Showing 96001 words to 99000 words out of 231718 words

Chapter 33 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14711


Anty Suwaiba ta ce "kwantar da hankalin ki, ki shirya akwai mafita, gurin malami zamu kai shi, a rufe masa baki, dolensa ya amine Salman ya bar ƙasar nan" shirya komai suka yi, Na'ima ta amince akan zasu wajan wani malami, saboda samun mafita, kar ramin muguntar da take shiryawa ya rufta da ita.

Kamar yadda Abbi ya yi alƙawari, haka ya cika ta hanyar yin bincike har Kaduna, akan Sp Adnan Aliyu Matawalle, ya samu good Information. Halin Adnan mai kyau ne, kuma mutum ne mai asali, mahaifinsa sanannane ne.

A satin Abbi ya nemi ya zauna da Adnan, shi kansa Abbi ya yaba da hankali nutsuwa, da kuma kamala ta Adnan, dan haka ya bashi damar ya turo magabatansa, su nema masa Auren Abra.
Ko da Adnan yaje da wannan batu gida, farinciki gurin iyayensa ba'a magana, mussaman Hajiya Mama, bata taɓa tunanin abubuwa za su zo da sauƙi haka ba, saboda gani take Adnan ba zai iya kwantar da kai yayi Soyayya ba, saboda tsananin zafin zuciyar sa.
Sosai Mama da Abba suka yaba da Abra, da ya nuna musu hotonta, kuma suka yi duk binciken da za suyi a kanta, amma ba su samu wani mummunan abu ba akanta, mussaman da ya zamana Major Khamal Khamis, sunansa shahararre ne a ƙasa.

Abban Adnan ya wakilta 'yan uwansa, zuwa nemawa Adnan ɗin Auren Abra, kuma, Abbi ya basu auren cikin aminci, farin ciki wajan Mami ba'a magana, gani take ta samu mafita da kaso mai rinjaye na matsalolinta.
gefe guda a ranar Sp Adnan Aliyu Matawalle da Abra Khamal Khamis raya daren sukai da Soyayyar juna ta waya.
Sp Adnan ya koyar da Abra Soyayya, ita kanta wasu lokutan har mamakin kanta take, saboda irin soyayyar da take nuna masa. Duk zafin zuciyarsa, ya ƙware a fannin iya rarrashi da tarairayar Abran, da biyewa dukkanin shagwaɓarta da shirmenta. Haka suka raba dare, Adnan yana tsara musu yadda zasu gina rayuwarsu, bayan sun yi Aure, har sai da ya kusa fara sakin layi, Abra tayi masa sallama ta kashe wayar.



A hankali ta tura ƙofar ɗakin yana kwance ya juyawa ƙofar baya babu abun da yake bayyane a jikinsa sai fuskarsa, gaba ɗaya jikinsa rawar zazzaɓi yake. Da ɗan sauri Abra ta ƙaraso tare da zama a bakin gadon daidai kansa muryarta na rawa ta ce.
"Subuhanallahi Faris baka da lafiya? Wayyo Allah na"
gaba ɗaya idanunta ya cicciko da hawaye. Wata irin soyayya ce tsakanin Abra da Salman irin soyayyar da Ubangiji ne kawai ke haɗata, raba irin wannan soyayya kan iya jawo rasa rai ko rayuka.

Juyawa ya yi tare da Kallonta da idanunsa wanda sukai jaa sosai tamkar gauta. Kallon ta ya ke kamar bai taɓa ganinta ba a hankali ya kama hannunta tare da riƙewa cikin nasa.
Abra ta ƙara hawa kan gadon tare da shafa sumar kansa muryarta na rawa ta ce.
"Meke damunka Faris ɗi na? bari na faɗa wa Mami, Abbi ya riga ya tafi, ya tambayi kana ina Mami ta ce ka fita"
Girgiza mata kai ya yi, yana ƙara matse hannunta da ke cikin nasa.

"Bari na kira Dr ya duba ka" Murmushi ya sakar mata cikin dauriya ya ce.
"Mami, Abbi, Dr. Basu da maganin abin da yake damuna Angel leave them"

"Jikin ka yayi zafi fa, ta yaya ka ke tunanin zan jure ganinka haka?"

"Zaki jure mana Angel? tunda gashi aure zaki ki barni" yayi Maganar a raunane.

Shiru tai ta kasa cewa komai domin ita ma tana hango ranar da za'a ce wai zata bar gidan kuma tabar Faris ɗinta?.

