Showing 87001 words to 90000 words out of 231718 words
Chapter 30 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
a duniya wallahi."
Rabi da ba fahimtar abun da yake cewa take ba ta ɗauki wayar da ya cillar cikin rawar jiki ta latsa, videon gawar Ihsan da bayanin abun da ya faru ya bayyana, ƙara ta fasa tare da zubewa a ƙasa sumammiya.
Na'ima na zaune a parlour ita kaɗai tana kallo wayarta ta fara ringing, murmurshi ta yi tare da ɗagawa.
"Hello Hajiya Maryam ya ake ciki ne?"
Daga ɗaya ɓangaren Hajiya Maryam ta ce. "Komai ya kammala ƙawata, ba dai level 1 take ba department of Mass communication?" Da sauri Mami ta ce. "Nan ne."
"To ki kwantar da hankalinki tamkar tsumma a cikin randa, wanɗanda na bawa aikin nan ba ni da haufi a kansu, gwanaye ne, ba su taɓa aiki an samu matsala ba, ke dai kawai da zarar aiki ya cika ki cika musu aljihunsu da ƴaƴan banki."
"Ba su da matsala da wannan, kin san kuɗi ba damuwata ba ne, ni dai kawai buƙatata ta biya, tsinanniyar yarinyar nan ta bar mini gida ko na huta, haba na gaji, na yi makircin na yi amma har yanzu ban ci nasara ba?"
"To daga wannan karon kin gama cizan yatsa ƙawata."
Murmushi Na'ima ta yi ta ce. "Da kuwa na zuba ruwa a ƙasa na sha." Maryam na dariya ta ce. "Ko acikin kwata ne ma ki zuba ki sha, duk a cikin celebration ne." Dariya suka yi a tare cikin tsananin farinciki.
Washegari 8 Salman yake da lecture, Abra kuma sai 10 hakan ya sa ba su tafi tare ba. Ƙarfe 1 Salman ya fito daga lecture, bayan ya yi Sallah ya nufi department ɗin su Abra, ya jira har ƙarfe biyu suka fito daga lecture. Yana tsaye a bakin class dinsu yana zuba idon ganin ta, amma har kowa ya gama fitowa bai ga ko mai kama da Abra ba. Cikin mamaki ya shiga dudduba cikin department ɗin nasu amma bai gan ta ba, ya kira wayarta ya fi sau 20 ba a ɗauka ba. Hankali a tashe ya kira Na'ima ya tambaye ta ko Abra ta dawo gida? Sanar masa ta yi tana zaune a main parlour tun 12 amma ba ta ga shigowar Abra ba, direbansu ya kira ya tambaye shi ko Abra ta kira shi ya zo ya ɗauke ta? shi ma ya ce masa ba ta kira shi ba. Hankalin Salman idan ya yi dubu ya tashi, duk inda yake tunanin zai ga Abra ya duba amma bai gan ta ba, ya tattambayi classmates ɗinta amma duk amsar ɗaya ce ba su gan ta ba, majority ma ce masa suke yi ba su san ta ba, tunda kullum cikin facemaks take. University ba secondary school ba, balle ya yi report ya ce bai ga Abra ba, to wa ma zai yiwa report ɗin?
Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.
Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750.
[10/1, 3:01 PM] Abk: Wani irin Yarrr Abra ta ji a jikinta, saboda rashin sabo, nan da nan ta ji ta shiga wani yanayi, da ba ta taɓa tsintar kanta a ciki ba.
Ya janyo hannunta zuwa kan ɗaya daga cikin kujerun gurin ya zaunar da ita.
Abra kam ji take tamkar ta nutse a gurin nan, saboda yadda kusancin su yayi yawa, ga wannan turaren na sa mai matuƙar kashe mata jiki.
Adnan ya fuskanci yadda Abra ta shiga fargaba na rashin sabo, dan tamkar kace kyat ta gudu, sai sauke numfashi take yi.
Cikin dakakkiyar muryarsa mai cike da kwarjini yace "Abraaah" yadda ya ja sunan na ta ne ha sake jefata cikin wani yanayi, me wuyar fassara.
"Look up" yai maganar yana sake tsareta da idanunsa.
Yayi ajiyar zuciya yace "Shikenan, ba gaisuwa ma, ko ba ki yi murna da zuwana ba?"
Ta girgiza masa kai.
"Talk mana, ya kike mini rowar muryar ta ki".
"Ina wuni".
A shagwaɓe yace "gaskiya sai kin kalleni".
