Showing 39001 words to 42000 words out of 231718 words

Chapter 14 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14694

knowledgeable as you"
Jannat ta taɓe baki tace "Amma karatun na yawa, data rage dai"
Khairy tace "Ta ya ya karatu zai yawa Jannat Yusuf?" Jannat ta watsa hannunta tare da Miƙewa tsaye tace.
"It's just a suggestion"
"Oh, i see" cewar Khairy.

Da ga nan Jannat office ɗin staff ɗin makarantar ta yi, domin ya ce ta zo yana son ganinta idan har tana son passed all her exams, a hanya ta tsaya ta fesa turare a jikinta.

Abra Idanunta a ƙasa suna zaune Salman ya shigo hannunsa riƙe da takeaway da rubber ice cream, idanunsa akan Abra.
"Salman, you are not seen unless you bring Abra something to break" Khairy tayi Mgnar tana dry, Murmushi kawai yyi yana girgiza kansa can kuma yace.
"To ɗan matsa, aku Sarkin surutu" Khairy tace "Oh, haka zaka ce ko?" Bai ce komai ba ya zauna kusa da Abra dake Murmushi tana buɗe littafin English na gabanta yace.
"Yaya ya zaki karatu ne?"
Ta buɗe masa Idanunta tace "like how?"

Ya kalleta ya kalli littafan gabanta yace "kamar dai haka" lumshe idanunta kawai tayi, yabi zara zara eyes lashes ɗin ta da kallo kafin yace.
"Me za kici? Meat pie? Cake? Dunot? Shawarma? Pizza? Hamburger? Me za kici Yaya tell me"
Kamar zatai kuka tace
"Please Faris surutun yana yawa" shima ya marairaice mata yace "kefa kawai na kewa, yanzu me za kici"
Tace "I'm full, ina karatu yanzu..."
Kafin ta Ƙarasa maganar taji hannunsa cikin bakinta ya sanya mata cake a baki, da sauri ta amshi cake ɗin tana zaro idanunta waje, bayan ta ciye ta kallesa muryarta na harɗe wa tace.
"Faris"
"Angel" Salman ya faɗa yana kashe mata Idanunta ɗaya tace "but kasan ban fiya son zaƙi ba ko?" Yace "i knw Yaya, ni wlh karatun nan yana yawa, nifa ina mace ba ruwana da wani karatu tunda aure zan"
Shiru tayi masa, a hankali yace "nifa ba zan fita ba Yaya, sai kin faɗa min abinda za kici" ta girgiza kai tace.
"Bani da appetite, kuma ban san ɓata hannu"

Kallonta ya yi sai kuma ya girgiza kansa, a hankali ya dinga bata cake ɗin tana ci, yana bata exotic tana sha har taci sosai.
Kallonsa tayi sai kuma ta saki murmushi tace.
"Thank you Ɗan ƙanina"
"Uhm" yace kawai kafin ya miƙe har yaje waje sai kuma ya tsaya da ƙarfi yace.
"Angel" da sauri ta ɗago kanta tace "What happening Salman?" Gira ya ɗaga mata tare da kashe mata idanu yayi waje da gudu.
Ta girgiza kai tace
"Allah ya shirya"

A sati na gaba su Abra aka fara exam, Salman sam bai damu da karatu ba, ita kam ta dage tana fata ace wannan karan Mami ta sanya mata albarka idan ta ɗauki 1st position, Salman yana sane yaƙi mai da hankali sbd ya faɗi wanwar ta inda position ɗin Abra zai fi nasa.
Yau ma a gajiye Abra suka dawo daga Islamiyya ko kayanta bata cire ba ta faɗa saman bed sai bacci. Har aka kira magrib tana bacci.
Salman na zaune da Abbi wanda ya dawo gari a ranar cikin kulawa Abbi yace "Salman ina yayar taka?" Salman ya ajjiye handle ɗin game ɗin da yake yace "Tun da muka dawo islamiyya bata fito ba"
Abbi ya yi shiru sai kuma yace "is she alright?" Salman yace "not sure Abbi" yace "ok jeka kirata, zamu je shopping daga nan Granny na son ganinku sai mita take fa"
Salman ya miƙe daga shi sai farar vest wacce ta kama cikinsa wanda ya buɗe alamun zama saurayi, sai 3Qauter a jikinsa kai tsaye ya nufi bedroom ɗin Abra.
Abra na tsaye gaban mirror ta fito daga wanka, tana ƙoƙarin saka lace rapped bra a jikinta taji Salman na faɗin.
"Yaya.. Yaya..Yaya"
Gaba ɗaya ruɗewa tayi gashi ƙofar a buɗe take bata saka mata key ba,
Ruɗewar da tayi yasa bra ɗin kwacewa daga hannunta ta faɗi, daidai nan kuma Salman ya shigo yana faɗin "Angel..." Bai ƙarasa faɗa ba yaji ta fasa wata ƙara tace "No!! Salman get out I'm naked.......


