Showing 108001 words to 111000 words out of 231718 words

Chapter 37 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

Advertisement

28 Feb 2025

14851

Kawai kin ɗagawa mutane hankali".

"Mami ni bana son Auren nan na fasa, dan girman Allah Ku dawo mini da ɗan uwana" tayi maganar tana ƙoƙarin cire ɗaurin kanta, ga numfashinta da ya fara sama.

Ammi ta girgiza wa Na'ima kai, alamar ta dena yiwa Abra faɗa.

Granny ta ce "Ji min 'ya da wauta, ke yanzu sai ki fasa Auren, aikuwa da kin yiwa kanki kutunguilar tsiya, hmm jiya ba yau ba tsohuwa ta tuna kwanan turaka, yarinya karki cuci kanki" Granny ta yi maganar tana watsa guntun goronta a baki, ta bar ɗakin, murmushi Ammi ta yi, Granny ba ruwanta haka take sakin 'yan maganganunta idan ta raya mata".

Ammi ta maida hankalinta kan Abra, ta din ga yi mata Nasiha tana rarrashinta, ƙarshe sai da aka kira Abbi video call, shima yayi ta rarrashinta, Sannan ta haƙura.
Aka samo wata mai kwalliyar ta gyara mata kwalliyar da ta fara ɓatawa da hawaye.
Na'ima ma haɗawa tayi cikin wani rantsatsten leshi fari da golden, tun daga wuyanta zuwa yatsunta gwal ne.

Hakan yayi daidai da ƙarasowar Adnan da da abokansa, haka zalika mota mota na 'yan uwan Adnan ɗin suka hallara a ƙatuwar harabar gidan Major Khamal Khamis, wadda akai matuƙar ƙawatawa.

Mami ce da kanta ta kamo hannun Abra ta fito da ita daga cikin gida, duk da kanta a sunkuye yake, ta rufe jikinta da mayafi, amma hakan be hana Adnan tsinkayen farar fatarta da ta sha gyara ba.
Nan masu police band suka sauke gangunan su, suka fara bugawa domin gabatar da parrate na ban girma ga Ango sha guɗa Sp Adnan Aliyu Matawalle, da matarsa gimbiya Abra Khamal Khamis, abun na masu ɗamara ne, dan haka parrate ɗin ya ƙayatar matuƙa, tare da crossing sword da aka gabatar duk dan murna ga amarya da ango.
A ka zo ɓangaren kamu, a kama amarya ta buɗe fuskarta, ƙanwar Hajiyar Adnan, ta ce sun biya dubu ɗari biyar a buɗe musu fuskar Amarya.
Nan wasu suka shiga tafi, yayin da Mami ta ce "ita dubu ɗari biyar yayi kaɗan". Ammi ce tsawatar dan kar ayi halin ƙaranta.
Nan aka shiga gudanar da shagali, bayan Abra ta buɗe fuskarta, wanda ba su santa ba, suka dinga jinjina kyawunta, wasu kuma suna gulmar ya za tayi da Adnan, dan da kaɗan ta wuce cikinsa.

"Sweetheart,yau ranar farinciki ce, amma ya naga kamar za kiyi kuka?" Adnan ya faɗa a saitin kunnenta.

"Wani farinciki bai taɓa riskata, Faris baya kusa da ni ba, sai a wannan lokacin, wannan ne karo na farko, ban taɓa tunanin Faris ba zai kasance da ni ba, Ranar Aurena akan high table, ana mana hotuna da ni da shi da angona ba, sai dai....." Hawaye ne suka fara saukowa da ga idanunta.

Da sauri Adnan ya ciro hanky yana share mata ya ce "dan Allah kar ki ɓata mana Wannan Farincikin, ba kowane buri namu ne yake zuwa ya cika a yadda muke so ba, kiyi haƙuri" haka ya rarrasheta, aka kammala event ɗin wannan ranar.

Daren ranar, haka Adnan ya kasance da ita a waya, yana cigba da aikin rarrashi.






Zuba mata idanunsa yayi yana kallonta, yadda take maye, cike da rashin Sabo, sai tamɓele take ya sakata a gaba kawai yana murmushi, yana zuƙar shisha yana fesar da hayaƙin a cikin iska.
Ganin tana ƙoƙarin faɗuwa ne ya sanya shi tashi da sauri ya riƙota yana murmushi "Sweetheart, it seems like you are enjoying the moment" yayi Maganar tare da kissing ɗin goshinta.

