Showing 69001 words to 72000 words out of 231718 words
Chapter 24 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
da Khairy suka fito, suka tafi masallaci dan yin salla.
Bayan sun idar Khairy tace "Abra muje Cafeteria mu samu Abunda zamu muci".
Abra tace "A'a ni ba zani ba"
"Me yasa, ba kya jin yunwa ne?"
"Zuwa zan in jira Faris, idan ya fito daga lectures maje muci Abincin"
Khairy tace "Ikon Allah, ko kashin awaki kuka fito da Faris ɗin nan, wataran zaki Aure ku rabu, ai se kije ki tayi me ɗan uwa, nikam na tafi cin abinci bana iya ba".
Abra gyara zaman facemask ɗinta tayi, ta miƙe tare da ɗaukar jakarta ta nufi hanyar barin masallacin.
Wani guri ta samu can nesa da ɗalibai, ta zauna ta cire mask ɗin fuskarta, ta ɗakko wayarta tana trying lambar Faris.
Jikinta ne ya bata ana kallonta, lokaci ɗaya kuma wani irin ƙamshi ya mamaye ilahirin gurin nan, duk da ba ta samu ɗaga kai taga waye ba, amma wani irin tsoro ya shigeta, a jikinta taji cewar kowaye yake ƙamshin nan ma'abocin kwarjini ne.
Ba ta gama tunanin ba taji mutum ya zauna a kusa da ita, a razane ta fara bin ƙafafuwansa da kallo, sai dai ta kasa ɗaga kai ta kalli waye.
Kamar an masa dole yace "Abra Khamal Khamis"
Dam ƙirjinta ya buga, jin yadda ya ambaci sunanta, bata san lokacin da ta buɗe manyan idanunta, ta kalleshi ba, sai dai kallon nasa ya sake jefata cikin wani rikitaccen al'amari da ita kanta ta kasa gane wane irin yanayi ne haka?.
"Is that not your name?" (Ba sunanki bane?) Ya tambayeta.
Sunkuyar da kai tayi, ta ƙi yi masa Magana.
"Are You deaf?" (Ke kurma ce?)
Da sauri ta jinjina masa kai alamar eh.
Yace "And how do you heard what I said this time?" (Ya akayi ki ka ji abunda nace, a wannan karon?)
"Am using aid to hear" ta faɗi Maganar ba tare da ta shirya ba.
Jin maganar ta ta yayi, tamkar rainin hankali, amma ya basar yace "Yaushe kuka fara lectures?" Ji tayi gaba ɗaya ya takura mata, ita ba ta sani ba malami ne ko ɗalibi, to yama za'yi malami ya zo ya sakata a gaba haka.
Wayartace ta fara ringing, tayi sari ta ɗaga ta kara a kunneta tace "Hello Faris".
"Angel kina ina ne? Na zo department ɗinku ban ganki ba, ko kinje cin abinci ne?".
Tace "Aa banje ba, dama kai nake jira, bari yanzu zaka ganni" ta ƙarasa Maganar tare da miƙewa tsaye, Caraf ya sa hannu ya riƙo hannun Abra, wanda ya koma ɗan ƙarami a cikin nasa hannun, sai laushi hannun nata tamkar ya riƙe audiga.
Zare ido tayi, tana bin hannunta dake cikin nasa da kallo, take hawaye ya taru a idonta tace "ka cika mini hannu na".
Sai da ya ƙurawa kyakywar fuskarta ido sannan yace "Ina miki magana zaki tashi ki tafi?"
Da ƙyar ta iya cewa "Brother na ne yake jirana, zanje muci Abinci".
"Saurayinki dai ko?" Yayi Maganar ba tare da ya saki hannunta ba.
Tayi sarin girgiza kai tace "A'a ni bani da surayi, ƙanina ne".
Kallon Abra yake, tare da jinjina rainin hankali irin na Abra, wai duk wannan kyan nata take ce masa bata da saurayi, dan ta raina masa hankali.
Hannunsa ɗaya ya sanya a cikin aljihunsa, ya ciro ID card ɗinta, ya danƙa mata a hannunta.
Ɗan buɗe idanunta ta kuma yi, tan juya ID card ɗin ta kalleshi, amm ta kasa ce masa ta gode.
Wayarta ce ta sake ɗaukar ruri, tana ɗaga wayar cikin shagwaɓa tace "Faris, gani nan yi haƙuri"
Ta katse kiran, ta kalli Adnan tare da ƙoƙarin zame hannunta daga nasa, amma yaƙi sakin hannun, sai ƙara riƙe shi da yayi gam.
