Showing 129001 words to 132000 words out of 231718 words
Chapter 44 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
cigaba da abin da yake gabansa.
Da yaga zata dame shi, ya buga masa wata razananniyar tsawa, wadda ba shiri ta bar masa ɗakin, tana mamakin meke faruwa.
Kusan awanni biyu da dawowar Major, ya sami Na'ima a ɗakinta yana binta da wani mugun kallo ya ce "Na'ima, ubanwa ye ya sanya ki gayawa Abra cewar ba mune muka haifeta ba?"
Dafe ƙirji tayi tana faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ita Abran ce ta ce maka ni na gaya mata?".
"Shut up! Sai ta gayamini cewar ke ce? Ta kirani tana kuka cewar wai ba mu muka haifeta ba, shiyasa mijinta ya ƙwace wayoyinta saboda kar ta kira ta ɗaga mini hankali? Waye ya sa ki gayawa Abra am talking to you".
"Wallahi ni ban gaya mata ba, bani bace ba"
"Ashe har kin manta sharaɗin dana sa miki akan, daga ranar da wani ya san bamu muka haifeta ba, ta dalilinki a bakin Aurenki ba? Ashe zaman haramci muke yi, ki tattara ki bar mini gida na sake ki, saki ɗaya".
"Na shiga uku, baka sakeni tun da ƙuriciyata ba sai yanzu, da girmana har na kai 'ya ɗaki".
"Ƙarya ki ke yi, munafuka"
"Ni kake kira munafuka, a kan laifin da ba......
"Shut up! Kar ki bari in dawo ɗakin nan in tarar ba ki tafi ba.
Har ya juya zai fita ya hangi takarda a ƙasan madubi, da irin signing ɗin Salman.
Littafin kuɗi ne,biya ₦300 via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank... Idan katin waya ne zaka Turo 500 shaidar biya 08081012143
[10/14, 1:45 PM] Abk: Ɗauke idonsa ya yi daga kan takardar ya juya da niyyar fita amma sai ya ji zuciyarsa na son sanin me takardar ta ƙunsa, ko don yana cikin kewar ɗan nasa ne? A hankali ya juyo ba tare da ya kalli inda Na'ima take ba, wadda ke gunjin kuka kamar za ta shiɗe. Sunkuyawa ya yi tare da kai hannu zai ɗauka, kamar an cillo kibiya daga cikin baka haka ya ga Na'ima ta yi tsalle ta dira a gabansa, da mamaki yake kallon ta bai ce komai ba. Cikin bugawar zuciya Na'ima ta matsar da takardar gefe cikin pretending irin ba ta san ta yi hakan ba. Wani mugun kallo ya watsa mata ya miƙe ya ɗauki takardar ya fara karantawa a zuci.
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, na shiga uku!" Naima ta faɗi haka a fili cikin tsananin ruɗewa da rawar jiki.
Kallo mai kama da na tsana Abbi yake jifan ta da shi, cikin matuƙar takaici da ɓacin rai ya ce. "Me takardar nan take nufi Na'ima?" Kasa magana ta yi sai rawar baki take tana haɗa hannayenta alamar roƙo.
"I'm asking you Na'ima me kika aikata? Wacce irin soyayya Salman yake nufin yana yi wa Abra?" Ya yi maganar cikin ƙaraji da tsawa, wanda hakan ya ƙara firgita ta."
Cikin rawar murya ta ce. "Don Allah My Man ka saurare ni, wallahi ban aikata abin da kake zargi na da shi ba."
"Wannan takardar kuma ita ta ƙirƙiri kanta kenan?" Ya yi maganar cikin hucin ɓacin rai.
Rasa abin cewa ta yi sai matsanancin kuka da ta fashe da shi cikin nadamar faɗawa Salman ba su suka haifi Abra ba, da ta san haka al'amarin zai juye mata da ba za ta soma faɗa masa ba.
