Showing 159001 words to 162000 words out of 231718 words

Chapter 54 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14698

ta kanta ba ya yaye labulen ɗakin zai shiga. Saurin shan gabansa Nurse ɗin ta yi tare da faɗin. "Malam ya haka? Daga ina? Who are you?" Mugun kallon da ya watsa mata ya sa ta yin baya ba shiri ta ba shi hanya ya wuce, zuciyarta cike da matsanancin tsoro, don ba ƙaramin firgita ta yi ba da jajayen idon Adnan.

"Abra! Abra! Abra!"


Shi ne abin da Adnan ya faɗa cikin matsanancin tashin hankali, lokacin da ya yi tozali da ita kwance cikin jini babu alamar numfashi a tattare da ita. A ɗimauce ya cicciɓe ta ya yi waje da ita, har ya yi gaba ya juyo ya dubi Nurse ɗin da jikinta ke ɓari ya ce. "Wallahi wallahi idan har na rasa matata sai na yi da Shari'a da ko ma wanne shege ne ya yi sanadin mutuwar ta." Da kallo kawai Nurse ɗin ta bi shi, cikin zuciyarta tana sakin ajiyar zuciya.


Ganin yanda Adnan ya dauko Abra jini na zuba a jikinta ya sa su Maman Rahama bin bayansa hankali a tashe, suna ƙoƙarin fita daga reception Doctor Bulama ya sakko daga sama. Wani irin kallo ya bi bayansu da shi, kafin ya taɓe baki ya dubi wata Nurse cikin yamutsa fuska ya ce. "Murja ku saka a gyara gurin nan yanzu-yanzu, ko wanne mara hankalin ne ya ɗauki patient jini na zuba daga jikinta ya ɓata mana wuri oho? Sometimes wasu mutanen they behave like animals." Ya ƙarashe maganar tare da jan tsaki.


"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! Waye yake zubar da wannan jinin haka?" Nurse Jamila da ta fito daga wani ɗaki ta faɗi haka cikin bin wajen da kallo."


"To uwar kwakwazo, sai ki bi su ki tambaya." Bulama ya faɗi haka tare da yin gaba.


Cikin damuwa Jamila ta ce. "Hasbunallu'wa'ni'imal'wakil, ba dai fita aka yi da wanda ya zubar da jinin a haka ba, ba tare da an yi masa wani taimako ba? Idan jinin nasa ya ƙare kuma fa kafin su je wani asibitin? Wannan wacce irin rayuwa ce? Ba na raba ɗayan biyu kuma don ba su biya kuɗi ba ne."


"To za a yi musu abu kyauta ne, ke fa wani lokacin kina da matsala."

"Haba sister Murja, amma ko taimakon tsayar da jinin aka ba su ai an yi wani abu, don ba ɗan'uwanki ba ne ko ke ce shi ya sa."

Taɓe baki Murja ta yi ta ce. "Sai ki faɗa wa mai asibitin ai." Daga haka ta yi gaba ta bar ta a gurin. Girgiza kai Jamila ta yi tare da barin gurin ita ma, zuciyarta babu daɗi.



Wani Babban Private Hospital Adnan ya kai Abra, wanda anan take awo. Suna zuwa aka karɓe ta cikin sauri aka yi emergency ward da ita. Bin bayansu Adnan ya yi, amma wani babban likita ya hana shi shiga ɗakin da aka kai ta. Ba don ya so ba ya tsaya a bakin ƙofar ɗakin, amma yanda yake jin zuciyarsa tamkar ya kutsa kai ya shiga.

"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Allah ka tashi ƙafaɗun matata, Allah ka ba ta lafiya, Allah na roƙe ka kar ka ɗauki ranta a yanzu, Allah ka ba ta lafiya ta koma gidana da ƙafafunta in nuna mata tsantsar soyayyar da nake mata, in nemi yafiyarta a kan muzgunawar da na yi mata, Allah na tuba Allah." A fili yake maganar cikin tsantsar damuwa da nadama, wasu hawaye masu ɗumi na zuba daga idonsa. Shi kaɗai ya san abin da yake ji a cikin ransa na halin ganin halin da Abra take ciki.