*We are still in free pages.... A koda yaushe zamu iya tsayawa... Ka hanzarta biyan kuɗin ka domin a dama dakai.. littafin daban yake.. kada ku manta marubuta uku ne suke rubuta muku wannan Labarin Nimcyluv🤘🏼 Ayushercool🍷Zee kumurya💘*
[9/30, 8:55 PM] Abk: *DARE DA DUHU*

_Brigh pens✍️_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee Kumurya

                               P11

Domin samun complete litattafanmu, ku yi following ɗin wannan accounts ɗin a Arewabooks

https://arewabooks.com/chapter?id=6316f4af434cfeb9e7fe2949

https://arewabooks.com/u/nimcyluv
https://arewabooks.com/book?id=

Elegant online writers

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.





Cak ya tsaya kamar wanda aka dasa shi a gurin cikin rashin sanin abun yi, shi kansa ya rud'e balle kuma ita, cikin rawar murya ya ce. "I'm
.so.. sorry Yaya."

Juya masa baya ta yi da sauri tare da ƙanƙame jikinta guri guda, kamar za ta yi kuka ta ce. "Salman! I said get out please!"

Bai ce komai ba ya juya ya fice daga ɗakin cikin wani irin yanayi na sanyin jiki.

"Ya dai? Ko wani abu ne ya same ta?" Abbi dake duban sa bayan ya dawo ya zauna, ya faɗi haka.

Daidaita nutsuwarsa ya yi ya ce. "Nothing Abbi, tana wanka ne."

Gyaɗa kai Khamal ya yi ya cigaba da latsa wayarsa.

Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi jin ƙarar buɗe ƙofa tare da fitar shi, kamar mai tsoron wani abu ta juyo a hankali, saurin ɗaukar brar ta yi ta saka ta ƙarasa shiryawa, cikin wani hadadden less wanda aka yi masa ɗinkin tea bubu. Ta yi kyau sosai duk da ba wata kwalliya ta yi ba, bayan ta feshe jikinta da tsadaddun turaren da Abbinta yake siyo mata, ta ɗauki medium vail ta yafa sannan ta fice, bayan ta ɗauki Small handbag ɗinta.

Tunda ta fito Na'ima ta kafe ta da ido wanda hakan yasa ta jin kamar za ta faɗi, Salman ma jin ƙamshinta ya ɗago kansa a hankali yana kallon ta, a ransa yana yaba tsananin kyawun Yaya tasa. Ita kuwa Na'ima baƙin ciki ne ya cika mata zuciya, na kyawun da Abra take shi da kuma takaicin yanda Khamal yake siya mata suturu masu kyau da tsada, gami da duk wani abu na kwalliyar ƴa mace. Duk abun da ya gani indai na gayu ne sai ya siyo mata, idan ta yi magana ya ce, ai ita ƴa mace ƴar kwalliya ce, idan bai siya mata ba wa zai siya mata? Ita ma babu yanda ta iya haka take siya matan saboda gudun kar ya gane har yanzu ba ƙaunar Yarinyar take yi ba.

"Kai Masha Allahu laƙuwwata illabillah, ƴata tafi kowa a kyau da iya ɗaukar kwalliya, gaskiya sai ɗan Sarki ko ɗan gwamna zan bawa, dan Ƴata mai tsada ce."

Na'ima ta faɗi haka cikin murmushin da bai kai zuci ba.

Sai a lokacin Khamal ya ɗago ya dubi Abra, cikin murmushi ya ce. "To Allah ya kawo mana na gari." Lumshe ido kawai Salman ya yi ya buɗe bai ce komai ba.

"Sannu da hutawa Mami."

