Showing 174001 words to 177000 words out of 231718 words

Chapter 59 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14703

kuma ta ce "Oh i almost frgt tafiyawta kama shi urgent he's alright left" "Mama me naiwa Abba ne haka? Idan zai tafiya duk sauri baya yi sai ya faɗa mini he has changed totally"

"No, kasan Abbanka bai iya fushi ba, yana cikin damuwa da abin da ka aikata wannan shi ne kawai" shiru yai ganin yadda ya sauya yasa ta tallafo haɓarsa ta ce "What again? Laifinka ne, amma kada ka damu kaci gaba da addu'a kana tura masa saƙon apologies ta E-mail nasa yana son ka dole zai sakko" kai ya jinjina ba tare da ya ce komai ba yana ƙoƙarin fita ta ce.
"Car key? Ina zaka bari na saka ai driving naka" idanunsa ya rufe a hankali ya ce "No Mama I can drive with myself ki mini addu'a" "To Allah ya tsare ya kai ka lafiya" da Amin Ya amsa tare da barin gidan.

A hankali yake driving sbd rashin ƙarfin jiki yana hanya Fayyad ya kira shi amma ya kasa picking call ɗin har ya Ƙarasa police station ɗin kai tsaye Ɓangaren I.G ya nufa. Mutane sai zubewa suke suna gaida shi tare da faɗin "Wlcm Back sir" Duk wanda yai masa ta'aziyya ko ta kansa baya bi, a haka ya ƙara wani office.

Cike da mamaki I.g ya miƙe tsaye yana sakin Murmushi na jin daɗin Sp Adnan Aliyu Matawalle zama sukai a hankali ya ce "Allahamdulillah, thank you sir" I.g ya ce "Good amma daka ƙara hutawa till now baka dawo daidai ba fa".

"No bad, am okay sir" shiru duk sukai can I.g ya ce "ina tun wani case na ɗan mafiya ɗin nan wanda ake zarginsa da sace yara yana cire wani sashi na jikinsu?" Adnan ya jinjina kai alamar ya gane domin da case ɗin a hannunsa "Ana zargin mutumin yana ƙauyen Samil babu da tabbaci sai mun bincika,kasan ƙauyen babu hawaye musamman yanzu lokacin siyasa kada a cutar dasu sosai".

"Yanzu waye za shi can ɗin?" Sp ya tambaya yana katse kiran da Fayyad ke sake yi masa. "Ina ci-gaba da bincikawa, Private investigator muke buƙata wanda zai komai cikin sirri ba tare da mutumin ya fahimta ba" shiru Sp yai can ya ce "Ok a bani case ɗin zani" I.g ya zare idanu yana faɗin "Rufa mini asiri, a ba aikin bane kai kake da ikon zaɓar wanda za shi ma, rashinka ya sa na tsaya a akan abun ba girman ka bane sam".

"Ina son barin ƙasar ne daman, sabida na samu peace of mind amma zan bar komai naje ƙauyen da kai ne a can na samu nutsuwar zuciyar ka amince kawai, ba ruwana da girman aikin da nayi" I.g ya daɗe yana jinjina al'amarin, ta ya ya Sp da kansa zai je bincike? Amma kuma zuwan Sp ɗin shi ne daidai domin ya san me yake. "shikenan All the best yaushe zaka tafin?"

Sp na Miƙewa tsaye ya ce "Gobe" Sallama sukai Sp Adnan Aliyu Matawalle ya koma gida yana zuwa ya samu Usman da Fayyad a can gidan suna zaman jiransa.

Abbi na zaune hannunsa riƙe da Aishatul-humaira yana mata wasa, ta kafesa da fararen idanunsa duk idan yai da fuskarsa tana biye da ita dai na wasan zata saka kuka tana harba ƙafa, yana ci-gaba kuma zata kafesa da idanu wani lokacin har dariya take masa. Kamar daga sama yaga Mami ta faɗo cikin ɗakin nasa tana huci kamar zakayya. Kallonta kawai yake ba tare da ya ce komai ba. "Ni zaka ci amana kayi mini kishiya ba tare dana sani ba Khamal? Ban cancanci haka daga gareka ba, me na aikata maka har haka da zafi?" Kwantar da Aishatul-humaira yai yana gyara zama ya ce "Ba kiyi mini komai ba Na'ima, kawai naji ina son ƙara auren ne saboda Ubangiji ya bani dama kuma ya hure mini arziƙin da zan haka daga ɗaya har zuwa huɗu" cikin raunin murya Mami ta ce "Me na yi maka to? Ka rasa wacce zaka aura sai wannan Shegiyar karuwar? Wallahi idan ina gidan nan babu Shegiyar data isa ta shigo gidan nan a matsayin kishiyata, zan nuna mata asalin haka wallahi akan son ka sai na illata yarinya"

