Showing 24001 words to 27000 words out of 231718 words
Chapter 9 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
da sa'arta.
Yadda Na'ima ke kumfar baki zaka ɗauka da wata ƙatuwar mace, sa'arta take wannan ihun, ba da little Abra da ba ta wuce a goyata. A. Abra kasa kuka tayi sai sakin ajjiyar zuciya kawai take, bayanta yayi kwance da zanan bulala, ta kasa ko ɗaga kai ta kalli Na'ima.
Tana bala'i da kumfar baki ta wanke wa Abra kashin, tare dayi mata wanka. Na'ima ta kalli Abra kafin da ɗan ƙarfi tace "Tsinanniyyar yarinya, Allah ya isa tsakani na dake, wlh da ƙafarki zaki bar gidan nan" Abra bata san me Na'ima take faɗa ba, hakan yasa bata ma fahimta ba, wani irin tsoron Na'ima ya kama Abra, tsoran dake neman sanyata cikin mugun hali, da son raunata mata ƙaramar ƙwaƙwalwarta.
Kama gashin kanta tayi da ƙarfi, cikin tsanar Yarinyar tace "Keee!!"
Abra ko motsi ba tayi ba, sai jikinta kawai take tsuma da karkarwa na azaba.
"Kika sake, naji kin faɗawa Abbi wannan maganar sai na yanka ki" Na'ima ta faɗi maganar cikin kunnen Abra, tana nuna mata wuyanta da hannu.
“A...Abbi jani" cewar Abra wanda ilahirin jikinta rawa yake, Na'ima ta figi hannunta zuwa bedroom tana faɗin "Abbin uwarki, ko na Ubanki? Baki da Uba a gidan nan Wallahi zan tabbatar dana gurɓata wannan muguwar fuskar taki. Kura da fatar Akuya!" Abra bata fahimta, da alamar yarinyar ta gama gigita da Na'ima, a haka Na'ima ta shirya Abra cikin Pria shirt short dress. Red colour, ta ɗaure mata tulin sumar kanta da ribbon.
Yadda Na'ima taji ana knocking ƙofar ta, yasa tayi saurin Miƙewa tare da gogewa Abra Fuskarta tas, ta nemi perfume ta fesa mata, hannunta ta saka ta ɗauki Abra tana gasa mata mintsini a haka ta nufi ƙofa da ita.
Tana buɗe ƙofar taga Captain Khamal tsaye sanye cikin ƙana nan kaya masu kyau, sai ɗaukan idanu yake.
Na'ima tai murmushi, tace "Man, ina son yarinyar wallahi ta shiga raina daka jiya zuwa yau" tai maganar dan kar ya fahimci wani ab7
Ganin Khamal yasa hankalin Abra tashi, ta shiga miƙawa Abbinta hannu tana son zuwa gareshi.
"Haba Daughter, nifa Mami ce mene yasa kike gudana" Na'ima ta faɗa tana rungome Abra. Kafin ta ɗaga idanunta zuwa ga Khamal tace. "Ina jin babu daɗi, yadda Abra bata son na ɗauke ta, ba na jin daɗin ƙyuyar nan ta ta." kwantaccen Murmushi Khamal ya saki tare da saka hannunsa ya amshi Abra dake hannun Na'ima, Abra ta ƙanƙame Khamal kamar zata shige jikinsa sai ajjiyar zuciya take saki.
A nutse Captain Khamal ya kalli Na'ima yana kashe mata idanunsa yace "Bata da yarda, kin san Uba yafi gaban wasa, shiya sa tafi yarda dani akan kowa"
“Uba yafi gaban wasa?” shine kalmar da ya nemi zautar da tunanin Na'ima, tunanin da ya sanya ta ƙara ninka ƙudirinta akan Abra, cikin fuskewa tace "I see, ka fahimtar da ita cewa nice mahaifiyarta, bana son yadda take guduna ina son yi mata riƙo irin na uwa da ƴa, ina nufin A good mother, who stands by her child, ba zan ji daɗi abinda yake cikina ya fito duniya har ya girma ba, ace Abra na guduna ina son nunawa, Ɗa na ko Ƴa ta cewa Abra ita ce babba"
Kalman Na'ima sunyi tasiri a zuciyar Kham, wani farin ciki ya kamashi cikin nuna kulawa ya bawa Na'ima side hug yace.
"Kada ki damu, rashin sabo ne da kuma yadda ta tsinci kanta, zan yi ƙoƙarin fahimtar da Ita"
Murmushi Na'ima tayi da saurin kuma tace.