"Yawwa Daughter, kun dawo daga islamiyya ina sama ina shiryawa, sai yanzu na sakko, ya makarantar?"

"Alhamdulillah."

Ta faɗa cikin siririyar muryarta.

Mayar da duban ta, ta yi ga Abbinta ta yi masa sannu da gida, ya amsa cikin fara'a sannan ya miƙe ya ce su huce. Abra da ba ta inda za su je ba ta yiwa Mami sallama ta fara fita, ita wannan shiryawar da ta yi da niyyar ta tambayi Abbinta za ta gidansu wata friend ɗinta, dan su yi totorial akan last paper ɗinsu da za su yi ranar Monday ta literature. Amma kasancewar ba ta saba musu ba sai ta hak'ura ta fasa zuwan, tunda Abbi ya ce za su fita.

"Kai kuma lafiya kake ta bin mutane da ido?"

Cewar Na'ima tana duban Salman.

"Lafiya Mami, bari mu wuce sai mun dawo." Ya yi maganar tare da miƙewa ya fice.

Na'ima ta ce. "To Allah ya kiyaye, sai kun dawo ɗin."

"Yaya! Angel."

Salman ya faɗa bayan ya fito cikin ƙoƙarin cire moment ɗin ɗazu daga cikin zuciyarsa, na ganin ta nicked da ya yi.

Abra dake tsaye ta ɓata fuska ba ta ce komai ba.

Ya ƙaraso ya tsaya a gabanta ya ce, "Kin yi kyau sosai." Tana ware manyan idanunta a kansa ta ce. "Ko? Kai da ba ka gajiya da faɗar haka as always." Ya ce. "Ai hakan ne shi yasa, kullum fa ƙara kyau kike yi da wani irin fresh kamar sabuwar amarya." Ta ce. "Kai kuma fa? ai kai ma haka Handsome ɗin Mami." Murmurshi ya yi cikin jin daɗin yabon shi da ta yi. A haka khamal ya fito ya same su suna hira gwanin sha'awa.

Wani haɗɗaɗen gurin sayar da snaks da ice_cream dake cikin Nasarawa Khamal ya kai su, ya yi musu order na abin da kowa yake so. A hankali Abra take shan Vanilla ice cream ɗin dake gabanta, duk da ba wannan ne first time da suka saba zuwa irin guraren nan ba, amma duk a takure take jin kanta. Sai gyaggyara mayafinta take ta kasa zama guri ɗaya. Salman dake gefenta yana lura da yanayin da take ciki ya ce. "Ko in baki a baki ne, na ga kamar ƙiwar sha kike yi?" A hankali ya yi maganar yanda Khamal ba zai ji ba.

Tura masa baki kawai ta yi ba ta ce komai ba. Murmurshi ya yi ya cigaba da cin meatpie ɗinsa, lokaci ɗaya murmushin ya ɗauke daga fuskarsa sakamakon four eyes da suka yi da wani matashin Saurayi da yake pacing ɗinsu, wanda ya ƙurawa Abra ido kamar zai lashe ta.



Wata Uwar harara ya galla masa ya ce. "Yaya tashi ki je Mota ki ƙarasa sha, kafin Abbi ya gama mu wuce." Ya ƙarashe zancen tare da ajiye meatpie ɗin hannunsa, dan ji ya yi gaba-d'aya ya fice masa daga rai.

Da mamaki take duban shi amma ba ta ce komai ba, Khamal da ya ji abun da Salman ya faɗa, ya dube shi ya ce. "Me yasa zaka ce ta tashi?"

"Abbi na ga sai kallon ta ake yi a gurin nan, kar ido ya yi mata yawa ta je ta ƙware."

Ya yi maganar da iya gaskiya. Murmurshi Khamal ya yi, cikin ransa yana jinjina al'amarin Salman, yanda yake acting akan Abra sai ka ce shine sama da ita.

"Ki tashi Please." Ya faɗa yana narkar da idanunsa a cikin nata.

"Ka fiya takura Faris, mu jira Abbi ya gama mana, sai mu fita gaba-d'aya."

Ɗan ƙaramin tsaki ya ja idanunsa akan Matashin nan da ya kasa ɗauke idonsa daga kan Abra, wani irin kallo yake wurga masa. Har suka bar gurin mutumin nan bai daina kallon Abra ba, Salman kuwa sai cika yake yana batsewa. Sai da Abbi ya yiwa Mami da su Ammi take away sannan suka tafi. Suna hanya aka yi Sallar Magriba, hakan yasa Abbi tsayawa a wani Masallaci suka yi Sallah shi da Salman sannan suka wuce.

