Showing 204001 words to 207000 words out of 231718 words
Chapter 69 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
lallaɓata.
Adnan kuwa yana kwance a gadon asibiti, an ɗaura masa drip, sai dai yadda yake numfashi kawai ya isa ya tabbatar maka da cewar, yana jin jiki, daga nesa ana iya ganin yadda ƙirjinsa ke fat-fat da sauri da sauri.
Abbi kam mamaki ya cigaba da yi, dama Adnan ya san mahaifin Abra, amma yayi shiru da bakinsa bai faɗa ba? To yaya ma aka yi ya tabattar da Bulama ne mahaifinsu, ko dai zafin ciwo me ya sanya shi faɗar hakan, suka biye masa suka kira bawan Allah.
Hajiya Saudat ta rasa in da zata saka kanta, abin duniya ya isheta, ga Meenal a kwance ba lafiya tun da aka yi aikin nan, ta ƙi lafiya, an cire mahaifa ɗungurun gum, ba ta taɓa sanin Meenal na bin maza ba, ga uwa ba, abin da Bulama ke shirin yi, idan bar tone tone yayi yawa, tabbas akwai Matsala, dan daga ita har shi suna cikin tsaka mai wuya, nan ta koma tunanin yadda zata shawo kan lamarin.
Wayarta ta ɗauko, ta kira layin Bulama, ba ta damu da kuɗin da za a ja ba a waya, saboda kiran lambar ƙasar waje.
Har ta fidda ran zai ɗaga, ya ɗaga wayar.
"Hello, kana ina ne?"
Haushi ne ya kama Bulama ya ce "Meye hak sai kace wani ɗanki? Ya ma dace ki kirani a halin yanzu? Kin fi kowa sanin ina na tafi, ina tare da Rumaisa, kuma sai ki kirani a waya?"
"Dan me ba zan kirak a waya ba, in ruwana da wata Rumaisa? Ka tafi ka bar ni da yarinya da larura, ko ka kira kaji ya jikin nata"
"Saudat, abin da ya samu Meenal, ke ta shafa da ke da ita, ni ban yiwa Meenal tarbiyyar taje ta bi maza a waje ba, har ta zubar da ciki wanda ya kusa ajalinta ba, dan haka ki gaggauta rabata da gidana kan in dawo, i disowned her as my child, taje ta nemi wani uban".
"Wallahi ƙarya kake yi, Meenal jininka ce, 'ya ɗaya tilo da Allah ya baka, dan haka dole muyi haƙuri da ain daya sameta mu riƙeta".
"Dole kiyi haƙuri dai, amm banda ni ku san yadda zaku yi ke da ita" ya katse wayarsa.
Jifa tayi da wayar tare da taune lips ɗinta na ƙasa 'Anya zancen nan bai tabatta ba na cewar yaran nan suna raye ba, tun da har ya iya nuna halin ko in kula ga 'yar da ya ƙallafa ransa a kanta kasancewar ita kaɗaice ba? To yaya aka yi yaran suka rayu, bayan tun a Asibiti aka ce ba su zo da rai ba? Wane al'amari ne haka mai ban mamaki? Anya ba ƙarya bace da rainin hankali kawai? To amma hotunan da aka aiko masa fa kika ƙona' wata zuciyar ta tambayeta. Tabbs yarinyar jikin wannan hoton duk in da ta fito tana da alaƙa da Bulama. To ko dai matan banza ya fara bi? Aka haifa masa ita? Haka ta dinga tunani barkatai, ba tare da ta samo amsoshin tambayoyin ta ba, sai dai ta san tasowar wannan lamari barazana ne a gareta da Bualaman kansa, mussaman a kan sirrin da suka yi shekaru suna binnewa.
Abba ne da Abbi tsaye a kan Adnan, da aka samu ya ɗan farfaɗo daga fita hayyacin da yayi, lokaci ɗaya duk ya yi rama, yayi zuru-zuru, Mami da Hajiya Mama kuwa suna reception, suna wa Adnan Adduar samun lafiya, saboda ya sha wahala.
Abbi ya numfasa ya ce "Yanzu muna jiaran dawowar wannan mutumin, sannan shi Adnan ya ƙarasa warkewa, mu ji yaya aka yi suka zama 'ya'yan mutumin?".
Abba ya ce "Ba zamu jira sai ya warke ba, dole ai wadda za ayi idan mutumin ya dawo gari, ko mu muje, ko shi ya zo ya same mu".