"Dan Allah ka sakar mini hannuna, jirana ake".
"Baki iya godiya bane?".
"Yi haƙuri nagode" a hankali ya sakar mata hannu, cikin hanzari ta bar gurin ko waiwayawa baya ba ta yi.
A ƙofar ajinsu ta tarar da Salman, aikuwa tana zuwa ya fara mita "Wai ina kika je ne haka?"
A ɗan dirirce tace "Can gurin naje karatu, mu tafi kawai"
Ya ɗan dubeta yace "meye wannan a hannunki?"
Ta duba hannunnata tace "ID card ɗina ne"
Yace "Hmm, a ina kika ganshi?"
"Wani ne ya tsinta shine ya kawomin"
Tsuke fuska Salman yayi yace "Wani kuma?"
Tace "eh"
Ya yi tsaki yace "wataƙila ma zama yayi yaita kallon hotonki da yake jiki".
Murmushi tayi tace "Faris Allah ya shiryeka"
Ƙara tsuke fuska yayi yace "Ki mai da mask ɗinki, har an fara binki da kallo".
Ta sa hannu ta ja mask ɗin, ta rufe fuskarta sosai tace "Shikenan?"
"Muje" yai maganar cikin bada umarni.
Adnan kuwa yana nesa da su Abra kaɗan, yana hangota ita da Salman, kallonsu yake sosai yana ƙoƙarin tabattar da abunda Abra ta gaya masa na cewar Salman Brother ɗin ta ne.
Salman ma dai Fari ne sosai, sai dai babu ta in da suka haɗa kamanni da Salman ɗin, kamanninsa daban nata daban.
A hankali ya juya, ya bar department ɗin gaba ɗaya.
Hajiya Na'ima ce ta shiga sashen Abbin Abra, ta tarar da shi yana ta shiri, ta kalleshi tace "Yallaɓai ya naga haka? Jiya fa ka dawo kuma na ga kana haɗa kaya, ina zaka kuma?"
Ba tare da ya kalleta ba ya cigaba da haɗa kayan yace "lamarine na gaggawa, akwai buƙatar inje Abuja a yau ɗin nan"
Tace "Amma meyasa?".
"Sojojin da ake bincike akansu ne, wai sunci guba sun mutu".
Tace "ta yaya? Waye ya basu gubar?"
Yace "Nima ban sani ba, abunda zanje inji kenan, ya akai suka ci gubar suka mutu, ba tare da an samu wani cikakken bayani a bakinsu ba".
"Kai amma ban so ba, daga dawowarka jiya ko gama ganinka ba muyi ba zaka juya?".
Ya ɗago ya kalleta yace "Am sorry, nima ba hakan na so ba, amma kuyi haƙuri ya zama dole in tafi, lamarin akwai alamar tambaya".
Tace "Shikenan, Allah ya tsare bari in ƙarasa haɗa maka kayan".
Ta cigaba da haɗa masa kayan, shi kuma ya shiga wanka.
Successfully, GY BULAMA ya cirewa 'yan matan nan ciki, bayan tafe masa uwar kuɗinsa da suka yi, ya rubuta musu magunguna tare da kafa musu dokokin da za su bi, dan gudun kar Matsala ta biyo baya.
Suna tafe a mota, Baby na driving tana cigaba da shirya musu yadda zasu damfari Alhazan dake mu'amala da su kuɗi, Mussaman wanda yai mu'amala da Ihsan, wanda ya kasance babba ne sosai.
Tace zasu koma gidan da suke su huta, idan suka warware zasu tafi Abuja, aje ayi wadda za'ayi dan su zasu biya kuɗin cire cikin da aka yi.
Yauma a gajiye Abra suka koma gida, duk ta gaji jikinta har wani ciwo yake, Wanka kawai tayi, tai sallar la'asar,ta hau gadonta dan ta ɗan huta, ta lumshe idanunta sai dai gabanta ya faɗi, a lokacin da tuno da mutumin da ya tsinci ID card ɗinta, Mutumin da ko sunansa ba ta sani ba.
Guntun tsaki ta ja, tare da ƙoƙarin gyara kwanciyarta, amma wayarta tai wata 'yar ƙara, alamar saƙo ya shigo.
Ta miƙa hannu ta ɗau wayar, ta fara duba saƙon.
*Sky is beautiful, especially when the millions of Stars appears in the dark, but is not that beautiful if the Moon doesn't appear. You are always that Moon that make the Sky beautiful, Stay bless my Angel.
