Showing 156001 words to 159000 words out of 231718 words

Chapter 53 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

Advertisement

28 Feb 2025

14914

kaji dalilin kiran ko?".

"Ba zan ɗaga ba idan na ɗaga me zan miki?".

Cikin shagwaɓa ta ce "Please calm down baby, dan Allah ka fuskance ni".

'malama ki faɗi abin da zaki faɗa ina da ayuukan yi".

"Amma ai naga yanzu ba lokacin aiki bane".

"Zaki faɗa ko sai na kashe wayata?"

Meenal ta marairaice ta ce "Yaushe zaka zo, sai mu yi magana".

"Haba Meenal, ai ni da gidanku har abada, ko har kin manta wulaƙancin da ki ka yi mini?"

"Dan Allah baby ka daina tunawa, sharrin shaiɗan ne, Please come to me haba My usy".

Usman ya ce "Ke dakata, ba wata yaudara ko kalaman ƙarya da zaki yaudareni da su in amince da ke".

Kawai ta fashe da kuka "Allah ba kalaman yaudara bane, dan Allah baby ka zo, Wallahi kai nake so".

Usman ya ce "Eh saboda wancan ya gudu ko?"

"Wallahi be gudu ba, kawai dai zuciyata kai take so".

"Kin manta da rashin ɗaga wayata, da wulaƙanci da ki ka dinga yi mini a kan saurayinki ko?".

"Dan Allah ka daina tunawa, kuskure ne ba zan sake ba".

"Shikenan zan yi shawara".

"A'a dan Allah ba sai kayi ba, Please Baby me, wlh Ina sonka Sosai na yi missing ɗin ka".

'hmm Allah yasa da gaske ki ke".

"Wallahi da gaske nake".

"Shikenan zan duba".

"Yawwa Baby ina nan ina jiranka" bayan sun yi sallama tayi ajiyar zuciya ta kalli wayar ta ce "Gara tun wuri in yiwa kai na ƙiyamul laili, in lalaɓo shi ya dawo".

Jin Abra ta zo,  ya sanya su Ammi suka zo, suka cika gidan wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Abra ba, Mutanen da ba ta da wata alaƙa da su ta jini, amma suna nuna mata soyayya haka, har hawaye ta dinga yi wanda basu san dalili ba, suka din ga yi mata nasiha a zatonsu duk kewarsu ce ta sanya ta haka.
Sai da duk sun lura da irin ramar da tayi, ba wanda yayi Magana sai granny, da ta dinga bin ƙwaƙƙwafi a kan lallai sai ta ji mai ya samu Abra haka dan da alama ba iya laulayi ke damunta ba, amma Abran ta ƙi faɗa.

Kwanan Abra biyu Adnan ya zo ya ce tafiya za suyi, Abra tamkar ta ɗora hannu a ka tayi ihu, gashi tun da ta zo Abbi baya gari basu haɗu ba, ta shiga cikin fargabar komawa cikin uƙubar Adnan, amma ta koma duba abinda ka iya faruwa idan da ta sanar da halin da take ciki, haka nan ba yadda ta iya, ta bishi suka koma Kaduna.

Faris na zaune a aji ana mus lectures, sai dai ya ji bugun zuciyarsa na matuƙar ƙaruwa, ya rasa abin da yake masa daɗi, kuma ya rasa dalilin faruwar hakan, yayi ta maimaita "Hasbunallah wa ni'imal wakil" hakan ya sanya ya ɗan samu sassauci.

Malamin da ke musu lectures na Anatomy yace su yi connecting Wifi a system ɗin su, zai tura musu wani abu.

Salman yana Connecting, yaga messages na shigowa ta Gmail ɗinsa, dan rabonsa da amfani da daya har ya manta.

