Showing 114001 words to 117000 words out of 231718 words

Chapter 39 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14806

ne?" Miƙewa ta yi tsaye zuciyarta na yi mata zafi, wani irin kishi ya rufeta har bata san lokacin da ta wurgawa Surry uwar harara ba. Da sauri kuma ta juya zata shige part ɗin ta.

"Idan har kika bar parlourn nan wallahi na lahira zai fiki jin daɗi Abra Khamal Khamis"
Cak Abra ta tsaya ba tare da ta kallesa ba, a wannan lokacin ba komai ta ke ganewa ba, ji ta ke inama ba zai auren ba, an faɗa mata daɗin aure an kuma faɗa mata duk soyayyar dake tsakani wata rana ana samun saɓani domin ko harshe da haƙori ana sabawa, balle mutum mai ɗauke da Zuciya wacce jiki ke gudana a cikinta.
Sai dai tunaninta ya samu tawaya ta wannan ɓangaren, babu abu mai muhimmancin kamar daren farko na rayuwar ma'aurata amma ita nata daren ya zo mata a yadda ba tai tunani ba, ta kasan fahimtar Dare da duhun da ke cikin al'amarin. Wanne al'amarin ya ke shirin faruwa acikin rayuwarta dama duniyar ta baki ɗaya?. DESTINY.

Wata zuciyar ta ce.
"Ƙaddara ta ki har nawa ne? U have to think Abra, think think think.... Ta tashi cikin rashin kulawar uwa, ta girma da ƙaunar ƙarninta farin cikin ta, lokaci ɗaya ƙaddara tai mata kutse cikin rayuwarsu aka rabata da jinin jikinta Faris, ta ɗauki ƙaddara ganin yadda Adnan ke nuna mata kulawa tare da yi mata Al'ƙawari kala-kala, hakan duk a cikin tsarin ƙaddarorinta suke? Ko kuma wani abun ke son faruwa ne?... Wani abu mai kama da JUYAYI.

"Heyyy You jakanesss"
Muryar Sp Adnan Aliyu Matawalle ya sauka a kunnanta a gigice ta dawo hayyacinta duk ba sosai ta jisa ba, hannunta na rawa ta taɓa kunnanta sai a lokacin ta ji hearing aid ɗin ne ya goce.

"20mints ya yi maki yawa wajan kawo sweetheart ɗina abinci" zaman hearing aid ta gyara idanunta cike da hawaye ta kallesa ba tare da ta ce komai ba.

"I'm i your mate da ina magana kika zuba idanu ko matar amarci ke damunki ki ke son cinye ni eye?" Murmushi kawai ta yi irin Murmushi da gwanda mutum ya yi kuka akan ya yi irinsa.

"Idan kai zanwa zan yi, it's my responsibility nauyin ka yana kai na, amma ba zan taɓa yiwa karuwar can abinci ta ci ba....,"

"Kauuu!! Kauuuu!!!"
Ya sauke mata wasu tagwayen maruka kamar kumurciu zaki haka ya ke huci idanunsa akanta ya ce. "How dare you da zaki faɗa min haka Ehh? Kada ki dama idan kin amsa Sunan Abra Khamal Khamis kiga, and wannan da kike maganar karuwa ko....?" Ƙwafa ya yi tare da juyawa ya kama hannun Surry suka shige ɗakinsa sai maƙale jikinsa ta ke tana sakin kuka ance mata karuwa.

Dafe kanta da ke juyawa mata tayi, da ƙyar ta ja ƙafafuwanta zuwa kicthen domin ko ta kansa bata sani ba, ganin da akwai komai ta ɗauki Onion da red pepper ta ɗauki Egg da Indomie, tana aiki tana tana sakin ajjiyar zuciya, ga jiri dake ɗaukanta.