Murmushi ne ya suɓuce mata, har sai da ta rufe bakinta tana dariyar.
Yace "Na baki dariya ko? In dai ni ne za ki sha shagwaɓa, dan shagwaɓaɓɓe ne ni, the only son of his parents, dan haka sai kin yi haƙuri".
"Ba ka da ƙanne?" Ta tsinci kanta da yi masa tambayar, ba tare da ta shirya ba.
Ya yi murmushi ya ce "Ni ka ɗai ne, shiyasa Aka takura mini in yi Aure, ko iyayena saga jikokinsu, ban yi planing ɗin yin Aure ba yanzu Abra, na fi son mai da hankalina akan aikina sosai, saboda yanayin aikina na rashin zama guri ɗaya, amma ina ganinki komai nawa ya canza, ni ban ma zaci zan iya soyayyar ba, dan ban taɓa yi ba, shiyasa na ke jin tsoro, Allah ya sa kar wani ya yi mink kutse" shiru Abra tayi ba tace Komai ba.
"Angel" ta ɗago ta kalleshi.
Yace "Say something mana".
"To me zance?" Yadda tayi maganar ne, cikin halin na ta na shagwaɓa ya sa ya sake ƙure ta da ido.
"Abra kina son Adnan?".
Jin Maganar ta yi a bazata.
"Ki gayamini, ba na son doguwar magana, amma saboda ke sai surutu na ke, duk na gaji, kuma kin ƙi yin Magana".
"Ba ka sha ruwan ba" Abra ta faɗa tana ƙoƙarin basar da Maganar da yake yi.
"Ni ba ruwa zan sha ba, ki gaya mini idan kina so na?".
Tura baki tayi, ta ƙi magana, sai ma ta nuna kamar ya takura mata.
Hannayenta ya sake haɗewa a cikin nata, yana ƙurawa fuskarta ido, "Abra talk, do you Love me?"
Ɗago fararen idanunta ta yi tace "ka sakar mini hannuna".
"Sai kin bani amsa tukuna" wata irin kunya ce ta mamaye Abra, ga kwarjini da yayi mata.
"Shikenan, bari in tashi in koma, in gayawa Abba na kince ba kya sona" yai maganar yana ƙoƙarin tashi tsaye.
"A'a nifa ba haka nace ba" tai maganar kamar me koyon magana".
"To me ki ka ce?".
"To ni kunya na ke ji"
Adnan ya zauna yace "Na rufe idona, gaya mini".
"A'a ba Yanzu ba"
"Sai Yaushe?".
Tace "in ba ka nan" murmushi yayi, gaba ɗaya yarinyar ba ta da wayo.
Ya ce "Shikenan, tun da kin mini wayo. Kin yi kyau sosai kamar in tafi da ke gidana daga nan".
Lumshe idonta tai, ta na jin daɗin yabonta da yake yi.
"My wife, ina Faris ne?"
Murmushi tayi tace "ya tafi ball"
"Da alama, dan da yana nan wataƙila tare zaku zo zancen"
Ba ta san lokacin da dariya ta ƙwace mata ba, ƙasan zuciyar ta na fargabar kar ma Salman ya dawo ya tarar da Adnan, dan zai iya ɓata mata rai, kuma ga Adnan ba sa'an Faris ɗin ba ne.
"My wife, zuba mini ko ruwan ne in sha".
Ba musu ta fara ƙoƙarin zuba masa ruwa, ya zuba mata ido yana kallon yadda take komai a nutse.
"Which tribe are you?" Ya tambayeta.
Abra ta ɗan yi Jimm sannan tace"Hausa Fulani".
"I doubt" ya faɗa a taƙaice.
Tace "Why?".
"You are very beautiful My Wife, kamar ba kya jin Hausa ma, gaskiya zan so in ga Abbi da wuri, kar wani ya rigani, a sa ranar Aurenmu nan kusa".
Zaro ido tayi tace "Aure kuma?".
"Yes my dear, ko ba kya sona ne?"
Jiki a sanyaye tace "Abbi ba ze mini Aure yanzu ba, ni karatu na ke so".
Murmushi yayi bece komai ba, ya kai ruwan bakinsa yana sha, idanunsa akan Abra.
Hannunsa ya miƙa ya riƙo ɗan ƙaramin hannunta cikin nasa, yana ɗan murzawa a hankali, Abra tai tsuru-tsuru.
Adnan yace "kinga yadda ki ka haskani, nifa cewa Hajiyata nai zan Auri balarabiya, zaki Auri baƙi?".
