Showing 153001 words to 156000 words out of 231718 words
Chapter 52 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
zaki ban bane?" Idanunta ta buɗe tare da kallonsa cikin sanyin murya ta ce "Kaji nai mgn Bisimillah, ba zan taɓa hanaka ba" tana faɗin hakan ta ja bakinta tai shiru. Zama ya yi akan gadon yana kallonta sai bai lura da yadda jikinta ke rawar sanyi ba, a haka yaje gareta tare da sauke buƙatarsa da maitarsa. Nan kwance ya barta tana sauke numfashi, baƙin cikin yadda take sake masa jiki sai dai yai komai da kansa shi ke cika masa zuciya a kullum. Yana fita Abra ta ƙanƙame jikinta da shiga addu'ar neman sauƙi wajan Ubangiji. A fili kuma ta fara addu'ar yaye damuwa da ƙunci.
*”لا إلهَ إلَّا أنتَ سبحانَك إنِّي كنتُ من الظالمينَ”*
Daga wannan addu'ar ta koma wannan.
*{اللهُمَّ رحمتَكَ أرجُو ، فلَا تكلْنِي إلى نفسِي طرْفَةَ عيْنٍ ، و أصلِحْ لِي شأنِي كلَّهُ ، لا إلهَ إلَّا أنتَ}*
Haka ta dinga yi da ƙarfin da rage mata har barci ya ɗauke ta bakinta na motsawa.
A hankali Meenal ke fitowa daga cikin part ɗinta zuwa Main Parlour, ganin babu kuwa yasa da sauri ta bar parlourn tai waje, jikinta na rawa ta shiga motarta gatekeeper ya buɗe mata gate tabar gidan cikin 160, na giyyar motarta. Sai da tayi nisa taja tsaki ta ce. "Haba aita takura mutum ana saka masa Idanu, duniyar nan kowa abinda yaga dama yake, amma an tirkeni kamar wata saniyyar ɗaure, daga nan sai club wallahi" number Abdul ta kira ta ce "Hy sweetheart, jiya na kwana da mafarkin madararka" shiru tai tana dry ta ce "Haba never nai maka sambatu sai dai kai, now tell me kana ina?" Jim tai ta ce "Oops hotel ɗin ranar nan? Kai kam kamar mara gsky, shikenan bani 10mnts I'll be there" kashe wayar tayi babu jimawa ta Ƙarasa kai tsaye room ɗin daya kama ta shiga. Knocking ƙofar ta fara, da sauri Abdul ya miƙe yana kallon Zee baby dake kwance a kan gadon ya ce "Hehhhh beb Meenal ta ƙaraso tashi ki ɓoye" taɓe baki tayi ta ce "Wai kai ina ruwana da wata Meenal" "No Beb, kin san bana son abin da zai dameki ke nake so kuma ke zan aura waccar ƴar wahala ce" miƙewa kawai tayi ta nufi toilet. Sai a lokacin ya buɗewa Meenal tana zuwa ta rungomesa ta ce "Me kake yi ne?" Kissing bakinta yai ya ce "Ina shirin yadda zan tarbeki mana, u knw you're special" suna tsaka da yin abin da suka saba. Zee baby ta fito tare da yi musu vedio tana sakin Murmushi duk irin ihu da sumbatun da suke yana cikin Vedion.
Bayan faruwar komai ta ce "Abdul ina da ciki yaya zan?" Murmushi yai ya ce "Abin da aka saba mana" shiru tai ta ce "Na gaji da zub da ciki fa, ya kamata a nemi mafita" "ok kima Usman mgn ya fito ai auren, kin san daman matan aure sunfi daɗin harka tunda kince ba zaki auren ba" daga nan hospital suka nufa aka cire cikin.
Abra na zaune a Parlour kamar daga sama taji ana faɗin "Huhuhu azaba ita daman kadunan haka take bani da labari? Wallahi kamar dai tafi Saudia nisa, wannan azababbiyar tafiya kamar za'a sai da mutum" Granny ta faɗa tana turo ƙofar. Murmushi kawai Adnan ya yi, Ammi ta ce "haka fa" a haka suka ƙarasa shiga Parlour, wayyooo Allah daɗi duk irin ciwon da Abra take ji haka ta miƙe jiki na rawa kai tsaye wajan Mami ta nufa tana zuwa ta faɗa jikinta tana sakin wani irin kuka kamar ranta zai fita.
