Showing 63001 words to 66000 words out of 231718 words

Chapter 22 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14822

2:40 PM] Abk: LITTAFIN DARE DA DUHU NA KUƊI NE, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.




Cikin mamaki Khamal ya ce. "Subhanallahi! Granny wai me ya faru ne?"

"Mene ma bai faru ba Kamalu? Wannan matar taka mai kama da bayi ba matar arziƙi ba ce, mugunta ce fal cikinta da kake ganin ta haka, munafuka mai fuska biyu." Granny ta a faɗi haka tana hararar Nai'ma.


Salman dake tsaye ya juya tare da ficewa daga parlour'n, dan bai ɗauki maganganun Granny da mahimmanci ba, a soki burutsunta ya ɗau abun, dama fitar da ya yi gidan Aunty Iman zai je ya ɗauko Abra, tana can tun safe ta kai mata ziyara.



Nai'ma da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi ta dubi Granny tare da faɗin. "Haba Granny, wai me na yi miki kika tsane ni haka?"

Kama baki ta yi ta ce. "Au ba ki san me kika yi ba? To ba za ki taɓa sani ba kuwa, tashi maza ki ƙara mai ki bar mini gidan jika, takardarki kuma na nan tafe zan kawo miki da kaina, as'as'as."

"Wai dan Allah Granny mene haka? Ya zaki zo ki ɗaga mana hankali."

"Abun da ya fi hankali ma zan daga muku, kai da ba ka gane mai ƙaunar ka saboda Allah, wannan matar da ka ji abun da ta aikata wallahi da tuni ka sallame ta kafin ma wani ya ji."

"Me ta yi toh?" Khamal ya tambaya cikin ƙosawa da hargagin Granny.

"Ban sani ba Ubana! Wato ƙarya nake yi kenan, tsofai-tsofai da ni amma kake ƙaryata ni Kamalu? akan wannan makirar matar taka?" Sai ta fashe da kuka tare da faɗin. "Da A'isha ce ai ba za ka ƙaryata ta ba, to wallahi yau sai matar nan ta bar gidan nan, idan kuma ka ƙi in saka direba ya kira mun Hamisu da A'isha in sanar musu na saka abu ka ƙi yi."

Cikin sauri Khamal ya ce. "Ki yi haƙuri abun bai kai haka ba." Sannan ya kalli Nai'ma ya ce. "Ki ba ta haƙuri." Kafin ya gama rufe baki Granny ta ce. "Kamalu mahaukaciya ka mayar da ni ko me? Uban haƙuri za ta ba ni ba haƙuri ba, to ba zan haƙuran ba, wallahi in dai ƴar halak ce ni sai wannan abar ta bar gidan nan a yanzun nan, munafuka ta san ba ta da gaskiya ai, sai fiƙi_fiƙi take da ido."

Marairaicewa Nai'ma ta yi ta ce. "Dan Allah Granny ki yi haƙuri, duk da ban san laifin da na aikata ba."

Mitsss, ta ja dogon tsaki tare da ƙanƙance ido tana jefawa Nai'ma wani irin kallo ta cikin glass, ba tare da ta yi magana ba ta fice daga parlour'n fuu tana faɗin. "Ka nuna mini ban isa da kai ba, bari na saka a kira mini wanda ya isa da kai, shi ai bai isa ya ƙetarewa umarnina ba."

"Oh My God, rigimar Granny ta yi yawa, mene fa'idar wannan abun da ta zo ta yi?"

Hawayen munafurci Na'ima ta fara ta ce. "Ban san me na yiwa Kakarka ba Khamal ba ta so na, kullum zancenta za ta ƙaro maka Aure, ko kuma ta ce ka rabu da ni." Cikin rarrashi Khamal ya ce. "Halin Granny ne ba ki sani ba Wifey ko me? Rikicinta ne kawai ba wani abu ba, idan ya tashi kowa ma yi masa take babu wanda ta ƙyale."

"Wannan ba rikici ba ne Khamal, tsana ce kawai."

Daidai nan Granny ta dawo hannunta riƙe da wayar Driver ta miƙawa Khamal. Ba tare da ya karɓa ba ya ce. "Me zan yi da ita?"