"Wannan takardar ta ƙara tabbatar mini da ke kika faɗa wa Abra ba mu muka haife ta ba kamar yadda kika faɗa wa Salman, tabbas biri ya yi kama da mutum, yanayin Salman kafin ya tafi china irin na wanda yake cikin tsantsar damuwa ne, na so na fahimci hakan, amma saboda kin san me kika shirya da na faɗa miki sai kika ce ba haka ba ne, miskilanci kawai ya koya. Kin cuce ni Nai'ma da kika bari yaran nan suka san su ba ƴan'uwan juna ba ne, kin kuma cuci kanki, domin ba zan ƙara zaman aure da ke ba har abada, I hate You!"
"Khamal ni ce fa, ni ce Na'imanka don Allah kar ka mini haka, na san na yi kuskure amma ka yafe mini, ka tsaya ka fahimce ni." Na'ima ta faɗi haka tare da riƙe ƙafafuwansa.
Hamɓare ta ya yi a zuciya ya ce. "Last maganata da ke, na ba ki 30 minutes ki tattara kayanki ki bar mini gidana."
Bai jira cewarta ba ya fice daga ɗakin, part ɗinsa ya nufa ya shiga bedroom ɗinsa ya kulle ƙofa. Innalillahi.... kawai yake maimaitawa a cikin ransa cikin tsantsar damuwa, sai taune lips ɗinsa yake tamkar zai tsinka shi, kyawawan fararen idanuwansa sun yi jajur saboda tsananin ɓacin rai. Ji yake kamar ya rufe Na'ima da duka saboda baƙin ciki, damuwarsa halin da Abra take ciki a yanzu, ya san ba ƙaramar damuwa za ta ɗora wa kanta ba. Tsaki ya ja cikin jin haushin kansa na amince wa Na'ima da ya yi akan Abra, gaskiya ne da aka ce bakin da ya furta ƙi ba zai taɓa furta so ba. Amma me ya sa ya kasa gane pretending kawai Na'ima take? Duk da kasancewar shi mai saurin fuskantar abu. _ƙaddara_ zuciyarsa ta ba shi amsa.
Hand bag kawai Na'ima ta ɗauka ta saka hijabi tare da zira takalmi ta fice cikin tsananin tashin hankali. Domin ba ta ji a ranta ta bar gidan Khamal kenan, zuciyarta ba za ta iya ɗaukar hakan ba, tana son Mijinta ba ta son rabuwa da shi.
Aunty Suwaiba ce ke kaikawo a parlour bayan Na'ima ta gama zayyane musu abun da yake faruwa. Cikin damuwa ta ce. "Wautarki ta yi yawa Na'ima, abun da nake jiye miki kenan tun farko, shi ya sa nake tausar ki akodayaushe akan ki dinga danne ƙiyayyar yarinyar nan da kishinki a kanta, amma ki ka ƙi ji, gashi nan ya sake ki." Cikin kuka Na'ima ta ce. "Wallahi Aunty ba ni da masaniyar abun da yake zargi na da shi, ni ban faɗa wa yarinyar cewa ba mu muka haife ta ba har yau."
"To waye ya faɗa mata? Ni dai a sani na ko Kaduna ba ku taɓa zuwa ba, balle a ce wani ya san ku a can ya faɗa mata. Kuma abubuwan da kike yi wa yarinyar ne ya saka ko da ba ke kika faɗa mata zai ce ke ce."
"Dan Allah Aunty ki bar ni da maganganun nan, in ji da abun da yake damu na mana, haba."
"Na bar ki Na'ima, amma ko kin ƙi ko kin so shegen kishin da ɗora wa kanki ne ya jawo miki."
A ƙufule Mama ta ce. "Wai wannan maganganun na mene ne? Abin da ya faru ya riga ya faru sai dai mu nemo hanyar da za a gyara shi, tunda kin ce saki ɗaya ne ko?" Ta ƙarashe maganar idanunta a kan Na'ima. Gyaɗa mata kai ta yi tana sharar hawaye. Duk wannan fafutukar da boloƙon da ta yi saboda Abra ta bar musu gida amma ƙarshe abin a kanta ya ƙare, tana murna shirinta ya tafi daidai ashe zai warware ne tas.
