Showing 6001 words to 9000 words out of 231718 words

Chapter 3 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14678

faɗar haka Zainab, kinga hankalin mutane ya fara dawowa kan ki, ana gaya miki magana, Khalifa lokacinsa ne ya riga ya yi, Allah ya karɓe shi, Allah ya jiƙansa bari in je in samo adaidaita sahu, mu ɗau gawar".

Haka ya fita dan neman adaidaita sahun da zata kai su gida.

Bayan ya samu adaidaita sahun ya shigo Asibitin, ya koma reception ya tarar da wanda ya biya kuɗin Asibitin a gurinta ya ce "To, baiwar Allah tunda ba'a kwantar da yaron nan ba, Allah ya karɓi abunsa, ko ba duka ba dan Allah ku rago min kuɗin da na biya"

Jinjina kai tayi tace "Ga doctor Bulama can, shine mai Asibitin wanda ya duba ɗanka, kaje ka same shi kai masa bayani".

Bai yi ƙasa a gwiwa ba, yabi bayan doctor Bulama, tare da maimaita masa abunda ya gayawa receptionist.

A wulaƙance ya dube shi sannan yace "Ka taɓa ganin wanda ya je ƙiyama ya dawo?"

Ya girgiza Kai yace "A'a"

"To nan Asibitin, no refundable after payment, kuɗi sun riga sun shiga asusun Asibiti, dan haka sai dai ka haƙura".

Kamar zai shige cikin doctor Garba, haka ya duƙa yana cewa "Dan Allah ka taimaka min, Wallahi babur ɗina da nake neman Abinci na bada jingina, na karɓo kuɗin"

A fusace doctor yace "kaga i have something to attend to, ka san ba ka da ƙarfi meyasa ka taho nan?"

"Wallahi an rasa gado ne, kuma akace ma yajin aiki likitoci za su tafi shiyasa, dan Allah ka temaka mana..."

Ai bai tsaya saurar sauran zancen ba, ya wuce a bar shi a gurin, ɗauke da baƙi ciki goma da Ashirin!.








Kantagora Army barrack Naija state, nan ne in da aka kai gawarwakin sojojin da suka rasa ransu, da wanda a kaiwa rauni, kai tsaye aka wuce da su babban Asibitin da ke cikin barikin sojojin.
Duk in da Faruk ya saka ƙafarsa, a nan yarinyar nan take mayar da tata ƙafar, ita kaɗai a cikin zaratan sojojin nan sai binsu take.

Wani Babban soja yai umarni da a kaita cikin yaran da aka kuɓutar, ko itama a samu nata iyayen.

Wani soja ya ce "To ai wannan yarinyar ba tai kama da 'yan Nigeria ba ma, ko ma dai daga maƙotan ƙasashen nan akai kidnapping ɗin ta?"

Faruk ya ce "i have no idea about it, abunda na sani shine ba ta cikin wancan yaran da aka kuɓutar, dan haka ba cikin su Yakamata a haɗata ba, daban za'ai cigiyar iyayenta, abunyi Yanzu shine ko Madam Halima ce a bata ita ta zauna da ita, kan a san abunyi akanta".

Su kai na'am da shawarar da Faruk ya bayar, akan ta zauna a gurin Madam Halima, itama soja ce a cikin tawagar, mijinta ma soja ne suna zaune a nan cikin barrack ɗin tare.

Madam Halima ta kalli kyakkyawar fuskar yarinyar, wadda tai duƙun duƙun, 'yar rigar jikinta tai futu futu da datti, ga gashin kanta a hargitse duk datti da ƙasa.

Cike da tausaywa yadda 'yar ƙanƙanuwar yarinyar tai rayuwa a hannun 'yan ta'adda babu kulawa ta ce "ya sunan ki?"

Maimakon ta amsa sai tai ƙuri da ido tana kallon Madam Halima.

"Ya sunan ki na ce?" Madam ta kuma maimaitawa, amma shiru ba tai responding ba.

Faruk ya ce "ina ga fa ba ta Magana, da tunda aka tsinto ta banji tayi Magana ba".

Madam ta ce "Allah sarki, Allah kaɗai ya san halin da iyayenta ke ciki, ai ita ma a Asibitin zamu bar ta a duba lafiyar ta tukunna"

Faruk ya ce. "ok hakan ya yi".

'Yan matan nan ma da aka kuɓutar, duk nan Asibitin cikin barrack aka kawo su, dan binciken lafiyar su, kafin a miƙa su ga iyayensu.