Murmushi Abra tayi tare da furta "Allah ya shiryeka Faris"
Ta gama hutawarta, ta tashi ta shiga kitchen, a Wannan karon akai sa'a Mami tayi girki, ta shiga kitchen ta zuba ta fito falo, dan taci.
Hakan yayi daidai da fitowar Salman falon shima, yana ganin Abra yace "Alhamdilillah, thank God dama nima banci Abincin ba, let's eat together".
Ya ƙarasa kitchen, ya ɗakko spoon ya dawo ya zauna a inda Abra take, yasa cokali suka fara cin Abinci.
Abra tace "Wai nikam ina Abbi? Naga motarsa a gida, kuma banga alamar yana nan ba".
Salman yace "Mami tace mini aikin gaggawa ne ya kama shi, ya koma ɗazu muna school".
Abra tace "Amma be bari mun dawo ba, ban gama ganinsa ba fa".
"To ga hanya nan, maza bi shi" Salman yayi Maganar yana saka lomar Abinci a bakinsa.
Mami ce ta fito daga sashinsa, cikin faɗa tace "Salman meye haka? Wai ba hanaka wannan abun ba, ka zauna kuna cin abinci tare, kai kaga dacewar hakan? Ko da duk ka nunamin ban isa bane?".
Salman yace "Mami, Yaya ce fa ba wata ba, banga aibun haka ba".
"Ai dama ba zaka gani ba, tashi ka bar gurin nan kafin in ɓata maka rai".
Kan Salman ya yunƙura, Abra ta miƙe, ta bar masa Abincin, ta koma ɗakinta rai a ɓace.
Wayarta na hannunta, taji tayi vibrating.
I want you in my life for today, tomorrow and forever, have a cool evening my Moon.
Ɗan shiru Abra tayi, Salman dai gashi can a Falo Mami na yi masa faɗa, to waye ya turo mata wannan saƙon? Sai yanzu ta duba labar taga baƙuwar lamba ce.
Ɗan taɓe baki tayi, tana tunanin kawai mistake ake gurin turo mata saƙon.
Kafin lokacin da zata kwanta bacci, aƙalla an tura mata messages kusan biyar.
Haushine ya fara kamar Abra, ta replying da wrong number.
Daga haka ba a kuma turo mata message ɗin ba, kan ta kwanta bacci sai da ta kira Abbi, sukayi hira, ta yi masa Adduoi da fatan Alkhairi.
Haka nan ta samu kanta da jujjuya messages ɗin da aka dinga turo mata yau, sai ta samu kanta da tunanin ko yaya masu soyayya suke ji oho, ita dai Allah be sa ta taɓa yin saurayi ba, balle taji me ake ji.
'to ke meye naki na soyayya, ke da kike karatu, ki maida hankali akan karatun ki, ko dan ganin Farincikin iyayenki' wata zuciyar ta gargaɗeta.
Ta ture tunanin komai, ta cigaba da karatun ta, ƙarfe ɗaya ta tashi, tayi alwala tayi sallar nafila, sannan ta nemi guri ta kwanta bacci.
Da Asuba ƙarar shigowar saƙo ne, ya farkar da ita, ta ɗau wayar ta sake dubawa.
"I pray Allah Khair for you now and always, include me in your prayers dear, you will always be in mine, have a wonderful Morning, i will be in your department to".
"Ikon Allah" shine abunda ta faɗa, ta ajiye wayar.
Abu kamar wasa kusan kwanaki uku, Ana turowa Abra ire-iren wannan saƙonnin, ba tare da ta san waye ake turo mata ba, da fari abun haushi yake bata, daga bisani kuma har Alla-Alla take, me turo saƙon ya turo, sai dai be taɓa kiranta ba.
Tayi saving ɗin lambar a wayarta da Mr. Unknown.
Ko da ta duba what's app ɗinta, labar ta bayyana a contact ɗinta, amma dp ɗin lambar babu hoto.
Ji tayi tana son yiwa lambar magana amma kasa, kuma gashi tunda ake turo mata saƙon, tunda tayi reply da wrong number, ba ta sake replying ba.
A wannan karon sai taji tana son yun replying, a message ɗin da aka turo mata, wanda yake cike da Adduoi da kuma koɗa ta.
Tayi Replying da "Ameen, Nagode sosai, amma da Allah ko zan iya sanin waye?".
Tun safe da tura message ɗin be mata reply ba, haka ana lectures amma hankalinta na kan wayarta, tana jiran ayi mata reply.
Sai bayan da ta koma gida, sannan akayi reply "Is someone, who want a chance to be with you for ever".
"May i know you please?" Ta kuma tanbayarsa.