"Huhuhu, yau na ga jaraba, to wacce ta yi cikinka ta tsuguna ta haife ka ce take son magana da kai." Granny ta faɗi haka kamar za ta ki fa masa mari.


Karɓar wayar ya yi ya kara a kunnensa. Kafin ya yi magana muryar Ammi ta doki kunnensa a kausashe da faɗin. "Khamal ka yi abin da Granny ta ce."

"Amma Ammi..."

"Ba na son jin komai, ka yi ko mene ne, daga baya ma yi magana."

Jiki a sanyaye ya ce. "Shikenan." Tare da katse wayar. Kallon Nai'ma ya yi ya ce. "Ki je gidan, I will come tomorrow." Fashewa da kuka ta yi ta ce. "Yanzu Khamal yau ni kake kora daga gidanka? Ni Nai'ma uwar Ƴaƴanka kake cewa in bar maka gida?"

"Babu yadda zan yi ne Nai'ma, umarnin mahaifiyata na bi, but don't worry, everything will be okay insha Allahu." Daga haka ya miƙe ya nufi part dinsa.

"A tashi a tashi da Allah, gida ne tunda ba na Ubanki ba ne sai kin bar shi wallahi, kuma a cikin satin nan zan aurawa Kamalu zankaɗeɗiyar budurwa, kuma ta cikin gida ce ba bare ba, bari uban nasa ya dawo."

A zuciye Nai'ma ta goge hawayen fuskarta tare da miƙewa tsaye ta nufi ɗakinta kamar za ta tashi sama. Tafa hannuwa Granny ta yi ta ce. "Au da bangaje ni za ki yi? To Uwarki kika yi niyyar bangajewa ba ni ba, kuma gidan jikana yau dole a bar shi." Guri ta samu ta zauna ta kunto goro dake ɗaure a jikin zaninta ta basga tana karkaɗa ƙafa, idanunta akan ɗakin Na'ima."

Sai da Granny ta ga fitar Nai'ma daga gidan sannan ta tafi, zuciyarta fess yau ta kawo ƙarshen iskancin Na'ima.

Fayyad na gaba Adnan yana bin shi a baya suka shiga parlour'n gidan, wata farar matashiyar matar dake zaune akan kujera ta amsa musu sallamar da suka yi cikin fara'a.

"Wow Masha Allah, yau ga Sp Adnan a gidana, kullum ana mini hirar ka, yau ma tun safe ake maimaita mini zaka zo, welcome." Ta faɗi haka tana miƙewa tsaye.

Murmurshi Adnan ya yi bai ce komai ba, gurin zama Fayyad ya nuna masa ya zauna. A hankali ya ce. "Yana yi miki gulmata kenan Maman Boy?" Still tana murmurshi ta ce. "Sosai ma, kai dai a yi shiru kawai." Fayyad ya zauna a gefensa ya ce. "Ai bana gulamar tuzurai sai ta Ma'aurata." Ko kallon shi Adnan bai yi ba. Dariya Maman Boy ta yi ta haye upstairs.

Tare suka dawo da wata budurwar yarinya, wadda da alama K'anwarta ce saboda kamar da suke. Tunda suka sauko ta zuba wa Adnan na mujiya, har plate ɗin da ta ɗoro drinks a kansa ya kusa suɓucewa daga hannunta, cikin son burge shi ta gaishe shi, ba tare da ya ɗago ba ya amsa mata. Maman Boy ta miƙa masa Boy sannan suka koma saman.

Suna shiga ɗaki K'anwar Maman Boy ta ce. "Wow amma Aunty guy ɗin nan ya haɗu, ga kyau ga aji, yanda kika san irin Black Americans ɗin nan, ni na taɓa ganin baƙin mutum mai kyan shi kuwa?"

"Kai Ramlah uwar zuzuta, daga ganin mutum sau ɗaya har kin ƙare masa kallo?"

"Aunty ba za ki gane ba ne, amma guy ɗin ya haɗu over, Matarsa ta more."

Murmurshi Maman Boy ta yi ta ce. "Ko dai kin ƙyasa ne?"

"Rufa mun asiri, kar Matarsa ta ji ta mun duka, kawai dai na faɗi abun da yake da akwai ne, kin san ni ba na gani in yi shiru."

Maman Boy ba ta kuma cewa komai ba, Ramlah kuwa cigaba ta yi da yaba kyawu da zubin halitta irin na Adnan.