"Oh! Wannan kukan har yanzu yana nan ni Na'ima yaushe zaki girma" kuka kawai Abra take har da shassheƙa. "Ji Algunguma bafa kukan take ba sai yanzu data ganmu to kukan na menene ma ai babu kyau" Adnan dake tsaye ya ce "haka take Granny, kullum wai akaita wajanku shi ne nace bari ta haihu to" zare ido Granny tai ta ce "Ciki ne da ita? Oh na shiga uku abin babu wahala to wata nawa kuma?" Shafa kai Adnan ya yi ba tare da yace komai ba.
Farin cikin da Abra tai ba zai misaltu ba, ta rasa inda zata saka kanta, Adnan komai Angel har kunya yake bawa su Ammi, Abra ko inda yake bata kallo. Sai da ya kirata tare da Kaɗa mata warning na zamantakewarsu. Da zasu tafi kuka tayi kamar ranta zai fita, a haka suka rakasu zuwa airport dake jirgi zasu shiga.
Washegari ya kama Monday tana zaune a ɗaki Adnan ya shigo kallo ɗaya ya yi mata ya ce "12 jirginmu zai tashi zuwa Dubai sai ki shirya" da sauri ta kallesa ta ce "Dubai? Akan mene ko sbd ka samu damar wulaƙantani?" Kafaɗa ya ɗaga ya ce "Duk yadda kika ce, amma bana mgn biyu ki tabbatar kin shirya" yana faɗin hakan yai waje. Babu yadda ta iya bisa dole ta shirya kamar yadda ya ce 12:3 jirginsu ya tashi zuwa Dubai.
*DUBAI*
Dubai, da Larabci دبي, birni ne dake a masarautar Dubai, A ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Shi ne babban birnin masarautar Dubai, kuma da babban birnin tattalin arziƙin Hadaddiyar Daular Larabawa. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2018, akwai jimillar mutane 3,137,463.An gina birnin Dubai a ƙarni na sha takwas bayan haihuwar annabi Isah.
Kai tsaye wata unguwa mai suna Madinat Jumeirah. Motarsu ta nufa, cikin wani haɗaɗɗan gida mai kyau da tsari wanda ya kasance mallakin Aliyu Matawalle. Gaba ɗaya a gajiye suke musamman Abra wacce bata saba tafiya haka ba, ɗaki ya nuna mata ta kwanta shima ya nufi wani ɗakin. Bayan sallar issha tana tsaye a gaban mirror ta gama shiryawa cikin wata abaya mai kyau, Adnan da tun ɗazo yake tsaye yana kallon ta ya ce "Bani da time Malama" bayansa tabi har zuwa mota, shine da kansa yake driving dare ne amma sai ka rantse rana ce haske kamar zai illata ido sbd yawan da yayi. Wani mall suka shiga yace ta ɗauki abin da take so, yana faɗin hakan ya shige ciki. Juyawa Abra tayi a hankali ta rasa me zata ɗauka sai kawai ta nufi wani waje ta da nufin zama, kamar daga sama taga mutum a tsaye a gabanta, da sauri tai baya tana girgiza kanta mutumin data gani yasa hankalinta ta shi. Abdullah ya gyara tsaiwa tare da faɗin "You? Nasan dole zan sake ganinki" jiki na rawa ta juya zata bar wajan ya yi saurin kama hannunta yana faɗin "No please, may i have your number?" Shiru tai masa ya sunkuyar da kansa yana zaro Wayarsa tare da faɗin "Jikina yana bani daman zan sake ganinki please samin number ki" wayam babu Abra babu mai kama da ita, neman duniya babu ita a haka ya koma gida rai ɓace.