"Sai kin sanni sanni sannan zaki so ni? Bana iya komai a rana idan har ban ganki ba".
Sai da ta ɗan ware idonta, sannan tace "A ina kake gani na, bayan bana zuwa ko ina sai Makaranta".
"Zan ajiye miki saƙo a what's app, wanda zai tabattar miki da hakan, aini bana ƙarya sai bisa kuskure".
Cikin hanzari ta shiga what's app ɗinta, aikuwa saiga saƙo a what's app ɗin, hotonta ya turo mata, tana tsaye a ƙofar ajinsu, saye da doguwar rigar abaya, wanda sam ba ta san an ɗau hoton ba".
Mamakine ya sake kamata tace "A makarantar mu kake kenan?".
"Neither No, Nor Yes"
Kamar tana gabansa ta tura baki ta tura masa "Please tell me".
"Me kike so in gaya miki?"
Abra ta tura masa da "Ka gaya mini idan a makarantar mu kake, sannan ka turomin hotonka"
"Idan na turo miki hotona na san ba zaki yadda ki soni ba"
"Meyasa?"
"Saboda ni mummuna ne, muni me ban tsoro, ke kuma kyakykyawa ce Masha Allah, kyawu mai ɗaukar hankali".
Abunka da farin shiga, Abra ta ture litattafanta gefe, ta gyara zama tana cigaba da hira da wanda ba ta san kowanene ba.
"Ni koma a ya kake, dan Allah ka turomini hotonka in gani".
"Gaskiya ina tsoron bayyana miki kaina, kar Major ya sa sojoji su zane ni, bani da ƙwari zasu iya yi mini illa".
Tayi reply da "Eyya, ai ba haka Abbi na yake ba, ba abunda zai sa ayi maka, ko hotonka ka nuna mini".
"Ba zan turo miki hotona ba, amma zaki ganni very soon insha Allah, ina Faris?"
Saida t buɗe baki da mamaki tace "Ya akayi ka san Faris, ko a Makaranta ba kowa ya san ina gaya masa wannan sunan ba".
"Yanzu idan nace miki da Faris kike magana me zaki ce?"
"Kaiiii Faris kuma, i dont think Faris will prank me with this".
"Are you sure my Angel?"
Gaba ɗaya Abra ta rikice, banda Abbi da Salman, ba wanda yake kiranta da Angel.
Da sauri ta ajiye wayar, ta fita falo, aikuwa ta tarar da Salman a kwance a ka kujera, yana danna wayarsa.
Da sauri ta ƙarasa, ba tare da tayi masa magana ba, ta miƙ hannu zata ƙwace wayarsa, caraf ya riƙe hannun, ya kalleta yace "Ya dai?"
"I want see your phone" ta faɗa tana tsare shi da ido.
"For what?"
Abra tace "I just want to see it".
Salman yace "aikuwa ba zaki gani ba".
"Please Faris, ka bani in gani".
"Me zaki yi da ita?".
"Kai dai kawai ka bani".
Miƙewa Salman yayi yace "tun da ba zaki faɗa mini me zaki da ita ba, na hanaki".
Diddira ƙafarta ta shiga yi, cikin shagwaɓa tana cewa "dan Allah Faris ka bani in gani"
Dariya yake yi yace "sai kin gaya mini me zaki da ita".
Shagwaɓa take sosai, wanda hakan ba ƙaramin burge Salman yake ba, ganin za ta yi masa kuka, ya sanya ya miƙa mata wayar ta sa.
Sai dai duk wani bincike da tayi, ba ta ga wani abu makamancin saƙonnin da ake tura mata ba a wayar ta Salman.
Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.
Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750.
[10/1, 2:40 PM] Abk: Ƙara rikicewa Abra tayi, ganin yadda ya tayara da motarsa ya bar gurin. Gaba ɗaya ta rasa abunda yakamata tayi a gurin nan, ihu za tayi ko kuka za tayi? Bata koma gurin cin Abincin nan ba, ta nufi department ɗin su, tana zuwa ta tarar da Salman da waya a hannunsa yana lelleƙawa yaga ta in da zai hango Abra.
Yana waiwayowa ya sukai ido huɗu da Abra da take ta tsuma.
Da sauri ya ƙaraso in da take yana faɗin "Wai ina kika shiga ne? Over 15 missed calls, amma baki ɗaga ko ɗaya ba.
Shiru tayi tana rarrraba ido, ta kasa ce masa uffan.
A ɗan hasale yace "ki yi mini magana ma, kin tsaya kina kallona".