Tana ji Adnan ya shiga toilet ya yi wanka ya fito amma ita ta kasa ko da ɗaga ɗan'yatsanta ne, wani irin nauyi take jin kanta ya yi mata, ga duk jikinta dake mata ciwo saboda gajiyar da Adnan ya tara mata. Ita kaɗai ta san me take ji a cikin ranta na tsantsar damuwa, addu'a take yi Ubangiji ya sa mafarki take ba gaske ba ne ABBI BA SHI NE YA HAIFE TA BA. Zuciyarta ta kasa yarda da hakan duk kuwa da yanda Adnan yake ta nanata mata, tabbas a yau ta yarda Adnan ba ya ƙaunarta kamar yadda yake furtawa, tunda har iya faɗa mata abin da zai tarwatsa mata zuciya. Idanunta a kansa yana shiryawa cikin kwanciyar hankali da nishaɗi, alamun rayuwar tana yi masa daɗi. Wasu hawaye masu ɗumi ne suka shiga kwaranya daga cikin idanunta. Cikin dauriya ta tashi zaune da ƙyar ta ja rigarta ta saka, hannunta dafe da ƙirjinta saboda nauyin da ta ji ya yi mata, cikin haki ta ce. "Adnan! Don girman Allah dan darajar iyayenka ka taimake ni ka sauwaƙe mini aurenka, ba don ni ba." Sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya da karyar da zuciyar duk wani mai imani. Wani mugun kallo ya wurga mata cikin tsawa ya ce. "In kin ga kin bar gidan nan to gawarki a ka fitar." Kallon shi ta yi tana son ta yi magana amma ta kasa. A tsawace ya ce. "Malama ki tasar mini daga kan gado da najasa a jikinki, ki kuma gyara mini shi kafin warin abin da kika fitar ya hautsina mini ciki." Duk da yanayin da take ciki amma sai da ta yi wani murmushi da ya fi kuka ciwo sannan ta yunƙura ta sauka daga kan gadon. Kamar yadda ya umurce ta, ta kama zanin gadon da nufin cire shi amma sai ya bar hannun nata saboda rawar da jikinta yake yi kamar ana kaɗa mata gangi. Dafe kanta ta yi da sauri saboda juyawar da ta ji yana mata, ƙofa ta nufa don ta fice zuwa ɗakinta, kafin ta kai ga yin hakan ta faɗi a ƙasa sumammiya. Adnan dake kallon ta ya ja tsaki cikin takaici ya ce. "Yarinya sai ka ce mai farfaɗiya, abu kaɗan sai ki zube salon ki janyo wa mutane masifa." Kamar wata Dabba haka ya ja ta ya fitar da ita parlour ya juya ya koma ɗakinsa ba tare da ya ƙara bi ta kanta ba.
Sai wajen ƙarfe ɗaya na dare Adnan ya fita dan da ya haɗa coffee, a inda ya bar ta ya tarar da ita kwance tamkar gawa, tsaki ya ja ya ƙarasa ya buɗe fridge ya ɗauko ruwa mai sanyi ya shiga sheƙa mata daga tsaye, kusan 3 minutes sannan ya ji ta ja dogon numfashi tare da motsawa. Taɓe baki ya yi ya tafi ya bar ta. A hankali ta buɗe idonta da suka yi mata nauyi ta bi bayansa da kallo, ta daɗe a haka sannan ta miƙe da ƙyar ko gani ba ta yi sosai ta shiga ɗakinta ta faɗa kan gado.
Rabi da rabi baccin Abbi ya kasance a yau saboda tunanin halin da Abra take ciki. Washegari da sassafe ya shirya direbansa ya kai shi airport ya bi Flight ɗin ƙarfe takwas zuwa Kaduna.
Wata dattijuwar mata ce zaune a gaban gadon marasa lafiya da wani tsoho yake kwance, ta yi tagumi tana kallon yanda numfashisa yake fita da wani irin sauti gami da ɗagawar da ƙirjinsa yake yi, lokaci zuwa lokaci tana share hawayen dake fita daga cikin idonta. A hankali ta ɗaga kanta tare da amsa sallamar da wani matashi yake yi a kusa da ita. Cikin damuwa ta ce. "Ba su zo ba ko Musa?"
Numfashi ya sauke cikin damuwa ya ce. "Ba su zo ba Inna, sai waɗannan masu fararen kayan ne kawai."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, kalli yanda numfashin Malam yake fita fa musa, wallahi gabana sai faɗuwa yake, ina tsoron kar mu rasa shi." Inna ta faɗi haka cikin kuka.