Kan makeken gadon dake tsakiyar ɗakin ya kaita, ya kwantar da ita, yana shafa dogon gashinta. Gaba ɗaya Meenal ba ta hayyacinta, ba ta tashi farkawa daga mayen da take yi ba, sai bayan magariba.
A hankali ta buɗe idanunta ta kalli in da ya idar da salla, ta tashi da sauri ta kalli agogo, a gigice ta ce "Ya a kai na kai wannan lokacin? Me ka bani haka na sha?".

"Calm down Baby, kayan caji ne fa kawai"

"Kamar yaya kayan caji, lokacin komawata gida tuni ya ƙure, me zanje in ce a gida?"

"Haba ke kuwa, kamar ba babbar yarinya ba, da alama fa kin ji daɗin cajin nan da kika yi"

Wani gululun baƙin ciki ne ya cunkushe mata zuciya, a gurguje ta tattara kayanta da mukullin motarta, tai waje.

Gudu take tamkar zata tashi sama, saboda tsananin tashin hankali, cike da fargaba da zullumi ta shiga cikin gidan, a Falo ta tarar da Mummy tana kaiwa tana komowa, tana ganin Meenal a rikice ta ce "Ke daga gidan ubanwa kike Yanzu?".

"Amm...mm..... Mummy da..dama".

"Dama me? Gidan ubanwa kika tafi? Ƙarfe nawa yanzu? Kin sanya ya tayar mini da hankali, yanzu haka ya tafi kai report gurin hukuma, akan cewar kin ɓata, ina ki ka je?".

Kan Meenal ta bata amsa, sai ga Doctor Bulama ya shigo, yana ganin Meenal rai a ɓace ya ce "Ke! Daga ina kike?"

"Ba ko ina".

"Daga ina kike?!" Ya sake tambayar cikin tsawa.

Rawar baki ta fara yi, amma ta kasa Magana, aikuwa yayi kanta ya shaƙota yana zazzare ido tare da maimaita tambayar daga ina take?"

"Haba doctor,ka bita a hankali mana, idan ka illata ta fa, ko ka manta uta kaɗaice da mu?".

"Dan ita kaɗaice da mu ba shi ya bata lasisin yin iskancin da ta ga dama ba, gidan wa kika je?".

A shaƙe Meenal ta ce "Dan Allah Daddy ka yi haƙuri, ƙawata na bi gidansu, muka tafi gurin biki daga school".

"Meyasa baki kira kin gaya mini ba, aka dinga kiran wayarki amma a kashe?".

"Nayi kuskure, amma dan Allah kayi haƙuri kar ka kasheni" da Doctor ya ƙyale Meenal, bayan ta sha shaƙar da sai da ta kusa zuwa lahira.

Hall ya haɗu iya haɗuwa, Abra ta haɗe cikin wani danƙareren Material, kai da gani ka san ba duk jiki ba, sai jikin 'yar gata.
Adnan kuwa gaba ɗaya kishi ne ya mamaye masa zuciya, yadda kowa ke ɗaukar hoton matarsa a waya, shifa wannan taron bidi'ar dan anfi ƙarfinsa ne, amma da babu dalilin da zai sanya ayi wannan taron ana kallon matarsa.

MC ne ya kira Amarya, tare da umartar ta da taje ta taho da mamanta.
Cikin takun Abra na nutsuwa, taje gaban table ɗin da Hajiya Na'ima take, ta durƙusa ta kamo hannunta zuwa filin rawa.
MC ya ce "Ki kalli Mamanki, ki ce nata kin gode, kuma kina sonta"

Abra ta kama hannun Hajiya Na'ima, ta kalli idonta murya na rawa ta ce "Thank you very much Mamina, for all you did for me Bani da Abun da zance miki sai Allah ya baki Aljanna maɗaukaiya, and I love You Mamina" ta ƙarasa Maganar tana rungume Na'ima, tare da sakin wani irin kuka mai ban tausayi.
Nan dj ya saki waƙar Wayyo Allah mamana, Na'ima ma rungume Abran ta yi tana ɗan dukan bayanta alamar rarrashi. Yayin da ta ɓalle bakin jaka, ta dinga zubawa Abra kuɗi kamar ba gobe, ji take dama Abra 'yar ta ce ta halak, da shagalin da za tayi a bikin nan yafi haka.
Haka aka yi Dinner, 'yan uwa da abokan arziki, duk sun yi bajinta, ta hanyar liƙi da bada gudunmawa.