Ana tsaka da lectures, amma hankalinsa na kan saƙonnin, ya fita ya tafi Gmail ɗin sa, ya ci karo da saƙon Abra. Cikin hanzari ya buɗe ya fara karantawa.
Subhanallah duk da yadda sanyin A.c ke Ratsa ko ina a ajin, amma wani irin gumi ne ya shiga karyo masa, ya kasa gane kan in da saƙon nata ya dosa gaba ɗaya, take jikinsa ya ɗau rawa ya kasa mayar da hankali a kan karatun.
Har aka kammala bai fuskanci komai ba, haka ya koma masaukinsa, ya karanta saƙon nan ya fi sau talatin yana sake jujjuya saƙon a zuciyarsa.
Tuni zuciyarsa ta fara raya masa ya bar abin da yake, ya shirya ya tafi Nigeria ya ga Abra.
"No she's married now" ya faɗa da ƙarfi yana rintse idanunsa.
So yake ya cire Abra daga ransa, ya manta da shafin soyayyarta, dan haka dole ya nesanta kansa da duk wani abu da ya shafe ta.
Kai tsaye ya fara ƙoƙarin goge message ɗin da ta turo masa, amma hannunsa ya hau rawa, ga wasu zafafan hawaye da suka fara sauka a fuskar sa.
Copying ɗin message ɗin yayi, daga nan ya goge shi gaba ɗaya ya dangwarar da system ɗin ya zauna yana kuka.

Tafiyar Abra da kwanaki uku Abbi ya dawo gari, sai dai haryanzu tsawon wannan lokaci ya ƙi sakin jiki da Mami su koma kamar da.
Ta same shi a part ɗinsa, ta kai masa Abinci, bai ce mata uffan ba ya ci Abincinsa ya cigaba da sabgar gabansa.

Ta ɗan gyara zama ta ce "Amm, Man Abra ta zo ita da Adnan kwananta biyu sannan suka tafi".

"Good, Allah bai yi zamu haɗu ba, na je gidan nata da kaina in dubata".

"Hmm, wai ashe Salman ya je gidanta bamu sani ba?".

Ɗan juyowa Abbi yayi ya kalli Mami ya tsuke fuska ya ce "A kan me zai je mata gida, ko bai san matar Aure ba ce yanzu, salon yaje ya janyo mata matsala a gidan Aurenta?"

"Ai shiyasa na ke son a yiwa tufkar hanci, har ya iya zuwa Nigeria yaje gidanta amma mu bamu ganshi ba, Akwai matsala, akwai buƙatar kaje can ƙasar da kanka".

"Ban gaya miki kar ki sake yi mini zancen inje nemo miki ɗanki ba? Ba in da zani".

"Dan Allah kayi haƙuri ba dan halina ba, kar in rasa ɗana kuskure ne na riga na yi shi, dan girman Allah Major ka yi haƙuri".

Miƙewa yayi ya ce "Sai kuma ki yi". Da sauri ta zube a kan ƙafafuwanta ta riƙe ƙafarsa tana kuka "Don Allah Maajor kar ka yi mini haka, dan Allah ka yi mini afuwa". Kuka take sosai kamar ƙaramar yarinya wanda hakan ya sanya tausayinta ya kama shi.

Hannunsa ya sanya ya ɗagota tsaye ya ce "ki daina mini kuka, zan ga abin da zan yi a kai"

Rungume shi ta yi tana kuka ta ce "Thank you very much dear".

Abin duniya ya sanya Abra a gaba, dan yanzu idan jikinta yayi ƙaiƙayi ta sosa sai wani irin dabbare dabbare ya fito a kan fatarta ga wasu irin ƙananan ƙuraje da ke fito mata har cikin kanta, ta yanke shawarar idan lokacin komawarta awo yayi, za tayi musu bayani su bata magani.

Haka nan tana kwance ta ji ba abinda take buƙata sai kasancewa a jikin Adnan.

Miƙewa tayi ta fito falo, ta tarar da Adnan yana zaune yana aiki a kan system ɗin sa, takawa tayi a hankali ta ƙarasa in da yake ta zauna, ba tace masa komai ba, shima bece mata ba, a hankali ta zame ta kwanta a jikinsa tana sauke numfashi, tana cigaba da jin tamkar ana kakkarya ƙasusuwan jikinta.
Ture system ɗin yayi ya janyota jikinsa, sai da a wannan karon yayi mamakin samun haɗin kanta, sainda ya bari tayi reaching highest peak, Sannan ya tureta da ga jikinsa, tare da faɗin "Jarababbiya kawai" bin sa ta yi da ido galala tana kallon ikon Allah. Ya miƙe ya bar mata falon baki ɗaya.

Haushin kanta ne ya kamata, da ba ta zo in da yake ba da duk haka bata faru ba, amma ya za tayi ita kaɗai ta san mai take ji a jikinta, kasancewarta a jikinsa skin to skin yana sanyawa ta ji sauƙin zafin da take ji a cikin jikinta.

Haka ta lallaɓa ta koma ɗakinta, sai dai ba kunya Adnan ya dawo cikin dare yayi abin da Allah ya nufe shi da yi.

