Showing 12001 words to 15000 words out of 231718 words

Chapter 5 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14674

rundunar sojoji million aka turo za ka iya gamawa da su, na baka komai a tsare, umarnin harbin da aka basu ne ya ɓata komai, kuma aka shirya wata rundunar aka tura ba tare da sanina ba,  shiyasa su suka yi galaba a kanku. Babban baƙin cikina da wancan yaron Khamal ya dawo a raye ba, kuma na san duk nasarar da aka samu sanadiyyar sa ne, dan ba ƙaramin jajircewa ce da shi akan aikinsa ba, yana aiki ne da jikinsa gami da zuciyarsa, He knows the value of his work, especially if he wears military uniforms on his body, he feels like he is carrying the whole country in his shoulder, gaba ɗaya yanzu idan manyanmu a kansa yake".

Gwaska ya yi wata shegiyar dariya ya ce. "Indai kere na yawo, zabo na yawo wata rana za'a haɗu, Wallahi sai na ɗauki fansar kisan yarana da akai mun da kuma harsashin da ya huda jikina, zan yi ɓarnar da sena girgiza ƙasar nan girgiza ta gaske makuwa, kuma dole a sakarmin yarana da aka kama ko kuma aga abunda ba'a so" Cikin mamaki General ya ce. "What? You mean kai ma sun yi nasarar harbin k......,"

kiran da ya shigo cikin wayarsa ne ya katse masa abun da yake cewa. Janye wayar ya yi daga kunnensa ya duba, ganin Chief of Army staff ne yasa cikin sauri ya cewa Gwaska "Ina zuwa, I will call you later." Bai jira amsarsa ba ya ɗaga kiran Chief ɗin.

Ƙamewa ya yi kamar yana gabansa with so much respect ya ce. "Morning Sir." Daga ɗaya ɓangaren Chief ya ce. "Morning General, ka shirya kai da sojoji kamar 20 anjima za mu zo mu je mu dubo yaranmu na Naija state, sanann mu jagoranci miƙa yaran nan ga iyayensu "

"Done Sir." General ya faɗa tare da sara masa.

Dungurar da wayar ya yi bayan ya katse kiran cikin tsananin takaici. Abun da yake ƙara baƙanta ran General idan ya tuna yanda Nigeria da duniya gaba-ɗaya ta ɗauka da zancen nasarar da su Captain Khamal suka samu akan ƴan ta'addan, duk inda mutum ya duba a social media zancen ake yi ana yaba musu da jinjina musu akan bajintar da suka yi. Kuma daga faruwar abun jiya har Chief zai je ya dubo su da kansa da sauran manyan muƙarabban gwamnati, duk kuwa da tarin sabgogin dake kansu. Tsaki ya ja a fili ya ce

"Sai ka ce akansu aka fara fita operation, mu da duk da muke zuwa uban wa ya yi mana haka?" Sumar kansa ya yamutsa cikin rashin sanin abun yi, duk wannan abubuwan ba su wani dame shi ba kamar irin ace za'a ƙarawa Captain matsayi, domin ya san tabbas idan hakan ta faru gaba_gaba Captain zai kamo matsayinsa ko ma ya wuce shi tunda mutum ne shi jajirtacce akan aikinsa, kuma ze iya bankaɗo muguwar harƙallar da yake aikatawa.

Table ɗin gabansa ya ƙara bugawa da dukkan ƙarfinsa idanunsa duka a waje ya ce "Impossible! Wallahi ko zan rasa aikina ba zan taɓa bari a ƙarawa yaron nan girma ba." Kamar mahaukaci ya ɗauki wayarsa ya fice fuuuu!! daga office ɗin tamkar zai tashi sama.


A hankali ta buɗe idonta tana bin inda take kallo, kunnuwanta na jiyo mata sauti mai kama da maganganun mutane ƙasa_ƙasa. Hannun hagunta ta ji ya ɗaure mata, ga wani abu da take ji daga hannun yana shiga cikin jikinta a hankali. Yunƙurin tashi zaune ta yi, Madam Halima dake zaune a kujerar gaban gadon da take, ta yi saurin tashi tsaye tana faɗin. "Kin farka, sannu Dear."

Da ido kawai take bin ta dan ba ta jin abun da take cewa sosai, kamar mai yin magana cikin raɗa haka take ji. Madam Halima ta mayar da ita ta kwanta, cikin kulawa ta ce.