Abbi tuni ya sauka garin Kano tare da tasa tawagar, kasancewar bayan ɗaurin Aure akwai reception na mussaman, da kuma parrate na sojoji, abunka da masu abu da abunsu.

A can birnin Sin kuwa, Salman ne zaune a wani katafaren ɗaki, a gaban madubi ya sanya hoton Abra a gaba, ya ƙura masa idanu, idan lissafinsa daidai ne, yau ne ake ɗaurawa Abra Aure, Abran da ya ƙallafa a rai, ya taso ya rayu da soyayyarta, a yau ta zama mallakin wani ba shi ba, ina ma Mami ba ta sanar masa Abra ba 'yar uwassa ba ce ta jini, da duk wannan al'amuran basu faru ba, gaba ɗaya tun da ya zo China ba ya jin daɗin garin, komai nasu daban kamar ba Normal Mutane ba, gashi ko turancin ma ba kowane ya iya ba a cikinsu, dan haka abubuwa suna masa wahala, duk da wai kafin su fara lectures, sai sunyi wata shida ana koya musu Yaren Chinese.


An ɗaura Auren Adnan da Abra, wanda dubban mutane suka sheda hakan, ɗaurin Auren da ya samu halartar manyan ƙasa daga ɓangarori daban-daban ciki har da Captain Faruk da aka tsinto Abra da shi.

Daidai gwargwado an yiwa Abra Nasiha mai ratsa zuciya game da rayuwar Aure, yayin da Granny ta ta Nasihar mai ɓaro_ɓaro ce ba rufi ba kunyar komai.

Da la'asar aka shirya Abra cikin wata dakakkiyar rantsatsiyar lafaya, Mami ta kaita gurin Abbi, yayi mata nasiha sosai tare da Adduoi da fatan shiga ɗakin miji a sa'a.
Dangin Adnan sun zo da manyan motoci, domin ɗaukar Amarayar su.

Sai dai Abra ta ƙanƙame Mami tana kuka, karo na farko a rayuwar Na'ima, tun da ta fara riƙon Abra, taji jikinta yayi sanyi, dan tun a gurin Dinner jiya Abran ta sa jikin Na'ima yin sanyi.
Abra ta ƙanƙame Na'ima tana faɗin "Mamina, a zaman mu idan na yi miki laifi ki yafe mini, Mami bana son barinki".

Anty Suwaiba ce cikin masifa ta ce "Wai ke bayinki ne mutanen da suka tsaya suna jiran ki, dalla ki fito ki wuce mu tafi"

A hankali Na'ima ta shafa bayan Abra ta ce "Na yafe miki Abra, Allah ya baku zaman lafiya, muje in rakaki bakin Mota".

"Mami to ke yaushe zaki zo?".

"Very soon" daga haka ta ja hannun Abra zuwa bakin mota. Da ƙyar Abra ta yadda ta shiga, tana kuka tana ɗagawa Mami hannu.

Anty Suwaiba ta ce "Ke Na'ima, wai me kike yi hakane kamar kin damu da tafiyar yarinyar nan? Allah ya raba ki da ƙwallon mangwaro kin huta da ƙuda, amma naga kamar kina cikin damuwa? Wai ni fa kamar ƙwalla nake gani a idanun ki".

Jiki a sanyaye Na'ima ta ce "Gaskiyar Husawa da suka ce, 'Sabo turken wawa' a zamana da yarinyar nan ban taɓa jin abunda na ji ba jiya da ta kalli idanuna tana mini Addu'a tare da jaddada soyayyarta a gareni, idanunta ɗauke da zallar soyayyar uwa da ɗa, duk da kwashe shekarun da nayi ina azabtar da ita, amma tana mini biyayya fiye da yadda ɗan da na durƙusa na haifa yake mini, ko ba komai da ina ganin gilmawar ta da ta Salman, amma Yanzu shi ya tafi, ita ma kuma haka".

"To shine me? Ke ba hutunki bane bama, ta je can ta ƙarata Allah ya tsare miki mijinki da ɗan ki".

Na'ima ta ce "Hakane, dama babban fatana kenan, ta bar mini gida, shekarun da mukayi Allah ya amfana, kawai dai kin san zuciya".

"Ke dalla can manta da ita".


Awanni uku cif, da magariba su Abra suka isa garin Kaduna, aka fara kaita gidan su Adnan, aka yi mata nasiha, suka bata kyaututtuka, sannan suka wuce da ita gidanta.

