Showing 42001 words to 45000 words out of 231718 words
Chapter 15 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
ciki, amma sauran mutane gani suke yi ana yin iyakar bakin ƙoƙari dan ganin an kula da mutum da yi masa abun da ya dace. Kuma kar ki manta, shi fa Doctor Bulama indai zaka cika masa ƴaƴan banki to zaka ga aiki yanda ya kamata, zai kula da kai tamkar ɗan cikinsa."
"Kai amma abubuwan nasa sun yi yawa, ya kiyayi ƙarshen sa, dan ba zai masa kyau ba, matuƙar bai tuba ya daina abun da yake yi ba."
"Ke dai kawai Allah yasa mu dace, amma ana abu a ƙasar nan, gashi shuwagabanninmu babu ruwansu, tunda ba su ko Ƴaƴansu ake yiwa ba, su in dai zaka ba su Haraji mai tsoka to duk ma abun da zaka yi ka je ka yi."
"Akwai Allah."
Jamila ta faɗa cikin rauni da damuwa.
Sha biyu da ƴan mintuna na rasa su Abra suka dawo gida, yau sun yi final exam gaba-d'ayansu.
Na'ima tana zaune a parlour ita da wata ƙawarta da ta kawo mata ziyara, suka yi sallama suka shigo, ta amsa musu tana bin Abra da wani wulaƙantaccen kallo, ƙasa ta yi da kanta gabanta na fad'uwa, ta san watan shan wahalarta ya kama tunda Abbi ba ya gari. Cikin girmamawa ta gaishe da baƙuwar tare da yiwa Nai'ma sannu da gida, sannan ta wuce ɗakinta. Salman kuwa zama ya yi ya gaishe da baƙuwar tare da faɗin. "Mami yau mun gama exam ɗinmu ta third semester Ss 1, ranar Saturday ɗin nan za mu yi speech in Allah ya kai mu. Na'ima ta ce. "Masha Allah, Allah ya nuna mana ya bayar da sa'a." Ya amsa da Amin sannan ya tashi ya nufi ɗakinsa.
Ƙawar Mami mai suna Maryam ta dube ta cike da munafurci ta ce. "Na'ima kar dai ki ce mun har yanzu kina riƙe da wannan Shegiyar yarinyar?"
"To ya zan yi, tunda mai gidan ya dage."
"Taɓ kin ga zaki iya ne, amma da ni ce da tuni ta bar mun gida wallahi, yanda take da kyan nan ai sai ta raba ki da mijin naki ma."
"Khamal ba zai taɓa son yarinyar nan ba na sani, dan a matsayin ƴa ya ɗauke ta, kuma ba ya son ta san ba shi ya haife ta ba, dan haka ki ma bar wannan zancen kar zuciyata ta buga, dan wallahi idan hakan ta kasance sai na kashe ta na kashe kaina na kashe khamal! Damuwata a yanzu yanda Khamal yake nuna mata ƙauna shi da ƴan'uwansa, dan a yanda suke nunuwa sun fi ƙaunar ta akan Salman, abun nan yana ci mini tuwo a ƙwarya ba kaɗan ba."
"To ai ke kika zauna komai yake faruwa, ta ƙarƙashin ƙasa zaki bi ki yi yanda dole ta bar gidan, azabtar da ita zaki na yi bana wasa ba idan baya nan."
"Hakan nake yi ai, dan kin ga bana komai a gidan nan ita take yi."
"Dan girki da su wanke_wanke ai mai sauƙi ne, aiki zaki na ba ta wanda sai ta kwanta ciwo dan wahala, idan wuya ta ishe ta da kanta za ta gudu."
Na'ima ta ɓata fuska ta ce, "To su girkin da nake ba ta ma cewa ya yi aikin ya yi mata yawa, a samo masu aiki suna yi, sai dabara na yi masa na ce ai ita ƴa mace dole sai an yi treating ɗinta a gidan iyayenta, kar ta je gidan Miji a ce ba ta iya komai ba, sannan fa ya hak'ura ya bari take yin aikin."
Maryam ta ce. "Ai idan baya nan zaki na ba ta ayyukan wahalar."