Gaba ɗaya ganinta take kamar a wata duniyar ta daban, Madam Halima taiwa yarinyar nan wanka tsaf, aka samo wata rigar aka saka mata, aka kwantar da ita akan gadon marasa lafiya, ba ta umm ba ta um'um, sai aukin rarraba idanu, babban burinta bai wuce ta ga wannan mutumin da ya ɗakkota daga hannun wannan mutanen ba.
Sai dai ba ta san in da aka kai shi ba, wasu mutanen ne daban suke zuwa suna duba ta, suka dinga soka mata allura suna ɗibar mata jini, sai da suka saka ta kuka, dan haka gaba ɗaya tsoron gurin take ji.

"Ashhadu alla ila ha illallah, Rabbana alaika tawakalna wa ilaika anabna wa ilaikal masir" shine abunda ya ke ta maimaitawa, tare da ƙoƙarin buɗe idanunsa a hankali.

Dumm yake ji a kansa, ga shi dishi dishi yake gani, a hankali ya cigaba da lumshe idonsa yana buɗewa har Allah ya sa ya buɗe su yana ganin komai clearly.

"Congratulations Captain, you survive" wani matashin likita ya faɗa yana murmushi.

A hankali ya yunƙura zai tashi zaune, amma Likitan yai saurin cewa "No relax, ba'a daɗe da fitowa da kai daga tiyata ba, mun cire maka bullet a cikinka ne.

Ajiyar zuciya yai yace "Alhamdilillah, yaran fa suna ina?"

"Suna nan tare da mu a cikin Asibitin nan, ana musu gwaje gwaje kan a sada su da 'yan uwansu"

Kamar dirar mikiya, haka yarinyar da ya tsinta ta faɗo masa, da sauri ya ce "There was one little baby, da na samo a cikin dajin, tana ina?"

Likitan ya ɗan yi shiru sannan yace "kai gaskiya ni banga yarinya ƙarama a cikin yaran nan ba, duk 'yan makaranta ne"

Da sauri ya ce "No, their is one little girl, ba tafi 3 years ba, wata fara haka"

Doctor ya ce "Please calm down, kaga yanzu muka fito da kai, ka kwantar da hankalinka kar jininka ya hau".

Captain ya girgiza kai yace "dole a nemo ta, she's not among the students, ba a cikin su take ba".

"Shikenan is ok, za'a nemo ta insha Allah, bari inje in duba amma for now, dan Allah ka kwanta ka samu nustuwa"

"Nutsuwata ɗaya, shine a ga yarinyar nan"

"Ok, bari inje a duba".

Captain ya koma ya gyara kwanciyar sa yana lumshe ido.

Doctor da yaiwa Captain aiki ya cire masa bullet ya fita, dan neman yarinyar da Captain ya saka shi.

Sai dai duk iya binciken da yai, babu wanda ya ga yarinyar, kowa ya tanbaya sai ya ce bai ganta ba, iya ɗaliban nan suke nan babu wata yarinya 'yar shekaru uku a cikin su.

Har mutuary ya je, ya duba cikin gawarwakin yaran, amma babu wata yarinya ƙarama a cikin su.

Komawa ɗakin da Captain yake yai, ya tarar an zaunar da shi, wani likitan ya kammala yi masa dressing ɗin in da ya samu rauni a bayansa.

Ɗagowa Captain yai ya ɗan tsura masa idanu, yana jiran jin amsar da zai ba shi, duk da kasancewar likitan soja ne, amma sai da gabansa ya faɗi da irin kallon da Captain ke masa, saboda kasancewar sa mutum me matuƙar kwarjini.

"Am.. duk cikin yaran nan an duba ba ta ciki, kuma har gawarwaki na duba amma babu ita a ciki, kowa na tambaya sai ya ce babu wata yarinya ƙarama a cikin yaran da aka kuɓutar duk matasa ne 'yan makaranta.

"Impossible" Captain ya faɗa yana ƙoƙarin tashi.

Saurin riƙe shi su kai suna cewa yayi haƙuri.

"Ya za'ai yarinyar da na saka a Mota, ace ba'a ganta ba, a gabana fa ta shiga Motar?"

"Ka yi haƙuri a sake dubawa za'a ganta".

"No, zan duba da kaina" yai maganar yana ƙoƙarin miƙewa, sai dai jiri ya kwashe shi, da tsananin azaba da cikinsa ke yi, hakan ya tilasta masa komawa ya zauna.