Abbi ya gyara tsayuwarsa, yana kallon Adnan, a lokacin da Adnan ya gyara kwanciyarsa, yana bin sun Abbi da ido.
Abbi ya ce "sannu Adnan, Allah ya baka lafiya, in dai a ka Afra ne, ka kwantar da hankalinka, ni zan rarrasheta, za a aura maka ita insha Allah, dan ita ya dace ta maye maka gurbin 'yar uwatta".
Abba ya ce "In ji wa? Ai ida har ina raye Adnan ba zai auri Yarinyar nan ba, Salman shi ya dace ya auri Afra".
Abbi ya ce "Me yasa zaka ce haka?".
"Wa zai bawa Mutumin banza 'ya, ai shi ya san mai nake nufi"
Adnan ya haɗa hannayensa biyu, alamar ban haƙuri, yana girgiza kansa, hawaye na fita daga idonsa.
Abbi ya ce " Bai kamata ka faɗi haka a gabansa ba, bayan ga halin da yake ciki".
Abba ya ce "Wannan yaron ba abin tausayi bane, gara a bari ya ɗanɗana kuɗarsa, kuma sati mai zuwa zan karɓawa Salman Auren Afra a wurinka, idan har zaka mini kara, Salman ɗana ne"
Cikin hanzari Abbi ya janyo hannun Abba, zuwa waje ya ce "Duk laifin da yayi bai cancanci wannan horon ba, magana fa ake ta rayuwarsa".
Abba ya ce "Amma dai ka san Aurensa da Afra ba abu ne mai yiwuwa ba ko? Alhalin ga Salman".
"Na sani, amma sai a tausayawa halin da ya tsinci kansa a ciki, koma wani irin laifi ya aikata maka, bai kamata ace ka ɗau wannan zafin ba, har ka nesanta shi da tausayawarka ba, haba Alhaji Aliyu, ka zafafa da yawa, akwai buƙatar ka sassauta masa haka"
Abba ya girgiza kai ya ce "Ba zaka gane bane Major, halin da Adnan yake ciki, dai-dai da shi ne, shiya janyowa kansa".
Abbi ya ce "Ba ina son jin laifin da ya aikata maka bane, ina nema masa alfarma ne, dan Allah dan Annabi, a sassauta masa a duba halin da yake ciki, ka rage wannan fushin da ka ke da shi".
Abba ya ce "Na ji, amma ni yanzu babbar damuwata shi ne, ba zan bar garin ba, sai Mutumin nan ya dawo, mun cinma matsaya, na tabattar da abin da Adnan yake faɗa, gaske ne ko kuma ƙarya yake yi".
"Haba Alhaji Matawalle, ga gidana mai zai sa kaje ka kama hotel ka zauna, idan ma ba zaka zauna a gida na ba, akwai guest house ɗina, sai kaje can ku zauna, mu jira zuwan mutumin, Allah dai ya sanya mu ji alkhairi".
Afra sai koke koke take yi, gaba ta ma rasa kukan me take yi ne? Damuwa da halin da Adnan yake ciki? Ko kuma farincikin an san waye mahaifinta? Bana wannan ba, ai haryanzu lalube ake a cikin duhu, ba tare da an tabattar da sahihancin cewar wanda Adnan ɗin ya ambata shi ne mahaifinta ba, wataƙila ma ƙarya yake mata, kamar yadda ya yi mata ƙarya a ƙauye.
Kwanakin Adnan uku a Asibiti, ya ɗan farfaɗo jikinsa da sauƙi, Afra taje duba shi sau ɗaya yana bacci, ya yin da Salman kuwa, sai da Mami ta haɗa masa da zagi, sannan ya yadda yaje duba Adnan, duk da a ƙule yake da Adnan, amma ya tausaywa yadda ya ga Adnan ɗin ya koma.
Akwa abubuwa da yawa da Salman ba zai taɓa mantawa da su ba a rayuwarsa, daga shigowar Adnan rayuwarsu, ya rusa musu farinciki, zuwa ga mutuwar Abra, ba zai taɓa manta lokacin da a gaban idonsa, Adnan ya mari Abra ba dan kawai ta ce tana son sa, da ya tuna ire-iren wannan abubuwan da suka faru, sai tsanar Adnan ta ninku a zuciyarsa, ban da zuciyar musulunci, da kuma yadda Mami ta dage da babu abin da zai sanya ya zo duba Adnan. Kuma a wannan karon ya ƙudirce a zuciyarsa ko mai za ayi, ba zai barwa Adnan Afra ba, a wannan karon Afra tasa ce.