"Ki yi haƙuri Inna, insha Allahu Malam zai samu lafiya, cuta ai ba mutuwa ba ce.
"Ba za ka gane ba Musa, ka kira masu fararen kayan don Allah su zo ko za su iya yi masa wani taimakon."
Wata mata dake zaune a kusa da gadonsu tana jinyar nata mai gidan ta ce, "Sai haƙuri Baba, haka muke fama da likitocin nan, ba sa son zuwa da wuri, Nurses ɗin nan kuma ba wani abu za su iya ba, sai dai kawai su ta ƙara wa mutum ruwa da ɗan abun da ba za a rasa ba."
"To me ya sa su likitocin ba sa zuwa da wuri? tun cikin dare Malam yake wannan abun, waɗanda suka yi aikin kwana sun yi masa gwaje-gwaje sun ce mu jira sakamakon idan likitan da zai karɓi aikin safe ya zo zai ba mu, muna ta jira har ƙarfe tara amma babu wanda ya zo."
"Hmm, asibitin gwamnati kenan, sai haƙuri, ku yi ta addu'a kawai. Dan shi wannan likitan ma da zai duba shi sau ɗaya yake zuwa a sati"
Girgiza kai Inna ta yi ta ce. "Allah Sarki takaka, shikenan bari mu jira."
Sai Asuba sannan Abra ta iya tashi ta shiga toilet ta yi wanka tare da ɗauro alwala ta fito ta yi sallolin dake kanta a zaune. Sosai ciwon da kanta yake mata ya tsananta, tamkar zai tarwatse haka take ji. Ga wani irin zafi da raɗaɗi da zuciyarta ke mata. Tana idar da Sallar ta koma kan gado ta ƙudundu ne a cikin bargo saboda sanyin da ta ji yana ratsa ta, wani irin zazzaɓi mai zafin gaske ne ya rufe ta wanda ya haifar mata da rawar ɗari. A haka Adnan ya shigo ɗakin ya tarar da ita tana numfarfashi. Cikin nuna ko in kula da halin da ya gan ta a ciki ya watsa mata singlets and boxes ɗinsa a jikinta tare da ba ta umarnin tashi ta wanke masa a lokacin.
Ɗaga kai ta yi da ƙyar ta dube shi amma ta kasa magana, hawaye ne kawai yake zuba daga cikin idonta. Ƙoƙarin jan bargon da ya yaye mata ta yi amma ya riƙe bargon tare da buga mata tsawa da faɗin. "Tashin ne ba za ki yi ba ko me da kike ƙoƙarin jan bargo? Wato ga mahaukaci yana magana ba za ki tashi ki yi abin da na saka k....." Ƙarar doorbell ta hana shi ƙarasa faɗar zancensa. Ƙwafa ya yi tare da nuna ta da hannu ya ce. "Na dawo na tarar ba ki tashi ba, wallahi na lahira sai ya fi ki jin daɗi." Ya ƙarashe maganar tare da yarɓar mata da bargon a fuska. Lumshe idonta kawai ta yi tana jin yanda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri. Adnan da matsalarsa ba su ne damuwarta ba a yanzu, damuwarta kawai sanin gaskiyar abin da Adnan ya faɗa mata na cewa ita TSINTACCIYA ce, Abbinta mafi soyuwa a gare ta ba shi ya haife ta ba, ba ta fatan hakan ya kasance, domin ta san zuciyarta ba za ta iya ɗauka ba bugawa za ta yi. Addu'a take Allah ya sa Abbinta ya musan mata ya ce ba haka ba ne, domin ta ƙudurce a ranta duk wanda zai faɗa mata ba za ta taɓa yarda ba, ko da Mami ne da Salman kuwa, Abbi kawai zai tabbatar mata da gaskiya ne ba shi ya haife ta ba ta yarda.
Adnan yana buɗe ƙofa kamar a mafarki ya ga Abbi tsaye cikin wani irin yanayi, sai da gabansa ya faɗi amma bai nuna hakan ba, murmushi ya yi tare da yi masa iso zuwa cikin parlour'n cike da girmamawa.