Comment and Share please
Nimcyluv
Ayshercool
Zee kumurya.
[9/30, 8:55 PM] Abk: *✷ DARE DA DUHU ✷*

_Bright pens✍🏾_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee kumurya

*4.....*
Elegant Online writer's

_Kuyi following wannan acct ɗin a Arewabooks_
https://arewabooks.com/u/nimcyluv

Captain Khamal ya yi saurin zame kan matarsa dake kafaɗarsa, idanunsa ya ware tare da sakin kwantaccen Murmushi, saboda ganin waɗanda suka shigo Room ɗin. Babbar mace ce, fara tas da ita zata iya yin shekaru hamsin a duniya.

"Finally, my son survived Alhamdilillah" Hajiya A'isha ta ce, tana ƙarasawa bakin gadon da Major Khamal yake kwance.

Lumshe idanunsa ya yi, He breathed slowly kafin ya ware idanunsa akan matar cikin ƙasa da murya yace.
"First love" Ya Faɗi maganar yana ƙara sakar mata Murmushi. hannunsa ta kama tare dayi masa ƙuri da Idanunta, she tries to understand, if there is something wrong with him.

A Hankali tace "Hankali na, ya tashi sosai Babana, na kasa samun nutsuwa bana son aikin nan naka, kullum cikin zullumi nake da tashin hankali" Captain Khamal ya kama hannun Hajiya A'isha wacce ta kasance Uwa a gare shi, ya ɗan yi murmushi yace

"First love, ba gashi kinga lafiya nake ba? Zan warke insha Allah"

"Tsoro take kada a kashe mata Jaruminta" Da sauri Captain Khamal ya ɗaga kansa, with so much surprise yake kallon mai maganar, Sai a lokacin ya kula dashi.

"Baffa" Captain ya ce, yana ware idanunsa akan mahaifinsa dake tsaye cikin shigar manyan kaya, kamarsa da Major Khamal ta bayyana sosai, hatta baƙar fatar Captain irinta Baffa ce.

Baffa ya harari Khamal, cikin wasa ya ce "An manta da Baffa saboda anga first love? Shine ni aka ƙi kulani"

"It's not like that, Baffa" waje Baffa ya nema tare da zama cikin tausayin ɗan nasa ya ce "Ya jikin naka?" .

"Jiki Alhamdilillah Baffa"
Jinjina kai Baffa ya yi yana kallon wajan da aka harbi Khamal, cikin sanyin murya Baffa yace

"I received a call on phone, from the military command in Abuja, sun gaya min Wanda suka rasa rayukansu a dajin, hankali na ya tashi sosai, mun ɗauka ko har da kai, Sai daga baya muka samu full information akan cewar kai raunuka ka samu"
Captain dai murmushi yake, yana son iyayensa bashi da kamar su.
"Yaya K, ya jiki?" Cewar wani matashin saurayi. Khamal ya kalli ƙaninsa Shureim yace "You?" Shureim ya kwaɓe fuska tare da faɗin "Duk na damu zan rasa Big bro, shine ya kula kowa banda ni"

"Sorry Shureim"
Shureim ya ce "Ya jikin Yaya K?" Captain ya rufe idanunsa A hankali ya ce "I'm good" surutun da yake yi, gaba ɗaya ya fama masa ciwon, yana jin yadda gurin yake masa zafi sosai.

Na'ima dake gefensa, ji take kamar ta ɗauke mijinta su tafi gida haka take ji. Tayi kewarsa sosai, har tsanar aikin take saboda tsayin lokacin da suke ɗauka basa tare.

Army Doctor ɗin daya shigo ne, ya kalli su Baffa cikin sakin fuska ya ce "Ana buƙatar ya samu nutsuwa, wajan harsashin bai warke ba haryanzu"
Baffa ya miƙe tsaye, Yana faɗin "Daman da yaya aka barmu muka shigo ganinsa, tafiya za mu yi tunda kun mana fin ƙarfi" Dr ɗin dai murmushi ya yi, Baffa ya yi waje. Hajiya A'isha ta kalli Captain ta ce "Allah ya ƙara sauƙi Babana, Zuwa yaushe zaka dawo gida ka huta?".

"First love ban sani ba, but Soon in sha Allah"
ta ce "To, Allah ya tsare min kai"

yunƙurawa ya yi zai tashi da sauri Na'ima ta kamashi tana faɗin "Be careful"
Duk yadda yaso miƙewa kasawa ya yi, Dole ya koma tare da zama ya ce "Allah ya kiyaye hanya first love" fita duk sukai hadda Shureim.