"Oh, i almost forget bari naje na haɗa mata something Liquid, tai breakfast"
Yace "thats good, I don't want my girl to starve" yai maganar yana sake rungume Abra tare da juyawa zuwa part ɗinsa.
Na'ima tace "Yanzu ta fara zama da yunwa" Khamal dake ƙoƙarin buɗe ƙofa, ya juya gaba ɗaya yace "magana ki kai?" Na'ima ta buɗe idanunta tace "Nace bani 10 minutes" ta faɗa tana saurin shigewa cikin kicthen.
A hankali Khamal ya fara ƙoƙarin sauke Abra, wata gigitacciyar ƙara ta saka tana ƙanƙame shi tare da ɓoye fuskarta a jikinsa, jikinta na rawa tace "Abbi"
Kallonta Khamal yake, He is trying to understand, what scared her.
Zama ya yi da ita saman Royal bed ɗin sa, cikin nuna kulawa yace "Daughter" ya faɗa yana kallon Fuskarta, ganin Idanunta ya yi jaaa sosai, Fuskarta ta kumbura alamar tayi kuka yasa, da sauri Captain ya kamata a jikinsa yace "Mene ya baki tsoro? Waye ya saki kuka Abra Khamal?" Yai maganar yana ɗaga muryarsa dan ta ji me yake faɗa.
Abra babu damar magana, sai ɓoye jikinta take a jikinsa tana ajiyar zuciya, Tsam-tsam Khamal ya rungume ta a jikinsa, yana jin tausayinta na kamashi. Bai yarda da ƙwaƙwalwar Yarinyar ba, baya son ta samu “Depression” saboda alamu duk sun nuna a firgice take, Kamar ma wani abu ne ke tsorata ta, ƙara rungumeta yayi a jikinsa jin yadda take ta sauke ajjiyar zuciya!
"I'm sorry Daughter, Abbi is here with you" ya faɗa yana shafa kanta.
Kwanciya tai lamooo, a jikinsa bayan wani ɗan lokaci, ya ji Saukar numfashinta a ƙirjinsa, hakan yasa ya ɗan ɗagota sai a lokacin ya lura bacci tayi, gaba ɗaya a firgice take, kwantar da ita yaso yi, amma Abra taƙi sai ma sa ka masa kuka da tayi.
Kwanciya ya yi saman gadon, ya ɗora ta a jikinsa yana bubbuga bayanta alamar rarrashi, a nutse ya yi kissing cheeks ɗinta, Muryar can ƙasa yace.
"Ba zaki taɓa kukan rashin iyaye ba, zan baki kulawa, Soyayya, tattali, zan yi maki dukkan abunda Uba na gari ya dace ya yiwa yaransa, zan bada ke ga miji na gari wanda zai so ki Love forever, love without deception insha Allah."
Ya faɗi Maganar yana shafa sumar kan Abra, wata irin soyayya ya kewa yarinyar, wacce baya tunanin ko ɗan cikinsa zai iya yi masa irin wannan Soyayyar. Ya kuma fahimci cewa haɗuwar jini ce Abra ta kasance kyauta a gareshi ( A gift from God).
Zameta yayi daga jikinsa yana gyara mata kwanciya tare da ja mata duvet ya lulluɓe mata jikinta, ya jima yana kallon yadda take sauke numfashi a wahale kafin ya juya zuwa waje.
A dinning area, ya samu Na'ima tsaye, tana shirya breakfast, tayi adonta kamar kullum cikin doguwar rigar Abaya, fuskarsa babu walwala yaja Kujera ya zauna, without looking at her direction. Murmushi tayi cikin ƙasa da murya tace.
"Ya na ganka kai ɗaya? Where's my Daughter?"
A kasalance yace "Mene ya samu Abra Khamal?"
Dam! Zuciyar Na'ima ta buga, bata ƙaunar yadda Khamal ke maƙala sunan Abra da nasa, gani take babu wanda ya cancanci wannan sunan irin (Biological Child) ɗin sa.
"Wani abu ya samu Abran bayan na kawo maka ita?" gaba ɗaya ya ɗaga kansa ya kalli Na'ima kafin yace.
"Na fuskanci ta yi kuka, a launin Idanunta na gane" Na'ima taja Kujera bayan ta kammala haɗawa Captain breakfast ta du be shi sosai kafin tace.
"Oh, ina son faɗa maka daman, ɗazu tayi kashi a ƙasa kasan daman ba yarda take dani ba, saboda na ɗauke ta zuwa Part ɗina, na wanke mata tare dayi mata wanka shine take ta kuka"
Jinjina kansa yayi tare da fara yin breakfast, ba tare da yace komai ba, sai da ya kammala ya miƙe tsaye, a tare suka dawo Main Parlo shi da Na'ima, tana ta faɗa masa how she loves Abra.