"Sai haƙuri Sp, mu za mu koma gida Allah ya tashi ƙafaɗunta ya ba ta lafiya."

Ko kallon Alhaji Nura Adnan bai yi ba, saboda gani yake duk abin da ya faru shi ya ja, sanadiyyar kai Abra matsiyacin asibitin Bulama. Jiki a sanyaye Alhaji Nura ya juya suka tafi.


Duk yadda mutum yake tunanin tashin hankali Adnan yana cikin wanda ya fi shi, bai taɓa tunanin abun zai kasance masa haka ba, kuka sosai yake yi tare da surutai tamkar wani zautacce, duk wanda ya zo wucewa sai ya kalle shi, don ba shi da maraba da mahaukaci, ga jini duk ya ɓata masa kaya amma ko ajikinsa. Likitoci kusan biyar ne suka rufu a kan Abra, sun yi nasarar tsayar da jinin da take zubarwa tare da saka mata oxegen don taimaka mata gurin yin numfashi, bayan sun yi mata allurar bacci suka fito suna share zufa. A haukace Adnan ya yi kansu yana faɗin. "Doctor ya jikin nata? Ta farfaɗo? Tana numfashi? Ba ta mutu ba?" Numfashi likitan da ya kasance babba a cikinsu ya ja ya ce. "Mu je office na maka bayani."

"Office ɗin me? Ka faɗa mini halin da matata take ciki a nan, ba zan iya ɗaga ƙafata ba, ba tare da na san a halin da take ciki ba." Ya yi maganar cikin tsawa.

"Ranka ya daɗe ka yi haƙuri dai mu je, and ka kwantar da hankalinka mun yi nasarar tsayar da jinin da take zubarwa."

Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi tare da faɗin. "Is she alive?"

"Yes."

"Alhamdulillah." Adnan ya faɗa tare da tsugunnawa cikin sauri ya yi sujjada ga Ubangiji. Girgiza kai likitan ya yi cikin tausayawa sannan ya yi gaba, maimakon Adnan ya bi bayansa sai ya shige ɗakin da Abra take. Sai da doctor ya shiga office ɗinsa sannan ya farga Adnan bai biyo shi ba, ko tantanma ba ya yi gurin Abra ya tafi. Yana da numbern Abban Adnan saboda asibitin suke zuwa kuma already ya san shi, hakan ya sa ya ɗakko wayarsa ya kira shi ya sanar masa halin da ake ciki, domin su zo ya yi musu bayanin abin da yake damun Abra, don yanayin halin firgicin da Adnan yake cikin bai zama lallai ma ya fuskanci abin da yake nufi ba, sai dai ya ƙara hargitsewa.




Cikin rawar jiki da bugawar zuciya Adnan ya ƙarasa gaban gadon da Abra take kwance ya tsugunna tare da kamo hannunta mara drip ya riƙe gam tare da fashewa da kuka. Cikin tsantsar nadama da ƙaunar ta ya ce. "Na yi kuskuren ɗaukar fansar abin da mahaifinki ya yi mini a kanki, don't leave me please, kar ki mutu ki bar ni Abra, wallahi ke ce rayuwata, duk abubuwan da na miki na yi ne cikin fushi gami da radad'in abin da mahaifinki ya mini, but I love You since the first day I saw you. Ina son ki Abra, don Allah kar ki tafi ki bar ni, Please my love, my life, my everything, na yi nadamar duk abubuwan da na yi miki dan Allah Abra ki tashi ki kalleni, i regret what ever I deed to you, ba zan iya jure ganinki a wannan yanayin ba, dan Allah ki tashi." Ya ƙarashe maganar tare da manna hannunta a ƙirjinsa ya ɗora kansa a kai yana zubar da hawaye.



Tare Abba suka zo da Hajiya Mama, direct office ɗin likitan da ya kira su suka je. Bayan sun gaisa ya dube su tare da gyara glass ɗin fuskarsa ya ce. "Adnan ya kawo mana matarsa cikin wani irin mawuyacin hali, ba don Ubangiji ya yi da sauran kwananta a gaba ba da tuni ta riga mu gidan gaskiya." A rud'e Hajiya Mama ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, me ya same ta har haka Doctor?"


