Showing 219001 words to 222000 words out of 231718 words

Chapter 74 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14821

da ingancin ma'aikatan. Aka ƙi bada belin Dr Bulama yana tsare labarin ya ɗaga hankalin Abra da Afra duk da laifin na Mahaifinsu ne amma ta wani ɓangaren suna tausaya masa ainun.

A week later.
Tana durƙushe gaban Abbi tare da sauraran abin da zai faɗa mata, zuciyarta sai bugawa take..
Abbi ya gyara zama ya ce "kamar yadda na baki umarnin sati guda ki fito da miji, na zuba miki ido amma shiru, to a yau bayan sakkowa masallaci na ɗaura miki aure da wanda zuciyata ta amince da shi, ga sadakin" ya faɗa yana miƙa mata damin kuɗi a lokacin nan idanun zuciyarta yarinyarta Aishatul-humaira da tsohuwun mijinta Sp Adnan Aliyu Matawalle kawai suke hango mata, har bata gane mai Abbi yake ce mata.
"Daughter?" Ya kira sunanta da ƙarfi ta saurin cewa "Na'am Abbi" ya kalleta da kyau ya ce.

"Kiyi mini alfarma a matsayin na wanda na isa a gareki, duk mijin da kika riska a matsayin shi ne mijin ki, ki amince da shi don Allah Abrana, kada ki watsa miki ƙasa a idanu, a wannan karan miji mai nagarta na zaɓa miki wanda ya dace da rayuwar da kike mafarki,
Kada kiyi baƙin ciki da duk wanda kika gani don Allah ki yarda dashi,ki bisa sau da ƙafa aljannar ki na ƙarƙashin shi, wanda kuma sai kin yi biyayya zaki same ta, maza tashi kije yana waje yana jiranki zaku shige ba zaki sake kwanar mini a gida ba"

Abra ta rushe da kukan da ita kanta bata san na menene ba, a karon farko hukuncin Abbi ya yi mata tsauri, ba damuwarta wanda ya zaɓa mata ba,
Kawai Aishatul-humaira take tunani.
"Insha Allah Abbi, nayi maka al'ƙawari"

"Allah ya yi miki Albarka" ta faɗa jikin Mami tana kuka kamar ranta zai fita. Salima murmushi kawai take wacce take ɗauke da jaririn cikin Abbi a jikinta.
Mami taiwa Abra nasiha sosai mai ratsa jiki. A tare suka rakata waje idan akace mijin nata yana nan.
Wani magidanci ta gani tsaye fari ba sosai ba, suka haɗa idanu haka kurum ƙunci ya kama zuciyarta a haka ta shiga mota suka ɗauki hanyar da ita kanta bata sani ba.
Bata kula shi ba, bai kulata ba har bacci ya ɗauke ta.
Sai dare suka shigo garin cikin wata hadaddiyar unguwa mai kyau da tsari, har cikin gidan ya yi parking ya fita, itama ta fito tana mamakin abin da yana mutumin magana ita ko sunan shi bata sani ba.
Ya kalleta ya ce "Madam shiga ciki, ina zuwa just 10 minutes" bata ce komai ba ta nufi hanyar shiga gidan tun a parlour ta san Mai gidan Ubangiji ya hure masa arziƙi ba a magana.
Ta zaɓi ɗaki guda ɗaya wanda ya haɗu sosai, ta jima zaune kafin tai sallah ta kwanta har barci ya ɗauke ta bata ji motsin Mai gidan ba.
Can cikin barci taji an rungome ta tsam a lallausan ƙirji wani ƙamshi na ratsa hancinta, ya sumbaci labbanta masu taushi a hankali ya ce "Wake up My Queen, heartbeat, my rigimammiyar matata" yaja hancinta yana ƙarasa zame rigar jikinta cike da soyayya, yai holding nata very tight. Abin da taji ya sanya Abra ta buɗe idanunta, da sauri ta ƙarasa buɗe idanun mamaki ya kasheta muryarta na rawa ta ce "Adnan.... You?' ya ɗora bakinsa akan nata ya yi kissing sosai yana kashe mata ido ya ce "Yes My Queen waye yace zan iya rabuwa dake?" Ya faɗa yana mirgina ta zuwa ƙasa.....