Zame hannunta tayi daga nasa tace "bari in barka kaci Abinci".
"A'a zauna inci ina kallon ki, Abbi yana nan ne?".
Abra tace "A'a".
"Ok na gaisa da Maman kan in wuce".
Adnan ya ci Abinci yana ta santi yana yabawa Abra, yau gaba ɗaya Abra Adnan mamaki ya bata, farkon mu'amalarsu ta ɗauka ba shi da mutunci, amma yau ta ga saɓanin abunda take tunani.
Ya ce ta kira masa Maminta su gaisa, Abra ta ji daɗin hakan, dan dama a takure take.
A falo ta tarar da Hajiya Na'ima, ta kalleta tace "ya na ganki kamar korarriya?".
"Mami wai gaishe ki ze yi".
Hajiya Na'ima tayi murmushi tace "Masha Allah, babu laifi, amma dai ba zuwa ki kayi kina wannan zazzare idon ba, kamar wadda za'a kashe".
"Mami cewa yai wai sai na gaya masa idan ina son sa".
"To ke kuma sai ki ka ce masa me?".
"To ai Mami kunya nake ji".
"Kunya, waike yaushe zakiyi wayau, kamar ba mace ba, sam baki da wayo, in kika ce kina son sa gutsurar ki zai yi?"
Shiru Abra tai ba tace komai ba.
'duk jarabarki da gidan nan dai, dole kiyi aure ki bar shi, gara tun wuri ma ki san abun yi.
Ki je ki ɗakko mini mayafi na, ki shigo da shi". Abra ta kaiwa Mami mayafinta, tana tunanin tayaya za ta gayawa Adnan wai tana son sa?.
Haka taje ta taho da shi falon.
Tun da yai Sallama Na'ima ta ƙare masa kallo, Abra ba ta fi iya ƙirjinsa ba, dogon namiji ne, duk da baƙi ne amma yana da haske, gashi Kyakywa Masha Allah.
A ranta tace "taɓ, wannan ya za tai da shi, oho mata ma koma dai menene sai ta bar mini gida kawai'.
Suka ƙarasa falon, Adnan ya kame a kan kujera ya ɗan sunkuya ya gaida Hajiya Na'ima.
Cikin mutunci ta amsa ta ce "Kai ne sirikin namu?".
Adnan yayi ɗan murmushi yace "Eh ni ne".
Ta ce "Masha Allah, ya sunanka?"
"Adnan Aliyu Matawalle".
"Madalla, insha Allah idan har dagaske ka ke, in megidan ya dawo, za'a sanar masa".
Adnan yace "Nagode sosai da sosai, kuma insha Allah ni da gaske nake, da zarar an bani dama zan turo magabatana ayi magana".
Zaro ido Abra ta yi, Hajiya Na'ima tai wurga mata wata irin harara. Wadda ta sa Abra shan jinin jikinta.
Nan dai ta gama yi masa tambayoyi, duk ya amsa mata, sannan suka yi sallama Abra ta tafi raka shi.
Har gaban motarsa ta raka shi, sai dai kanta a ƙasa ba ta iya cewa uffan.
A jikin motar ya tsaya yana cigaba da kallon yadda dressing ɗin jikinta ya karɓeta matuƙa "My wife, gashi zan tafi, amma ba ki gaya mini abunda ke ranki game da ni ba".
Murmushin da ya zame mata ɗabi'a, shi ta cigaba da sakar masa.
Adnan yayi ajiyar zuciya yace "Yaushe zan dawo?"
"Gobe" ta bashi amsa.
Murmushi yayi yace "Lallai kin kamu da son ɗan baƙin mijin nan na ki, tun da har kike son in dawo gobe".
Ɗauke kai tayi, kamar ba ita tace ya dawo goben ba.
"Wai Nikam da wa kike kama ne, a tsakanin Mami da kuma Abbinki?".
Tace "Da Faris nake kama"
"Shi Faris ɗin da wa yake kama?"
"Da ni" ta bashi amsa.
Dariya yayi yace "da alama zan sha fama, haryanzu kina fama da yarinta, zan koma My Angel, insha Allah zan dawo in ga Abbi, nan kusa nake son muyi Aure"
Ɗan yamutsa fuska tayi, ta kau da kai gefe.
"My wife, ya naga kin haɗe rai haka, ko ba kya sona ne?".
Ta girgiza kai, yace "to meyasa kika haɗe rai?"