Murmushi Abbi yai yana faɗin "Ashe? Ita karuwa ba mutum bace? And don Allah ki daina kiran matar da zan aura da karuwa kuma aure babu fashi duk abin da ki kai niyya Bisimillah ki aikata ban hanaki ba Na'ima, amma ki sani a wannan karan idanuna akan ki suke ba kamar baya ba, kuma baki isa kin yaudareni ba" zubewa tai a wajan tana sakin kuka ta ce "Wallahi Khamal ina son ka, ba zan iya jure ganinka da wata ƴa mace ba, kada ka hutani ta hanyar kishiya don Allah" "look Na'ima, idan hukuntaki zan yi da tuni nayi, aure ra'ayina ne ba sbd ke zan ba, don haka bana son wata fitina please" miƙewa tai idanunta cike da hawaye ta ce "Ok fine idan ba danni zakai ba, ai ka faɗa mini zakai aure na shirya? Ko yanzu ma ba kai ka faɗa mini ba a wajan ƴan uwanka na gani, zan bar maka gidan ka kawo Shegiyar karuwar taci gaba da zama a gidan" tana faɗin hakan ta saka hannu tare da ɗaukan Aishatul-humaira zata fita ya ce "Dawo ki Ajjiye mini Aishatul-humaira, Salima za taci gaba da kulawa da ita" cikin ɗaga murya ta ce "Wallahi babu tsinanniyyar da zan bawa Aishatul-humaira balle ta cutar mini da ita, kuma ni da Aishatul-humaira butu karaba" fuuuu tai waje tana zuwa ta ɗauki mayafi ta goya Aishatul-humaira tare da yin waje.

Abdullah dake zaune saman Kujera idanunsa akan Ummi ya ce "Bana son ganinki cikin damuwa Ummi" Murmushi Ummi tai ta ce "Gajiyar azumin da nake ne Abdullah, ba damuwa nai ba, burina daman an rufe Companyn kuma an rufe Alhaji ya ce mini yana hanya, munyi waya da Shuwa itama ta ce tana hanya" Murmushi mai kyau Abdullah yai cikin nutsuwa da kamalarsa ya ce "Shikenan Ummi, kici gaba da kulawa bana son komai ya sameki" hararar wasa tai masa ta ce "Uhm sannu Audu, bayan kai na lura kana cikin damuwa amma u can't sharing with me" shafa kai kawai yai cike da kunya ba tare da ya ce komai ba. Ummi ta miƙe tana ɗaukan plate ɗin Apple ta ce "Ina son a turawa gidan marayun nan kuɗin da suka buƙata na taimako kamar 2.3m ne ko?" Abdullahi ya ce "Sure Ummi za a tura kije ki kwanta ki huta yanzu don Allah" dungure masa kai tayi ta ce "Wallahi ka nemo matar aure kafin na fita na nemaka da kai na tuzurun kawai" kunnensa ya riƙe da hannu bibbiyu ya ce "Afuwa Ummi am still searching" dry tai tana faɗin "Keep searching har network ya samu, wallahi ka kiyayeni Abdullah" ta faɗi hakan tana shigewa part ɗin ta. Fararen idanunsa ya rufe yana sauke numfashi ina zai ganta? Mene ya sa bashi da Sa'a a duk sanda zai ganta ne? Babu inda bai duba iya inda yake tunanin zai ganta a Dubai amma babu ita. A fili ya ce "Me ya sa kika tsaya mini arai ne?"...



" 'Yar Baba mai sunan larabawa, kwanciyar ta isa haka, ki tashi ki je gangare ki karɓo mini gyaɗar nan"

Wadda aka kira da 'yar Baba ta tura baki, ta ce "Ni wallahi ba ni da lafiya ki aiki Yaya Musa"

"Ai na san baki da lafiyar, dan ki ji daɗin jikinki ne, kwanciyar ta isa haka" tana yamutsa fuska haka ta tashi daga kwanciyar, ta fita tsakar gida ta ɗebi ruwa a bokiti ta shiga wanka.

