Showing 57001 words to 60000 words out of 231718 words
Chapter 20 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
ni kamar kowacce Uwa da ɗanta!"
Ta ƙarashe maganar cikin kuka.
Cikin damuwa ya ce. "Dan Allah Angel ki bar wannan maganar, kin ga baki da lafiya, kar ki ƙarawa kanki wani ciwon."
Daƙyar Salman ya rarrashi Abra ta yi shiru, dan sosai ta birkice take kuka, ba ta yi tunanin tsanar da Mami take mata ta kai haka ba, ba ta da lafiya har kwanciya ta yi a asibiti amma ba ta je ta duba ta ba, a matsayinta na mahaifiyarta, dole abun ya taɓa zuciyarta sosai.
Sai da ta yi bacci sannan ya bar ɗakin, zuciyarsa cike da damuwa, shi kansa abun da Mami take yana damun shi ba kaɗan ba.
Washegari bayan su Abra sun karya Ammi ta haɗa su da driver ya mayar da su gida, saboda kiran wayar Ammi da Khamal ya yi da sassafe ya ce su koma gidan, Na'ima ta gan su ta ji daɗi dan duk ta damu, shi ma yana hanya yau zai dawo. kasancewar jikin Abra ya yi sauƙi sosai sai Ammi ta bar su suka tafin. Duk da ta so su zauna su kwana biyu ko dan ta kula da Abra sosai, kuma gidan ita kaɗai ce Baffa ma baya nan ya yi tafiya.
A parlour suka tarar da Na'ima hakimce akan kujera tana karkaɗa ƙafa, ta ci kwalliya kamar wadda za ta wani gurin, ƙamshinta ne kawai yake tashi a cikin parlour'n.
Salman ne a gaba Abra na bin shi a baya, kanta a ƙasa suka yi sallama. Ba ta amsa musu ba sai bin Abra da ta yi da wani mugun kallo. Cikin sanyin murya Abra ta ce. "Sannu hutawa Mani, Ina kwana?"
"Yana gidan Ubanki!"
Ba ta kuma cewa komai ba ta nufi ɗakinta da sauri cikin sanyin jiki, Salman ya bi ta da kallo.
"Sannu Salman, Na mamajo, bita zai_zai, cingum, maƙale mata duk sunayenka ne, abun da ka yi kuma ka kyauta na tafiya gidan kakaninka ku kwana, saboda ka ja mun baƙin jini a gurinsu ko? a ce bana kula da ita, wannan jarababbiyar tsohuwar ta zo ta cinye ni da masifaffen surutunta mara ma'ana."
"Ki yi haƙuri Mami don Al.."
"Ba zan yi ba, kullum kai kenan daga an yi magana a yi haƙuri a yi haƙuri, wallahi Salman ba dan a gida na haife ka ba sai in ce canza mini kai aka yi, na rasa me yasa kodayaushe ina ƙoƙarin raba wannan Shegiyar shak'uwar taku da waccan mayyar yarinyar amma shaƙuwar taku sai ma ƙara gaba take yi, ba ka jin maganata kwata_kwata Salman, ba ka bin abun da nake faɗa."
Tsugunnawa ya yi cikin raunin murya ya ce. "Ki yi haƙuri Mami, ba na son in ga kina ɓata ranki a kaina ko akan Yaya, kin san fushinki masifa ne a gare mu, don Allah Mami ki yi haƙuri."
"Idan ba ka son fushina da ɓacin raina ka daina shigewa waccan shegiyar yarinyar."
"I'm sorry to say Mami, ba zan iya fita daga sabgar Yaya ba, ita ɗin wata aba ce mai matuƙar mahimmanci a cikin RAYUWATA, tana da matsayi mai girma a cikin zuciyata, bayan ke da Abbi ba ni da kamar ta a cikin faɗin duniyar nan, dan Allah Mami ki daina yunƙurin raba mu, domin ɗayanmu ba zai iya rayuwa ba idan babu ɗaya."
"Ko kashin awaki ne ku wallahi sai na raba ku Salman, kai ɗa ne tsaftatacce mai ƴanci kamar ko wanne ɗa, ita kuma SHEGIYA ce Ƴar Zina, wadda ta fito ta haramtacciyar hanya! Dan haka kar ka ƙara haɗa kanka da ita, idan kuma......."