*🔥 IDAN BA KE 17🔥*


Marubuciyar

Tsintacciya (Published)
Kwaila ce
Moon
Uncle ne
Sirrin mu
Zain Abeed (Published)
Auren fansa
Abu maleek
Lamrat
Jidda
Juyayi
Raino ne sila
Sai na aureta
Izzar so
Dare da duhu
The new emir



Ban sani ba ko wannan zai samu daidaito a zuciyoyinku? Tafiyar ƙaddara ce wacce ban saba yinta zallah ba... A wannan karan nace me zai hana muyi labari zallah akan *SOYAYYA*

*SOYAYYA TSAKANIN MUTUM DA ALJANI???* Idan kun taɓa ji to labarin zai zo da salo na musamman.

*IDAN BA KE* zan kashe dubban rayukan jama'a,na kuma shirya kashe duk mai son raba tsakanin ruhina da naki.... Shi ne alwashin da *ALJANI PRINCE BILAL* ya yi.

Labarin *IDAN BA KE* Labari ne dana share shekara a zuciyata ina tsara yadda zan labaranta muku shi, Labarin Babban Malami ɗan kimanin shekaru 34 da haihuwa wato *YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU* da yarinyar da *ALJANI PRINCE BILAL* ya aura. Waye zai ci galaba? An bashi shekara guda domin kare rayuwarta tunda ya dai na yi mata kallon matar shi ta aure da sunan tai masa ƙanƙata kuma *MATSAYIN ƳA* take a wajansa. Kwatsam sai ciki ya bayyana, cikin waye? *YAA SHEIKH KO PRINCE BILAL???*

Yayin da ya gama lalacewa da soyayyar ta a zuciyar shi, a lokacin aka raba zuciyoyin su da ƙaddara mafi muni ta yadda sam bazu zatta ba. TAYAYA Suka fito daga *CIKI ƊAYA?*

gaba ɗaya wannan a cikin labarin IDAN BA KE. Wanda bai karanta ba ya nema ya karanta. Mun jima da gama free pages GOBE 29/11/22 zamu ɗora da posting ga wanda suka siya iya PAID GRP.

Hanzarta biya ta nan 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank. Ka tura shaidar biya ta nan 08119237616.... Salon na musamman ne🔥TEAM HALISA DANEJO ROME a shirya masoya ALJANI PRINCE BILAL A shirya. tawagar YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU a shirya🔥🔥🔥 yanzu zamu fara...


SARAUTAR MARUBUTA
[12/2, 2:49 PM] Abk: A gigice Abra ta ce "Adnan, you again? Wai me ya dawo da kai cikin rayuwata, a kan me zaka kuma dawo mini, ka shirya sake ƙarasa ni har lahira kenan?".

"No Angel, please understand me"

"Shut up Adnan, you have nothing to tell me, babu abin da zaka gaya mini, in dai halinka ne sai dai na gayawa wani".
"Wallahi Abra nayi nadama, dan Allah dan Annabi ki taimaka mini ki yafe mini"
"Kaga saurara mini, ɗan cikani malam"
Adnan ya sake marairaicewa ya ce "Abra please, dan girman Allah ki saurareni ki yi haƙuri".
"Adnan ka rabu dani nace maka, haryanzu ina kan bakana bana sonka bana ƙaunarka, kuma har in koma ga Allah ba zan manta cin zarafin da kayi mini a rayuwar aurenmu ba, dan haka ka ƙyaleni" a zuciye tayi Maganar, wanda hakan ya tilasatawa Adnan cikata, bata saurari komai ba ta diro daga kan gadon, ta nufi hanyar barin ɗakin. Bashi da zaɓi illa ya bi bayan Abra yana faɗin "Dan Allah ki tsaya ki saurareni" tsaki tayi ta koma falo, ta hau kan doguwar kujera ta kwanta.
"Shikenan, ba zan kwana a ɗakinki ba, zan kwana a ɗaya bedroom ɗin, ki koma ɗakinki ki kwanta Please".
"Malam dan Allah ka rabu dani Adnan, meye haka ne wai, Wallahi ka matasa mini barin gidan zan yi a daren nan, ba sai zuwa wani lokaci ba"
"Yi haƙuri na ƙyaleki, amma dan Allah kar ki kwana a kan kujerar nan wuyanki zai yi ciwo" ko kallonsa ba tayi ba ta gyara kwanciyarta, ta rufe idanunta, sai da ya bar falon sannan ta tashi ta koma ɗakinta, ta kulle ƙofar ta saka key.