"Yanzu me ka ke so?"
"I  just need you by my side, stay with me Angel don Allah".

Kansa ta ɗauka tare da ɗorawa akan cinyarta a hankali take shafa sumar kansa hawaye na saukar mata ta ce.
"I'm here I'll Spend all my time with you Faris".
Lamo ya yi akan cinyarta yana murza hannunta zuciyar sa sai bugawa take.

"I love You. I love you Angel" Murmushi tayi tana jan hancinsa ta ce.
"I know, and I love you too u don't have to  worry bloody..."

Shiru duk sukai ga mamakin Salman, numfashin Abra yaji yana sauka a hankali, alamar bacci ya ɗauke ta, gently ya miƙe da ga kan cinyarta.

"Angel ragowar yarinya, dana aureki kin daina wahala Insha Allah, da yardar Ubangiji ke matata ce mallakina ce"

A hankali ya sumbaci goshinta ya ce "you're my life"
Gently ya yi 6nata nose Kiss ya ce "My everything" a nuste ya yi mata cheeks kiss ya ce "rest of my life. Mother of my children" ji yake kamar ya maida ita cikinsa, kowama ya dena ganinga.

Wayar Abra ce ta fara ringing kallon screen ɗin wayar ya yi yaga _Heartbeat_  kallon wayar ya yi har kiran ya katse. Sai da akai kira uku a fusace ya ɗauka.

"Ruhin Sp Adnan Aliyu Matawalle. Na kusa mutuwa da rashin jin muryarki"
Adnan dake tsaka da driving gefensa kuma Usman ne yana ta tsokanar sa. Jin shiru Adnan ya ce.
"Hello Angel are you there?"

"She's sleeping in my laps u can call later" Salman ya faɗi maganar hankali kwance.
"Who are you? And  a ina take bacci?" Adnan ya furta rai ɓace.

"Tana wajan wanda ya dace mana? Ka faɗi yaren da kake ji, idan baka gane wanda nayi ba, sai nayi maka bayani da shi" sai yanzu Adnan ya ɗauki murya murmushi ya yi yace "Oh! Faris ƙaninmu how are you? I'll call later bye"

Yana faɗin hakan ya kashe wayar, Salman datse lip's ɗinsa ya yi yana jin duniyar na juya masa. Ranar da ya fara arba da Adnan a gidan ya zo gurin Abra, ji yayi tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu.
Shi kansa Adnan ya lura da irin mugun kallon da yaron yake masa idan ya zo, amma bai ɗauki hakan a matsayin komai ba.
Gyara mata kwanciya Salman ya yi yana zame mata rolling ɗin kanta.

An saka ranar bikin Abra wata biyu kacal. A satin kuma Adnan ya sauka Kano, ko da suka haɗu da Salman kamar haɗuwar zaki da damusa haka ta kasance, saboda Salman ji ya dinga yi tamkar ya kashe Adnan ya huta.

Haka ya shiga ɗakinsa, ya kulle kansa ya dinga kuka kamar ƙaramin yaro.
"Abra is leaving me, why? Abbina kaima ba ka fuskanci halin da nake ciki ba? Na kamu da soyayyar yarinyar da ka tsinta ka riƙe tsawon shekaru, a matsayin yayata, Abbi I love her, meyasa zaka bawa wani?" Haka ya dinga surutai tamkar yana gaban Abbi.

Salman ne zaune sanye da farar singlet ya rame sosai, abun duniya ya yi masa yawa, soyayyar Abra na addabar zuciyarsa, ga tsinewar da Mami ta ce za tai masa, ga lokacin bikin Abra na kusantowa, gaba ɗaya baya hayyacinsa, ko Makaranta ya je, baya gane komai ba ya iya cin abinci sam.
Ga shi ita kanta Abra yanzu, tafi maida hankali akan wayarta, ta dena bashi attention ɗinta kamar da, kullum tana maƙale da waya tare da Adnan.
Gashi Adnan ya auri hanyar Kano, kullum yana hanyar zuwa gurin ganin Abra, hakan ya sa sukayi wani irin sabo da shaƙuwa, wanda yasa Abra sakewa da Adnan Sosai. Sai dai duk da haka, tana damuwa da halin da Salman ke ciki, wanda ba ta san asalin abun da yake damunsa ba, ta barshi a alhinin rabuwa da za su yi, wanda ita kanta tana tsintar kanta a irin wannan yanayin, ba ta jin ko Abbi za tayi missing Kamar yadda za tai missing Faris. Ta kan yi kuka sosai da sosai, idan ta tuna lokaci ƙalilan ya rage, su rabu da Faris ɗinta.