Wasa-wasa, sai da Bulama ya kwana biyar a Dubai, sannan passport ɗin Rumaisa ya zama ready, gaba ɗaya a kwanakin nan, banda aikin rarrashinta babu abin da yake yi, kullum cikin kuka take, ga gefe guda Saudat ta uzzura masa da kira, ƙarshe sai kashe wayarsa ya yi gaba ɗaya.
Ranar Asabar, Bulama da Rumaisa tare Abdallah suka sauka a Nijeriya, a garin Kaduna, sai dai a guest house ɗin sa na Kaduna suka sauka, saboda baya son wani dalili ya sanya wani ya san da cewar, sun sauka da Rumaisa a Nigeria.
Lambar Adnan Bulama ya duba, ya kira shi, sai dai sam Adnan ya ƙi bawa kiran mahimmanci balle ya ɗauka, kasancewar yana tare da su Abba a guest house ɗin Abbi, Yana kwance a falo, Hajiya Mama na gefensa tana jan carbi, ta ji wayar Adnan ta cika mata kunne, amma ba shi da niyyar ɗaukar wayar.
"Adnan ba wayarka ce take ringing ba"
Cikin numfarfashi na marasa lafiya, Adnan ya ce "Mama I can't pick it".
Mama ta miƙa hannu ta ɗaga wayar, cikin nutsuwa Bulama ya yi sallama, Mama ta amsa suka gaisa, Bulama ya ce me wayar yake nema.
Mama ta ce "Bashi da lafiya, yana kwance"
Bulama ya ce "Subhanallah, Allah ya bashi lafiya, dama nine Yusif Garba Bulama, wanda aka ce yarana na wurinku".
Mama ta ce "Ahh, Allah sarki, ka dawo garin ne?"
"Eh mun dawo, naje na taho da mahaifiyarsu ne, dan mu samu a tabattar idan yaran namu ne"
Mama ta ce "Alhamdilillah, muna nan Kano dama ku muke jira, da ka ce tun a washegari zaka zo".
"Eh, an tsaya gyara passport ɗin mahaifiyarsu ne, insha Allah gobe in Allah ya kaimu, da wuri zamu taho, sai a bani Address ɗin in da zamu zo".
Mama ta tashi, taje ta kaiwa Baba waya, suka sake yin magana da Bulama, ya yi masa bayanin Adress ɗin.
Washegari, wajen ƙarfe goma sha ɗaya na rana, Abba ya shigo ɗakin da Adnan yake ya ce "Ka tashi ka shirya, muje mu tari Mutanen nan, sai ka tabbatar mana da dalilin da yasa kace shi ne mahaifinsu, kuma ka gaya musu da ka auri 'yar su me kayi mata, da kuma dalili da ya sanya ka san in da mahaifin na su yake, amma ka ƙi faɗa da wuri". Marairaice fuska Adnan ya yi zai yi magana, amma Abba ya dakatar da shi ya ce "Kar ka gaya mini komai, ka tashi mu tafi, mutumin banza kawai, ai kai ba abin tausayi bane"
Jiki ba ƙwari haka Adnan ya kammala shiryawa, suka tafi gidan su Salman.
Suna zazzaune a falo, suna jiran zuwan su Bulama, Little da tuni ta fara rarrafe, ta na jikin Adnan tana wasa, ta ja masa gemu, ta ja masa gemu, yana kallonta yana murmushi, lokaci lokaci yana share ƙwalla.
Ko da Afra ta fito falo ta yi tozali da Adnan sai da gabanta ya faɗi, yayi rama tamkar ba shi ba duk yayi wani iri, gashi yadda numfashinsa ke fita ma zai ƙara tabattar maka yana cikin mawuyacin hali.
Kallo ɗaya yayi mata ya kauda kansa, ya cigaba da yiwa Little wasa, yana share hawaye, gaba ɗaya sai jikin Afra yayi sanyi, ko ba komai mijin 'yar uwatta ne, abin da tayi na nuna masa ƙiyayya, bai kamata ba, amma ba yadda zata yi, dan ita tafi son Salman a kansa.