Adnan kuwa kasa bacci yayi gaba ɗaya, juyi kawai yake a kan gadon nan, zuciyarsa na masa wani nauyi, yana tuna irin abubuwan da ya aikatawa Abra, duk da a lokacin yana sonta, da yadda yake fama da ita yanzu, taƙi ta tsaya ta saurare shi, balle ta bashi damar da zai gwada mata irin son da yake mata.
"Koma me kika zama laifina ne Angel, ni ne silar sauyawar halayenki, amma ki yafe mini, na shirya baki dukkanin farinciki Abra Khamal Khamis" ya faɗs yana ƙanƙame pillow a ƙirjinsa, yana jin wata irin kewarta na ƙara ratsa zuciyarsa, ya tuna yadda ya dinga zuwar mata kamar ba matarsa ba, ba shi da tabbacin a zaman da suka yi Abra ta san menene ma daɗin auren, saboda buƙtarsa kawai a gabansa.
"Am sorry Angel, ki yafe mini mana, Allah yana son bayinsa masu afuwa da yafiya".
Abra kam zullumi ta shiga da tunanin kar da wani sabon salon yaudarar Adnan ya kuma zuwar mata, amma yanayinsa ya nuna tabbas yayi nadama, kuma ta san su Abbi ba zasu zaɓa mata abinda zai cutar da ita ba, sai dai duk ƙoƙarin da za tayi wurin manta abinda Adnan ya aikata mata ta kasa, saboda girman tarin laifukansa a gareta, da haka wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita.

Duk wata kulawa da ta dace mace ta samu a wurin miji, Salman ya dage yana nunawa Afra yadda ya dace, gaba ɗaya Salman ya mantar da ita tarin damuwa da ƙuncin rayuwa da ya samu kansa a baya, Yanzu haka shirye shirye sun yi nisa, zai koma china dan ɗora karatunsa daga in da ya tsaya, kuma tare da Afra zai koma, domin ita ma ta cigaba da nata karatun a can.
Washegari da safe, Adnan ya tashi ya gyara komai, ya dafa tea da kansa ya sayo bredi, already akwai kayan tea dan duk wani kayan Abinci ya saya ya ajiye. A falo ya koma ya zauna, yana jiran Abra ta fito, dan yana tsoron kar yaje tasota ta kuma yi masa wulaƙanci.
Sai wurin ƙarfe goma ta fito, ta fito cikin wata doguwar riga mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, rigar tabi jikinta ta kwanta luf.
Kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kanta, shi kuwa gogan murmushi ya yi ya ce "Good morning my Angel".
"Ina ne kitchen, zan samawa kaina abin da zan ci ina jin yunwa".
"Ai na haɗa breakfast, gasu can a kan dining na ajiye komai, ga kazar kuma ki a fridge idan ita ki ke so, sai in warming ɗin ta ki ci". Ba ta bashi amsa ba ta wuce dining, ta zauna ta fara haɗa tea.

Dining ɗin ya bi Abra ya zauna, yana satar kallonta da yadda ta ƙara kyau da ƙiba, wata irin kewarta na kuma ratsa shi, wannan dogon gashin da ya zube lokacin da tayi rashin lafiya, duk ya dawo. Yayi mata do tun daga gaban goshinta gashin yake, baƙi ƙirin ya kwanta a bayanta.
Tana ankare da yadda ya zuba mata ido kamar bai taɓa ganin mace ba, ta fara karyawa tana kaɗa ƙafarta, kamar ba san da wanzuwar sa a wurin ba.
Shima karyawar yake yi, amma hankalinsa gaba ɗaya yana kanta, can ba tare da yayi tsammani ba yaji ta ce "Ammm nace ba, ina ka kai mini 'ya ta ne? Ina buƙatar ka bani abata".
" 'yarki tana nan lafiya"
"Ba lafiyarta na tambaya ba, ina ka kai mini ita, ina buƙatar a dawo mini da ita".
"Tana wurin... Bai ƙarasa ba, suka ji ana kaɗa ƙararrawar falo. Adnan ne ya miƙe ya tafi ya buɗe.
Direban gidansu ne, ya kawo Abinci daga gida, wanda Hajiya Mama ta aiko musu da shi.
Adnan ya karɓa ya maida ƙofar ya rufe ya dawo dining.
"Angel kinga Mama ta aiko da Abinci, bari in ajiye a kitchen maci da rana ko?" Ba ta ko ɗaga kai ta kalleshi ba,balle ya sa ran zata amsa masa. Ya tafi kai fulasan kitchen kar ya dawo ta bar falon.
Akwatunan dake ɗakinsa ya kwaso, ya kai ɗakin Abra, Akwatuna duga shida ya zube a gaban Abra, da murnarsa ya ce "Angel, ga kaya na saya muku ke da little, gashi nan naki akwatuna huɗu nata kuma biyu, dama sauran kayan lefenki na wancan gidan ma suna gidanmu, suma zan ɗauko miki su".
Abra ta kalli Akwatunan ta ce "Madalla, little ta gode, ni kuma ka bar kayanka, babana na riƙo bai bar ni tsirara ba"