"Yaya.. Angel Zanci Indomie Yaya please yunwa na keji"

"Yaya gidan wani zaki,kina gwarara jikin ki" "Angel waya saki aiki, ba Abbi ya ce ki daina aiki ba"

Ajjiyar zuciya ta sauke sbd wuƙar data ya ke. "My Angel kalli hannunki kin yanke, matsa zan yi aiki jeki zauna"
"I love You Angel wannan girki kamar a restaurant"

"Idan ban kula dake ba, waye zai kula dake ni ki daina ɗauka na matsayin ƙani kawai Yaya Angel"

Wani Uban Ihu Abra ta fasa lokacin da maganar Salman ɗaya-ɗaya ta shiga dawowa cikin kwakwalwarta tamkar yanzu ne muryarsa ke mata kuuwa a cikin kunnanta. sai da tayi kuka mai cin rai tana kiran sunan Salmanun-faris come to back to me zan bika duk inda zaka. Plate ɗin Indomie ta ɗauka, a Parlour ta samesu suna kallo da sauri ta ajjiye plate ɗin jikinta na rawa tabar parlourn sai numfashi ta ke fitarwa, har dare bata sake fitowa bata da tabbacin a gidan suka kwana ko a waje?.

China.
A hankali ya ke tafiya kansa a ƙasa, hannunsa duk biyun zube cikin Aljihu, da ga shi sai wata ƙaramar black t.shirt wacce ta kama jikinsa, sai ƙaramin wando mai kama da trousers. Ƙafarsa sanye cikin wani baƙin takalmi me kyau. Gefen wani kogi ya ja ya tsaya inda ake shan iska ga few mutane a wajan kowa yana abin da ya ke gabansa.
Iskar data kaɗa ya sa shi rufe idanu tare da zame hannunsa guda ɗaya ya ɗora daidai saitin ƙahon zuciyarsa "fat! fat!! fat!!" Haka sautin bugawar ta ke badawa, idanunsa ya ware akan ruwan tare da ƙurawa wasu tattabaro idanu farare tas dasu mace dana miji, irin tattabaron nan ne masu kama da ɗawisu sun ɗaga jela sama tai wani scale kamar zanan love Wayarsa ya ɗauka tare da ɗaukan su a taushashe ya ce. "With my heart desires my dream" idanunsa ya ɗan sauya kala kamar zai kuka hawaye kwance a idanunsa ya ƙara sakin Murmushi a karo na biyu "happy married life Angel stay blessings with your husband not ur choice"

Salman Khamal Khamis kenan, yaro mai mafarki wanda lokaci guda zanan ƙaddara ya rusa masa mafarkin. Yasa ko wacce kala rayuwa zai a yanzu zai yi ne kara zube ba tare da farin ciki ba, she tooks his happiness ta ɗauke komai nasa ta tafi da shi, baya jin tana da laifi zurfin ciki ya sanya komai faruwa. Komai jimawa soona or later sai ta zama mallakinsa halaliyyarsa.

Kujera ya nema ya zauna yana miƙar da ƙafafuwansa, jikinsa ya yi fresh ya murje but ya rame sai idanunsa da Matashin gemunsa haɗi da saje da suka fara cika fuska sbd sauyin weather ta ƙasa.

Washegari.
Kasa jurewar yunwar da ke damunta ta yi, a hankali ya dubi agogo 12:44 shi ne abin da Idanunta ya gani, da sauri ta sakko ko sallar wahalar da ta ke bata samu yi ba. Zaman rigar jikinta ta gyara har ta fita sai kuma ta dawo ta ɗauki perfume ya fesa ta gyara fuskarta, a hankali ta zame rolling ɗin kanta, sumar kanta ta sauka har baya, a tunaninta ko hakan zai burgesa duk da bata da tabbacin ko yana ma gidan.

"Allahumma ajirni fil musibatii, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ta faɗa ta sauri ƙirjinta na bugawa da ƙarfi kafin ta sake motsawa jiri ya kwashi ya kaita ƙasa, kanta ya daki jikin canter na parlourn. Ba ita ba shi kansa sai da ya ji kunyar yadda ta samesa tare da Surry, amma sai ya zame ko a jikinsa. Ta jima durƙoshe ko idanu ta kasa buɗewa sai duhu da ta ke gani kamar mai hawan jini. Sunayen Allah ta ke faɗa babu saurarawa, a hankali ta ɗauko tare da ƙara duban Surry wacce ke kwance jikin Adnan tana shafa gashin ƙirjinsa wanda da alama bai daɗe da yin wanka ba, ko ita bata samu damar yin haka ba, amma wata banza ce kwance jikin mijinta. Abin ka dame haƙuri wanda idan ya ta shi abu bai iya yinsa ba.