"Idan baya nan ai akwai mai yi masa c.i.d Salman, wannan yaron kamar cingum kullum yana naniƙe da ita, shaƙuwarsu da soyayyar junansu har tsoro take ba ni."
"Ke fa Na'ima idan kika yi wani abun kamar ba wayayyiya ba, yanzu komai sai an koya miki, ai da dabara zaki yi. Bari in faɗa miki yanda zaki na yi." Shawarwari kala_kala na mugunta da azabtarwa Maryam ta bawa Na'ima akan ta dinga yiwa Abra, ai kuwa ta ji daɗin su sosai ta ce a yau ba gobe ba za ta fara.
Fitowar ta kenan daga wanka ta zira riga mara nauyi da niyyar ta kwanta ta huta, saboda ciwon da kanta yake mata, dan jiya ba ta yi ishasshen bacci ba, ta tsaya karatun Nobels ɗin da za'a yi musu question a exam ɗinsu ta Yau. Mami ce ta banko ɗakin ta shigo ba tare da ta yi sallama.
"Ubanki kike yi a ɗakin da ba za ki fito ki ɗora mana girki ba? Ba ki ga rana ta yi ba ne?"
Na'ima ta faɗi haka cikin masifa tana wurga mata uwar harara.
Ƙasa ta yi da kanta ta ce. "Ki yi hak'uri Mami, ban san baki girka ba."
"Tunda ga baiwar Ubanki ko? In girka miki ki zo ki ci?" Ta ja ƙwafa sannan ta juya ta bar ɗakin.
Ba ta ce komai ba, ta ɗauki hijab ɗinta ta zira ta bi bayan Na'ima, ta san da Abbi yana nan kafin su dawo daga school Mami ta yi girki, shi yasa yau ma ta ɗauka ta yi.
"Salman! Salman!"
Firgigit ya farka daga baccin da ya fara ɗaukar sa, Mami ya gani tsaye a kansa.
"Ka tashi zan aike ka?"
Idanunsa dake cike da bacci ya lumshe ya ce. "To Mami ina zuwa."
"Kamarya kana zuwa? Hajiya Maryam ce fa za ta tafi, zaku bi ta gidanta kai da driver za ta ba ka saƙo ka kawo mini, saƙon kuma na gaggawa ne ina buƙatar shi yanzu."
Duk da baccin dake cin shi haka ya tashi zaune ya amsa mata, bayan ta juya ta fita ya tashi ya shiga toilet dan wanke fuskarsa.
Ƙarfe uku da mintuna Abra ta gama lunch, tana ƙoƙarin shiga ɗakinta ta kwanta ta ɗan yi bacci kafin lokacin islamiyya ya yi, amma Na'ima ta hana ta, umarni ta ba ta akan ta biyo ta ɗakinta, babu musu ta bi ta.
Zannuwan gado farare tass wanda Na'ima ta wawwatsa musu manja da gayya ta nunawa Abra ta ce. "Kwashe waɗannan kayan ki je ki wanke su tass yanzun nan, akwai sabulu da omo a cikinsu."
Abra ta kalli kayan ta kalli mahaifiyarta, ta ce. "Mami ba zan iya ba wallahi, sun mini nauy..."
Ba ta ƙarasa Maganar ba Na'ima ta ɗauke ta da wani gigitaccen mari.
"Dan kaza_kazanki in ce ki yi abu ki ce mun a'a? Wato kin fara riƙa ko? ina magana kina musa mun saboda kin raina Ni, kina ganin kin girma yanzu kanmu ɗaya."
Abra dake dafe da kuncinta tana hawaye ta ce. "Ki yi haƙuri Mami, zan yi."
"Kar ma ki yi, yanzu in saka ki tsallen kwado a gidan nan, ba ke mayya ba, kin nace sai kin zauna, wahala yanzu kika fara shan ta a gidan nan, kaɗan ma kika gani." Abra da ba fahimtar abun da take cewa ta yi ba saboda gigitar marin da ta sha, ta sunkuci bedsheets ɗin ta nufi bakin tap.