Lokacin da yake ƙoƙarin tashi, ta rirriƙe shi tana kuka ta ce "Dan Allah Sp ka tsaya tare da ni, ko bacci in samu in yi, ɗumin jikinka kawai nake buƙata, dan Allah".

"Kin daɗe ba ki ji ɗumin jikin nawa ba? Dalla cikani in je in kwanta, gobe in Allah ya kaimu ƙarfe huɗu zan  in tafi Enugu".

"Sp a haka zaka tafi ka bar ni? Dan Allah kar ka tafi ka barni a wannan halin".

"Hmm kalleki da Allah, ƙil da da ɗigon imani a zuciyar mahaifinki, da kin bani tausayi, amma da na tuno mahaifinki sam sai in kasa jin taisayinki, cikani dalla in kin ha dama ki tashi ki gyara jikinki, ko ki ta zama da najasa ƙazama" haka Abra ta bi shi da ido, tana zubar da hawaye.

Washegari da safe da ƙyar ta iya tashi, ji take tamkar iska zata ɗagata ta watsar, salla kawai ta iya yi ta koma ta kwanta ko Abinci ba ta ci ba.

Tana nan kwance salla kawai ke tashinta, Adnan ya shigo ɗakinta, ya tarar da ita a cikin bargo.
Haushi ne ya kama shi, gani yake har da langwai Abra ta ke yi.

"Wai ke malama meye haka? Sai kace a kan ki aka fara ciki? Dalla tashi". Shiru ta yi masa, ita da da wannan masifar da yake mata, dama rungumeta zai yi taji ɗumin jikinsa.

Yaye bargon yayi, ya janyota "Ke kullum cikin kwanciya kamar ruwa, ki dinga ƙwarara jikinki malama".

"Ba zan iya ba ne, ni kaɗai na san me nake ji, dan Allah ka yi mini Alfarma, ko mintuna uku ne in yi a jikinka".

Gefen fuskar Abra ya kalla, ya ga wasu ƙananan ƙuraje sun mata dabbare-dabbare a gefen fuskarta ba kyan gani, ya kalli hannunta in da ya riƙe, ya ga har hannunta duk sun feso. Da hanzari ya cikata ya ja da baya, saboda yadda tsigar jikinsa ta tashi.

"Meye wannan a jikinki haka?"

Ta kalli jikinta ta ce 'Nima ban sani ba".

"A haka kike cewa in rungume ki? Allah ya sa ba da wannan abun a jikinki na haɗa shimfiɗa da ke ba jiya, wannan ai ƙurajen ƙazanta ne, wannan ai ƙarzuwa ce. Kinga ni ga jakata can a Falo na shirya, sai jibi zan dawo an turani aiki"

"Dan Allah kar ka tafi ka bar ni a haka, dan Allah Adnan".

"Saboda me na zan tafi ba, in zauna in cigaba da kallon wannan ƙazantar".

"Adnan ka yaudareni da daɗaɗan kalamanka na amince na aureka, Ruhin Adnan Alyu Matawalle, Zan rayu da ke in kula da ke, zan kasance mai tausayi a gareki, da duk irin wannan alƙawarurrukan, amma ka kasa cika ko guda. Shikenan ka je Allah ya yafe maka, Ya kai ka in da zaka lafiya" ta juya tana ƙoƙarin kwanciya ya ga yadda tsakiyar kanta duk babu, ya zube. Ga wannan ƙurajen duk sun yi tambari a gadon bayanta.
Ya sa kai ya fice ya bar gidan, yana cigaba da jin yadda tsigar jikinsa ke tashi.

Kwana biyu ya zaman banɗaki ma da ƙyar take iya zuwa, dama Abinci ba'a magana ba iya ci take ba, ta yanke shawarar zuwa Asibiti, dan ba zata iya jure cigaba da zama a haka har ranar awonta ta zagayo ba, dan da wani irin ciwon baya da ƙafafuwa ta tashi.

Da ƙyar tana haki ta fito harabar gidan, da yake tun lokacin da ta gudu gidan su Adnan, ya kawo maigadi ya ajiye a gate.

Mai gadin na ganin Abra na bin bango, ya taso da gudu yana faɗin "hajiya lafiya?"
Kan tayi Magana, taga gari yayi mata duhu, yana jujjuya mata, ta yanke jiki ta faɗi a ƙasa.