"Wai kai lafiyarka kuwa kake ta ɓata rai?"

Abra ta tambayi Salman cikin kulawa, bayan sun fito daga cikin Mota lokacin da suka ƙarasa gidan Ammi."

"Babu komai, Ni ma kawai a haka na ji ni."

"Ka fiya rigima kai dai"

"Na kai ki?"

"Ka ma fi ni, Ni dai bana son ganin ka a haka, Please ka saki ranka ka ji ɗan ƙanina." Ta ƙarashe maganar cike da shagwab'a.

"Sai kin ce mun Yaya gaskiya." Ya yi maganar yana wani shan kunu.

Dariya ta yi ta ce. "Ba zan faɗa ba ɗin, Sarkin son girma." Ba ta jira amsar shi ba ta wuce cikin gidan. Murmurshi ya yi tare da shafa sumar kansa ya bi bayanta.


Da sallama suka shiga main parlour'n gidan, Ammi tana tsaye a dinning area tana yayyankawa Baffa fruits, Hajiya kuwa na kame akan kujera tana jan carbi mai dubu, da alama ba ta jima da idar da Sallah ba dan sanye take cikin Hijabi, ta ƙara tsufa amma har yanzu bakin nan nata yana nan bai mutu ba.

Cikin fara'a da murnar ganin su Ammi ta amsa musu tare da yi musu sannu da zuwa, Ƴaƴan Shureim guda biyu da suka zo Weekend suka taho da gudu suna faɗin. "Oyoyo Yaya da Ya Salman." Abra ta ajiye ledar hannunta ta rungume su a jikinta cikin murmurshi. Salman ya shafi kansu ya ce. "Oyoyo ƴaƴan gidan Ammi, kodayaushe aka zo gidan Ammi a gan ku."

Granny dake bin su da kallo ta cikin White medicated glass ɗin dake idonta ta ce. "Su masu zumunci kenan ai, ku kuwa uwarku saboda baƙin hali ba ta barin ku zuwa, ita ba ta zo ba ku ba ta bar ku kun zo ba." Ta taɓe baki ta ce. "Ba ruwana ma dai, lazimi nake yi bazan ce uffan ba sai na gama tunda babu kyau ana yi ana surutu."

Salman ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, ya ce. "Ai kin ɓata lazimin tunda kin riga kin yi maganar, sai dai ki sake daga farko."

"Ka ci kanka, ni ba zan biye maka ba, sunan Allah nake ambata bana wani garɗi Khamalu ba ko na wata garɗiya Nai'ma ba, ato, a sarara mun a bar ni in yi abuna cikin nutsuwa."


Abra ta ƙaraso cikin parlour'n hannunta riƙe da na Fadeela, Fadil kuma ya ɗauko ledar da ta ajiye, zama ta yi a kusa da Granny ta gaishe ta, ɗaga mata hannu ta yi tana ƙara fito da carbinta daga cikin hijabi tana ɗaɗɗaga shi, ita a dole a ga lazimi take yi ba za ta yi magana ba. Murmurshi Abra ta yi ta miƙe ta ƙarasa gurin Ammi ta gaishe ta, Ammi ta rungume ta tare da amsa masa mata. Daga nan ta wuce bedroom ɗin Ammi dan yin Sallah.

Sai wajen goma da wani abu suka bar gidan, kamar kar su tafi saboda yanda ake tarairayar su, da yanda suke cin dariyar Granny, har Baffa ma ya sakko anata hirar da shi tare da Khamal wanda ya shigo daga baya, bayan sun gama gaisawa da mai gadi. Granny sai mitar rashin zuwan su gidan akai_akai take yi, idan Khamal ya ce makaranta ce ta sa ba sa zuwan sai ta ƙanne ido ta ce. "To ni ina ruwana ma da zuwansu da rashinsa, tunda ba wata tsiyar suke mini ba in sun zo? Sai dai ma su sace mun ɗan tsirena da kilishina, da ɗan Albarkana yake siyo mini ban sani ba." Da za su tafi ta ce kar su tafi su zauna su kwana, Khamal ya ce gobe Monday akwai school sai dai in an yi hutu za su zo su yi hutunsu a nan insha Allahu. Sai ta tsuke fuska ta ce, "Allah ya raka taki gona."