"Abra Wannan ai wani abu ne na daban, wannan hakkina ne nayi muku".

"Ka yiwa 'yar ka dai, ai ni ban cancanci ka mini ba, ni da nake jinin Bulama, ai bai kamata ka mini abin da zaka kyautata mini ba, tunda auren na fansa ne" Dafe kansa Adnan ya yi ya ce "Abra why, na gaya miki nayi nadama, mai yasa kika canza hali ne?".

"Koma menene ai kai ka koya mini ba wani ba, a waccan rayuwar ka sanar mini zaman bauta zan yi, ka ɗau fansa, ban sani ba ko a wannan karon ma fuska biyu kake mini kamar yadda ka saba".

Sunkuyar da kai ya yi, a hankali ya matsa kusa da ita, yana kallon yadda doguwar rigarta ta ɗage santala santalan ƙafafuwanta suka bayyana, ya dubeta tare da ɗora hannunsa a kan cinyarta, ya ce "Believe me please, ba zan sake cutar da ke ba Abra"
Kallonsa tayi ido cikin ido, yadda suka samu kusanci da juna, har tana iya jin saukar numfashin sa a jikinta, ta kalli faffaɗan ƙirjinsa da take missing, ta cigaba da kallonsa zuwa kan lips ɗinsa, da idanunsa da suka yi jawur cike da nadama, ji tayi wani abu na taso mata, tsohuwar soyayyar Adnan na ƙoƙarin taso mata. Dakewa tayi a lokacin da wani sashi na zuciyarta ya gargaɗeta 'Me kike shirin yi ne Abra, kamar baki da zuciya?'.
Haɗe rai tayi ta ce "Ka zo ne dan kayi abin da ka saba, ka biya buƙatar ka sannan ka koreni a wulaƙance, kar warin abin da na fitar ya hautsina maka ciki? Ko kuma fyaɗen kake ƙoƙarin sake yi mini, kamar yadda kayi mini a ranata ta farko da kasancewa da ɗa namiji?"
Wata irin ajiyar zuciya Adnan ya sauke, ya dubi Abra yana tuna abubuwan da suka shuɗe, da wasu ya manta ma da ya aikata hakan.
"Ba zan gaza da cigaba da baki haƙuri ba Abra, na san ni mai laifi ne a wurinki, dan Allah ina mai kuma sake baki haƙuri".
"Can You excuse me please?" Abra ta faɗa in a serious tone, tana sake nuna masa bata buƙatarsa a in da take. Jiki babu ƙwari haka Adnan ya tashi ya bar mata ɗakin.
Kwanaki biyu da tarewar Abra, Hajiya Mama da Abba suka zo gidan da daddare, tare da little kasancewar dama tana wurin Hajiya Mama.
Abra tayi murna da zuwansu, tayi musu kyakywar karɓa cike da farinciki. Gefe guda ga murnar ganin 'yarta da tayi.
Abba ya yi musu nasiha me shiga jiki, da mahimmancin yafiya da haƙuri a zamantakewar aure, da kuma sake kashedi da jan kunne ga Adnan, a kan mahimmanci amana da riƙon iyali da adalci. Abra nasihar Abba ta ratsata, amma ba ta iya ji a ranta ta yafewa Adnan muzgunawar da yayi mata ba.
Da zasu tafi ta so Mama ta bar mata little, amma Mama ta ce ba yanzu ba, sai an kwan biyu tukuna.