"Makaranta fa" tai maganar idonta na tara hawaye.
A ransa ya ce 'lallai wannan yarinyar an shagwaɓata da yawa, komai kuka'
"To ai zaki cigaba da makarantar ki".
"Ni ba na son in tafi in bar su Abbi da Faris".
Yace "idan na Aureki sai in ginawa Faris ɗaki a gidan, tun da ba zaki iya rayuwa babu shi ba" yai maganar cikin gatse, dan ya fara ƙuluwa da yawan zancen Faris ɗin nan.
Ya saka hannu a aljihunsa ya ɗakko bandir ɗin kuɗi ya miƙa mata ya ce "gashi nan, kwalliya tayi kyau, Abinci yayi daɗi sosai, ga wannan kya saka a jakarki".
"A'a ka barshi nagode".
"Ba'a yi mini musu ai, ki dena mini musu bana so, karɓi"
Ta sake girgiza kai a karo na biyu.
"Ki karɓa bana son musu" yai mata wata razananniyar tsawa, wadda sai da ta ruɗe gaba ɗaya, ta karɓi kuɗin ba shiri jikinta yana tsuma.
Ya buɗe motarsa ya shiga ya zauna, ya kuma ɗagowa ya kalleta, kamar ba shi yayi mata tsawa yanzu ba ya ce "Ina sonki Angel, ki kula mini da kanki, I will call you when I reach home" ya kashe mata ido ɗaya, ya ja motarsa ya nufi barin gidan.
Ta jujjuya uban kuɗin da yake hannunta, ta koma cikin gida.
Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.
Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750
Part ɗin Hajiya Na'ima ta wuce, ta tarar da ita a bedroom.
Tana ganin Abra tace "Lallai Yarinya kin iya zaɓen miji, bari Abbin ya dawo, a san abun yi".
"Mami nifa bana son Aure Yanzu".
Sheƙeƙe Hajiya Na'ima ta kalleta tace "Au zaman jiranki za ai har sai kin shirya Auren? Ko kuma jiƙaki za muyi a ruwa mu sha? Aure kuwa dolenki ba bu fashi".
Jiki a sanyaye ta miƙawa Mami kuɗin da Adnan ya bata.
Ta kalleta tace "wannan kuma fa?"
"Bani yayi" tai maganar a sanyaye.
"Roƙarsa ki kayi ko?" Da sauri Abra ta girgiza kai tace "A'a Mami, wallahi ban roƙe shi ba, cewa yayi dole sai na karɓa".
Na'ima tace "Shikenan, ajiye mini su a kan side bed".
Ta ajiye mata kuɗin ta juya ta bar ɗakin.
A ɗakinta kuwa, wayarta ta ɗauka ta duba, ta tarar da saƙonnin unknown ɗinta.
Murmushi tayi ta fara yi masa reply, daga bisani kuma saƙon dodonta ya shigo wayar, wato Adnan.
"I miss your fume my cuty" tura baki tayi kamar tana gabansa tace "ba zan reply ba, bayan kayi mini tsawa ɗazu".
General Ibrahim kuwa kamar jira akeyi, shedu suka dinga fitowa a kansa, a kan zagon ƙasar da ya dinga yiwa harkar tsaro lokacin yana bakin aiki.
Major Khamal Khamis, zai iya cewa ya fi kowa farincikin wannan kame da akayi, dan ya daɗe da sanin da hannun General Ibrahim a ayyukan ta'addanci, sai dai babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da ze iya bayyanawa, wadda za ta sanya a kama General Ibrahim ɗin da laifi kai tsaye.
Aka same shi da badaƙalar kuɗin siyan makamai, a gwamnatin baya, tare da wasu manya -manyan ƙasa, da wasu ƙusoshin gwamnatin da ta gabata, abun takaici kuma sune da a cikin Gwamnatin da take mulki.
Abun takaici, Manyan mutane ne, da al'umma suke yiwa kallon jagorori, kuma madubi, wanda suka saka ran samun sassauci daga gare su, ashe sune suka maida harkar tsaro, harkar kasuwancinsu. Suka yi sanadiyar tarwatsewar al'umma da dama da aka daɗe ana ginawa.
Tofin Allah tsine da General Ibrahim da iyayen gidansa, da kuma yaransa suka dinga samu kuwa ba a Magana, tabbas ya ci amanar ƙasa, mussaman da a dalilinsa rayukan iya sojojin da suka salwanta ba adadi, ba'a ma kallon wancan laifin da ya aikata, ni lalalata da kuma kisan kai, tsabar Mamaki da takaicin taƙadirancinsa ya hana mutane magan, sai zuba ido domin suga, irin matakin da za'a ɗauka a kansu.