Maimakon da ta fito daga banɗakin ta saka kaya, kawai sai ta bemi wuri ta kwanta tana kuka.

"Wai ke meye haka ne? Wane irin sakarci ne haka?".

Ƙara sautin kukan ta yi tana faɗin "Wayyo Allah Babana, Allah ya jiƙanka Baba"

Matar ta ƙarasa gaban matashiyar yarinyar, ta shiga share mata hawayen fuskarta tana faɗin "Kiyi haƙuri 'yar Baba, muma duk zaman jiranta muke yi, kuma ba a yiwa mamaci kuka, ki daina addu'a zaki yi masa" da ƙyar ta rarrasheta ta yi shiru, ta saka kayanta, ta ɗauki wani ƙaton farantin silba, ta fice daga gidan.



Sannu a hankali yake tuƙin, yana ratsa 'yar siriyar hanyar da ke tsakanin gonaki, sam hanyar ba ta da kyau, duk uban kwazazzabai, ga ƙura, yana yi yana duba kwatancen wurin a wayarsa. Kamar yadda aka tsara idan yaje garin, zsi sauka a gidan maigari ne, amma hanya na neman ta ƙwace masa.


Tana tafe tana zancen zuci, da tunani daban daban a ranta, lokaci lokaci tana share hawaye da gefen ɗan ƙaramin mayafin da ta yafa a kafaɗarta, tayi tafiya mai nisa sosai sannan ta isa gidan da aka aiketa.

Wani matashi ne ya washe korayen haƙoransa da ya ganota " 'yar Baba kin fi zinare, sarauniyar kyawawan garin nan, farin wata sha kallo, ke ɗaya kin fi duk matan karkarar nan, daga ina haka?".

"Daga gidan ubanka" ta bashi amsa kai tsaye, tana watsa masa wani irin mugun kallo da idanuwanta da suka ƙanƙance suka yi jawur, saboda kuka.

Buɗe baki yayi ya ce "Ni kike zagi?"

"An zage ka ɗin, idan ka kuma shiga sabgata, ba zagi ba marinka zan yi, mutumin banza kawai".

"Zaki gane kuskuren ki, zaki san ni kika zaga, ai mai goya miki baya kina iskanci a garin nan, ya mutu ba zamu ƙara ɗaga miki ƙafa ba".

"In kun sake ɗaga mini ƙafa, Allah ya tsine muku" ta ƙarasa Maganar ta wuce shi ta shiga gidan da aka aiketa.

Da an saba idan aka aiketa gidan, ai ta hira ana wasa ana dariya, amma ganin yadda ta shigo ranta a haɗe, ba wanda ta gaisar daga sallama sai miƙa farantin gyaɗa, ya sa ba wanda ya kulata suka bata saƙon gyaɗarta ta fito.

Tafe take tana tunani, a kan abinda yafi komai ci mata tuwo a ƙwarya tsawon rayuwarta, ga rashin Babanta maganin kukanta.

Wani uban ihu ta saki, ta faɗi ƙasa farantin gyaɗar ya faɗi, gyaɗar ta zube a wurin, ta sa hannayenta biyu ta ɗora a kanta. Sam ba ta san ta hawo hanya haka ba, saboda tunanin da take yi.

Cikin tashin hankali Adnan ya fito daga motar, ganin babu abin da ya sameta amma ta ɗora hannun a kanta ta rintse ido, duk ta firgice ya sanya shi harzuƙa, ya kalli bayanta da ta juya, fari tas ga gashinta ta tufke amma ya fito ta ƙasan ɗankwalin ya kwanta a bayanta.

"Mahaukaciyar ina ce ke, zaki hawo kan hanya haka ina miki horn, amma ki ka yi banza? Wace irin mara hankali ce ke?".

"Kar ka sake ce mini mara hankali, kai ne mara hankalin ai, Yanzu da na mutu..... Kasa ƙarasa Maganar ta yi, ganin mutumin da yake tsae a kanta, sankacecen ingarman namiji, fuskarsa a ɗaure babu walwala, ko da idanunsu suka sarƙe a na juna, take ta ga ya sake ware idanuna a kanta.

"A..Ab....Abra..My Angel you are still alive, dama na gaya musu ba ki mutu ba, dama nan ki ka taho ki ka ɓuya?"