Mai gadin ya fita da gudu, ya ƙwanƙwasawa maƙwabtansu ƙofa, da gudu suka dawo tare da maigidan, suka tarar da Abra a kwance a ƙasa, maƙwabcin ya kira matarsa suka sanya Abra a mota zuwa Asibiti.

GY BULAMA HOSPITAL AND MATERNITY


Ba free bane na kuɗi ne ₦300 kacal ku tuntuɓe mu a kan lambar wayoyin mu
08081012143
09047871750
[10/28, 5:00 PM] Abk: Cikin gaggawa suka shiga da Abra Asibitin.

Bulama baya nan, doctor Aminu ne a bakin aiki, cikin gaggawa suka biya kuɗin ganin likitan, kasancewar maƙocin su Abran yana da file a Asibitin.


Doctor Aminu ne yaje kan Abra, ya tambayi ina document ɗin ta na awo?

Maƙwabcin ya ce "Wallahi ban sani ba, matar maƙwabcina ce".

Doctor Aminu ya ce "Babu halin in taɓa ta ban san history ɗin ta ba, dan haka a nemo mijinta".

Aka kira lambar Adnan ta ƙi shiga, gashi ba wanda ya ke da lambar wani na Abra.

Maƙwabcin ya ce "A taimaka a duba ta, a bata taimakon gaggawa mana".

Doctor ya ce "Bani da ikon taɓa ta banga documents ɗinta na awo ba, kuma kaga tases na ANC a Asibitin nan dubu hamsin ne, abu ɗaya zan iya yi muku, kuju ku yi scaning yanzu a kawo, kan in tashi idan na tashi sai dai ku jira likitan yamma.

Haka suka kwashi Abra suka tafi sacaning, sai dan kan su dawo liktan ya tafi, sai dai su jira Bulma, wanda sai biyar zai shigo.

Gaba daya kuma an rasa lambobin Adnan, maƙwabciyar ta koma gidan Shi ta duba ko zata ga wayar Abra, amma ba ta gani ba.

A haka Abra ta farfaɗo, tana kiran sunan Allah sai juyi take Saboda azabar ciwon da take ji. Ba yadda ba suyi da Abra tayi magana ba, amm ta kasa salati kawai take yi, tana ambaton Allah.

Sai biyar da kwata sannan Bulama ya shigo, ko da ya shigo Nurse ɗin da take duty taje ta yi masa bayani, bai je kan Abra ba sai cewa ya yi sai sun biya wannan dubu hamsin ɗin ta awo, sannan zai dubata kuma wannan scaning ya nuna akwai matsala dole ayi aiki, a cire cikin da gaggawa kar a rasa jaririyar, saboda ruwan da take ciki yayi kaɗan, dan haka sai an biya wannan dubu hamsin na awo da ba ta yi a Asibitin ba, sanan a biya dubu ɗari biyu da hamsin wanda za a yi mata aiki.

Maƙwbcin ya ce Gaskiya ba zai iya biyan wannan kuɗin haka bai sai dai aita jarraba lambar mijinta har a samu.

Matar maƙocin ta je ta samu Nurses ta ce "dan Allah ko wata allurar ce ku yi mata kan mijinta ya zo, Wallahi ko nawa ne zai biya"

Ɗayar ta ce "Wallahi bamu da ikon yin hakan, tun da baku biya kuɗi ba, amma bari inje in tambayi likitan.

Nurse ɗin ta koma gurin Bulama a fusace ya ce "Ke kar ki isheni, ba a biya kuɗ ba ya zan yi? Kuje ku yi mata wata analgesic ɗin ta samu releif.

Nurse ɗin ta fito tana tunain wace allura ce analgesic, tun da ita food hygiene ta karanta ba Nurse ba ce.

Gashi ita ganinta abun kunya ne ta tambayi abokan aikinta, da haka ta jeta ɗauko wata allura  da take kyautata zaton ita ce Analgesic.

Ta huda Abra ya kai sau bakwai sannan ta samu jijiyarta, ashe ba a allurar a jijiya, bayan ta gama yin allurar ta tafi mintuna talatin jini ya ɓallewa Abra.

Innalillahi wa Innalillahi raji'un, a guje matar da suka kawo Abra ta je ta samu Nurses ɗin ta gaya musu, suka zo suka duba suka tafi suka gayawa Bulama, amma ya ce 'ba Abin da zai iya a kai sai an biya kuɗin aiki.