Buɗo Kofar parlour'n da aka yi aka shigo ya katse wa Na'ima maganarta, a tare suka juya suka kalli mai shigowar cikin tsananin mamaki da kaɗuwa.
LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.[10/1, 2:40 PM] Abk: LITTAFIN DARE DA DUHU NA KUƊI NE, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
Da sauri Abra ta ɗauke idanunta saboda kwarjinin da mutum ya yi mata, amma har yanzu jikinta rawa yake na rashin sabo da kallon da jama'ar wajan suke mata. A hankali ta yi ƙasa da kanta tana mai jan idanunta ta rufe ruf sai ƙanƙame hannunta take.
Taɓe baki ya yi yana mai zame idanunsa daga kallon tsautsayin da ya yi mata, cikin takun nan nasa na natsuwa da kamala fuska ɗaure yaci gaba da tafiya yana mai gyara zaman bluetooth ɗin kunansa a hankali kuma a fili ya ce.
"I am not a child, Abba, I will take care of myself"
A sanyaye yake maganar yana shafa sumar dake kwance a kansa, a nutse yake tafiya yana waya da mahaifinsa. Abba dake sauraran S.p Adnan Aliyu Matawalle ya ja numfashi ya ce.
"Me yasa ba zan damu da kai ba Son? Ina tsoron matsala ta haɗaka da wani, You are stubborn and hard-hearted. Baka son cin abinci ina kasan yanayin Olser ɗin ka idan ya tashi?"
Adnan ya marairaice fuska tamkar yana gaban Abba cikin ƙosawa da kallon da ƴan matan wajan ke masa ya ce. "I am thirty-two years old, but you still look like a child to me, Abba. Don mind me nasan yadda zan kula da kai na"
Da sauri ta cikin wayar Abba ya ce.
"Baka sani ba Adnan, idan ka sani ba zaka dinga hora kanka da yunwa ba, sai wife ta takura ka kake cin abinci, naso ace tare da Usman kuka tafi, da iya takurar Usman dole ta sanya ka kaci abinci ko da something liquid ne haka"
Adnan dai ya yi shiru yana sauraran faɗan da Abba yake masa, sai da ya gaji da faɗa ya ce.
"Ina da meeting bye take care of yourself ok"
"I'll. Love You Father, please ka sha maganinka ok" ya faɗi hakan yana yatsuna fuska tare da rufe idanunsa ya ɗan buɗe a lokaci guda, a hankali ya fara ƙarewa cikin B.U.K ɗin kallo yana ƙara tuna rayuwar makarantar da ya yi a ciki.
Ba tare daya lura da cewa ya ƙaraso inda Abra Khamal Khamis take zaune ba, sai ji ya yi ta miƙe da sauri har tana yin tuntuɓe da ƙafarsa, ko ta kanta bai bi ba, ya nemi waje ya zaune tare da sauke ajjiyar zuciya mai ɗan ƙarfi wacce take nuni da zallar gajiya da ya yi.
A karo na biyu ya ƙara rufe idanunsa yana sauke numfashi, jin mutum kusa da shi ya sanya ya buɗe ido da sauri. With so much surprised yake bin mutumin da ya zaune kusa dashi da kallo, kafin kace me ɗalibai sun rufe Sp Adnan Aliyu Matawalle, kasancewar ya riƙe muƙamin _“The student president of the university”_ a nan Cikin B.U.K. Ya sanya da yawan ɗaliban sun san shi, suna da labarin komai ance ba'a taɓa student mai farin jinin Sp Adnan Aliyu Matawalle ba.
Kallonsu kawai yake But he could not hide his surprise. Fayyad ya saki dry yana ware hannunsa yace "Surprised, Surprised Our ex- president" murmushi ba ɗabi'ar Adnan bace hakan yasa da idanu kawai yake binsu, Fayyad wanda ya kasance Class mate ɗin Adnan tun daga secondary har zuwa University da sukai Department ɗaya ya ce "yau dai ka ziyarci makarantar mu bayan wasu shekaru, You are Welcome." Sauran Students suka ce "We appreciate your visit, Sir" kai kawai ya jinjina musu Fayyad ya ce musu "You can go, yana godiya" gaba ɗaya suka bar wajan.