"Mun yi mata scanning mun gano wani ruwa ne ya kwanta a cikinta, wanda ake buƙatar a yi mata aiki cikin gaggawa a fito da abin da ke cikinta gudun kar a rasa ta ita da shi, sannan kuma bincikenmu ya nuna mana sun kai ta wani asibitin kafin su zo nan, an yi mata wata allura ba bisa ƙa'ida ba, wadda ta haifar mata da bleeding. Mun ɗibi jikinta don yi mata teses, a nan muka gano tana ɗauke da Blood Cancer stage two."


"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, doctor cancer fa ka ce?" Abba ya tambaya a rud'e. Hajiya Mama kuwa tsabar firgici kasa magana ta yi.


"Eh Alhaji, yanzu dai muna buƙatar jinin da za a ƙara mata cikin gaggawa, don ta zubar da jini sosai. Kuma jinita ya hau fiye da kima, akwai yiwuwar tayi jijjiga, kuma still akwai hatsari mu shiga da ita aiki, shi ya sa zamu bari zuwa safiya"


Cikin hawaye Hajiya Mama ta ce. "Allah ka ba wa wannan yarinyar lafiya, Allah ka taƙaita mata, yanzu tana ina Doctor? Ina shi Adnan ɗin yake ya zo a gwada jininsa ko zai ya yi daidai da nata a ɗiba a ƙara mata."


"Tana emergency ward room 3, v.i.p part."

Godiya Abba ya yi wa likitan sannan suka miƙe suka fita, zuciyoyinsu cike da damuwa gami da zullumi. Turus Hajiya Mama ta tsaya tana kallon ikon Allah, Tsabar mamaki kasa magana ta yi. Duban Abba ta yi suka haɗa ido wanda shi ma ke cike da mamakin ganin hawayen Adnan, abin da suka manta rabon da su gani.

"Haba Adnan, ya za ka tasa ta a gaba ka dinga kuka kamar wani ƙaramin yaro, ai addu'a ita ce mafita ba kuka ba." Hajiya Mama ta faɗa cikin tausasa harshe.

A zabure ya juyo tare da sakin hannun Abra, lokaci ɗaya ya miƙe yana jan hanci ya ce. "Mama don Allah ki ce kar ta tafi ta bar ni, wallahi na yi nadama, ba zan ƙara cutar ta ita ba, da na sani ban yi tafiya na bar ta ita kaɗai a gida ba, na san ƙila da haka ba ta faru ba, da ba a kaita Asibitin waɗancan marasa imanin ba." Cikin mamaki Hajiya Mama ta ce. "Ban gane me kake faɗa ba Adnan, ƙara tafiya ka yi ka bar yarinya ita kaɗai a gida? Kai ba ka da hankali ne? Ba ka ganin yanayin da take ciki? Ai idan mace ta kai wannan lokacin ba a tafiya a bar ta ita ɗaya a gida. Kuma don iskanci maimakon ka kawo ta gida idan ba za ka iya tafiya da ta ba ko ka ce a zo a zauna da ita sai ka tafi ka ba bar ta?"


"I'm sorry Mama, wallahi ƙaddara ce, don Allah ku taimake ni kar na rasa matata, wallahi ina son ta, ita ce rayuwata, na yi nadamar duk muzgunawar da dinga mata, akan lefin da ba ta ji ba, ba ta gani ba." Abba dai bai ce komai ba sai bin Adnan kawai yake da ido cikin nazartar shi, zuciyarsa take da takaicin shi. Juyawa Adnan ya yi ya riƙe Abra tare da jijjiga ta yana faɗin ta yafe masa cikin kuka da faɗar duk abubuwan da yake aikata mata na mugunta. Da ƙyar Hajiya Mama wadda ita ma ke kukan tausayin Abra ta janye shi. Gabaɗaya Adnan ya fita daga cikin hayyacinsa, surutu kawai yake yi cikin gigita kamar zararre.