Sai magariba Salman ya dawo daga gurin ƙwallo, dan sai da yayi sallar magariba sannan ya dawo gida.
Sashen Mami ya wuce da kofin juice a hannunsa.
"Sai yanzu ka dawo?"
"Na tsaya nayi Salla ne Mami, baƙi mukayi a gidan ne? Naga guest room da kayan ciye-ciye, suwaye suka zo?".
"Abra ce tai baƙo".
Turus yayi yana kallon Mami yace "Wane irin baƙo kuma?".
Hajiya Na'ima tace "Ah, saurayi tayi, shine ya zo gurinta, kuma very soon zai zo yayi Maganar Aure".
"Impossible, akan me za'ai mata Aure? Idan har ina raye ba wanda zai auri Abra" yayi Maganar jijiyoyin kansa na miƙewa.
Na'ima ta ce "ba ka da hankali ne? Uban me za'ai da ita idan ba tayi Aure ba? Ai gara tai Auren ta bar mana gida, ko mahaifinka ya maida hankali sosai a kanka".
"Ba wanda zai Auri Abrah Mami? Abra tawa ce, Wallahi duk wanda ya kuma zuwa gidan nan da sunan yana sonta, sai na masa illa".
A fusace ta miƙe ta ce "Salman, ka san me kake faɗa kuwa? Me kake nufi da Abra taka ce?".
"Mami, let me voice out my secret to you, Wallahi Mami am in love with my sister, ina kishinta, Mami tun lokacin da kika gaya mini ba ke kika haifeta ba, na gane son da nake mata ba na 'yan uwanta bane kawai, Auren Abra nak..... Marin da ta sauke masa ne, ya hana shi ƙarasa Maganar, ya dafe kuncinsa yana kallon Hajiya Na'ima.
"Baka isa ba Salman, Wallahi kayi kaɗan, ni zaka tonawa asiri, yarinyar ta girmeka da shekaru uku, kace mini ita ka ke so, kwata kwata shekarunka nawa zaka yi wani zancen soyayya, ko dan kana ganin ka haka da girman jiki?, yarinyar da ta zame mana alaƙaƙai nake neman maraba da ita.
Wato so kake ka tona mini Asiri, mahaifinka ya san na gaya maka ba ni na haifeta ba ko? Wai kai banda hauka irin na ka ka manta ubanku ɗaya da ita? Karuwar babanka ce ta haifeta ta yaya za kuyi Aure?".
Girgiza kai Salman yayi yace "A'a Mami, Abbi ba ze taɓa aikata abunda kika faɗa ba, ina nan akan bakana Mami, Abra nake so, Ina sonta Sosai".
"Shut up Salman! Wato ba zaka dena wannan banzar Maganar ba ko? Gara yayi ya dawo in sanar masa, ayi a aurara da ita in ga ta tsiya, idan kuma shirya tona mini Asiri ka yi a gurin mahaifinka ga fili ga mai doki. Amma duk jarabarka Wallahi ba zaka auri yarinyar nan ba, dole ta auri wani ta bar gidan nan".
"Am sorry Mami, amma babban kuskuren da za'a aikata shine a aurawa Angel wani ba ni ba, zan iya aikata duk abunda zuciyata ta raya mini, dan cinma burina, she's mine" ya faɗa tare da nuna ƙirjinsa da yatsa, daga nan ya fice daga ɗakin.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta ce "tirƙashi, lallai Salman ba ka da hankali, ba za ka janyo mini sakiyar da babu ruwa ba, dole in maganinku gaba ɗaya.
Major Khamal kuwa, cike da farin ciki, gefe guda kuma baƙin ciki ya dawo Kaduna, dan ji yake ko ba duka, an samo lagon rashin tsaron da ya addabi ƙasar mu, daga gefe yana sake jinjina tare da baƙi cikin samun bara gurbi a cikin rundunar tsaro.
Bayan Adnan ya sauka a Kaduna, har dare Abra ba ta neme shi ba, sai shi ya nemeta duk da kuwa yadda tai kewarsa.
Ita Abra babban abun da ya dameta rashin ganin Faris, taje ɗakinsa ta tarar ya rufe ƙofa, dan haka ta haƙura ta koma ɗakinta.
Tana zuwa ta tarar da kiran Adnan na shigowa wayar