Fayyad ya miƙe tsaye yana faɗin "mu ƙarasa office ko?" Nan ma kai Adnan ya jinjina yana ƙoƙarin Miƙewa daga kan kujerar da yake idanunsa ya sauka akan wani I.d card fari tas dashi. A nutse ya miƙa hannunsa ya ɗauki I.d card ɗin a hankali ya duba sunan da yake jiki. ABRA KHAMAL KHAMIS. Shine Abin da idanunsa suka fara gani a jikin I.d card ɗin.
Gently ya fara bin Information ɗin dake cikin I.d card ɗin kamar haka:
Name: Abra Khamal Khamis
Reg No: ..................
Program me: Mass communication
Department: Department of Mass communication
Phone number: .............
Sai ƙyakkyawan photonta dake maƙale jiki, black ɗin Abaya ce jikinta tayi rolling kanta da veil, dimples ɗinta ya loma dalilin Murmushin da ta yi. Cikin wasu ɗakiƙo ya ƙare wa photon kallo kafin ya taɓe baki daidai nan Fayyad ya matso inda yake yana faɗin.
"What are you waiting for?" Girgiza kai Adnan ya yi a karo na farko cikin sautin Muryarsa ya ce "Nothing" "Ok.... Shall we?" Fayyad ya faɗa yana nunawa Adnan hanyar zuwa office ɗinsa, kasancewar a cikin University ɗin yake koyarwa. Kai tsaye suka nufi cikin office ɗin.
Tafiya kawai take kanta a ƙasa, gaba ɗaya hankalinta baya jikinta, jinta take wata uncomfortable ta saba duk inda zata suna tafiya tare da Salman, a yanzu kuma ita kaɗai ce gani take kamar mutumin ɗazo ne zai biyota, tana tafe kuma tana cin karo da Old Students na University ɗin, sai faɗin Sir S.p Adnan Aliyu Matawalle suke suna nufar hanyar data baro.
Ita dai ba wanda ta kula balle ta san meke faruwa, ji tayi yunwar ma ya tsaya mata.
Caraf taji an riƙe mata hannu, a gigice ta ɗaga idanunta wanda ta gani kuma yasa ta saki ajjiyar zuciya tana kwaɓe fuska tare da ƙanƙame hannunsa daya riƙe ta da shi. Salman ya ware idanunsa akan Abra yace. "Ya na ganki a hargitse?" Ta girgiza masa kai, nan da nan mood ɗinsa ya sauya a tunaninsa wani ya biyota, bai ce mata komai ba sai manyan idanunsa daya kafesa da ita.
"Let's go Faris"
Ta faɗa kamar zatai kuka tana mai sake damƙe hannunsa, Salman ya haɗe fuska a kaushashe ya ce "Ban gane mu tafi ba, you told me you are hungry" "yanzu kuma na ƙoshi, mu tafi gida tunda mun gama abinda ya kawo mu" ta faɗa tun kafin Salman ya sauke numfashi da ga maganar da ya yi.
Kasa ce mata komai ya yi, ya daɗe da sanin halin ya yar tasa, a hankali ya kama hannunta tare da nufar ƙasan wata Bishiya da ita, zaunar da ita ya yi saman Kujera a hankali Shima ya zauna cikin rarrashi ya ce.
"Kina jin yunwa sosai Yaya, ki fara cin abincin sai mu yafi ba zan barinki da yunwa har muje gida ba, kuma ba lallai Mami tayi abinci ba"
Abra ta haɗe rai, tama ƙi yarda ta kallesa baki ɗaya, ta lura akan buƙatar ta Salman baya jin mgnarta sam.
"Angel" tai masa banza, tare da ɗauke kanta gefe guda a hankali ta shiga wasa da yatsun hannunta. Salman ya zame ƙasan qwiwoyinsa hannunsa ya ɗora a cinyar Abra, yana leƙa fuskarta dake ƙasa, haɗa idanu sukai tai saurin rufe nata tare da ɗauke kai zuwa gefe.
Tashi zaune ya yi tare da zama gefen ta, takeaway ɗin daya kawo mata ya buɗe, wainar shinkafa ce mai zafi, da miyar agoshi ta sha nama sai ƙamshi take, bayan ya buɗe takeaway ɗin ya ɗauki ruwa faro tare da wanke hannunsa.