Tana kuka sosai ta tara ruwa a cikin bucket ta fara wankin. Har kusan Magriba ba ta gama ba, sai gurza su take yi da sabulu amma manjan ya ƙi fita, ga shi zanin gadon ya ƙara nauyi saboda ruwan da ya sha, ta rasa ma ta yaya za ta jujjuya shi ta wanke ko'ina, gashi abu ba guda ɗaya ba har uku. Hannayenta kamar ba'a jikinta suke ba saboda ciwon da suke mata, bayanta ya ƙame saboda sunkuyo, haka ma wuyanta, ga yunwa dake addabar cikinta. Matsalar kuma ita ba iya wanki sosai ta yi ba tunda ba sa yi, daga socks sai undies ɗinta kawai take wankewa, suna da masu yi musu wanki a gidan.
Bayan su Salman sun kai Hajiya Maryam gida ta dage sai ya shiga ciki ya karɓi saƙon, ba dan son ransa ba ya bi bayanta. Ta zaunar da shi a parlour ta ce bari ta shiga ɗaki ta ɗauko masa, ta yi kusan mintuna talatin sannan ta fito, Salman har ya gaji da jira.
Ta zauna akan kujera ta ce. "Salman na duba ban ga saƙon da zan baka ba, amma bari na yi waya yanzu a kawo wani sai na baka ka, ka kai mata." Cikin ƙosawa Salman ya ce. "Bari kawai mu koma Aunty, wani lokacin na zo na karɓar mata, yanzu lokacin islamiyya ya kusa." Hajiya Maryam ta ce. "Ka ɗan jira dai, yanzu fa za'a kawo, Mamanka tana buƙatar saƙon yanzu_yanzu shi yasa." Bai ƙara cewa komai ba, amma kallo ɗaya zaka yi masa ka san bai so hakan ba, Hajiya Maryam ta tashi ta kawo masa drinks da snaks.
Wasa_wasa har ƙarfe uku ba'a kawo saƙon ba, sai ƙarairayi Hajiya Maryam take yi masa, ta ce mai kawo saƙon ne Motarsa ta samu matsala, amma ya kusa ƙarasowa. Ganin la'asar ta kusa Salman ya ce zai tafi gida, sai Hajiya Maryam ta kira Na'ima ta sanar mata, Na'ima ta ce ta ba wa Salman wayar, yana karɓa ta balbale shi da faɗa, ta ce kuma ko dare zai kai ya jira ya karɓar matar saƙon. Sai shida na yamma saura aka kawo saƙon aka ba shi suka taho gida.
Sai da Na'ima ta ji shigowar Motar su Salman gidan sannan ta fito bakin tap ɗin cikin sauri, tana zuwa ta hand'aka Abra gefe ta ce. "Makirar yarinya, tun ɗazu Uwar me kika zauna baki gama ba? Sai ki wuce mu tafi ciki."
Ba ta ce komai ba, dan idan ta ce za ta yi magana kuka ne zai kufce mata. Mami ta tasa ta a gaba suka shiga ciki, saboda gudun kar Salman ya zo ya tarar da ita a gurin ya sanar da mahaifinsa.
Kamar za ta faɗi haka take jin kanta, daƙyar take iya taka ƙafuwanta, haka ta daure ta ƙarasa ta shige ɗakinta ta faɗa kan gado tare da sakin wani marayan kuka, ko'ina a jikinta ciwo yake mata, amma ita ba wannan ne ya fi damun ta ba, tsanar da mahaifiyarta take nuna mata ya fi komai damun ta, a kodayaushe cikin tambayar kanta dalilin da yasa take mata hakan take.
Bayan Salman ya shigo ya ba wa Nai'ma saƙon sai ya wuce kitchen ya ɗebi abinci ya ci, saboda yunwar da yake ji, dan ƙin cin komai ya yi a gidan Hajiya Maryam tsabar takaici. Yana Allah_Allah ya gama cin abincin ya je ya ga Yayarsa dan ba ƙaramin kewar ta ya yi ba yau, amma kafin ya gama aka kira Sallah, hakan ya sa yana gamawa ya wuce masallaci. Da ya dawo Na'ima ta tare shi a bakin ƙofa ta aike shi ya kai mata saƙo, bai dawo ba sai bayan isha'i, a lokacin kuma Abra ta gama cin kukanta bacci ɗauke ta, hakan ya sa ba su haɗu ba sai washegari.