"Let me call the doctor"

ta juya ta fara tafiya, Yarinyar dake kwance saman gado, ta bi ta ido har ta ɓacewa ganin ta, kalle-kalle ta shiga yi a ward ɗin da suke mai ɗauke da gadajen marasa lafiya guda huɗu, duk yara ne ƙanana kamarta sai masu jinyar su. Tare Madam Halima suka dawo da Doctor Zainab, dudduba jikinta ta yi bayan ta yi mata sannu, d Doctor ta dubi Madam Halima  ta ce "Madam a ba ta ko ruwan tea ne ta sha dan tana tattare da yunwa, anjima idan ruwan nan ya ƙare za'a iya discharging ɗinku, because gaba-ɗaya results ɗin gwaje-gwajen da aka yi mata ya nuna ba ta da wani ciwo mai illa a jikinta."

Madam ta ce. "Masha Allah, Mun gode sosai fa Doctor."

Doctor ta yi murmurshi ta ce. "Don't mind." Sannan ta shafa cukurkuɗaɗɗan gashin Yarinyar ta ce. "Cute Baby Allah ya ƙara lafiya." Da ido kawai yarinyar ta bita.

Bayan fitar Doctor, Madam Halima ta bar ta a hannun wata Nurse ta tafi haɗo mata kayan tea ta dawo.

Har lokacin idanunta biyu ba ta koma barcin ba. Bayan ta haɗa mata tea ɗin ta tashe ta zaune ta jingina bayanta a jikin pillow sannan ta ɗauko cup ɗin da spoon ta deɓo tea ɗin ta kai bakinta. Kawar da kai ta yi dan ba ta taɓa ganin irin wannan abun ba.

Madam Halima ta kamo hannunta ta ce "What happen?" Duk da ba ta ji abun da ta ce sosai ba amma sai ta girgiza mata kai. Tsayawa Madam Halima ta yi tana kallon ta, har yanzu yanayinta ya nuna tana cikin tsoro, ba tare da ta yi zato ba ta ji cikin muryar yara  da ƙarfin sauti ta ce. "Zan yi fitsari."
Madam Halima da ta yi tunanin duk  yanayin tsoron da yarinyar take ciki ne yasa ta yin maganar da ƙarfi, cikin farinciki ta ce. "Alhamdulillah, baki ya buɗe kenan?"

Yana nan kwance Likitan da ya je ɗauko masa wayarsa ya dawo ya kawo masa.

More than 50 missed call ya tarar, fiye da rabi duk na Family ɗinsa ne.

Numbern Mahaifiyarsa da ya yi saving da First  love ya fara bin bayan kiran, amma har ya kira sau biyu not
respond, numfashi ya sauke ya kira numbern My wife, still ita ma no respond.

Tsaki ya ja ya ajiye wayar  a gefensa tare da lumshe idonsa yana sauraren bugun zuciyarsa, gefe guda kuma raɗaɗi da ciwon harbin jikinsa na ɗan damunsa, musamman da ya kasance sai dai ya kwanta ta ɓari ɗaya. Gently ya ji an turo ƙofar ɗakin an shigo tare da yin sallama, buɗe idonsa ya yi ya sauke akan wanda ya shigo.

Lieutenant Faruk ne, da mamaki Khamal yake duban shi ganin hannunsa nannaɗe da bandage, alamar shima an harbeshi.

Murmurshi Lieutenant Faruk ya sakar masa tare da sake yin sallama. Amsa masa ya yi a can ƙasan maƙoshi. Faruk ya ƙaraso tare da janyo kujera da hannunsa mai lafiya ya zauna a gabansa.

"Good Morning Captain" Ya faɗa cikin respect.

Ɗaga masa kai kawai Captain ya yi.

Cikin kulawa Faruƙ ya ce "Ya jikin naka?"

Cikin dakakkiyar muryarsa ya ce. "Alhamdulillah, and you?" Faruk ya ce. "Da sauƙi Alhamdulillah." Jinjina kai Captain ya yi tare da runtse idanunsa, lokaci ɗaya kuma ya buɗe idon kamar an tsikare shi ya ce.

"Faruk I want to ask you something?" Faruk ya ce. "Okay Sir."

Captain yana kallon cikin idonsa ya ce. "Akwai wata little Baby da na ɗauko jiya tana ina, ance ba'a ganta ba?"

Faruk ya ce. "Tana cikin asibitin nan, ana bincikar lafiyar jikinta, Madam Halima ce tare da ita."

Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi ya ce. "Ina fatan dai babu wani abu da ya same ta ko?"

Lieutenant Faruk ya ce. "Babu Sir."

Ajiyar zuciya ya ƙara saukewa, yana jin yanda nutsuwa ta fara mamaye zuciyarsa.

Faruk ya cigaba da magana.

"Muna jiran a tabbatar tana cikin ƙoshin lafiya ne kafin mu fara cigiyar iyayenta, su sauran yaran ɗazu aka kaisu gidan gwamnati, za'a miƙa su ga iyayensu, ita kuma ba wanda ya san daga ina take, za'ai cigiyar iyayenta"

Da sauri Captain Khamal ya ce. "

No, not now."

Da mamaki Faruk yake kallon shi, da son jin dalilin da ya sa yace ba yanzu ba.

gyaɗa masa kai Khamal ya yi ya ce.

"A bar ta a hannun Madam Halima har zuwa lokacin da zan samu lafiya, da kaina nake son yin bincike a kanta."

"But Sir...."

Ɗaga masa hannu ya yi fuskarsa a haɗe, alamar ya ƙosa da maganganun Faruk, hakan yasa Faruk ya haɗiye maganarsa, amma cikin ransa fal mamaki ne akan abun da Captain ya faɗa.

A sanin da ya yi masa mutum ne wanda babu ruwansa da shiga shirgin da ba nasa ba, komai zaka yi sai dai ya bika da ido amma ba zai tanka ba. But bai san dalilinsa na yin hakan akan yarinyar ba. Ɗan taɓe baki ya yi ya miƙe ya yi masa sallama ya fita.

Ƙarfe ɗaya saura na rana tawagar su Chief of Army staff ta sauka a Kantagora Army barrack Naija state, direct inda Captain Khamal yake ya ce a fara kai su.

Su uku suka fara shiga ɗakin da yake,  Chief da General Ibrahim sai wani Colonel, daga baya kuma Ministan tsaro da na sufuri da wasu jami'an tsaron suma suka shiga.

Yana kwance idanunsa a lumshe kamar mai bacci, amma ba baccin yake ba, wani likita na tsaye a kansa yana dudduba shi. Ƙamewa Likitan ya yi ya sarawa su Chief of Army staff tare da welcoming ɗinsu. Hakan ya saka ya buɗe idanunsa ya waiwaya ya kalle su.

Da sauri ya ɗago kansa tare da ƙoƙarin yin salute daga kwancen da yake. Chief ya ƙarasa kusa da shi ya kama hannunsa yana murmurshi ya ce. "No need, our Lion the king of the jungle, I salute you Captain Khamal Khamis"

Ƙasa ya yi da kansa cikin respect ya ce. "Welcome Sir."

Chief ya ce. "Thank you, How are you feeling now?"

Ya ce. "Better Alhamdulillah." Chief ya ce.

"Masha Allah, Allah ya ƙara lafiya, rundunar soja tana matuƙar Alfahari da samun jajirtacce kamar ka, shugaban ƙasa ma ya yabawa ƙoƙarin da ku kai, duk da baya gari amma ya turo wakilansa, muna tare da ministan tsaro da na sufuri, duk muka zo duba ku."

Captain Khamal ya jinjina kai tare da faɗin "Thank you sir"

General Ibrahim ya ƙaraso cikin ƙoƙarin ɓoye halin da yake ciki ya yi masa sannu ba yabo ba fallasa, shi ma ya amsa masa a haka.

Minista kuwa cikin fara'a ya yi masa sannu tare da yi masa jinjina akan aikin da suka yi.

Ta gefen ido General ya dinga hararar Khamal cikin tsananin baƙin ciki. Chief ya zauna a kujerar da Likitan ya kawo masa, yana duban Captain Khamal cikin jinjina ya ce.

"Sannu da ƙoƙari Captain, tabbas kai ɗin na daban ne kuma mai sa'a ne ko a cikin sojoji. Irinku Jajirtattu masu aiki domin Allah ƙasar mu take buƙata, da ace ƙasar mu za ta samu kamar ka su fi rinjaye a cikin jami'an tsaro da ma mutane da  an samu sauƙin ta'addanci da duk wani criminals acts a cikin ƙasar nan. An daɗe ba'a samu Nasara a fita operation kamar wannan da kuka fita ba, hakan ya ƙara nuna mana jajircewarka Hukumar sojojin ƙasa ta yaba muku kuma ta jinjina muku."