Muryarsa bata fita sosai yace "Yaya" tai masa banza ya ƙara cewa "Angel" still taƙi kulasa, gyara zama ya yi yana tura hular kansa baya saboda damunsa da tayi, kamar da ga sama taji yace "Abra...!!!" Da sauri ta juya baki buɗe saboda Mmkin jin sunanta a bakin Salman wanda bata taɓa ji ba, suna haɗa idanu ya ɗauke nasa idon, shima fuska a haɗe.
Ganin sauyin nasa yasa ta marairaice fuska tace "Faris muje gida" bai bari ta sake magana ya kama Fuskarta da tafukan hannunsa ya tallafo haɓatar sosai, baki ta buɗe Zatai magana ya yi saurin ɗora yatsarsa a bakinta ya ce "Shhhhhh" shiru ta yi wanda ba tai niyya ba, a karo na farko wani kwarjinin Salman ya ziyarci ƙwayar idanunta, ƙasa tayi da ganinta.
"Hahhhh" Salman ya faɗa a sanyaye, ba tare da ta yi musu ba, ta buɗe cute small mouth ɗin nata wanda yake ɗauke da red ɗin laɓɓan masu taushi a hankali ya saka mata naman daya ɗakko har lokacin yana riƙe da Fuskarta yana ƙare mata kallo, ita kuma idanunta a ƙasa. Tana cinye naman ya fara bata wainar shinkafar bata wani ci da yawa ba, ta girgiza masa kai ya ce "Sai kin cinye fa"
Kamar zatai kuka tace "wallahi na ƙoshi, ka cinye sauran" shima ya ce "Ni ai bance ina jin yunwa ba, karatu zaki fara dole kici abinci ƴar nan" yana faɗin hakan ya ƙara tura mata wainar a baki. Da ƙyar ta haɗiye tana zare Idanunta tace "Zanyi amai fa" yana haɗe fuska ya ce "ba wani amai yaya, na fahimci sai nayi maki da gaske ba ruwana da girmata da kikai"
Ba zato yaji ta fashe masa da kuka sosai, da gudu kuma ta miƙe tsaye tana kakarin amai amma sam yaƙi zuba, kakari take sosai jikinta na rawa, da sauri Salman ya kama hannunta ganin zata faɗi yayi saurin yi mata side hug ruwa ya bata tasha yana bubbuga bayanta "Sorry Angel, I'm so sorry" ƙin kulasa tayi sai shassheƙar kuka take, ganin da taƙi kulasa duk ya rikice daidai nan ƙawarta Khairy ta ƙaraso itama an bata admission a B.u.k.
Cikin rashin damuwa da yadda ta gansu tace "Wow yau nayi Sa'ar zuwa B.u.k Wlh" Shiru Abra ta yi Salman ya ware idanunsa yana faɗin "Sbd kin samu course ɗin da kikeso?" Ta girgiza masa kai tace "Is not like that Salman, I have never seen a man so beautiful as him" daga Abra har Salman ba wanda yace mata komai, Salman hankalinsa na kan Abra ita kuma ta haɗe fuska tana kallon Wani wajan.
Khairy baki na ƙaiƙayi ta kalli Abra tace "Wai ashe a nan shcl ɗin ya yi karatu, ya riƙe muƙamin shugaban ɗalibai, ba kiga yadda aka rufesa ba kowa na son ganinsa, kai Ubangiji ya yi halitta a nan"
Abra ta taɓe baki tace "who asked you? We have nothing to worry about... let's go Faris" dry khairy ta saka tana tafa hannayenta cikin farin ciki tace.
"Ba lallai ki yarda da kyansa ba, tunda baki gansa ba, ni da har kallon sexy eyes ɗinsa na yi, gashi wani babba mai kyan sura, irin namijin da nake so mai baƙar fata" Haka kurum Salman yaji baya son jin maganar, duk da bai san Who is she talking about ba, amma yaji ransa ya ɓaci.