"Ka sha juice ɗin mana, ka wani lumshe ido ina magana ka mun shiru, tunanin me kake?" Fayyad da ya gama zuba drinks a cikin glass cup ya faɗi haka.

Ba tare da ya buɗe idon ba ya ce. "I'm okay, thank you."

"Wannan ai wulaƙanci ne, Matata ta kawo maka abu amma ka ce ba za ka sha ba."

"I will drink, amma ba dan kai ba."

"Na ji ɗin, Malam ka faɗi gaskiyar abin da yake damun ka, ka zo ƴanmatan Kano sun ruɗa ka shine kake wani babbasarwa, wannan yanayin da kake daga gani na fall in love ne.

"Ka fi kowa sanin ba ni da time ɗin shirme ko?" Ya yi maganar yana gyara kwanciyar Boy da ya yi bacci a jikinsa.

"Allah ya nuna mun ranar da ka zo kana cewa, dama Fayad haka so yake, lokacin zan ci dariyata in more, wai wa ya ga su Adnan ana Baby please sorry, you know I love you more." Ya ƙarashe maganar cikin dariya.

Taɓe baki kawai Adnan bai ƙara magana ba.


Abra ba ta nan Granny ta zo, kuma har ta tafi ba su dawo ba, saboda sun biya siyo school bag ita da Salman bayan sun baro gidan Aunty Iman, saboda normal handbag ba za ta ɗauki tarkacen school ba. Ba su farga Nai'ma ba ta gidan ba sai da daddare lokacin dinner, saboda sun saba idan Khamal yana gari kodayaushe tana part ɗinsa.


Ganin Khamal ya fito shi kaɗai yasa Salman ya ce. "Abbi Mami fa? Tunda muka dawo ban gan ta ba, na je ɗakinta ba ta nan."

"Ta je gidan Mama." Ya ba shi amsa

"Mama kuma? Lafiya?" Ya tambaya cikin mamaki.

"Lafiya ƙalau."

"Yaushe za ta dawo?"

"Gobe."

"Me ake yi a can Abbi?"

"I don't know, Mama ce ta kira ne za su tattauna akan something important."

"Me ne abun?"

"Na ce maka ban sani ba, Family issue ne, ka zama ɗan jarida ne Salman da za ka titsiye ni da tambayoyi haka? ka ci abinka, kar na kuma jin bakinka." Khamal ya faɗi haka cikin faɗa.

Ƙasa Abra ta yi da kanta tana wasa da cokali a cikin abincinta, amma ta kasa ɗiba ta kai bakinta.

"Ki ci abinci Malama, ba wasa za ki tsaya ba." Khamal ya faɗa mata haka ba yabo ba fallasa.

Gyaɗa masa kai ta yi a hankali ta fara cin abinci. Kaɗan Khama ya tsakuri abincin ya ci ya miƙe, shi ma dan kada yaran nasa su yi tunanin da wata matsalar ne, musamman Salman da yake da saurin fahimtar abu. Daga dinning area ɗin ɗakinsa ya wuce ya dauko car key ya fice zuwa gidan Ammi.


"Yaya, ba ki yi tunanin wani abu ya faru ba da bama nan?" Salman ya tambayi Abra cikin nazari.

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Like what?"

"Ko Mami sun samu matsala ne da Abbi shi yasa ta tafi gida? dan yanayinsa ya nuna yana cikin damuwa."

"I don't think that gaskiya Faris, kuma insha Allah ba haka ba ne."

"To Allah yasa." Ya yi maganar tare da cigaba da cin abincinsa.

ita kuwa kasa cigaba da cin abincin ta yi, don tana cikin damuwa, ɓoyewa kawai take dan kar Salman ya fuskanta. Ta damu sosai akan fushin da Abbinta yake da ita, na makircin da Nai'ma ta shirya mata, ta ba shi haƙuri ya ce ya haƙura amma ya ƙi sakar mata kamar da.