Murmushi kawai Captain keyi, feeling so happy ƙasa tayi da Murya tace.
"Ya kamata ai mata shopping, na kayan sawa masu kyau sosai"
"Nawa zai isa?" Captain yace kai tsaye idanunsa akan plasma yana kallon News.
"200k, zai Isa komai da komai Man" Kallonta kawai yayi ba tare da yace komai ba.
iya satin biyun nan da Abra tai a gidan Captain Khamal, tas ha Wahala sosai wajan Na'ima, bata barin alama guda ɗaya wanda Khamal zai fahimta, kasancewar baya gari yaje bada Wasiyyar da Captain Denial da Jamil suka bari.
Hakan yasa Na'ima ta samu full Chance na azabtar da Abra Khamal Khamis.
Da Yamma misalin 4:15 Motar Khamal ce ke tafiya akan titin Railway Quarters Nasarawa kano, kai tsaye motar a gida mai number 15 ta tsaya aka fara danna Horn, cikin sauri Mai gadi ya buɗe musu gate ɗin, ana yin parking da Motar, Captain Khamal Khamis ya fito, saboda yadda yaji zuciyarsa na bugawa, da sauri ya nufi cikin gidan, gaba ɗaya hankalinsa ya tashi tun daka Main Parlo kunnansa ya fara jiyo masa sautin Muryar Abra.
Tsaye ya yi yana son sanin inda kukan ke tasowa, da sauri kuma ya nufi kitchen a gigice yace. “Na'ima!!!!” Khamal ya dakawa Na'ima tsawa, tsawar daya sanya tayi saurin sakin cokalin hannunta, wanda ya yi jajir saboda gasa shi da tayi a jikin Gas!
Yadda jikin Captain Khamal ke rawa, haka na Abra ke rawa, Na'ima kam hatta ɗan dake cikinta sai daya motsa, bata taɓa tunanin zai dawo cikin wannan satin ba, ko ɗazu sun yi waya amma bai ce mata yana hanya ba.
Dawowar ta sa tazo mata unexpected, wanda yasa Na'ima ta kasa controlling kanta, tsoro ya kamata musamman yadda taga idanun Khamal na fitar da wani irin ruwan Masifa.
Da gudu Abra ta Ƙarasa wajan Khamal, tana saka wani irin kuka tare da zaro harshenta waje wanda ya yi jaa sosai, Khamal ya durƙusa tare da saka hannunsa ya ɗauki Abra, Gam! Gam! Abra ta riƙe Khamal tana sauke numfashi a wahale, cikin taƙaici Captain yace.
"Na'ima? Abun da na gani, gaskiya ne Ƙona mata harshe ki kai With spoon? Ke mahaukaciya ce? Me wannan yarinyar tayi Miki? ashe ƙarya ki kai baki shirya amsar Abra matsayin ƴa ba?"
Shiru tayi masa, gaba ɗaya Khamal yayi kanta cikin hargaginsu na sojoji yace "Ba magana nake maki ba?"
Tace "Na faɗa maka bana sonta, bana sonta yaya zan kuma.....," Marin daya sauke mata ya tilasta wa Na'ima haɗiye sauran maganganun, cikin fusata yace.
"You are evil, Na'ima!... Nayi nadamar bar maki Abra, Whatever happened to her ke ce sila, ba zan yafe Maki ba"
Cikin kuka Na'ima tace "Dama na san wannan shegiyar yarinyar 'ƴar kace, wacce karuwa ta haifa maka, wallahi sai na kasheta ba zan taɓa zama da ƴar karuwa a cikin gida na ba"
Tana faɗin hakan ta nufi inda wuƙa take ganin hakan yasa Khamal ya goya Abra a bayansa, ita kuma ta ƙanƙameshi, bai tsaya jiran komai ba ko tunanin cikin dake jikin ta ya sake ɗauke ta da mari, sai da ya jera mata mari har uku cikin ɗaga murya yace.
"Abra ƴa ta ce, jina ce, nina na haife ta, nina samar da cikinta tare da karuwar da kike magana, tun da baki da hankali ba ki san me kike ba, Abra Khamal Khamis is my biological Daughter! Kuma zan kawo karuwar da ta haifa min ita a matsayin mata taci gaba da riƙe ta..." Yana faɗin hakan yayi waje, kai tsaye motarsa ya nufa Driver na ganinsa ya buɗe masa mota ya shiga ɗauke da Abra wacce take ta sauke ajjiyar zuciya na azaba.