Tubarkallah Adnan ya ƙera mata gida na gani na faɗa, Abbi kuma da Hajiya Na'ima sun cika gidan da kaya na kerewa sa'a, Masha Allah gida yayi komai tsaf.

Wanda suka rako Abra daga Kano, suka koma gidansu Adnan su kwana a can, daga nan su koma Kano, Abra ji tayi Kamar ta tashi ta bisu, haka suka watse suka bar Abra.

Abra ta zauna jiran shigowar Ango, sai dai har ƙarfe goma sha ɗaya ba ango ba dalilinsa, tun Abra na jira har ta fara gajiya, tsoro ya fara kamata, ta takure a ƙuryar gado, gaba ɗaya tsoro ya baibayeta.
Abu kamar wasa har ƙarfe biyu na dare, Adnan be shigo ba, ta ɗauko wayarta domin ta kirashi amma wayarta ta ɗauke babu caji.
Rashin sanin abun yi ya sanya ta fara kuka.
Haka Abra ta kwana a zaune, sai ɗan gyangyaɗi da ta dinga yi daga zaune a haka har Asuba tayi.

A tsorace ta lallaɓa ta shiga banɗakin da ke cikin ɗakin tayi alwala, ta gabatar da sallar Asubahi, ta koma gefe ta takure.

Mami 'yan biki sun watse, sai wanda ba'a rasa ba.
Tayi wanka tana ƙoƙarin shiryawa, ta ga wata takarda ta faɗo daga cikin wardrobe ɗin ta.
Ta sunkuya ta ɗau takardar ta buɗe, rubutun Salman ta gani a jiki, hakan ya sanya ta sake gyara tsayuwarta ta fara karantawa.
*Assalamu alaikum warahmtullah. Ina fatan lokacin da saƙon nan zai riskeki kina cikin ƙoshin lafiya Mamina. Na san zakiyi mamakin ajiye miki wannan takarda da nayi, amma ba abun mamaki bane, duk da ba zan kira hukuncin da kika yanke a kaina kuskure ba, amma zan iya kiransa da shamaki da farinciki na, ta hanyar nisata ni da abu mai daraja da nake matuƙar ƙauna. Domin sake nesanta kaina da Abra kasancewar na san mallakin wani zata zama, ina mai sanar miki da cewa daga ranar da na bar Nigeria ba zan sake dawowa ba har Abad, dan muddin ina Nigeria, ruhina yana tare da Soyayar Abra, dan tabbatar da samun farincikinki da nutsuwar ki, ba zan sake dawowa Nigeria ba. Idan kuma kika yi ƙoƙarin tursasa sai na dawo, zan bar China in koma ba im da ba wanda ya sani. Ki huta lafiya Mamina, ki gaishe mini da Abra tare da yi mata fatan Alkhairi a rayuwar Aurenta. Salman Khamal Khamis*.



Littafin kuɗi ne,biya ₦300 via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank... Idan katin waya ne zaka Turo 500 shaidar biya 08081012143
[10/11, 7:20 PM] Abk: Take jikin Hajiya Na'ima ya ɗau rawa, hannunta ya fara karkarwa, ta nemi guri ta zauna a gefen gado, wani irin gumi yana tsatstsafowa a goshinta, a hankali ta furta "Na shiga uku, mai yaron nan yake nufi dani ne?" Cikin azama ta miƙe, ta ɓoue takardar ba tare da ta nunawa kowa ba.


Sai ƙarfe takwas na safe sannan Adnan ya shigo gidan, shi ma bai shigo inda take ba, maganarsa ta jiyo a parlour suna gaisawa da waɗanda da suka kawo ta, hakan ya sa ta fita parlour'n da sauri, zuciyarta cike da ɗokin ganin shi.


Gaishe shi ta yi, sarari ya ji ta amma ya ɗauke kai kamar bai ji ba, hakan ya faɗar mata da gaba. Amma dai ta daure suka yi sallama da waɗanda suka kawo ta, har da kukanta lokacin da suka fice daga parlour'n.