Abbi ne ya shigo tare da Abba ya kalli Mami sannan ya kalli Afra ya ce "Afra tashi ki koma ɗaki, make sure baku bari ta fito ba, sai mun gama tattauanawa, gasu can sun ƙaraso" Afra tana ji tana gani, aka kaita ɗaki aka rufe.
Abbi ne ya yiwa su Bulama jagora, zuwa cikin katafaren falon gidan Major.
Rumaisa sai rarraba ido take yi, Mami ta tsurawa Rumaisa ido, a ranta ta ce "Tsarki ya tabbata ga Allah, su Abra dai 'ya'yan balarabiya ne".
Abdullah ya kalli hoton falon, cikin harshen larabci ya ce wa Rumaisa "Ai wannan ita ce yarinyar da nake baku labari, na haɗu da ita karo biyu".
A gigice Rumaisa ta nufi hoton, tana ta larabci, ba komai suke ganewa a maganar ta ta ba, saboda kukan da take yi, da ƙyar Bulama ya rarrashi Rumaisa, su Abbi suna ta rarrashinta cikin harshen turanci.
Tabbas babu wanda zai kalli matar nan ya ce ba ita ta haifi su Abra ba.
Har ta zauna ta miƙe a gigice ta nufi in da Adnan ke zaune yana binta da ido, dan hatta yanayin rikicewarta tana kuka tamkar Abransa.
Little ta ɗauka ta ƙanƙame, tana cewa Bulama wannan ma 'yar ta ce.
Cikin harshen turanci Bulama ya ce "Ta yaya wannan zata zama 'yar ki, bayan 'ya'yanki sun kai aƙalla shekaru ashirin da huɗu".
"To ina yaran nawa suke?" Ta tambaya tana zubar da hawaye, tare da sumbatar Little, duk ƙyuyar yarinyar amma ba ta yiwa Ummi ba, saima kallonta da take tayi.
"Bayani za ai miki ai, amma ki zauna"
Da ƙyar Rumaisa ta zauna, aka gaggaisa aka kawo musu ruwa, aka samu Rumaisa ta ɗan nutsu, sannan Abba ya kalli Adnan ya ce "To ka san dai kai ne silar taruwarmu a nan, dan haka saika warware mana abin da ka ƙulle a ranka, kayi da turanci yadda zata fahimta".
Adnan ya ɗan yi jimmm, sannan yai ajiyar zuciya, jiki a sanyaye idonsa fal ƙwalla ya fara bada labarin abin da ya faru.
Ya fara da irin soyayya da shaƙuwar da ke tsakanin sa da mahaifiyarsa, har zuwa lokacin da ta rasa ranta a sanadin Sakaci da son abin duniya na Bulama.
Ya cigaba da bada labari, yadda ya rayu, da kewar rashin mahaifiyarsa har zuwa ranar da ya raka Usman gidan Bulama wurin Meenal, da hoton Bulama da ya gani, da fari a kan Meenal ya so ya aura, kuma ga Usman, katsam da yaje Kano, ya haɗu da Abra. Nan ya basu labarin yadda ya je har Yola, garin su Bulama samun bayanai a kansa, a nan ya tabattar da Abra 'yar sa ce.
Rumaisa ta ce "Ita ba ta fahimta ba, wacece Meenal da ake magana a kanta, kuma wane Asibitin ake magana ba ta gane zancen ba?!
FARKON LABARI
YUSUF GARBA BULAMA ɗan asalin garin Adamawa ne cikin Yola
NA KUƊI NE, A BIYAMU HAKKINMU KAN A KARANTA
08081012143
[11/23, 12:57 PM] Abk: Su biyu kacal iyayensu suka haifa, daga shi sai ƙanwarsa Murja. Sun taso cikin kulawa da soyayyar iyayensu, duk da ba masu ƙarfi ba ne sosai amma suna da rufin asiri daidai gwargwado, kuma babu abin da suka nema suka rasa a rayuwa. Yusuf ya kasance mutum ɗan gayu, mai son rayuwar ƙarya da sabgar masu kuɗi. Tun yana karami Mahaifinsa Garba Yusuf Bulama ya fahimci wannan halin nasa, hakan ya sa kodayaushe cikin masa nasiha da nusar da shi ya tsaya a duk inda Ubangiji ya ajiye shi a rayuwa yake. Yusuf ya kan nuna kamar ya ɗauki maganar mahaifinsa, amma cikin ransa ƙara burika ma yake yi, addu'ar shi da burinsa a kullum Allah ya sa ya zama shahararren mai kuɗi, wanda za a dinga kwatance da shi saboda kuɗinsa.