Zazzare ido ta shiga yi tana kallonsa, ita dai bata taɓa ganin sa ba, ko mai kama da shi a ƙauyen nan babu, ga kayan jikinsa masu kyau balle ta ce ko mahaukaci ne.

"Abrana ki yi magana mana, Angel ashe baki mutu ba" ya ƙarasa Maganar tare da miƙa hannunsa zai ɗagota!!!



Ki biya mu haƙƙinmu kan ki karanta, na kuɗi ne ₦300 kacal.

08081012143
[11/7, 6:36 PM] Abk: Ganin da tayi ya miƙo hannayensa gaba ɗaya zai ɗagota tsaye, ya sanya ta daddage ta ƙwala ihu "Wayyo Allah na shiga uku mahaukaci" tsayawa yayi sororo yana kallonta, ta tashi cikin hanzari ta suri farantin gyaɗar ba ta tsaya ta bia ta kan gyaɗar da ta watse ba, ta fyalla da gudu kamar ba zabgegiyar budurwa ba, binta Adnan ya yi yana kiran "Abra, dan Allah ki tsaya ki ji" sai dai kan kace Kobo, ta ɓace ɓat a cikin gonaki.
Dawowa yayi, wurin da gyaɗar ta ta watse a ƙasa, ta bar mayafinta a wurin, ya durƙusa ya ɗauka yana jujjuya mayafin, take hawaye ya cika idonsa "Angel, Allah ya sa ba gizo kike mini ba, ko dai haukacewa na yi ne ban sani ba? Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ya daɗe a wurin a tsaye, sanan ya shiga motarsa ya ja ya cigaba da tafiya, ji yake tamkar an zare masa lakar jikinsa, ya rasa duk wani kuzarin sa.
Ya samu ƙasan wata bishiyar tsamiya, yayi parking ya kifa kansa a kan sitiyarin motar, ya shiga duniyar ta sa ta tunani, da hasaso lokutan da suka shuɗe wanda ya kasance tare da Abra.
Haka ya ɓata lokaci a wurin, yana ƙara rirriƙe mayafin yarinyar nan mai gyaɗa, yana son tabattar a zahiri Abra ya gani, ko mai kama da ita ce kawai, ko kuma dai duk gizo ne?
Ganin ba shi da mai ba shi wannan amsar ne, ya sanya ya fito daga motar ya tambayi wasu samari, gidan maigari, suka kwatanta masa yayi musu godiya ya koma motarsa.
  Tunani ya dinga yi ya aka yi bai tsaya ko sunanta ya sani ba, to ta yaya ma zai san sunanta yarinyar da ko tsayawa ba ta yi ba ta kwasa da gudu.
"No my Angel can't run like this, sje might be her ghost, or am just hallucinating" ya yi maganar a fili yana taune leɓensa na ƙasa.

Gaba ɗaya Hajiya Na'ima ta rasa me yake mata daɗi, duk ta birkice ta fita hayyacinta jin batun kishiyar nan, gashi Abbi ya sa ana ta gyaran gida, zai ƙara Aure, kuma duk wannan haukan da take, ko kallo ba ta ishe shi ba, balle ya bi ta kanta, sabgar Aurensa ce kawai a gabansa sai jikarsa Aishatul Humaira.
  Na'ima na zaune a ɗakinta, tana rungume da Little Abra, sai dai gaba ɗaya hankalinta ba ya jikinta, she can't imagine sharing her husband with a prostitute.
Sallamar Abbi a ɗakin ce ta dawo da ita hayyacinta, ba ta amsa masa ba, kuma ba ta kalli in da yake ba.
Ya ƙaraso yana yiwa little murmushi, ya yin da ita kuma take ɗan murmusawa har dimples ɗinta suna lotsawa, haryanzu ba ta da wayo sosai, dan baka ba ta wani gane wasa, amma duk in da ta ga Abbi, tana yawan bin sa da idanunta, ko ma ta ɗan dinga yi masa murmushi.
Abin har mamaki yake bawa Na'ima, dan Aishatul Humaira ba ta yi wayon gane wasa ba, amma tana gane Major.
Ya miƙa hannu zai ɗau Little, amma Naima ta ƙanƙameta a jikinta tana watsa masa wani mugun kallo.
"Ya haka? Ki bani yarinyata in gani".