Captain ya ce. "Thank you Sir." Chief ya ce. "Allah ya ƙara lafiya, bari mu zagaya mu duba sauran soldiers ɗin daga nan zamu wuce government House na nan garin, dan miƙa yaran nan ga iyayensu.

" Captain ya ce. "Okay Sir, a fito lafiya."

Cikin yaƙe General Ibrahim ya ce masa. "Allah ya ƙara lafiya Captain" A ransa kuwa cewa ya yi. 'By the grace of God ba zaka tashi daga wannan ciwon ba sai dai a ɗauki gawarka daga gurin nan, ba dai ka taka da ƙafafuwanka ka bar shi ba.'

Da ƙyar Madam Halima ta saka yarinyar, ta sha tea ɗin kaɗan bayan ta saka mata Fo ta yi fitsarin a ciki.

Abun mamaki kuma mijin Madam Halima yana kawo  Banana ta karɓa ta fara ci cikin sauri-sauri, hakan ya ƙara nuna tana jin yunwa sosai.

Cikin mamaki Madam Halima ta dubi Mijinta Captain Abdussamad ta ce. "Captain ka ga abun mamaki, yarinyar nan ɗazu daƙyar ta sha tea kamar zata yi kuka, amma ka ga yanzu yanda take cin Bananan."

Captain dake kallon Yarinyar ya ce. "May be tana son ta ne that is why." Madam Halima ta jinjina kai ta ce. "She is so cute, amma har yanzu a cikin firgici take, ta ƙi sakin ranta ta nutsu, kamar ma a firgice take da environment ɗin"

Captain ya ce. "Dole ai, tunda babu wanda ya san tsawon lokacin da ta ɗauka a hannun azzaluman mutanen can, kuma a cikin dokar daji"

Numfashi Madam Halima ta sauke ta ce. "Allah Sarki, yanzu haka maybe iyayenta sun yi cigiyar ta har sun gaji."

Captain ya ce. "Wa ya faɗa miki iyaye suna gajiya da neman ɗansu? Ai sai dai masu bincika musun su gaji."

Madam Halima ta ce. "Haka ne, amma yarinyar nan ba ta mun kala da 'ƴan Africa ba, ko shi yasa idan muka yi mata magana ba ta ganewa, ko ba bahushiya bace? amma kuma ɗazu ta yi mun Hausa."

Captain ya ce "Komai ma zai iya kasancewa, may be ba ta jin hausan ne sosai."

Jinjina kai kawai Madam Halima ta yi Idanunta akan yarinyar, ita kam har cikin ranta take jin tausayi da k'aunar Yarinyar, ko dan ba ta Ƴaƴa ne ya saka?

Gaba ɗaya ransa a dagule yake, yana cigaba da lissafin ta ina ze sake ɓullowa lamarin, dan wannan galabar da aka samu akan 'yan ta'adda kamar koma baya ne a gare shi, da samun raunin yadda a tsakanin sa da su Gwaska.

Wayarsa ce ta fara ringing, kamar ba ze ɗauka ba, se kuma ya miƙa hannu ya ɗauka, cikin hamzari ya miƙe tsaye yana sarawa wanda yake Maganar da shi a waya, kamar yana gabansa.


Daga cikin wayar aka ce "Mr. President ya dawo gari, ze yi zaman gaggawa da mu yau da daddare, akan harkar tsaro"

General Ibrahim yace "ok Sir" ya sake ƙamewa, sannan ya ajiye wayar.

Yana ajiyewa ya wani sake haɗe rai, tare da yin ƙwafa, ya daki tebur yai waje cikin sauri.

Manya manyan masu ruwa da tsaki a harkar al'amuran tsaro duk sun hallara, kama daga Chief of Army staff, AVM General General na sojoji, babba da ƙaramin ministan tsaro, masu bawa shugaban ƙasa shawara akan harkar tsaro, da sauran manya masu bada shawara akan harkar tsaro, da shi kansa shugaban ƙasan, sun hallara a cikin katafaren ofishin da shugaban ƙasa ke ganawar sirri, babu ɗan Jarida babu masu saka ido, babu duk wata Camera ta ɗauka, saboda ganawa ce ta sirri.