Salman ya lula a duniyar tunani, Kamar da ga sama yaga Abbi ya shigo bedroom ɗin nasa, hannunsa riƙe da tarin takardu. Miƙewa tsaye Salman ya yi yana faɗin "Wlcm back Abbi ya hanya? Ashe ka dawo?"

ba yabo ba fallasa ya ce "Yawwa, tun ɗazu nake cigiyarka ai, naga ba ka da niyyar fitowa, ko ba ka ji dawowata ba ne oho"

Salman ya ce "Abbi na ɗan yi bacci ne, shiyasa".

miƙawa Salman takardun ya yi Salman ya bisu da idanu kafin ya ce "Na mene wannan Abbi?" Abbi ya kalli Salman sosai ya ce "Na gama dukkanin shirye shiryen da ya dace, na biya maka Makaranta a China, a can zaka cigaba da karatunka, saboda karatu a wannan ƙasar sai a hankali, babu wani inganci, dan haka next week zaku fara lectures, jibi in Allah ya kaimu zaka tafi, dan haka ka shirya!!!




LITTAFIN RUƊI NE ₦300 NE
Via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750
[10/5, 5:43 PM] Abk: Saroro Salman ya bi Abbi da kallo, kamar bai gane da yaren da Abbi yai Maganar ba.

Abba yace "Look Salman, mahaifiyarka ce ta zo mini da batun gara a kaika karatu China, kuma ba mun yanke wannan hukuncin ne dan ɓata maka bane, ka san karatun Nigeria sai a hankali".

Cikin rauni Salman ya ce "Abbi, exams ɗin first semester fa zamu fara, you are planing to make me far away from my sister, ko Auren na ta ba zaku bari in gani ba Abbi?"

"My Son, ban amince da hakan dan nesan ta ka da Abra ba, ko ba daɗe ko a jima dole wataran zaku rabu, tafiyar ce ta zo daidai yanzu kayi haƙuri ka ji Salman, idan ka zo hutu sai kaje har gidanta, ai ba wanda ya isa ya raba hanta da jini"
Salman ya jinjina kai, Abbi kuma ya juya bar ɗakin.
Abbi na fita Salman ya saki takardun a ƙasa, ya faɗa kan gadonsa ya lumshe idanunsa, hawaye na zuba daga idonsa a hankali ya ke furta 'Mami why? Har abun ya kai kisa a rabani da ƙasar, Mami why" haka ya dinga maimaitawa a hankali.

Na'ima kuwa ba ƙaramin farinciki ta yi ba, dan tun bayan da Anty Suwaiba ta rakata gurin malami, ta biya kuɗi dan a rufe bakin Abbi a kan tafiyar Salman ƙasar waje, kuma a cire Abra daga zuriyar Salman.
Bayaj sun dawo gida ne, ta kuma samun Abbi a kan tafiyar Salman, da fari yayi mata buyagin na sa, amma ta kwantar da kai, tare da nuna masa illar barin Salman a ƙasar nan yaga bikin Abra, Abra za ta iya tuburewa ta ce ta fasa Auren, ko kuma ya ce zai dinga zarya a gidan Abra, wanda ba kowane miji ne zai yadda ba, da haka ta lallaɓa Abbi ya amince, ya nemawa Salman Makaranta a China.





Sallama ya ke ta kwaɗawa a falon, kamar baza'a amsa ba, sai kuma can a kasa amsa cikin siririyar muryarta mai cike da iyayi.
Cikin Palourn ya shiga, Meenal ta kalli mutumin ta ce "ya dai?"
"Dama saƙo ne wani mutum ya kawo, ya ce a bawa doctor idan ya dawo".

Maman Meenal da ke zaune ba tace uffan ba, sai yanzu da ta ji ance saƙo za'a bawa Doctor sannan ta kalli mai gadin ta ce "Bani nan" ya ƙarasa ya miƙa mata envelope ɗin ya fice.

Meenal ta kalli Mummynta ta ce "Mummy, sai na dawo"

"Shikenan, ki kula da hanya, ayi tuƙi a hankali".

"Ok Mum" Meenal ta amsa tana ficewa daga falon.

Mummy ta fara buɗe envelope, dan ganin mai aka kawo a ajiyewa doctor.