Sai ƙarfe tara da rabi wani likita ya zo ya ƙara dudduba jikin malam, bayan ya gama ya ce su Inna su same shi a office. Bayanin ciwon dake damun Malam ɗin ya yi musu wato ciwon zuciya wanda already sun san da shi.
Ya ƙara da faɗin, "Ciwon nasa ya yi tsanani sosai, don haka ana buƙatar yi masa aiki cikin gaggawa. Amma gaskiya wannan Asibitin ba mu da kayan aikin, sannan likitan da yake aikin bai ƙaraso ba"
A ruɗe Inna ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! To likita ku yi masa aikin mana, don Allah ka taimake mu ka ceto mana rayuwarsa, idan muka rasa shi za mu shiga cikin wani hali, shi ne bangon rayuwarmu."
Cikin son kwantar mata da hankali likitan ya ce. "Kar ki damu Hajiya, zai samu lafiya insha Allahu, sannan kuma a nan asibitin ba mu da kayan aiki masu kyan da za mu yi masa aiki, amma zan tura ku wani babban Private Hospital wanda da yardar Allah za a yi aikin successfully."
"Likita ina ne firaben honfital kuma?" Inna ta tambaye cikin damuwa.
"Asibitin kuɗi kenan, sunansa G.Y BULAMA, suna da ƙwararrun likitoci gami da kayan aiki masu inganci."
"Asibitin kuɗi fa ka ce ɗana, ai ba mu da kuɗin da za mu biya, na gwamnatin ma da ƙyar muke iyawa."
"To Hajiya, in dai kuna son samun lafiyar shi gaskiya ku je can ɗin."
Inna za ta kuma magana Musa ya hana ta da faɗin. "Shikenan likita, mun gode sosai." Sannan ya dubi Inna ya ce. "Mu je Inna."
Bayan sun fita Inna ta saka kuka ta ce. "Allah ka fitar da mu daga cikin wannan tashin hankalin, yanzu Musa ya za mu yi?"
Cikin damuwa Musa ya ce. "Inna mu je can inda ya ce manan kawai, don gaskiya likitan nan ya faɗa mana a asibitin nan ba yi masa aikin za su yi ba, kin manta yanda aka yi ne wancan karon, kullum cikin saka mana ranar aikin suke amma ba su yi ba har Allah ya ba shi lafiya muka koma gida."
Gyaɗa kai Inna ta yi ta ce. "Haka ne, to amma Musa kuɗin nake ji, ba mu san nawa za su ce mana ba."
"Allah ba zai hana mu yanda za mu yi ba, mu je ya yi mana kwatancen asibitin."
Jiki a sanyaye Inna ta ce. "Toh, addu'ata kullum kar Allah ya karɓi ran malam ba tare da ya sanar da mu aihinin gaskiyar al'amarin nan ba, domin mu san ta inda za mu fara bincikawa, tunda komai daren daɗewa sai gaskiya ta yi halinta."
"Insha Allahu Malam zai samu lafiya har ya warware komai da kansa kamar yadda yake da buri, ki kwantar da hankalinki Inna, mu dai mu yi ta addu'a Allah ya ba shi lafiya kawai."
"To amin amin .Amma naji ance shi likitan da zamu je gurin nasa yana zuwa nan duba marasa lafiya, ba za mu jira shi ba?"
Musa ya ce "Inna ance yau babu lallai ya shigo, kawai gara mu bishi can ɗin, bari in je sun ce zasu bamu wata takarda mu tafi da ita".
Inna ta ce "Shikenan, je ka dawo mu tafi". Musa ya juya ya fice, yayin da mara lafiyan ke ta cigaba da kakari.
Kamar yadda aka yi musu kwatance haka suka isa GY BULAMA HOSPITAL AND MATERNITY.
A gaggauce Musa ya shiga cikin Asibitin, ya fito da Wheel chair, suka ɗora Malam a kai, ya tura shi zuwa cikin Asibitin.
Gaba ɗaya Musa a rikice yake, bai tsaya saurarar kowa ba ya fara bulayin in da zai kai Malam ya kwantar.
Wata Nurse ce tayi masa