Na'ima ta kalleshi tace "My man, ni ina nan tare da kai ko?"

Ya ware Idanu ya ce "Are You sure?" Kai ta ɗaga masa tana kama hannunsa tace "I really really miss you Man, Over eight months banji ɗumin ka ba"

hancinta ya ja "I miss you both, i mean you and my unborn child" Lamo tai a kafaɗar sa, kewarsa na fisgarta, She misses every single thing about him, she wants to be with her husband.

Madam Halima kuwa ta rasa ya ya zatai da Yarinyar kuka kawai take tana kiran "Abbi" cikin damuwa da kuma son rarrashin Yarinyar Madam Halima tace

"Me kike so?" Yarinyar
Taƙi cewa komai, domin bama ta gane me Madam Halima ta ce ba.

Madam Halima tace "Jama'a na shiga Uku, wacce irin yarinya ce wannan?"

Miƙewa ta yi tare da zama kusa da yarinyar cikin rarrashi tace.
"Kin ga stop crying, A good child never cry."

Ƙanƙame jikinta tayi, bata so ko taɓa ta ayi, She's afraid of everything. Babu wanda take son gani sai Mutumin daya ɗakko ta, Idanunta na hango mata shi cikin jini.

Da hannu Madam Halima tai mata nuni irin Sign language ɗin nan tace.
"Ke, kuka ki daina babu kyau".

"Abbi..."
Yarinyar Ta faɗa da ɗan ƙarfi, shiru Madam Halima tai, ko mahaifinta ne Abbi?.

Kallon yarinyar tayi, fara ce sosai, irin farin nan ƙal, But she looks very similar to Arabs, her eyes, hair, almost everything.

"ماذا تريد اين والدك"
Ma'ana "me kike so, ina mahaifin ki yake?" Madam Halima ta tambayeta da larabci, a tunaninta tunda tayi mata kala da Larabawa, may be tana jin larabci, bata san cewa gaba ɗaya maganar ce ba sosai take jinta ba.

Cikin rarrashi ta ce
"Kee, yanzu zan kira Abbinki.. kina so?" Da sauri ta ɗaga mata kai tana mata ƙuri da Idanunta, ta fuskanci hakan ne saboda bakin Madam da ta kalla, Madam Halima tai Murmushi tana bata Teddy tace "sai Kinyi bacci Abbi zai zo, kwanta" tai mata alama da data kwanta, ganin ta sake ambatar Abbi yasa Yarinyar kwanciya ta sakin ajjiyar zuciya, kana ganinta kasan akwai ɓoyayyan abu a tattare da ita.

Sai da Madam Halima taga tayi bacci, ta zare mata yatsarta dake baki, a firgice ta farka tana shirin sakin kuka Madam Halima ta mayar mata da yatsar bakinta.

Duk a wahale take, ta jima Idanunta bai ga bacci ba, ihun dabbobin jeji, da kuma tsoro yasa bata wani baccin kirki. Girgiza kai Madam Halima tayi Ubangiji kaɗai yasan halin da Yarinyar ta shiga, ko ƴar ina ce? Su waye iyayenta, they are alive or dead, Ohho!?. Wayarta ta ɗauka tare da kiran Lieutanant Faruk, ta faɗa masa She wants to see him immediately.

Faruk daya shigo yanzu, shima ya kalli yarinyar kafin ya juya ya kalli Madam Halima yace "what happened now?"

Madam Halima ta ce "Honestly, Her memory may be impaired idan taci gaba da kasancewa haka, a Yanzu ma kamar tana da wata ɓoyayyiyar larura" Faruk kasa cewa komai ya yi, yana mamakin yadda ƙaramar yarinya ta kasance a cikin wannan jejin, ko me ya kaita oho? Ko iyayenta akai kidnapping tai escaping ko wani abun ne, Allah ne ya barwa kansa sani.

Faruk yai ajiyar zuciya yace "I will speak to Captain Khamal, Whatever he said, I will get back to you, Amma Banga kyautatuwar zamanta a nan ba"

Madam Halima taja numfashi kafin ta nemi waje ta zauna tace "you said she was not among the school children kidnapped?"

"Haka yace" Faruk ya faɗa yana taɓe fuska.
Madam Halima tace "Waye yace?"
yace "Captain Khamal, kin san taurin kansa ai, bakomai ze tsaya yai maka bayani ba"
Tace "To, Allah ya kyauta"
Daga nan Faruk juyawa ya yi, tare da yin waje, yabar Madam da baki a buɗe.