Abbi ne zaune a saman carpet yana operating system, lokaci ɗaya ya ture system ɗin tare da dafe kansa. Nai'ma dake gefensa ta kalle shi cikin kulawa ta ce. "Wai me yake damun ka ne man? Yanayinka kamar wanda yake cikin damuwa, ka sa na hado maka coffee kuma na kawo maka ba ka sha ba, abinci ma yau ka ƙi cin na kirki " Numfashi ya sauke ya ce. "Ba na jin daɗin jikina ne, gabana kuma sai faɗuwa yake yi, kamar wani mugun abun zai same ni." Cikin marairaicewa ta ce "Hasbunallahu, insha Allahu babu komai sai Alkhairi, ka daure ka sha coffee din, bari na hado maka wani." Kai kawai ya gyaɗa mata. Bayan ta dawo ya ce ta dauko masa wayarsa, Abra ya kira amma wayar ta ƙi tafiya. Cike da damuwa ya ce. "A cikin week din nan dole na je na gano daughter, kwana biyu ita take ta faɗo mini a rai." Na'ima ta ce "Allah ya kai mu, ni ma ina yawan tuna ta, kodan ta kusa haihuwa ne, Allah ya dai ya sauke ta lafiya."


"Amin."



Maman Rahama ce tsaye a kan dinning tana zuzzuba abinci, bayan ta gama ta zauna tare da rafka tagumi. Duban tsanaki Baban Rahama ya yi mata ya ce. "Ki ci abincin mana, tun ɗazu kin tasa shi a gaba, ko da akwai wata matsalar ne?" Tagumin ta sauke tare da faɗin. "Babu komai Abbansu, tunanin yarinyar nan da halin da take ciki ne kawai ya cika mini zuciya, ga shi mu ba numbern mijin nata ba bare mu kira mu ji ya jikin nata." Cikin damuwa Baban Rahama ya ce. "Ni ma yadda na ga jikin yarinyar nan ya tsaya mini a rai, abin tausayi wallahi."


"Hmm, ai daga ganin mijin nan nata ba shi da kirki, ban da haka ya za ai ka yi tafiya ka bar yarinya mai tsohon ciki ita kaɗai a gida? Kuma ga dukkan alamu ta daɗe tana cutar, ba wai yau ta same ta ba. Ya zo ya ga kuma za ta mutu duk ya burcike, ni duk abubuwan da ya dinga yi ko kaɗan bai ba ni tausayi ba sai ma haushi, da ka ce mu bi shi lokacin da ya ɗauke ta kamar na ce ba za ni ba sai kuma na yi shiru muka bi shin, don dai kawai ina son sanin halin da yarinyar za ta kasance a ciki ne."


"Sai haƙuri, kin san kowa da irinsa."

"Amma dai wannan mutumin ba shi da kirki gaskiya, kana gani fa ko godiya bai yi mana ba sai masifa, a lokacin da ya zo so nake na yi masa bayanin halin da ake ciki, amma ganin yanayinsa na san ma ba saurara ta zai yi ba."

"Allah ya dai ya ba ta lafiya kawai."

"Amin ya Allah."


An yi sa'a jinin Adnan ya zo daidai da na Abra, don haka aka ɗiba aka ƙara mata. An yi an yi da Adnan ya kwanta ya huta saboda ɗiban jinin da aka masa amma ya ƙi, duk da kuwa yana jiri na ɗiban shi. Da ƙyar Hajiya Mama ta lallaɓa shi direbansu ya kai shi gida ya sauya kayan jikinsa ya yi sallolin dake kansa. Abba kuwa ya ƙi kula shi, don zuciyarsa cike take da haushin shi akan abubuwan da ya ce ya yi wa Abra, ko kaɗan bai yi tunanin Adnan zai aikata irin wannan rashin imanin ba. Ba a yi wa Abra c.s ba a wannan daren, likitocin sun ce sai gobe ƙarfe bakwai na safe. A daren Abba ya saka Hajiya Mama ta kira su Abbi ta sanar musu halin da ake ciki, hankali a tashe Abbi ya ce za su yi asubanci su zo gobe. A asibitin Adnan ya kwana, duk yadda Hajiya Mama ta so ya koma gida amma ya ƙi, sai haƙura ta yi suka kwana tare. Yadda Adnan ya ga rana haka ya ga dare, a bakin gadon Abra ya zauna ya ƙura mata ido har garin Allah ya waye.