Misalin ƙarfe sha ɗaya na safe bayan ta gama ayyukan gida wanda duk tare suka yi da Salman, suna yi yana ba ta labarin yanda ya yi missing ɗinta jiya tare da yi mata mitar ta yi bacci ba ta jira ya dawo ba, haƙuri ta ba shi ta ce masa kanta ne yake mata ciwo a lokacin, shi ya saka ta sha magani ta yi bacci.
Suna zaune a parlour suna hira da tsokanar juna kamar yadda suka saba cikin nishaɗi Na'ima ta shigo parlour'n. Fuskarta ɗauke da fara'a ta cewa Salaman. "Son yau na cika maka burinka na nacin son driving da kake yi, jiya na saka an yi maka bucking a wani guri da ake koyarwa, yau zaka fara zuwa, sai ka tashi ka shirya ka tafi, direbanku zai kai ka.
Salman ya fasa ihu ya ce. "Wow, thank you Mamina, na ji daɗi sosai."
"Sai ka tashi ka tafi, kar su yi ta jiran ka."
Cikin murnar Salman ya miƙe ya ce, "Amma har da Yaya ko Mami?"
"Sai dai Kakan Yaya ba Yaya ba, tana macen zan yi asarar kuɗina in biya mata ta koyi wata Mota, sai dai ta mutu ba ta iya ba."
Ɓata fuska ya yi bai ce komai ba, sam ba ya jin daɗin abun da Mami take yiwa Yayarsa.
Murmurshi Abra ta yi ta ce, "Congratulations Bro, Allah ya bayar da sa'a ya taimaka."
Murmurshin ya mayar mata ya ce, "Ina ƙwarewa ke zan fara kaiwa unguwa Yayata."
"To Allah ya nuna mana lokacin."
Ya amsa da Amin sannan ya fice bayan ya yi musu sallama. A rayuwar Salman yana son ya ga yana driving, tun da ya so ya koya amma Mami ta hana ta ce Ya yi ƙanƙanta sai ya ƙara girma.
Na'ima tana jin Motar su Salaman ta fita ta wurgawa Abra wani wulaƙantaccen kallo, cikin tsawa ta ce. "Tashi ki je ɗakina zaki ga labulaye a ƙasa ki ɗauka ki je ki wanke, saura yau ma ki zauna laƙai_laƙai irin na jiya, wallahi idan baki wanke su ba tass sai na lahira ya fi ki jin daɗi."
Jikinta a matuƙar sanyaye ta miƙe ta je ta kwaso labulayen, hannunta har yau bai daina yi mata raɗaɗi ba na dirzar zanin gadon da ta dinga yi jiya, ga jikinta ba wani jin daɗinsa take yi ba.
Jiya ta yi fashin islamiyya yau baza ta so ta kuma yi ba, hakan yasa cikin sauri ta jiƙa kayan a cikin ƙaton baho ta zauna ta fara wankin zuciyarta babu daɗi.
Ko 5 minutes ba ta yi da zama ba ta ji alamun ana kallon ta, juyawa ta yi suka yi ido huɗu da wanda ba ta taɓa tunanin ganin shi a wannan lokacin ba, sai da ta juyo ɗin ne kuma ƙamshinsa ya cika mata hanci.
LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
[9/30, 8:55 PM] Abk: *DARE DA DUHU*
_Brigh pens✍️_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee Kumurya
P12
Domin samun complete litattafanmu, ku yi following ɗin wannan accounts ɗinkin a Arewabooks
https://arewabooks.com/chapter?id=6316f4af434cfeb9e7fe2949
https://arewabooks.com/u/nimcyluv
https://arewabooks.com/book?id=
Elegant online writers
LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
Salman ta gani a tsaye yana bin ta da kallon mamaki, cikin hanzari ya ƙara so in da take durƙushe, yana faɗin "Yaya, me kike haka a durƙushe?" Yana ƙarasowa ya kalli tulin labulayen da ke gabanta tana murzasu da ƙyar.
Salman yace "Yaya? Waye ya sa ki Wannan aikin haka?" A wannan karon kasa jurewa ta yi, ta fashe da kuka.
Ɗagota Salman yai yana cewa "Am sorry, de na kukan gayamin waye ya saki Wannan aikin haka?".