Wata matashiyar budurwa ce tsaye, da gajeren wanddo da farar shirt irin na sojoji, kanta ya sha a wigs, tai parking ɗin sa a bayanta, ta sarawa Lieutanant Faruk daya fito ta ce "Sir, Abu babu daɗi Allah ya tsare gaba. Amma nayi farin ciki sosai da nasarar da kuka samu"

Faruk yace "Thank you,Salima yaushe kika shigo Naija state?"

Tace "Not too long, Ina Captain ne?"

Murmushi kawai Faruk ya yi mata, dan yasan tatsuniyar gizo baya shige koƙi Yace "Shi kika biyo ke nan?.

Tace "A'a, za'ai posting ɗin mu zuwa wani waje ne, shine muka biyo ta nan zamu shige da sauran"

Faruk yace "I see, yanzu Captain ba lallai ki ganshi ba, lokacin treatment ɗin sa ya yi"

Salima tace "My be zuwa Dare" Faruk ya kalli Salima in a serious tone yace "Zan iya cewa wani abu, Salima?".

"All ears. Sir Faruk"

Salima ta faɗi hakan tana kallon Faruk sosai. "Meyasa ba zaki iya haƙuri da soyayyar Captain Khamal ba?"

Salima was speechless. Bata san cewa Abinda Faruk zai faɗa mata ke nan ba. Cikin sanyin Murya ta ce "I can't stop thinking about him, I always want to be with him, Wallah Sir Faruk ban san me zan ba, nace masa koda bai auren ba, kawai mu kasance tare, duk abinda yake so zan masa, like how every woman takes care of her husband"

Shiru Faruk ya yi ta kallon Salima, If he is not mistaken, bata da burin daya shige Captain ya kwanta da ita, ta ɓullo masa ta barikanci ya ƙi yarda, tace ya aureta nan ma yaƙi.

Faruk yace "Captain daban yake a cikin mu, rashin matarsa kusa dashi bai sa yabi matan banza ba, Ni shaida ne, You are wasting your time Salima, ko Captain zai kula wata ai banda irinki,ke fa duk kusan mazan Barrack ɗin Abuja ba wanda bai san yaya kike ba, Among the men, including me"

"Alright, kace kishi ka ke dani? Ya ware hannunsa tare da yin gaba yana faɗin " ko ɗan, it's just a suggestion"...


The next day at night.
Captain na zaune Sanye da vest fara ƙal, sai gajeren wando, ƙafarsa sanye cikin wani baƙin takalmi, Leutanant Faruk ne ya buɗe ƙofar ya shigo, cikin girmamawa ya gaida Captain.

Sipping coffee Captain Khamal yake a nutse, a hankali ta dinga leƙo da kanta daga bayan Faruk tana leƙen Captain

Sam Captain bai lura da ita ba, yaji a jikinsa akwai wanda ke kallonsa dai.

"Abbi ɗin, kike leƙa kuma?" Faruk ya faɗa da ɗan ƙarfi yadda za taji abinda yake cewa. Captain ya ɗago kansa da sauri, farin hannunta mai ɗauke da Teddy ya hango. Gaba ɗaya ta ɓoye jikinta da fuskarta a bayan Faruk.

Da sauri Faruk yaja baya yana murmushi ya ce "Ai baki isa ba, yadda kika ɗaga hankalin kowa shine yanzu zaki ɓoye a bayana?" Yarinyar ta rufe Idanunta tana ƙanƙame Teddyn da Madam Halima ta bata, riga da wando ne jikinta masu kyau, peach colour. An raba mata gashin kanta gida biyu ya kwanta har baya.

A nutse Captain yake ƙare mata kallo, ko wanne kalar sauyin ta samu, ba zai mance kamanninta ba, duk yanzu tsaf take, saɓanin lokacin da ya tsinceta cikin datti. Zame Teddyn tayi daga kan fuskarta, tare da buɗe Idanunta.

Idanu suka haɗa da Captain Khamal, ya ware mata manyan idanunsa, ƙara ta saki tana ƙanƙame Teddy. Sosai ya bata tsoro, bayan kuma shi take ta kuka za tazo wajensa.

Murmushi Captain ya saki, yana ɗan rufe idanunsa, seeing how she was scared by what he did to her.

"Come here".
Captain ya ce mata, yana miƙa mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login