"Ba zan bayar ba, ka fita sabgata da ni da yarinyar nan, ka je ka yi rayuwarka mu yi ta mu".

"Hmm ikon Allah, madam kenan, har kin manta jikar karuwa ce Humaira?".

"Kar ka ƙara danganta mini 'ya da karuwa".

"Ohh sorry, ai ba ni na fara faɗa ba, ke ce ki ke faɗa, ko har kin manta Abra 'ya ta ce da karuwa ta haifa mini?"

Wata irin nadama da dana sani ne suka ziyarci Na'ima, ta tafka kuskuren da lokacin gyara ya ƙure mata.

"Kinga gara in kawo kakarta, ta kula mini da ita yadda yakamata, kar ƙiyayyar da ki ka nunawa uwatta ya shafeta ita ma".

"Ka ce mini ba zaka yi aure ne dan ka hukunta ni ba, amma wannan ƙananun maganganun da kake na menene?"

Bai amsa mata ba, sai murmushi da ya yi. Ya kuma miƙa hannu zai ɗau Little.
"Khamal ka ƙyaleni ka rabu da ni na gaya maka, idan duniya zata haɗu babu wanda ya isa ya rabani da jaririyar nan, kuma Wallahi ko ma wace tsinannaiyar zaka auro, babu ita ba Little, ka ƙyaleni ka rabu da ni".

Major ya ce "Allah ya baki haƙuri, zaki tsorata yarinyar ta ki, dama na zo ne in tambayeki, part ɗin ki kike so, ko wancan da ake gyarawa?"

"Ban sani ba, ida ka ga dama ka jani ka kai ni titi ka yar ka haɗa mini da saki, ka yi Aure ka sa a gidan".

"Hmm Na'ima mai rikicin gangan, ai duk wani abu da za ayi, muna tare forver, duk da ɓata mini rai da ki ke yi, kina da wata kima da daraja a idanuna, shiyasa na ke tambayar ki abin da ki ke so, amma tin da ba kya so, shikenan" ya ƙarasa maganar tare da miƙewa ya fice.

Yanzu da Abra tana nan, da wataƙila ita zata gayawa damuwar ta, ko ba komai ta tayata jin babu daɗi, amma Salman shi ba damuwa zai yi ba ko ta gaya masa, ga yadda suka ƙare da Anty Suwaiba, ta ƙanƙame Aisha ta fashe da kuka.




Da gudu ta shiga cikin gidan, tana ta uban haki kamar ta yi dambe da kura, Yaya Musa da yake jan ruwa a rijiya ya kalleta ya ce "ke meye haka? Gudun me ki ke yi ne?".

Da hanzari Inna ta fito daga wurin da suke girki, ta kalleta ta ce "meke faruwa haka? Ina gyaɗar?".

Jifa ta yi da farantin gyaɗar ta nemi wuri ta zauna tana ta haki.

Yaya Musa ya ce "Wai ma a haka ki ka fita aiken? Ina mayafinki?".

"Dan Allah ka bari in dawo hayyacina" ta yi maganar tana haki.

Sai da ta samu nutsuwa sannan ta fara ƙoƙarin tashi tsaye, Inna ta ce "Ina kuma zaki, ba ki mana bayanin mai ya faru ba? Ina aiken da na yi miki?".

"Wai Inna ke ta gyaɗar ki ma ki ke yi ba ta ratuwata ba ko? Wani mahaukaci ne fa ya buge ni da mota, kuma ya fara kirana da wani suna yana ƙoƙarin rungumeni".

Dafe ƙirji Inna ta yi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ban gane rungumeki ba, ya rungumekin ne ko kuwa?".

"A'a, kan ya rungumenin ne na ɗau farantuna na gudo gida".

"Ki gaya min gaskiya dan ubanki, mai ya yi miki?".

"Be fa yi mini komai ba, ban bari ya taɓa ni ba".

Yaya Musa ya ce "Wannan yarinyar wataƙila ma ƙarya take, wata maganar ta je ta ɗauko".

Murguɗawa Yaya Musa ba ki ta yi, ta nufi ɗakinsu.

"To ina gyaɗar? Ko baki karɓo ba?".

"Ni fa wannan gyaɗar ta watse a hanya, kuma ban tsaye tsintowa ba, dan ban san me zai mini ba idan na tsaya".

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, shikenan yau asara ta hauni, gyaɗar duk ki ka watsar mini, kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login