Labari ya ishe sauran 'yan uwan Bulama, a kan iftila'in da ya afka masa, amma babu mutum guda da ya iya jajanta halin da yake ciki, ciki kuwa har da 'yan uwan mahaifinsa, saboda yadda ya watsar da su, tun bayan aurensa da Saudat, da yadda ya daina zuwa inda suke, shi kuma babu wanda ya san in da yake zaune a cikinsu, dan haka babu wanda yabi ta kan a tallafa masa saboda yanayin da yake ciki.
Hajiya Saudat kuwa Nijar ta gudi can wurin wata ƙawarta ita da Meenal, sai dai tun bayan aikin da aka yiwa Meenal, aka cire mata mahaifa, ba ta samu lafiya ba, take ta rashin lafiya, duk ta ƙare ta rame, saboda kullum cikin ciwon ciki da zubar jini take. 'yan sanda kuma tuni suka baza komarsu dan ganin an daƙumo Hajiya Saudat bisa ga laifin da ta aikata.


Adnan yana ji yana gani, yana zaune gida ɗaya da Abra, amma tafi ƙarfinsa, saboda a wannan karon zama ne yake son su yi shi na soyayya wanda zai mantar da ita waccan rayuwar da suka yi, sam baya son takura mata gaba ɗaya.
Abra ko aikin gida sai ta ga dama take yi, Adnan ne yake komai, sai dai tana yin girki ta ajiye masa, saboda ko a lokacin da suka yi wancan zaman bai barta da yunwa ba. Shiga sai wadda ta ga dama take yi, wani lokacin haka zai kalleta ya haƙura ya bar mata falon ya koma sashinsa. Maganar arziƙi bata haɗasu saboda yana gudun samun matsala.


Gefe guda kuwa Abra damuwa ta fara yi mata yawa a kan halin da mahaifinsu ke ciki, gaba ɗaya media ta ɗauka kasancewar sa shahararren likita ne, har ga Allah duk da tarin laifukan da Mahaifin nasu ya aikata, tana jinsa a ranta, kuma ta fara tunanin tunda tana garin Kaduna, akwai buƙatar ta je ta ganshi, dan tuni an fara gabatar da shari'arsa, sai dai ana nema ayi defeating ɗin lawyoyinsa, saboda ƙwararrun lawyoyi ne suke tsagin gwamnati, kuma a yanzu babu kuɗin da Bulaman zai iya ɗaukar wanda zasu tsaya masa.

Kwanci tashi asarar rai, a daren yau Abra taci karo da message ɗin Salman, yake sanar mata da cewa ta tambayi izinin Adnan, zasu je Dubai tare da ita suje wurin Ummi, ita ta dawo gida, su kuma su wuce China shi a Afra.
Farincikin da Abra ta shiga ba zai misalitu ba, dan haƙiƙa ɗan zaman da suka yi da mahaifiyarsu bai ishe su ba, duk da ba wani sabo da shaƙuwa a tsakanin su.
Shirinta ta fara yi, ba tare da ta sanar da Adnan batun tafiyarsu ba, sai dai ta lura kamar ba shi da lafiya, rashin lafiyarsa ya ɗan tayar masa, amma bai gayamata ba, ita ma kuma ba ta nemi ta sani ba, ta shirya kayanta tsaf tana jiran zuwan su Faris.

Sam Adnan bai san da zuwan da su Salman ba, dan bata gaya masa ba sai ganinsu kawai ya yi a gidan, Abra ta rasa in da zata saka kanta dan murna, Afra ta ƙara ƙiba Salman ma haka, kana kallonsu ka san farinciki da kwanciyar hankali sun sami kyakykyawan matsuguni a tare da su.
Adnan ya dake ya daure, ya ɗan sake suka gaisa da Salman. Gefe guda kuma yai ta tsokanar Afra 'Su 'yar fara an auri fari, ni kuma Allah ya dawo mini da matata wurin ɗan baƙinta" Afra ta tura baki tana murmushi.
Ɗaki Abra ta janye 'yar uwatta, suka ƙule suna hira, Afra ta ce "Sister, wai haryanzu jikin baban little bai warke bane, naga sai kuma rama yake yi?".

"Oho masa" Abra ta faɗa cikin ko in kula.

"Ba dai kina nufin haryanzu ba kwa jituwa ba?".

"Kinga mu bar wannan maganar, me zamu dafa ne?".

"A'a magama ce me mahimmanci da Yakamata mu tattauna ta"
Abra ta miƙe ta ce "Sai kuma kiyi ai" ta fice ta bar ɗakin, ko da ta dawo falo da Salman da Adnan duk basa nan, dan haka ta mayar da hankali wurin ƙoƙarin ɗora girki. Hankalinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login