Khamal ne zaune a ɗakin Ammi yana zayyane mata abun da ya faru, bayan ya gama ta ce. "Yanzu ya kake so ayi?" Ya ce. "Toh Ammi, na rasa ma me zance, rigimar Granny ta yi yawa, haka kawai ta zo ta kora yar mutane gidansu, babu wani dalili." Ammi ta ce. "Ka kira Baffa ka sanar masa, zai yi mata magana kuma na san za ta haƙura." Numfashi ya sauke cikin damuwa ya ce. "Zan kira shi insha Allahu, amma ni Ammi ban so kika biyewa Granny ba, yanzu Nai'ma sai ta ga kamar na wulaƙantata ne."

"Hakan shi ne solution da kwanciyar hankali, ko so kake yau Granny ta hana ni bacci da mitar na ƙi bin umarninta, saboda ba ita haife ni ba?"

Girgiza kai kawai Khamal ya yi, zuciyarsa cike da takaicin halin Granny, amma abu ɗaya da ya daure masa kai shi ne, ya san duk jarabar Granny ba ta yin ta ba tare da dalili ba ko an taɓo ta, idan haka ne kenan Na'ima ta yi mata laifin da gaske, amma wanne irin laifi ne? Ko dai rikicin tsufan nata ne ya ƙaro?


Hankali a tashe Nai'ma ta ƙarasa gidansu, Mama tana ganin ta, ta san ba ƙalau ba.

"Ke lafiyarki kika faɗo mana gida babu ko sallama?"

"Ina fa lafiya Mama? Allah ya haɗa ni da matsiyaciyar ƙaddararriyar kakar miji, ƴar kaza_kaza." Nai'ma ta faɗi haka tana hawaye.

A ruɗe Mama ta ce. "Yanzu me ya faru, na gan ki a hargitse?" Labarin abun da ya faru ta sanar mata.

Cikin takaici Mama ta ce, "Wannan mata akwai bala'i, mata kawai ki ɗorawa kanki jaraba a rayuwa?"

"Shegiya ga shi ta ƙi mutuwa."

Jinjina kai Mama ta yi ta ce. "To ta je dan kanta, aniyarta ta bi ta, zama gidan Khamal ne yanzu kika fara, sai dai ta mutu dan baƙin ciki. Ki kwantar da hankalinki, na san Khamal ɗin zai zo ya mayar da ke cikin ruwan sanyi."

"Hmm, Mama babban tashin hankalina kullum cikin cewa za ta yi masa Aure take, tsorona kar zancenta ya tabbata, dan sai abun da ta ce iyayensa suke bi, idan ta dage amincewa fa za su yi." Ta yi maganar cikin tsantsar damuwa.

"Ba zai yiyu ba, wannan tatsuniya ce, ki daina damun kanki akan wannan soki burutsun tsohuwar mara ma'ana, ki ɗauki zancenta shirme kawai. Tashi ki wuce ciki ki huta, bari Suwaiba ta dawo ta dafa miki abin da zaki ci."

Zuciyar Nai'ma fal baƙin ciki ta miƙe ta shige ciki, wata irin tsanar Granny na cika mata zuciya, shegiyar mata ta yi sanadin da yau za ta kwana a cikin zafi ba a cikin AC ba, ita da ko taro ake a gidansu ba ta kwana, sai dai ta zo da sassafe saboda ba ta iya baccin cikin kwanciyar hankali. Babban takaicinta ba ta san abun da ta yi Granny ta yi mata haka ba, don ko kusa ba ta yi tunanin Salman ne ya sanar musu abun da ta yi wa Abra jiya ba.




Abra na ɗakinta tana zuba abubuwan school a cikin new bag ɗinta, sai a time ɗin ta farga da rashin ganin I.d card ɗinta. Ƙara checking tsohuwar jakarta ta yi ko za ta gan shi amma ba ta gani ba, parlour ta fito inda Salman yake zaune yana kallon Ball.


"Faris school i.d card ɗina yana gurinka?"

Ba tare da ya ɗago ba ya ce. "No." Cikin damuwa ta ce. "Na duba ban gani ba, Allah yasa ban yar da shi ba." Yana duban ta ya ce. "Ki ƙara dubawa dai sosai Yaya." Kamar za ta yi kuka ta ce. "Na fa duba ko'ina ban gani ba."


"To mene abun damuwa? Kar ki mun kuka ni akan ɗan wannan abun."

"Dole in damu Salman, idan aka hana ni shiga school fa saboda babu shi."