A razane ta miƙe tsaye, a lokacin da ta yi tozali da abun da yake cikin envelope ɗin.
Jikinta ne ya hau rawa, ta fara waige-waige don tabattar da babu wanda ya ganta.
Da hanzari ta nufi ƙofar falon, ta fito harabar gidan tana ƙwalawa maigadi kira.

Ya ƙaraso cikin rawar jiki yana faɗin gani Hajiya.

"Waye ya baka wannan saƙon?".

"Wasu ne Hajiya"

"Ba ka san su ba?"

"Eh gaskiya ban san su ba, dan ban taɓa ganinsu ba"

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan koma bakin aikinka".

Cikin gida ta koma, kai tsaye ta wuce kitchen, ta rufe ƙofar kitchen ɗin da key, ta yayyaga saƙon nan, ta kunna masa ashana ta ƙone tsaf, ta tattare tokar ta bar kitchen ɗin.


Salman kam nan da nan yayi wata uwar rama, ko falo ba ya fitowa kullum yana ɗaki, yana tunani tare da zullumin yadda zai tafi ya bar Abra ta auri wani.

Yana kwance a kan gadonsa, Mami tayi sallama ta shigo ɗakin.
"Kai Salman" a hankali ya buɗe jajayen idanunsa yana kallon Mami.

"Babanka bai zo ya gaya maka cewar ya biya maka kuɗin Makaranta, zaka tafi China ba? Na zubamaka ido inga iya gudu ruwanka, ko zaka zo ka sameni da batun, a fara ƙoƙarin fara shirin tafiyarka, amma kullum kana ɗaki ka ƙi zancen ma gaba ɗaya"

Lumshe idanunsa ya kuma yi, saiga hawaye na zubowa ta gefen idonsa.

"Sakarcin meye haka kuma Salman, kuka kamar wani yaro ƙarami".

Salman ya tashi zaune ya kalli Mamai ya ce "Mami, bayan kandagarkin da kika mini akan soyayyar Abra, shine kuma kika sa a rabani da ƙasar ma? Mami kin san wannan abubuwan zasu biyo baya, mai yasa kika bari na san Abra ba 'yar uwata ba ce, Mami ko kin rabani da ƙasar nan zuciyata na Nigeria tare da Abra, ina sonta Mami, amma ai ko Auren na ta kya bari in gani".

Ajiyar zuciya Mami ta yi, ta zauna kusa da Salman ta ce "Salman, kai baka tunanin halin da zata shiga idan har ta san cewa bamu muka haifeta ba, kai kanka kawai ka sani, baka tunanin abunda kake shirin yi mai zai haifar, barinka ƙasar nan shine samun nutsuwarka kuma ka manta da ita, haba Faris ɗina da kaina zan samo maka tsaleliyar yarinha da ta fita komai in aura maka, ka fara shirin tafiyarka ka ji Salman" tayi maganar tana share masa hawaye, daga haka kuma ta fice daga ɗakin.
Bin ta yayi da kallo, Maminsu a komai son kanta kawai take dubawa.

Abra kuwa yanzu kusan kullum tana kan wayarta, tare da Adnan hakan yasa ba ta iya maida hankali akan komai, sai dai ta lura tunda aka kawo kuɗin Auren nan, Salman ba shi da walwala, kuma a 'yan kwanakin nan kamar wani abu yana faruwa a gidan, wanda ba ta gane ko menene ba.
Lokaci lokaci, ta kan shiga cikin matsananciyar damuwa, idan ta tuna idan tayi Aure, zata rabu da Faris ɗinta, ba ta jin za tayi Missing ɗin wani kamar Salman ɗin ta.

Yanzu ma ɗakinsa ta nufa, tana shiga ta tarar yayi rigingine ya ƙurawa roofing ɗin ɗakin ido.
Sai dai yayi rama matuƙa, ga ɗan siririn saje da ya fara fito masa da gashin baki na girma.

"Bloody what's wrong with you ne? Gaba ɗaya gidan nan yayi duhu saboda baka walwala, meyafaru da ne?" Tayi maganar tana ƙarasawa kan gadon.
Juya mata baya yayi, yaƙi ko kallon in da take.
Zagayawa tayi ta hau gadon tana kuma cewa "Faris wai menene?"

Miƙewa yayi, ya sauka daga kan gadon, ya janyo Akwati ya fara ƙoƙarin zuba kayansa.

Cikin fushi ta ce "Faris wai meye haka ne? Wannan kayan na menene ina maka Magana ka mini shiru".