Duk da jirin da ke ɗau kanta haka tai kan Surry kamar mahaukaciya, yadda ta nufi Surry zaka ɗauka aljanu gareta. Tana zuwa ta damƙi wuyanta tana shaƙeta zafin shaƙar ya sa Surry sakin ƙara.
Hankali tashe Adnan ya yi kan Abra zai daka kafin ya ƙarasa Abra ta damƙe ƙirjin Surry wanda ya kewa Adnan iyayi dasu, wani ihu Surry ta kwarara tana faɗin.

"Wayyo Allah! Zata tsinka zata tsinka na shiga uku" ganin yadda Adnan yayu kanta gadan-gadan ya sanya ta ƙara fisgar ƙirjin Surry. "Wayyo uwata wayyo wallahi ta tsinka" da gudu Abra ta saki Surry ta koma part ɗin ta.
Tun kafin ta ƙarasa jikin gado jikinta ya fara rawa numfashinta ya fara fisga kamar mai Asthma idanunta rufe ya ɗauki Alkur'ani ta fara karatu da dukkan muryarta wacce ta kusa cika part ɗinta dana Adnan Aliyu Matawalle ɗin. A karatu ta ke da iya ƙarfinta tun tana yi da ƙarfi har numfashinta ya kasa jurewa, a hankali tai gaba tare da kifawa muryarta a sanyaye ta ce.

"Ka gani ko Faris?"
Cak kuma Numfashinsa ya tsaya. A haka rayuwar Adnan da Abra ta kasance tsayin sati biyu tun daga ranar kuma bata sake saka shi cikin idanunta ba.

Mami damuwa tai mata Abbi ya tsallake ya barta, babu Salman ɗan da ake tutiyya da shi kullum gida shiru kamar mayya lokaci zuwa lokaci kewar Abra na damunta ko za ta ce za kici Ubanki Abra yau ta ji zamanta na ɗauke mata kewa. Faris baya nemanta wani time ɗin ta kira number Abra sai ace a kashe.

Cikin sati na uku mafarin faruwar komai tare da toshe da kuma asalin abin da zuciya ke ɗauke da shi, mafarin rusa farin cikin wasu.
Iddar da sallarta kenan ta nufi bathroom tare da yin wanka, a hankali ta fito da ga cikin toilet ɗin ɗaure da ƙaramin towel wanda ya tsaya iya cinya ruwa na zuba a jikinta, ga gyaran jikin nan nata yana nan fata sai glowing ta ke. Tana cikin tsane jikinta ta ji an murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin kafin ta motsa ya shigo cikin bedroom ɗin, a hankali ya ke binta da kallo kamar wanda baya cikin hayyacinsa, hannunsa dafe da cikinsa wanda ya ke masa matsanancin ciwo har idanunsa sai da suka nuna alamar hakan. Fararen ƙafarta yabi da kallo zuwa hips ɗinta kana ya maida kallonsa zuwa sama. Kamar wanda ake fisga da mayan ƙarfe haka ya nufi inda ta ke, tsoran yanayinsa ya sanya Abra fara yin baya tare da ɗaga ƙafa zata gudu, domin tunaninta dukanta zai. Gaba ɗaya ta jita male-male a saman ƙirjinsa ya rungome ta tare da bata ƙyakkyawan ma sauki a ƙirjinsa. Bai zo da niyyar hakan ba amma gaba ɗaya a kallon farko tunaninsa ya tsaya, cikin ƙaramin lokacin abubuwa da suka faru suka zama abu mai matuƙar baƙin ciki a rayuwar Abra Khamal Khamis, domin babu imani cikin lamarin Adnan bata taɓa tunanin haka al'amarin ya ke ba, bai saurara mata bai nuna mata soyayya kulawa tare da tattali ba, bai barta ba sai daya tabbatar da ita matsayin cikakken mace wacce tabi layin saurin mata.
Wani zazzafan zazzaɓi ya rufe Abra jikinta sai rawa ya ke, haƙoranta na haɗewa a haka ya tsallake ya barta ya nufi nasa Part ɗin yana jin ciwon cikin ya lafa sai kansa da zazzaɓi shima daya saukar masa.

Duk inda kake tunanin azaba a wannan daren Abra ta shata, sai Subhi ta samu tai wanka tai sallah jiki na rawa ta koma ta kwanta tana jan numfashi, a hankali hawaye ya sakko mata tunanin kiss ɗin Faris ne ya faɗo mata, soyayya da ƙauna haɗi da kulawa sune ta ke gani cikin idanun Salmanun-faris a lokacin da ya ke sumbatar bakinta. Misalin 1:20 ya turo ƙofar ya shigo kamar ma ƙasar zai bari sai dube-dube ya ke alamar abu ya ke nema ko inda ta ke bai kalla ba. A hankali ta sauka da ga gadon ba zato ya ji ta riƙe masa ƙafafuwa tare da ɗora kanta a jikin ƙafar tasa, wani raunataccen kuka ya ƙwace mata cikin kuka ta ce.