Wani irin ciwo ne ya tasowa Na'ima, ba tare data shirya zuwansa ba, wata irin ƙulewar mara, da ciwon baya ne taso mata gadan gadan. ba tare da zato ko tsammani ba, nan take kuma wani ruwa ya fara bin ƙasan ƙafarta, idanunta har rufewa suke saboda kalman ƴa, da karuwa da suke mata kai kawo a kunne! Da gaske Khamal yake Abra 'yar sa ce? Wani gefe na zuciyar Na'ima ya tambayeta. Tuna shaƙuwa mai ƙarfi dake tsakanin Abra da Khamal yasa, marar Na'ima ƙara ƙullewa wayarta ta ɗauka a kiɗime jin kamar abin cikinta zai faso ta cikinta ya fito, cikin kuka tace.
"Na shiga uku, zan mutu wallahi ƴarsa ce" Aunty daga can cikin wayar tace.
"Meke faruwa kuma yanzu Na'ima?" Na'ima na durƙushe dafe da cikinta tace "Duk abinda kika ce min nayi, na ƙona mata hannu na ƙona mata harshe da cokali, yau ma ina shirin ƙona mata harshe sai ga shi ya dawo" Aunty ta buɗe idanunta With shock tace "mene yasa wani lokacin daƙiƙiyar ƙwaƙwalwa ce take Na'ima? Ba nace idan yana nan babu ruwanki da yarinyar ba?"
Na'ima na kuka tace "Baya nan, ban san yau zai dawo ba..." Ƙara Na'ima ta saki ba tare data ƙarasa maganar ba, Anty tace "Lafiya kike ihu kuma?"
tana yarfe hannu tace "marata ce za ta fashe Antyy, please Anty kizo na shiga uku...." Jifa tai da wayar jikinta na rawa tana haɗa gumin azaba, da wani irin ciwo da ba ta taɓa jin irinsa ba, da ma kwana kusan biyu mararta na mata ciwo, amma da yake ta saka bala'i a ranta ba ta damu taje Asibiti ba.
Mintuna talatin da wayar da su kai, Anty Suwaiba ta ƙaraso cikin gidan hankali tashe, tun daga tsakiyar Main Parlo ta fara jiyo kakarin Na'ima tana nishi.
Hankali a tashe tace "Ina kayan haihuwar suke, mu tafi Asibiti wannan ai kin kusa haihuwa?"
Da ƙyar Na'ima tace "Cikin ɗakina, kan mudubi" da sauri Anuty ta nufi ɗakin Na'ima bata sha wahalar ganin kayan ba, tana ɗakko wa suka ci karo da Granny a Parlon.
Kallon tsaf Granny ta yiwa Anuty Suwaiba kafin tace "Ya na ganki duk a hargitse kamar wata taɓaɓɓiya Suwaiba?"
Kafin Suwaiba tace komai Ammi dake bayan Granny wanda zuwansu kenan tace "Badai haihuwa Na'ima tayi ba Suwaiba?"
"Haihuwa za tayi, Asibiti zamu tafi" Anty ta faɗa a gajarce tana nufar kitchen ɗin.
Granny ta buɗe baki sosai tana girgiza kai tace "To mene ya kawo Bazawara gidan Kamalu kuma? Ina da labarin baƙin halin matar nan, yaza tazo tayi kane kane a gidan jikana kamar ita yake Aure?" Ammi dai ba tace komai ba, tabi bayan Anuty Suwaiba zuwa kitchen ɗin.
Se dai miƙewar da Na'ima za tai, tai nishi se ga jariri.
Ammi tace "Iko se Allah, tun farko be kamata ta zauna a gida ita kaɗai ba ga watam haihuwa ya kama".
Ammi ta amshi jaririn hannun Subawai wanda yake ta tsala ihu, tai waje ta ba su guri, cotton da zaiton ta ɗauka ta shiga goge masa jiki, cikin ikon Allah kuma mahaifa ta faɗo, Anuty ta gyara wajan tass, Na'ima ta haihu a kitchen saboda 5sabar jaraba.. a ranta tana jinjina rashin kirki irin na Khamal Khamis.
Na'ima wacce ta fito wanka yanzu ta shirya cikin atamfa sai kuka take tana faɗin "Ammi kin gani ko? ya gwammace ya ɗauki yarinyar yayi waje da ita, akan ya kai ni asibiti, Duk abinda muka tsara a rayuwar mu amma Zuwanta ya fara lalata komai, wlh ba zan iya ba"
Ammi da take riƙe da kyakykyawan jaririn Na'ima wanda ya kwashe kamarta tas, babu abinda ya ɗauka na khamal sai kyawawan fararen idanunsa, amma kamar yaron da Na'ima ta ɓaci.