"Wani lecturer ne ya ƙwace mini waya"
"Me ki kayi masa da ze ƙwace miki waya?".
"Wayata ce tayi ringing a aji, shine ya ƙwace mini wayar" tai maganar tana tsilli-tsilli da ido, saboda ƙaryar da tayi.
Salman dai kallonta kawai yayi, yace "to yanzu daga ina kike?".
"Cafeteria naje inci Abinci".
"To Yanzu kinci Abincin?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
"Wai meke damunki ne, gaba ɗaya kamar a tsorace kike fa" yai maganar yana kallonta.
gaba ɗaya tunaninta da hankalinta yana kan yadda za tai ta karɓi wayarta, tare da jinjinawa ƙarfin hali irin na Adnan.
'yanzu idan da gaske yake ya tafi da wayata Kaduna ya zanyi?' wata zuciyar ta tambayeta, nan da nan wank irin gumi ya shiga tsastsafo mata, na tashin hankali da damuwa.
A haka suka nufi mota suka kama hanyar gida, Salman ya lura gaba ɗaya akwai abunda yake damunta, amma ganinaa yayi-yayi ta gaya masa taƙi, kawai sai ya ƙyaleta.
Tafe suke a mota, Baby na sake gwadawa Ihsan yadda za suyi da Sojan nan idan sunje Abuja, Ihsan tai shiru tana sauraren Baby kamar 'ya da uwa.
Baby tace "Maza ki ɗakko waya, ki sanar masa gamu nan".
Jiki a sanyaye Ihsan ta ɗakko waya ta kira wata lamba, wadda tai saving da Yallaɓai.
Sai data kusa tsinkewa, sannan ya ɗauka "Hello beb ya?"
Tai ajiyar zuciya tace "Ya kake? Ya aiki?"
Yace "Alhamdilillah, nayi missing ɗinki sosai fa".
Ihsan tace "gamu nan zamu shigo garin Abuja".
With so much excitement yace "Wow, are you sure?".
Tace "Quiet sure"
Yace "Can't wait to see you Baby, sai kin zo, ki sauka a guest house ɗina, za'a samar maku da komai".
Tace 'Alright, sai mun zo".
"Ok bye".
Baby tace "hmm zaka ga tsiya, ko ka saki kuɗi ka ƙwaci kanka, ko muyi maka bariki irin ta yaran zamani".
Gaba ɗaya Abra jinta take kamar mara lafiya, saboda rashin wayarta, gashi gefe guda tana ta tunani unknown ɗinta, da yake turo mata saƙonni. Allah sarki ta san yanzu zai tayi mata Magana yaji ta shiru, ba ta reply.
Da magariba, Abbi ya dawo daga masallaci suna hira shi da Na'ima, gefe Salman yana duba wayarsa, Abbi yace "Hope dai karatu kake ba shirirta ba?"
Salman yace "eh Abbi, ina duba wani abu ne".
"Ai nasan hankalinka ne, kafi maida hankali a kan, shirita fiye da karatu".
Na'ima tace "Eh amma ai Abra ka yadda karatu take a waya, amma shi kace ba karatu yake ba" wani mugun kallo da yayi mata ne, ya sanya ta haɗiye Maganar ba shiri.
Abbi yace "Ni ban ma ganta ba gaba ɗaya, me take yi a ɗakine iya kaɗai?"
Salman yace "I don't know what's wrong with her today, gaba ɗaya kamar wani abu yana damunta".
"Kira mini ita".
Salman ya miƙe ya nufi ɗakinta, ko da ya shiga ya tarar tana zaune, ta zube littattafai a gabanta, amma tunani takeyi, ba karatun ba.
Yayi ajiyar zuciya sannan yace "Idan kin gama tunanin kizo Abbi yana kiranki".
Ta ɗaga kai ta kalli Salman, wanda tuni ya juya zaia bar gurin.
Jiki a sanyaye ta miƙe ta biyo bayansa, ta tarar da su gaba ɗaya a falo.
Ta ƙarasa gaban Abbi ta zauna yace "Gani Abbi".
"Daughter na, meke damunki ne? Duk muna nan a zaune, amma kin keɓe kanki a ɗaki, gashi fuskarki ta nuna, kina cikin damuwa".
Abra tace "Abbi bakomai, na gaji ne kawai"
Abbi yace "Anya kuwa? Ki gaya mini gaskiya".
Salman yace "Wayarta akai seizing a Makaranta"
Abbi yace "Subhanallah, how comes?"
Salman yace "Wai ringing tayi a aji, shine aka ƙwace, shine take ta wannan