A tunaninta bayan fitar su Aunty Suwaiba Adnan zai taho gare ta cikin zumuɗi ya rarrashe ta, amma sai ta ga saɓanin haka. Ƙafa ya ɗora ɗaya akan ɗaya yana latsa wayarsa, tamkar bai san da halittar ta a parlour'n ba. Cikin tsananin shock Abra ta ce. "Baby! Me yake faruwa ne? Jiya ba ka dawo ba ka bar ni na kwana ni kaɗai cikin jin tsoro, yanzu kuma ka dawo amma ka yi kamar ba ka ganni ba." Tamkar da dutse take magana, ko motsi bai yi ba da sunan ba ta amsa. Ƙura masa ido ta yi tana kallon shi cikin mamaki, Adnan ɗinta ne kuwa wannan ko an canza mata wani? Adnan ɗin da ya ci burin ganin wannan ranar da za ta kasance a gidansa, amma me ya yasa ya yi mata haka? Me yasa tana yi masa magana ya share ta? Ko dai something bad happened to him? Tunanin hakan ya sa ta matsawa kusa da shi da niyyar ta ji abun da yake damun shi. Wata uwar harara da ya ɗago kai ya banka mata yasa ta tsayawa cak a inda take cikin bugawar zuciya. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un." Abun da ta ambata a fili kenan. Rasa abun yi ta yi hakan ya sa ta koma ɗakinta cikin sauri, faɗawa kan gado ta yi tare da sauke wani wahalallen numfashi. So take ta tuno ko ta yi wa Adnan wani lefin amma ta kasa, hakan ya sa ta fashewa da kuka. Sai da ta yi mai isarta sannan ta tashi ta shiga toilet ta wanke fuskarta. Bayan ta fito ta tsaya a gaban mudubi tana kallon kanta, cikin ƙoƙarin son gano ko wani abun Adnan ya gani a jikinta da bai masa ba, amma ba ta ga komai ba. Duk da ita ba ma'abociyar son kwalliya ba ce amma haka ta zage ta tsantsara ta tare da kafa ɗaurin ɗankwali mai kyau, ita kanta ta san ta yi kyau, duk da yanda take jin wata irin fargaba a cikin zuciyarta amma sai ta murmusa, ta san dole kwalliyar tata ta burge Adnan. Daddaɗar humra mai daɗin ƙamshi ta shafe jikinta da ita, sannan ta fita zuwa ɗakin Adnan. Sai da ta fara shiga kitchen ta haɗa masa breakfast wanda aka ajiye dan shi sannan ta nufi ɗakin nasa. A zaune ta tarar da shi a kan gado yana operating system. Cikin sanyin jikinta ta yi masa sallama, ko d'agowa bai yi ba balle ya amsa mata. Hakan ya ƙara tsinkar mata da gaba, zuwa yanzu kam ta gane da akwai matsala. Kanta a ƙasa ta ce. "Ga abinci." Nan ma bai kula ta ba, kawai sai ta fashe da kuka cikin rashin sanin abun yi. Ta daɗe a duƙurshe tana kuka mai tsuma zuciya, yana jin ta amma ko tari bai yi ba, ƙarshe ma tashi ya yi ya ɗauki car key ya fice ya bar mata gidan. Hasbunallahu..... kawai Abra take maimaitawa, a ranta tana tambayar kanta me yake shirin faruwa da ita ne? Me Adnan yake nufi da ita? Jiki a saɓule ta miƙe ta koma ɗakinta ta kwanta akan gado ta cigaba da kukanta, kewar Faris da Abbi da Mami na nuƙurƙusar zuciyarta, wani azababben ciwon kai ne ya far mata lokaci ɗaya, cikin dauriya ta janyo bargo ta lulluɓe jikinta, saboda yanda take jin wani sanyi na ratsa gaɓoɓin jikinta, tamkar wadda za ta yi zazzaɓi, a haka wani wahalallen bacci ya ɗauke ta.



Sai Azhar ta farka, shi ma ƙarar doorbell ya tashe ta, cikin sauri ta miƙe ta shiga toilet ta wanke fuskarta da ruwa sannan ta fito ta saka hijabi ta fita. Mata ne kusan su takwas ta gani, cikin fara'a ta tarɓe su tare da yi musu iso. Bayan sun zauna sun gaisa ta kawo musu drinks da kayan garar ta, anan suke gabatar mata da kansu. Dukkansu cousins ɗin Adnan, Ƴanmata shida sai matan aure biyu. Ta ji daɗin zuwansu ba kaɗan ba, dan ba ƙaramin ɗebe mata kewa suka yi ba. Sai dai duk bayan sakanni idan ta tuna Adnan da yanayin da ya nuna mata ɗazu sai gabanta ya faɗi. Da abinci suka zo, hakan ya sa ba ta yi girki ba shi suka ci, ita ɗan caccakalar abincin ta yi kaɗan ta ci ba don daɗi ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login