Mahaifinsu ya saka su a makarantar boko da islamiyya, amma sai ya fi mayar da hankali a kan karatun boko, a cewar shi saboda shi ne karatun samun kuɗi. Suna daf da kammala secondary school suna SS 3 Allah ya yiwa mahaifinsu rasuwa. Bayan Mahaifiyarsu ta fita daga takaba sai Bulama ya fito da buƙatar cewa yana son ya cigaba da karatu, Mahaifiyarsu ta ce A'a, ita dai ta fi son ya zauna ya cigaba da kiwo ya gaji mahaifinsa, a ganin Bulama hakan faɗuwa ce a ce kamar shi wayayye ɗan boko da kiwo, ba zai iya ba gaskiya. Lallaɓa mahaifiyarsu ya dinga yi tare da nuna mata alfanun karatun fiye da Noma, har ya samu ta amince, aka siyar da wasu daga cikin shagun da baffansu ya bari aka damƙa masa kuɗin akan ya je ya cigaba da karatun da su. Yadda ake ba shi labarin ABU Zariya da kuma wasu daga cikin abokansa da suke can ya sa shi ma ya je ya fara karantar medicine.
Shigar shi makaranta ya ƙara masa ƙarfin burinsa a cikin ransa, saboda ganin yadda ƴaƴan masu kuɗi suke rayuwa, abun yana matuƙar burge shi. Ba ya abota da ƴaƴan talakawa yan'uwansa sai dai da masu kuɗi, kasancewar shi kyakkywa kuma ɗan gayu ya saka ake ɗauka shi ma ɗan masu kuɗin ne. Suna level 3 aka tafi wani strike mai zafi, a lokacin wani abokinsa Munnir yake sanar masa mahaifinsa ya tura shi ƙasar Dubai akan harkar kasuwancinsa, zai tafi idan aka koma school sai ya dawo. Ranar da ya faɗa masa kasa bacci ya yi, don ji yake dama a ce shi ne zai tafi Dubai ɗin nan, ya dinga ƙissime-ƙissimen me zai siyar a cikin gadon da mahaifinsu ya bar musu wanda zai ishe shi kuɗin jirgi zuwa Dubai ya bi Munnir su tafi tare, amma duk abin da ya ayyana zai sanar sai ya ga ba zai kai ba, don duk saboda karatunsa da ƙaryayyakin da yake kiran Inna ya yi mata akan kuɗi, ya sa duk ta sissiyar da abubuwa da dama na gadon ta tura masa kuɗin. Bayan kwana biyu abin yana cin shi a rai ya kasa dannewa, hakan ya sa ya yanke shawarar kawai ya kira Munnir ya sanar masa, ko Allah zai saka a dace su tafi tare.
Kamar wasa Munnir yana kai maganar gaban mahaifinsa ya amince, bayan ya kai masa Bulama ya yi masa tambayoyi a game da rayuwarsa, jin Maraya ne kuma ba shi da aikin yi ya sa ya amince, amma bisa sharaɗin sai iyayensa sun amince. Cikin tsantsar murna Yusuf ya koma gida ya sanar da Inna, da farko ƙin amincewa ta yi, sai da ya kira mahaifin Munnir ya yi mata bayani sosai yadda za ta gane sannan ta amince da ƙyar. Sun ci kuka lokacin da zai tafi ita da Murja wadda ake shirin aurenta a lokacin, amma shi ko ɗigon hawaye saboda farinciki da murnar da yake ciki, a ganin shi wannan dama ce da za ta taimaka wajen cimma burinsa.
Sun isa garin Dubai lafiya, babu ɓata lokaci kuma suka shiga abin da ya kawo su na business, Bulama jin zuciyarsa yake fess yau ga shi a Dubai, tamkar wanda aka tsunduma a Aljannah haka yake jin kansa don farinciki. Ranar wata Juma'a da ba zai taɓa mantawa da ita ba a rayuwarsa sun je wani shago siyayya suka haɗu da Rumaisa.
Shagon sayar da Gold's ne, su Bulama sun zo siya wanda za su tura wa Baban Munnir Nigeria ya sayar. Suna cikin zaɓa Bulama ya kai hannu zai ɗauka ita ma ta kawo kyakkyawan farin hannunta. A tare suka janye hannayen