Abra tana son su je gidansu Ammi sosai, saboda nishaɗi da farincikin da take tsintar kanta a ciki, gashi ai ta nan_nan da su ana nuna musu ƙauna da kulawa.


Washegari da sassafe Khamal ya wuce Abuja gurin aiki.




G.Y BULAMA HOSPITAL AND MATERNITY.

A hankali take tafiya cikin sanyin jiki, tana sanye cikin fararen uniform na Nurses. Ƙofar wani office ta tura a hankali ta shiga bakinta ɗauke da sallama.



Wani baƙin likita dake zaune a mazauninsa shi kaɗai a cikin office ɗin, yana operating system ya amsa mata Sallamar ba tare da ya ɗago ba. Ƙaraso ta yi ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake gaban table ɗin.

"Barka da safiya Doctor."

Sai a lokacin ya ɗago tare da yin murmurshi ya ce. "Kin tashi lafiya Jamila? Ya su Mama?"

"Lafiya ƙalau, na zo ai Sister Basira ta ce mun ka zo kana nema na."

Ya ce, "Eh, me yasa yau baki zo akan lokaci ba?"

"Abun hawa ne ban samu da wuri ba."

"Da kin kira ni ai, da na biyo na ɗauke ki."

Yaƙe kawai ta yi ba ta ce komai ba, ɗan ƙura mata ido ya yi na sakanni, cikin kulawa ya ce. "Kamar wani abun yana damun ki Jamila." Numfashi ta sauke ta ce. "Babu komai Doctor." Ya ce. "Ban yarda ba, ga damuwa nan ƙarara a fuskarki."

Cikin yanayin damuwa ta ce. "Akwai abun da yake damu na, amma bazan iya faɗar shi ba."

"Saboda me? Please Jamila tell me, har kin saka hankalina ya fara tashi."

"Ba fa wani abu ne, kawai dai ina tsoron yin maganar ne."

"Oh My God! Tsoron me? Ni ne fa? You are free to tell me everything da yake ranki, ko baki yarda da ni ba ne?"

Ɗan jim ta yi kamar mai nazari sannan ta ce. "Yardar da na yi da kai ne yasa zan faɗa maka abun da yake raina, wani abu ne ya daɗe yana damu na, amma na rasa da wa zan yi sharing ɗinsa, Doctor! Abun da yake faruwa a cikin asibitin nan ya yi yawa, zaluncin ya yi yawa, Matar nan da Doctor Bulama ya hana ka, ka duba ta jiya mai naƙudar nan da ta matuƙar galabaita akan ba su biya kuɗin gado ba ta rasu, bayan ƴan'uwanta kuma sun yi fafutuka sun kawo kuɗin, wallahi jiya da ita na kwana a cikin raina, lokacin da ta zube a cikin reception ɗin nan tana mu taimaka mata kawai nake tunawa, ga ɗa ya kawo kai zai fito amma ya hana mu, mu taimake ta." Ta ƙarashe maganar kamar za ta yi kuka.

Doctor Lukman ya sauke numfashi ya ce. "In dai Doctor Bulama ne abun da ya fi haka ma zaki ga ya yi, ke baƙuwa ce a asibitin nan shi yasa abun da yake damun ki, amma mu mun riga mun saba da irin waɗannan abubuwan."

"Gaskiya idan aka cigaba a haka ba zan iya zaman asibitin nan ba Doctor, dan watarana sai zuciyata ta buga, a ce mutum babu abun da ya sani yake bawa muhimmanci a rayuwarsa sai kuɗi? Kuɗi abun banza da zaka mutu ka bar su, a yanda aka san likitoci masu tausayi da jan patients ɗinsu a jiki gami da kwantar musu da hankali, amma shi ko kaɗan bai san hakan ba. Abun da yake bani mamaki kuma yanda har yanzu asibitin nasa yake ƙara haɓaka, mutane suke ta yabon sa suna ƙwararrun likitoci ne a ciki waɗanda suka san aikinsu."

Murmurshi Doctor Lukman ya yi ya ce. "Ai komai da iyawa ake yi Jamila, ma'aikatan cikin asibitin nan kawai suka san halin da ake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login