotel, dan ba zai iya shiga wannan ƙauyen da daddare ba.
Sai washegari da safe, sannan ya fara shirin tafiya ƙauyen.
Har ya gama shiri, ya ga dacewar yakira Abba, ko ba zai amsa ba ya gaishe shi.
Sai dai yadda Abban ya amsa gaisuwar ne, za ka tabattar da haryanzu Abba yana fushi da Adnan.
A sanyaye ya shiga motarsa, ya cigaba da tafiya.
Yaran garin kamar ba su taɓa ganin mota ba, da zarar Adnan ya yi parking ɗin mota, suke zuwa su kewaye motar suna kallo, saboda haka mai gari ya sa aka samo wuri na musamman da yake ajiye motar, gudun kar yaran su mata illa.
Da yake har yanzu gajiya na damun Adnan, dan haka a ɗaki ya wuni, salla ce kawai take fito da shi.
Bayan la'asar ya ga dacewar ya zazzaga garin, ya jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, ya ga ta ina zai fara bincikensa, kuma ko Allah zai sa ya sake ganin Abra.
Sannu a hankali ya nausa cikin ƙauyen yana zagawa, sai ya ga wurin ya burgeshi, dan haka ya cigaba da kutsawa yana zagaye, har ya bar in da mutane suke.
Tafiya ya yi sosai mai nisa, wurin ba kowa sai bishiyu da kukan tsuntsaye, ga manyan bishiyun fruit kala kala a wurin.
Can ya hango wani tafki, ruwan ciki garai da shi, dan haka ya nufi wurin yana son ganin girman ruwan, sai ya tuna zamansu a Dubai, yadda Abra ke son ruwa, kuma tana tsoronsa.
Kamar Aljana, haka zalika kamar a yadda ya ganta wancan lokacin, ta juya bayanta, ta zuba su a cikin ruwan, tana ta kaɗa ƙafafuwan ta a ciki.
Da wata irin gaggawa, ya nufi in da take zaune.
Jikinta ya bata a na tsaye a bayanta, ga kuma ƙamshin turaren da ba zata ta;a mantawa da shi ba ya daki hancinta.
Ba tare da ta waigo ba, ta tashi da sauri, aikuwa gabanta ya faɗi da ta ga Adnan a tsaye kamar gini.
Juyawa ta yi zata taka da gudu, dan ba ta gama yadda mutum ba ne, wannan mutum haka mai siffar shago.
Yana gano nufinta ya danƙota, ya ja ta gefe, jikinta ne ya hau rawa "Ka ga dan Allah ka cika ni".
"Abra, wai har yanzu ba ki gane ni ba? Na san loosing memory ki ka yi".
"Allah ya sawwaƙe, kana nufin na haukace fa kenan, to Wallahi ni ba mahaukaciya ba ce".
"Abra dan Allah ki saurareni"
"Kai karka sake kirana da wannan sunan, wani suna kamar babur, kamar burabusko, ni ba sunana kenana ba, dan Allah ka cikani kar Inna ta gane Namiji yataɓa ni"
"To ai ni mijinki ne Abra"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ko dai aljani ne ya aure ni ban sani ba?"
Ƙara matso da ita jikinsa ya yi, yana ƙare mata kallo, duk da yamma ta ti sosai, Abransa ta fi wannan fari da ja, amma wannan ma fara ce tas, dan ba ta samu hutu bane, Abransa muryarta a hankali take yin ta, wannan kuwa muryar ta a tsaye take, cike da tsiwa da rashin kunya. Abra ta fi shagwaɓa a kan duk al'amuranta, wannan a tsaye take da ƙwarinta.
Mutsu mutsun ƙwacewa take yi, tana ta kurma ihu.
Adnan ya ce "Zan cika ki, amma muje in ga gidanku, zan magana da ke"
Ta ce "To, na yadda".
Adnan na cikata, kamar ya saki tattabara, ta watsa da gudu, ta nemi hanyar barin wurin.
Littafin kuɗi ne, don biya ku tuntuɓe mu ta wannan lambar. 09047871750
[11/9, 11:32 AM] Abk: Ƙoƙarin kamo ta ya yi, amma yadda take gudu kamar mai fukafukai ya sa cikin sakanni ta ɓace wa ganin shi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da shafa sumar kansa, lallai wannan aikin da ya zo yi ba ƙaramin Alkhairi ya zamo a gare shi ba, bai taɓa tunanin zai ƙara yin farinciki a rayuwarsa ba, amma ganin wannan halittar mai kama da Abra da acting ɗinta ya fara saka shi cikin nishaɗi. Ya yarda Abransa ta tafi ta bar shi wannan ba ita ba ce, amma tsananin kamar da suke yi idan ba wanda ya yi wa Abra mugun sani ba idan ya ga wannan zai ce ita ce. Saboda yadda komai nasu yake iri ɗaya, ido, dogon hanci da dogon baƙin gashi, cikakkiyar gira da ɗan ƙaramin bakinsu gami da jerarrun fararen haƙora, hatta hannu da ƙafarsu duk iri ɗaya ne. Banbancin su kawai Abra ta taso a birni gidan hutu, ita kuma wannan yar ƙauye ce. Murmushi ya kuma yi a karo na biyu ya juya ya tafi don aiwatar da abin da ya kawo shi, zuciyarsa cike da addu'ar Allah ya sa ya kuma ganin ta a yau.
"Wai don Allah ƴar Baba yaushe za ki yi hankali ne ki san kin girma? Sau nawa nake ce miki ki daina faɗo mana gida da gudu kamar wani filin ƙwallo"
Zama ta yi tana haki tare da turo baki gaba ta ce. "Wai Inna ba ki san me ya faru ba za ki fara yi mini faɗa, ba ke ba ce kullum kike cewa kar in bari Namiji ya taɓa ni ba?"
Inna ta ce. "Eh ni ce."
"To wannan mutumin da na ce miki ya biyo ni jiya yau ma shi na ƙara gani a bakin teku, ya riƙe ni yana kira na da wani suna kamar babur, wai don Allah in daina gudun shi."
Ido a waje Inna ta ce. "Wane shi? Me yake nema