"Kaji tsoran Allah ka daina azabtar dani da abin da bai san da shi ba,ka faɗa min laifina wallahi zuciyata zata buga,ina Soyayyar da kake min? Ina kulawar da ka ke faɗa min kayi min adaninta ko haka auren ya ke? Don darajar Allah da Manzonsa ka faɗa min abin da nai maka"

Kallon ta ya yi sai kawai ya juya zai fita da sauri ta ce. "Matar ka ce ni, har lahira da ke zanyi alfahari bani da kamarka a yanzu kai ne duniya ta, kai ne dangina kai ne komai nawa, ba danni ba ba dan na isa ba ka faɗa min abin da nai maka na san kana so na"
Murmushi ya yi tare da sunkuyawa ya ɗagota zuwa tsaye cije baki tayi sbd zafin da ta keji ko tsaiwa bata iyawa. Shoulder ɗinta ya riƙe tare da matsawa ya ce.
"You deceived yourself Abra Khamal Khamis, Adnan Aliyu Matawalle bai taɓa sonki ba, kuma bai taɓa sonki ba, infact mujiya ki ke a cikin idanuna" girgiza kai tayi bakinta na rawa ta ce "what... what do you mean by that? baka so na kake cewa" hannunsa ya sanya ya tallafo fuskarta ya ce. "Idan baƙin maciji ya sareki ina da tabbacin ki kaga baƙar leda cewa zaki shine, wallahi da naga fuskarki gwara na kalli mujiya, a duk lokacin da naji muryar ki ji nake kamar ana zuba min ruwan dalma a zuciya, idan kina kusa dani kowa ji nake kamar na saka hannu na shaƙeƙi na huta, babu abin da na tsana a duniya kamarki bana Sonki bana Sonki bana Sonki na tsaneki kamar yadda bana ƙaunar mutuwa ta a yanzu" baya Abra ta yi kamar zata faɗi tana riƙe ƙirjinta ɗakin ne ya shiga juyawa mata wani duhu na mamaye cikin idanunta gyara zaman hearing aid ɗin ta yi ko tunaninta ita ce bata ji daidai ba. "Baka so na mene yasa ka aureni?" "To take a revenge"

"Revenge? Me na yi maka ni? mene aikata maka da har zaka ɗauki Revenge akai na?" Murmushi ya yi kafin ya ce "Baki min komai ba, laifin da Ubanki ya yi min shi ne ya sanya zan ɗauki Revenge akanki, zan raba shi da farin cikin sa kamar yadda ya zama silar lalacewar nawa, ba zan taɓa yafe masa ba sai na tabbatar yaji Abin da naji this is my promise" Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wacce rana ce wannan me ya ke son faruwa da ita? Rarrafawa ta yi zuwa inda ya ke tana riƙe ƙafarsa ta ce "Me Abbina ya yi maka? Wallahi Abbina ba zai taɓa cutar da wani ba, idan ma ya yi sai dai kuskure kada ka cutar dani don girma Allah ban san komai ba" gyara tsaiwa Adnan ya yi ya ce "Ba muriƙinki nake magana ba, ba Abbinki ba Uba maifi wanda ya yi silar zuwanki duniya" "Abbine mahaifina bana da wani Uba sai shi shi ne mahaifina" dry Adnan ya sake yi kafin ya ce "Abra Khamal Khamis? To ba haka sunan naki ya ke ba, ke TSINTACCIYA ce, tsintar ki Abbi ya yi acikin jeji ya ɗauki tare da baki kulawa kamar ƴar cikinki, kuma ke ɗin bawai Shegiya bace mugun Ubanki shi ne yaja baki yadda ya rabani da farin ciki shima sai na raba shi da shi, zan ɗauki fansar abin da ya yi min akanki *REVENGE MARRIED* Sunan aurenmu" "bana da wani Uba wanda ya shige Abbi kai ma ka sani" hannunsa ya tsawa ya ce "bance ki yarda ba, amma ni da Abbin naki musan cewa ke ba ƴarsa bace kiyi tunani kaf dangin ku dawa ki ke kama? Just think bance ki yarda ba, amma zaki rayu a gidan nan tamkar baiwa!"
[10/13, 11:29 AM] Abk: Jiki na rawa, Khairy ta kira Mami tana salati tana salallami, Mami ta ɗaga wayar ta ce "Ya aka yi? Ta na ina ne, mutane sun fara taruwa fa?".