Shugaban ƙasa yai gyaran murya cikin harshen turanci yace "To nayi farin ciki matuƙa da irin nasarar da jami'an tsaron mu suka samu, akan ceto yaran nan da aka sace, dama gaba ɗaya idon duniya a kanmu yake, dan ganin ƙoƙarin da za muyi, to Alhamdilillah yaran sun kuɓuta kamar yadda na samu labari, duk da wasu sun rasa rayukansu, mun bada sanarwar jaje ga ahalin wannan yara.
Yanzu abu na gaba shine, wane mataki zamu ɗauka akan kawo ƙarshen sace mana ɗalibai da ake a makarantun kwana da ma na jeka ka dawo?

Ƙaramin ministan tsaro yace "Ai your Excellency, a nawa ganin a rufe Dukkanin makarantun sakandare da na primary na yankin gabashin ƙasar nan, tun da a nan rashin tsaron yake, zuwa a ga yadda hali ze yi"

Baban ministan tsaro yace "A' wannan ba shawara bace ai, shikenan se mu ajiye yaranmu a gida ba makaranta? Wanan ai kawo koma baya ne da naƙasu ga ilimin al'ummar yankin"

Ƙaramin ministan tsaro a ransa yace "wannan shine baban burinmu, al'ummar yankin suyi ta saun koma baya"


Haka akai ta tattaunawa, har aka samu matsaya akan cewar, dole a rufe makarantun a dakatar da ilimin wannan yankin, har se zuwa lokacin da za'a samar da tsaro.

Magana ta gaba kuma, shugaban ƙasa yai bayanin cewa, akwai ƙasashen da sukai alƙawarin tallafawa ƙasa da maƙudan kuɗaɗe dan siyo makamai da za'a bawa Sojoji dan cigaba da yaƙi.

Nan suma sojojin suka faɗi ƙorafe ƙorafensu, abubuwan da suke buƙata, da yadda kuɗaɗen da ake warewa harkar tsaro ba sa isa yadda Yakamata.

Shugaban ƙasa yai alƙawarin kafa kwamitin bibiya, akan yadda ake amfani da kuɗaɗen da ake warewa harkar tsaron.

Aka tattauna batutuwa masu mahimmanci, da shawarwari akan yadda za'a shawo kan matsalolin tsaro.

General Ibrahim yana komawa gida, ya samu wani keɓaɓɓen guri, ya fara kiran waya.
Dashshiyar muryar Gwaska ta bayyana a cikin wayar "ya, dama kai muke dako, kunyi zama da shugaban ƙasa, me ake ciki?"

"Dama kiran da nai maka kenan, yau me magana da yawun shugaban ƙasa ze sanar da rufe makarantun firamare da na sakandare na yankin gabashin ƙasar nan, har zuwa lokacin da za'a samu tsaro, Sannan akwai maƙudan kuɗaɗe da za'a bawa ƙasar nan tallafi dan siyo makamai da cigaba da yaƙar ku" gaba ɗaya ya kwashe Abinda aka tattauna ya gayawa Gwaska.

Wata irin mahaukaciya dariya Gwaska ya saki, kai da jin wannan dariya ka san me ita ya samu rauni a imaninsa ya tsagaita da dariyar yace
"Yankin mu na ta samun koma baya ta kowace siga, yayin da ta wani fannin hakan ya zama hanyar samawa ƙasa hanyoyin samun kuɗaɗen da manyan ƙasar suke kashe mu raba. Hakan yayi kya a satin nan zamu ƙaddamar da babban harin da yafi wanda mu kai a baya.
Muna nan muna cigaba da saurarenka, duk yadda ake ciki game da shirin rundunar ku, muna sauraren ka, abunda ya shafi shirin gwamnati shima muna da masu kawo mana rahoto, ka huta.." daga haka Gwaska ya kashe wayarsa.

Bayan Sallar la'asar Captain yana zaune yana shan coffee ɗin da ya saka aka kawo masa a hankali aka turo ƙofar ɗakin da yake da ƙarfi.

Ɗaga kansa ya yi cikin sauri saboda ƙamshin da yaji ya ziyarci hancinsa, da mamaki yake kallon matashiyar kyakkyawar matar dake tsaye tana kallon sa hawaye na shatata daga cikin idanunta.

Ajiye cup ɗin hannunsa ya yi cikin tsananin mamaki, duk da tsohon cikin da matar ke ɗauke da shi haka ta tako cikin gudu ta zo ta rungume shi tana sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da fashewa da kuka. Ɗan ture ta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login