Ta share hawayenta tace "labulayen ɗakin Mami ne, da na guest room"
"To waye yace ki wanke?"
"Mami ce"
Salman yace "What? Mami kuma, duk almajiran da ke gidan nan, a rasa wanda za'a saka wannan aikin se ke? Ba ta ganin ko ƙwarin kirki ba ki da shi, kalle ki fa, ajiye kayan nan muje ciki" yai maganar yana jan hannunta.
Riƙe shi tai ta girgiza masa kai tace "No Faris, please ka zo ka tayani mu wanke, saboda ina son zuwa Islamiyya, kaga jiya ban je ba, kuma ana screening na saukar Alqur'ani".
"What, jiyan ma ba ki je Islamiyya ba, why?"
Abra tace "a'a mantawa nai, naje ai ya nake nufi"
Salman yace "kin ga wuce muje".
"Faris please, Mami ce fa ta sani, ni dai kawai ka tayani mu gama".
Banza yai mata ya cigaba da jan ta zuwa cikin Falo, Mami na zaune tana kallo tana kaɗa ƙafa, ta tsikaro ɗauri gaban goshi, tana danna remote.
Babu tsammani Hajiya Na'ima ta ɗaga kai, ta ga Salman riƙe da hannun Abra, sai da ta sha jinin jikinta amma ta maze tace "Ya na ga ka dawo?"
Salman be amsa mata Maganar ba yace "Mami, wai ke kika saka Yaya wankin wannan manyan labulayen?"
"Eh, ni ma sata ko ban isa bane?"
"Mami kin isa mana, amma kina ganin yana yinta ba ta da ƙwarin kirki, ni Yakamata ki saka in ma wankewar ne, ga lokacin islamiyya yayi".
"Sannu ubana ka gama? Nace ka gama?, Ba mace bace? Idan ban sata aiki ba sai yaushe gidan wani fa zata, tana da tabbacin in da zata zata samu masu wanke mata ne, shine ki ka kai masa ƙarata?, algunguma kin wuce kin ƙarasa wankin nan ko sai na zo na kakkarya ki a gurin nan, shegen ido Kamar Magen mayu" Jikin Abra a matuƙar sanyaye ta zare hannunta daga ma Salman tai waje.
"Haba Mami, dan Allah meyasa kikewa Yaya Abra haka?, a duniya ban taɓa ganin uwar da takewa ɗanta haka ba, kinga ba ta da cikakkiyar lafiya, dan Allah Mami kar abunda kike mata ya kuma illata lafiyarta"
A hasale tace "Ka rufen baki ko se na ta so kanka, uban me ma ya dawo da kai gidan nan, bayan ga in da na turaka?"
Ransa haɗe yace "lokacin Islamiyya ne yayi" yana gama faɗin haka ya bar Falon, in da Abra take ya koma, ya tarar da ita a zaune akan labulayen, tana ta uban kuka, farar fatar fuskarta tai jawur.
Be ce mata uffan ba, ya matsar da ita gefe, ya tattara labulayen wankesu tsaf, har ya kammala kuka take ba ta dena ba.
Se da ya gama wankin sannan yace "tashi muje ki ci Abinci ki shirya mu tafi Islamiyya". Jiki ba ƙwari ta bi bayan Salman, se dai a wannan karon Mami ta bar Falon.
Ɗakinta ta wuce, Salman kuma ya wuce ɗakinsa, dan ya yi shirin islamiyya, sai dai gaba ɗaya ransa babu daɗi, sai ƙoƙari yake ya gano dalilin da yasa Maminsu ba ta son Abra, Abunda take mata ya yi yawa, ya wuce ace kara ce ta ɗan fari, ƙiyayya ce kawai, to amma ya za'ai mutum ya haifi ɗa kuma ya dinga ƙin sa.
Haka ya dinga tunani daban daban a ransa, har ya kammala shirin makarantar.
Dining ya tafi dan cin Abincin rana, sedai Abra ta faɗo masa a ransa, ya san babu tabbacin ta ci Abincin, wata ƙila tana can tana laƙai laƙai koma kukan ta cigaba.
Ya miƙe da plate ɗin Abinci a hannunsa, ya nufi ɗakinta da sallama a bakinsa ya shiga, ya tarar da ita a