Abra ta kalli Khairy tace "kuma sai ya zama dole na sani Ummulkhairy?" Khairy na ƙoƙarin magana Idanunta ya sauka akan Sp Adnan shi da Fayyad suna tahowa, jikinta na rawa tace "Look Abra, wlh shine wanda nake maki magana" daga Abra har Salman babu wanda ya juya balle suga wanda Khairy ke magana akansa.
Fayyad ya yi Murmushi yana dokan kafaɗar Adnan yace "You're kidding, it's just your pride that prevents you from finding a wife" Ya ƙare maganar yana ƙara kaiwa Adnan doka, kafin ya ɗora da faɗin.
"Aure duniya ne, ma'aurata sune kaɗai zasu fahimci abinda nake cewa, Let's keep the joke aside, you have education, money, health, you are handsome Adnan, babu macan da za tace bata sonka I'm still wondering akan abinda ya hanaka aure, Shawara nake baka tun kafin lokaci ya ƙure maka wallahi rayuwa bata da tabbas gwara ka Ajjiye masu yi maka addu'a kafin lokaci tsofa ya riske ka"
A karo na farko Sp Adnan yai wani irin Murmushi daya sanya fararen haƙoransa bayyana, wanda shi kansa Fayyad ya yi mamakin Murmushin nasa. A hankali yace. "Thank you Alhaji Aliyu Matawalle"
Fayyad ya ware idanu ya ce "it's just a suggestion. Ba lallai ka amince ba"
Su Adnan na zuwa daidai inda su Abra suke ya lumshe idanunsa kana ya buɗe ya ce
"I don't believe in true love, mata sai a hankali there is no Promise in their hearts"
Da sauri Abra ta matsa kusa da Khairy ganin Adnan na ƙoƙarin take mata ƙafa, amma yana zuwa inda take ya janye ƙafarsa zuwa wani gefe ko inda suke bai kalla ba, yana ji Khairy na cewa "Bye sir" amma ko amsawa bai ba. Salman ya nufi motarsu ganin Drivern gidansu, Abra tabi bayansa. Kusan lokacin ɗaya dasu da Adnan suka bar cikin B.u.k.
Washegari ya kama Weekend. Abra na tsaye a kicthen sanye cikin wata fitted gown ɗin green ɗin lace sai Stones masu ƙyalli, tayi simple ɗauri gashinta har baya, tattara carrot ɗin data yanka tayi, tare da green, yellow, and red pepper ta Ajjiye gefe guda. Green beans ta ɗauka wanda ta ɗan dafa, bayan ta kammala komai ta ɗauki shinkafar da tayi pi bowling ta juye ta zuwa cikin wata pot ɗin, another pot tai using wajan zuba mai mara yawa, ta zuba kayan miya, kana ta zuba su magi da spices in few minutes ta haɗa fried rice with chicken kabab. Tana gamawa ta haɗa salad wanda tai using lemon kaɗan a ciki sai pineapple juice.
Salman dake shigowa kitchen ɗin yai saurin tsayawa a bakin ƙofa yana jan numfashi tare da rufe idanunsa, na ƙamshin daya daki hancinsa. Idanunsa ya ware a kanta tun daga kan fararen yatsun ƙafarta ya fara Kallonta, zuwa hips ɗinta da gadon bayanta, a hankali ya maida idanunsa kan baƙin dogon gashinta. Cikin rashin sani ya furta.
"Rest of my life.... Angel na" Abra ta juya da sauri suka haɗa idanu ya kashe mata ido ɗaya tare da ɗaga mata gira. "like you said something?" Ta tambayesa bayan ta gama wanke hannunta a jikin sink. shiru ya yi mata sai idanu da yake binta dashi, ganin ta ɗauke kanta zuwa ɗaukan warmers ɗin data zuba abinci ciki a nutse ya ce.
"Sweetheart"
Juyawa ta kuma yi suka haɗa idanu, ta wani haɗe fuska tace "Wai me kake cewa ne,It's like calling someone's name?" Hannunsa da yake saƙale a ƙirjinsa ya zame tare da zuba su cikin Aljihu, a hankali ya ce "wane suna zan kira wanda ya shige Angel" tana miƙa masa warmers ɗaya tace "ba haka naji ba, kadai ce wani abu nada ban" Murmushi kawai ya yi mata yana girgiza kansa, shi kansa bai san lokacin da yace hakan ba.
"Kada ki manta kina using Hearing aid ne