Ammi tace "kiyi haƙuri, bani da bakin baki haƙuri Na'ima, amma bai dace ki dinga danganta Abra da Khamal ba, Khamal da ya iya riƙe kansa tun lokacin samartaka, tsayin shekaru mene zai sa kice wannan yarinyar ƴarsa ce? Da Khamal zai ajjiye shege da tun yana saurayi zai ajjiye ba yanzu daya yi Aure ba.
Ba ina kare Khamal ba ne, Saboda rayuwa ta sauya Mutane na iya canzawa a kowane lokaci, balle rayuwa irinta sojoji d suke cuɗanya da mutane daban daban.
Naima tace "Har mari na yayi akan gantalliyyar yarinya da babu wanda yasan Wacece ita, yanzu fa kiransa akai aka ce masa na haihu, haihuwar da yake ta burinta kalli yadda yayi watsi da komai? Bai damu da ɗan sa da yanzu duniya yake buƙatar jin ɗumin jikinsa ba,
Nasan Khamal sai ya nuna bambanci tsakanin Shegiyar da ɗan daya haifa Wallahi ba zan iya ba" Na'ima ta ƙare maganar cikin kuka, Granny dake zaune tun ɗazu baki saki tana kallon Na'ima na tatala rashin mutunci, ko nauyin Ammi ba ta ji, ta runste idanunta tace.
"Ki ga gantali a kanki, mace babu Tawakkali, nan nan fa naji ana cewa ƴar uwarki wacce ta mutu cikin Shege tayi, amma ke baki duba wannan ba? Kiyi ta zabga Masifa da wannan yammaci yanzu da kin mutu wajan haihuwa kice me?, to kawai a kiramin Khamal yaje ya nemo mace ya aura tun da ita wannan ba macan rufin asiri bace, wallahi Na'ima ke ba abokiyar zama bace ban taɓa jin haka ba"
Anuty Suwaiba dai na zaune tana ayyana irin yadda zata saka Na'ima taci Uban Abra, hankali kwance.... Ammi ta sake kiran number Khamal amma bai ɗauka ba.
Khamal Khamis dake zaune gaban likita Abra na jikinsa wacce ta samu yin Bacci, a hankali yace "Pardon! Ban gane mene kake cewa ba"
Likitan ya gyara zama bayan ya miƙawa Khamal scanning ɗin da akai ma Abra, tare da X-rays da kuma teses yace
"Binciken da mukai duk sun nuna lafiyarta ƙalau, amma akwai yiwuwar ta kamu da depression, gaba ɗaya yarinyar kamar wani abu na tsorata ta.
“Depression?" Khamal Khamis ya maimaita.
Likitan yace "ka kwantar da hankalinka mana"
Khamal ya girgiza kai yace "I can't, kayi min bayani menene Depression ɗin ma na kasa fahimta gaba ɗaya" Murmushi kawai likitan ya yi kafin yace.
"It's normal for kids to feel sad, act grouchy, or be in a bad mood at times. But when a sad or bad mood lasts for weeks or longer, and when there are other changes in a child's behavior, it might be depression" Major ya ƙanƙame Abra cike da tausayi a hankali yace.
"To me ze sa Abra ta kamu da depression" Likitan ya kalli Captain cike da kulawa kafin ya girgiza kai yace
" Yana iya faruwa, a dalilin gado idan suna da shi a family, ko yanayin environment ɗin da suke zaune, ko wani abu da yake damunsu ko yake takura su".
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun!" Khamal ya faɗa sannan yace "Abra tai ƙanƙanta ta kamu da irin wannan ciwon"
Likitan yace
"Ba abun mamaki bane ba, a wasu yaran akan iya identifying ɗin sa da wuri, kamar a shekarunta idan iyaye suka kula suka je Asibiti da wuri,"
Kallon Abra Khamal kawai keyi idan yace baya son yarinyar ya yi ƙarya, cikin kulawa ya kalli Dr yace.
"What Should I Do if My Child Is Depressed?" Kan Likitan a ƙasa yana duba abu ya bawa Khamal amsa da faɗin.
"A dinga bata isashen lokaci, a zauna da ita a tattauna a ji meye matsalolinta, a gane meyasa take takure kanta daga cikin mutane, kuma ba ta magana, tunda shekara uku a yara ai sun fara kiran sumaye da sauran surutu, amma ita kace