"Babu mai hana ki, wasu ma ba a ba su ba, ki bari gobe idan muka je school sai mu yi report a sake miki wani, kafin a sake sai ki dinga nuna admission latter ɗinki in za mu shiga."

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Amma na yi mamakin rasa abun nan, ko garin ya na yar oho?"

"Yarinya ce ke, shi ya sa komai naki sai addu'a, kuka, shagwaɓa, everything."


Dariya ta yi ta faki idonsa ta ja dogon hancinsa da ƙarfi ta ce. "Tazarar shekaru uku ba wasa ba ce yaro." Tana faɗin hakan sai Salman ya yunƙura kamar zai kamo ta, ƙara ta saki tare da yin baya da sauri tana dariya. Ƙwafa kawai ya yi bai ce komai ba.


Dawowa ta yi ta zauna a kusa da shi ta ce. "Please kar ka faɗa wa Abbi na yi loosing i.d card ɗina, ya ce daga fara zuwa har na fara yarda abubuwa."

"An gama My Angel, zo ki taya ni kallo."

"Maƙe kafaɗa ta yi ta ce. "Bacci zan yi, ka san gobe 8 muke da lecture, kai ma haka, saura kuma ka makarar da mu."

"Uhm, su Yaya ƴan University, inyee." Ya yi maganar cikin dariya."

"Na ji, ka kira Mami kuwa?"

"Na kira ta ba ta ɗauka ba."

Jinjina kai kawai Abra ta yi ta miƙe ta koma ɗakinta.




Washegari da sassafe Ammi tana kitchen tana haɗa breakfast Granny ta zo bakin kitchen ɗin ta tsaya ta fara magana.


"Kai jama'a, mutane babu Allah a ransu, ɗana yana can gurin neman halak amma saboda rashin tsoron Allah an kira shi an haɗa mu, jiya har na fara bacci kiran wayarsa ya tashe ni, to ni dai ba ruwana kowa ya haifa, kuma duk abun da mutum ya mun sai an yi masa shi ma, ato."


Murmurshi Ammi ta yi tare da juyowa tana duban Granny, cikin girmamawa ta tsuguna ta ce. "Ina kwana Hajiya?"

"Lau." Granny ta ba ta amsa cikin ɓata fuska.

"Bari na kawo miki abincin Granny, yau na makara ban tashi da wuri ba ne.

"To ba yunwa ce ta taso ni ba, a ƙoshe nake, kin san ni ƴaƴana ba sa cewa in yi abu in ƙi yi, tunda ni ma suna mun biyayya daidai gwargwado, abun da Hamisu ya faɗa mun ne na kwana da shi a raina, yau kuwa ina tashi na ce ba zan yi sanya ba, gidansu waccan gantalalliyar matar kamalun zan je in dawo da ita."

"Hajiya da kanki kuma? Da kin bari Khamal ɗin ya je ya ɗauko ta."

"Bar ni in je da kaina ɗin, ni yanzu ba dogon surutu na zo mu yi ba, kira direba ya zo ya kai ni."

Ammi ta ce. "Toh, amma dan Allah ki tsaya ki karya Hajiya." Granny ta ce. "To na tsaya, kuma fa da gaskiyarki A'isha, dan waɗancan ruɓaɓɓun idan na je babu abun da za su ba ni, sai dai su bar ni yunwa tai ta sakaɗa ta, Allah na tuba ma ko sun ba ni ba ci zan yi ba, yo me zan yi da kayansu?"



Takwas da mintuna a ƙofar gidansu Nai'ma ta yi wa su Granny, tana zaune a bayan Mota take bin gidan da wani irin kallo. Tsaki ta ja ta ce. "Tirrrr, ban da ƙaddara me zai haɗa Kamalu da ƴar wannan gidan? Gida ɗan tsurut haka kamar kabari, don ma Allah ya yi mu masu ilimi, mun san Talaka da mai kuɗi duk Allah ne ya yi su." Ta ƙarashe maganar tare da buɗe Motar ta fita, fuskar nan babu fara'a ko kaɗan, sai fama take da ƙatuwar jaka a hannu. Murmurshi kawai driver yake.


Aunty Suwaiba tana tsakar gida tana alwala Granny ta rafka sallama, cikin mamaki take kallon ta, lokaci ɗaya ta haɗe rai ta cigaba da abun da take yi.

"Ba mutane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login