"Leave me alone Abra!" Ya faɗa cikin tsawa, wanda saida ta firgita.

"Abra dama Akwai lokacin da zai zo ki manta dani? Kwana biyu ina cikin yanayi na damuwa, amma wands zai aureki ya ɗauke miki hankali ko nemana ba kya yi, ba ki san halin da nake ciki ba? Abra China zan tafi ina fatan Allah ya sa haka shine mafi Alkhairi".

"Faris, ka yi mini uzuri mana, muna cikin weekends ne, kuma ga shirin exams muna yi, don't judge me wrongly please, but ban gane China ba ina ne China?".

"Ohh baki ma san meke faruwa ba, Abbi ya biya mini Makaranta a China, jibi in Allah ya kaimu zan tafi, bana nan za'ayi Aurenki, ina fatan Allah ya baku zaman lafiya, ya dawwamar da farinciki a rayuwar Aurenki da wanda kike so".

"Impossible" Abra ta faɗa tana wani haɗe rai.

"Meye ma'anar tafiyarka China? Saboda me?"

"Bani zaki yiwa wannan tambayar ba, kamar yadda kika ji maganar sama ta ka, nima haka na ji ta".

Da gudu Abra ta juya, ba ta tsaya ko ina ba sai sashen Abbi.

"Abbi, Abbi!  Abbi".

Abbi ya ce "Na'am Sweetheart ya akayi?".

Na'ima ta ce 'Wannan wane irin rashin hankali ne?"

Abra ba ta kula Na'ima ba ta ce "Abbi, mai yasa za'a kai Faris China? Laifin me yayi? Mai yasa za'a rabani da shi tun Yanzu, har ace zai tafi jibi ban sani ba, amma dai Abbi Faris da wasa yake mini ko?"

Abbi ya ce "To Abra ya zanyi muku? Nace a bari ki kammala karatu, kince ke A'a, Aure zakiyi, kuma kinga tafiyarsa shine Mafi Alkhairi, idan ki kayi Aure zai shiga damuwa sosai".

"Abbi shine kuma za'a rabani da shi tun yanzu, duk duniya kun san bani da wani ɗan uwa bayan shi, ni na fasa Auren nan, dan Allah ku ƙyale mini Faris ɗina, na fasa Auren Abbi".

Gaba ɗaya Abra ta birkice, Abbi ya tashi ya riƙota yana faɗin "Calm down Abra, ai zai dinga zuwa har gidanki, kuma......

"A'a Abbi, ni rayuwar ɗan uwana ta fiye mini dukkan wani farinciki, Abbi na fasa Auren, dan Allah kar Faris ya tafi China".

Na'ima ta hayayyaƙo zata fara masifa, amma sai taga idanun Abra sun lumshe, jikinta ya saki ta tafi zata faɗi Abbi ya tare ta.

Abbi ya ce "Subhanallah".

Na'ima ta ce "wai ni wannan wace irin Yarinya ce? Ba damar ta shiga damuwa sai ta hau suma, yanzu da za tayi Aure, namijin ƙanin uwatta ne da ba zai ɓata mata rai ba?".

"Na'ima, this is not time for discussing this issue, kira mini Salman ya ɗakko mota mu tafi Asibiti.

Mami ta kira Salman a waya, nan da nan sai gashi ya zo.

Yana ganin Abra a kwance a jikin Abbi, ya rikice, da sauri yayi waje ya ɗauko Mota, suka tafi Asibiti.

Abbi yana mamakin irin wannan yanayi da Abra kan shiga, idan ta shiga firgici ko fushi, amma duk wani bincike da za ayi anyi, amma ba'a gano dalilin da yake sanyata haka ba.

Abbi ya ga dacewar idan Adnan ya kuma zuwa ya zauna da shi, ya sanar masa da wannan rashin lafiyar ta ta.

A hankali Abra ta motsa, tare da buɗe idanunta, da idanun Salman ta fara tozali, a hankali ta ce "Faris".

Salman yayi ajiyar zuciya sannan ya ce "Na'am Angel".

"Dan Allah kar ka tafi ka bar ni".

"Angel dole in tafi in barki, kin zaɓi wani a kaina".

"Faris, ina son Adnan, amma ba zan iya jure ganin ka nesanta da ni ba, dan Allah kar ka tafi ka ka barni".

Shiru Salman yayi bai ce komai ba.

Abra ta yunƙura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login