Khairy murya na rawa ta ce "Mami na kira mai kwalliyar ta ce mini tun uku, aka gama kwalliyar, kuma ta tafi".

Mami ta ce "Ta tafi taje ina?"

"Mami Wallahi ban sani ba, ba guri ɗaya muka je kwalliyar da ita ba, ni gurin da naje daban".

Mami ta ajiye waya tana faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yarinyar nan gidan ubanwa ta tafi ne? Ace an gama kwalliya tun uku amma har haɗu da rabi ba ta iso gida ba, ga mutane sun fara taruwa".

Anty suwaiba ta ce"Allah yasa ba guduwa ta yi ba".

Mami ta zare ido ta ce "Ta gudu ta je gidan uban wa? Lallai ma yarinyar nan".

Abu kamar wasa, ba Abra babu dalilinta, tun ana maganar ƙasa_ƙasa, har mutane suka fara jin halin da ake ciki.



Abokan aikin Adnan ne, suke ta shiri cikin shigarsu ta police, domin dai za'a yi parrate na ban girma ga Adnan da amarayarsa.
Usman ne ya kalli Adnan da ke ta haɗe rai ya ce "Wai haɗe ran me kake ne?".

Adnan ya ce "Am jealous ne, duk wannan garadan sai kun je kun kalle mini mata".

Aminu ya ce "Kai dalla ware, ai kaima gardin ne, sai kace a kanka aka fara Aure, ko da yake tsiyar mutum ya zama tuzuru kenan, duk sai ya fara behaving abnormal".

"Meye banbancina da kai? Har gara ma ni yanzu zan shige daga ciki, kai kana waje".

"Nima ina hanya ne" Usman yayi Maganar yana murmushi.

Daga haka suka kammala shirinsu, suka fara haramar tafiya gidansu Abra.



Granny ce ta shiga sashin Na'ima tana faɗin "Ke Na'ima, wai wace Maganar banza nake ji ne? Wai kamar Ana Abra ta ɓata, gidan ubanwa ki kai ta?"

"Haba granny, Ina kuwa zan Kai ta, daga zuwa kwalliya ba ta dawo ba".

"Ƙarya ki keyi, ana Magana kina wani ƙifta ido kamar ta Allah, ki fito da yarinyar nan duk in da ki ka kaita, kan in samo madoki in shemeki a gurin nan".

Ammi ce ta ce "Granny ki yi haƙuri, ya za'ayi ta aikata haka ga 'yar ta, Yanzu dai muyi ta addu'a, kuma a kira shi angon a sanar masa dan a san abun yi".

Granny ta ce "Wai ke Yaushe zaki gane kan makircin wannan yarinyar ne? Ai duk abun da akace tayi babu mamaki, yau duk abun da za'ayi sai an nemo mini jikata. Amm ke nace ina tabarau na ne? in ƙarewa wannan mara Kunyar kallo, in kalli idanunta sosai, dan ni idan na kalli idon mara gaskiya ina gane shi".

Ammi ta ce "Glass ɗinki yana in da ki ka yi salla, amma dan Allah ki dena wannan maganganun, bari a san abunyi, ko a tura wasu gurin mai kwalliyar".

Na'ima kuwa iya ƙuluwa ta ƙulu, ji take kamar ta rufe Granny da duka, shegiyar tsohuwa hayyataciya, sai tsawon rai kamar dabino, ta ƙi mutuwa kuma kullum cikin rikici take, tsawon shekarun da Na'ima tayi tare da Khamal Granny ba ta ƙaunarta sam.

Gida ya rikice ana neman Abra, ita kuma Granny ta rikice tana neman tabarau, ta ɗora da masifar cewa bayan sace Abra da Na'ima tayi, ta kuma sace mata glashinta, saboda baƙin hali.

Anty Suwaiba ta ce "Wai ke Na'ima ba wani mataki da zaki ɗauka a kan wannan sokuwar tsohuwar,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login