An yi wa Abra c.s lafiya an fito da baby girl mai kyau, kamarta ɗaya sak da mahaifinta, sai dai ta ɗebo farin mamanta. Kasancewar watanninta 7 da satittika sai aka saka ta a kwalba. Ko kallon yarinyar Adnan bai yi ba, saboda ta uwarta yake ba ta ita ba, wadda har ƙarfe takwas na safe ba ta farfaɗo ba daga allurar baccin da aka mata. A lokacin ne kuma Abbi da Mami suka ƙaraso asibitin.





It's paid book, contact us for more information. 09047871750[11/1, 1:10 PM] Abk: "Ya akai Abra ta samu blood cancer?" Abbi ya tambaya cike da damuwa da kuma tashin hankalin daya kasa ɓoyewa daga saman fuskarsa. Girgiza kai Abba yai Shima cike da damuwa makamanciyyar wacce Abbi yake ji. A hankali ya ce "It is what we do not know yet,she is in a difficult situation" dafe kai Abbi ya yi yana faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Ubangiji ka dubemu ka bawa daughter lafiya, kada ka ɗauki ranta ba tare data san wacece ita ba" ya faɗa cikin raunin murya mai nuna zallar damuwar da yake ciki. Ubangiji ya sani yadda yake jin Abra a ransa ko Salman baya ji haka, ita ɗin amanace a garesa,kusan marainiyya take,since he still could not find her real parents.

"Insha Allah zata samu lafiya, mu ci-gaba dayi mata addu'a. Kayi haƙuri komai zai shige ta zama kamar kowa" Abba ya ƙare maganar yana kallon cikin ƙwayar idanun Abbi. Abbi kasa cewa komai yai domin bai fahimci mgnar da Abban Adnan yake ba, tunaninsa ya tafi can wani waje.. A hankali suka ƙarasa Vip part ɗin da aka kwantar da Abra, a nan bakin ƙofa suka samu Hajiya Mama da Uncle ɗin Adnan.

Da sauri Mami ta ce.
"Hajiya ya jikin nata? ta tashi wanne hali ƴata take ciki ne don Allah?" "Ki kwantar da hankalinki Hajiya Na'ima, Addu'a kawai za mu yiwa Abra,tare da babynta" Ajjiyar zuciya Mami ta sauke a wahale, Allah yana gani har ranta ta damu da halin da Abra take ciki, tsoro da ladamar abin da ta dinga aikata mata ya wanzu a zuciyar Mami. Idanunta ta ɗaga ta kalli Hajiya Mama kafin ta ce.

"The baby is seven months pregnant?" Mami tayi tambayar cike da son jin cikakken bayanin da likita ya yi wa su Hajiya Mama. Jinjina kai Hajiya Mama tayi itama kafin ta ce.
"as the doctor said, an sakata cikin kwalba babyn ba lafiya gareta ba itama, rashin lafiyar uwar ya taɓa ta tun a ciki" "Ya Salam, Ubangiji ya basu lafiya duk"

Ammi wacce ta kasa mgn tun ɗazo ta kalli Hajiya Mama cikin jajintawa ta ce "Ya mai jikin? Allah yasa kaffara ne ya tashi kafaɗunta"

"Amin Ya Rabbi Ammi" a karo na biyu Ammi ta ce "ba'a iya ganinta ne? Naga tunda muka zo kuma kuke waje a zaune, banga wani likita ba?"
Hajiya Mama ta ce
"Sure, she still hasn't recovered from the surgery. But Dr yace at Anything zata iya tashi" jinjina kai Ammi tayi tana da faɗin.
"Allah sarki Abra Baiwar Allah,ta haɗu da mugun ciwo Allah ka yaye mata" duk suka amsa da Amin.

Duk yadda za'a bayyana maka tashin hankali to na Abbi yafi ƙarfin a faɗesa, tunda suka zo ya kasa zama, banda sunan Allah babu abin da yake ambato a cikin bakinsa, sai ajjiyar zuciya da yake saukewa haka kurum fargaba ta riski zuciyarsa, tsoro da tunanin faruwar wani abu ya wanzu cikin tunaninsa, yana gani a wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login