Adnan kuwan sai bayan magariba ya dawo daga tafiyar da ya yi, ya tarar gida ba kowa har maigadi, ransa ya ɓaci, ya duba ɗakin Abra amma bata nan, dama yana yi yan tsantsame jikinsa dan baya son ya ganta da wannan abun na jikinta.

Ya duba kaf gidan bai ganta ba, a fusace ya fito harabar gidan, zai ɗau mota ya fita sai ga mai gadi ya dawo.

"Daga ina kake? Dama na ɗauke ka ne dan ka dinga tafiya yawonka kana bar mini gida a buɗe?"

"Yi haƙuri Yallaɓai, matar gidan ce ba lafiya an nemeka a waya ba a samu ba, an kaita Asibiti"

"Asibiti, kamar yaya waye ya kai ta?".

"Ni da maƙota ne, ana ta neman layinka ance aiki za ayi mata, sun ƙi taɓata saboda ba a biya kuɗn aikin ba".

A gigice Adnan ya ce "Wane Asibitin aka kai ta?"




Dan jim mai gadin ya yi alamun son tuno sunan asibitin.

"I'm asking you Malam, Ina kuka kai mini matata? Ka tsaya kana kallo na kamar yau ka fara gani na?" Adnan ya faɗa cikin tsawa.

Cikin girmamawa mai gadin ya ce. "Yallaɓai sunan asibitin nake tunowa, na manta amma kamar ko BULAMA mene ne?"

"What! Me ka ce?" Adnan ya tambaya cikin ƙaraji tamkar zai fasa gidan da muryarsa.

"Asibitin Bulama." Mai gadin ya ba shi amsa.

Wani ɗan ƙaramin ihu Adnan ya saki ya nufi Motarsa cikin sauri-sauri gudu-gudu kamar sabon kamu, mara masa baya mai gadin ya yi zuciyarsa cike da mamakinsa gami da tausayinsa.


Duk da uban gudun da yake tsalawa a kan titi tamkar don shi kaɗai aka yi amma gani yake kamar ba ya tafiya baya ma yake komawa. Mai gadi kuwa addu'a kawai yake yi a cikin zuciyarsa Allah ya kai su lafiya.


Suna shiga asibitin ya yi parking a tsakiyar hanya ya fito ko kashe Motar bai yi ba. Cikin sauri mai gadi ya bi bayansa. Alhaji Nura maƙocin su Abra yana ganin Adnan ya gane shi, kamar yadda shi ma Adnan din ya gane shi, duk da ba sa wata mu'amala amma suna haɗuwa time to time su gaisa. Cikin jin daɗi da farinciki ya miƙe yana faɗin. "Ranka ya daɗe sannu da zuwa, tun ɗazu....."


"Uban wa ya kawo mini mata wannan tsinannen asibitin?" Ya faɗa cikin cika da batsewa.


"Subhanallahi! Me ya yi zafi ranka ya daɗe? Ni na ce mu kawo ta nan saboda muna da file, gudun kar mu je wani asibitin mu sha wuya, ganin mawuyacin halin da mai ɗakin naka take ciki?" Cewar Alhaji Nura cikin tausasa harshe.

Cikin tsantsar tashin hankali da damuwa ya ce. "Where is she? Ina Matata? Me ya same ta?" Ɗakin da take matar Alhaji Nura ta nuna masa, bai ce komai ya nufi ɗakin.


"Ikon Allah, baban Rahama lafiyar mutumin nan kuwa ƙalau? Daga taimako zai zo yana mana masifa? Mene aibun asibitin nan? Kuma ko tsayawa mu yi masa bayani bai yi ba ya yi gaba."

"Ki yi masa uzuri, kin san mu maza muna da rauni a kan ku matanmu, idan kika lura ba ya hayyacinsa, a birkice yake."

Tsaki Maman Rahama ta yi ta ce. "Ya san da hakan ya tafi ya bar ta ita kaɗai a cikin gida, kuma ya san ba lafiya ce da ita ba, ni wallahi duk haushinsa ma ya cika mini zuciya." Murmushi kawai Baban Rahama ya yi bai ce komai ba.


Nurse ɗin da ta yi wa Abra allura tana bakin ɗakin da take tsaye cikin tashin hankali, don ta rasa ya za ta yi ta tsayar da jinin da take zubarwa, kuma tana tsoron ta faɗa wa wani gudun kar ta fuskanci hukunci. A haka Adnan ya ƙaraso kamar wani mayunwacin zaki yana huci, bai bi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login