Yanayin Yadda ya shiga ya sanya ƙyakkyawar matar dake zaune saman Kujera hannunta riƙe da littafi tana dubawa ɗago kanta cikin kulawa ta ce "Lafiya dai Abdullah?" Girgiza kai yai ya ce "Ummi kai na ke ciwo" da ido ta kallesa haka nan taji bata yarda ba, a nutse ta ce "Ciwon kai?" "E, Ummi maybe gajiya ne" numfashi ta sauke ta ce "Allah ya sawwaƙe, kasha magani ina son muyi magana akan Sabon Companyn da aka buɗe last year,bana gane kan komai na Companyn Abdullah na zuba biliyoyin kuɗi amma yanzu duk babu su, hankalina ya fara tashi" Abdullah ya ce "Waye manager na Companyn ma Ummi?" Girgiza kai tayi tana ɗaukan Jarida ta ce "Jeka huta, we'll talk later" "Ok Ummi" part ɗinsa ya shige Ummi ta bisa da kallo.
Cike da tsoro Abra ta kwanta amma tana Mmkin gani na biyu da idanunta suka sake yiwa Abdullah waye shi? Mene yasa yake bibiyarta har haka? Da wannan tunani bacci ya ɗauke ta, cikin dare ta farka da matsanancin zazzaɓi hannunta ta miƙe da nufin riƙe kanta amma sai taji gashin kanta yana marmasuwa, da sauri ta saka hannunta duk biyu ai kam nan gaba ɗaya gashin ya shiga cirewa gefe guda na kanta tamkar wacce akai wa aski.....
Littafin kuɗi ne, mai buƙata ya yi magana ta wannan number 09047871750
[10/27, 3:04 PM] Abk: Gabanta ne yayi mummunar faɗuwa, wane irin abu ne haka gashin kanta zai dinga zuba? Shiru ta yi tana tunani, a iya saninta bata taɓa abu makamancin haka ba. 'may be sauyin weather ne' wata zuciyar ta bata amsa, haka ta yi shiru tana Adduointa, har bacci ɓarawo ya saceta.
Bayan sallar Asubahi ma, gado ta koma ta cigaba da bacci, tana cikin baccin taji an ɗagota daga kwanciyar da take gaba ɗaya.
Buɗe ido ta yi tana tura baki, ta kalli fuskar Adnan ta ce "Meye haka? Bacci fa nake yi".
"Ai na san baccin ki ke yi, ke baki san Yakamata ba ko? Kina da juna biyu amma har wannan lokacin kina bacci, ba zaki tashi ki nemi abin da zaki ci ba, baki san sai kin ci shima abin da ke cikin ki zai ci ba?".
"Au haba? Ya daɗe bai ci ba, ba zan ci Abincin ba, sai dai wahala ta kashe shi na huta nima".
"Aikuwa sai dai ku mutu tare, da in rasa abun cikinki gara ke in rasa ki, dama can ba ta taki nake ba, ki yi ƙoƙari mu rabu lafiya, ki haife mini yarona salin alin".
"Mu rabu ka ce?" Tayi maganar tana kallon fuskarsa.
"Eh mu rabu, ko da yake fa ashe ba zaki iya rayuwa babu ni ba ko?".
Abra tayi wani murmushi mai ciwo ta ce "Ai ko kashin awaki muka zo duniya da kai, na tsaneka ko sunan ka bana ƙaunar ji, idan har zamu rabu ka yiwa Allah da ma'aikinsa mu rabu yanzu kan mu koma Nigeria, daga nan in wuce gidan ubana".
"Gidan riƙo dai, a zatonki zan rabu da ke ne ki tafi da cikina gidan riƙo ya zama ɗan riƙo kamar yadda kika zama, no iya wuya banga wanda ya isa rabani da ke da cikin nan a jikinki ba".
Abra ta ce"Wanda yayi ni yaui cikin fa?" Kallonta yayi amma bai ce komai ba, ya basar ya ce "Malama ki tashi kije ki karya".
"Idan ka damu ɗanka ya ci Abinci, zaka iya zuwa ka haɗo Abincin ka kawo mini nan in ci, idan kuma ba ka matsu ba, kana iya ƙyaleni in cigaba da abin da yake gabana"
Tana rufe baki ya wani irin fizgota daga kan gadon, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Abra ji tayi tamkar an haɗa ilahirin ƙasusuwan jikinta ana ƙoƙarin kakkaryawa saboda azabar ciwon da ya ratsata tun daga kwanyarta zuwa yatsun ƙafarta.
"Na shiga uku Adnan, kasheni zaka yi ne? Ka san yadda nake jin jikina kuwa?".
"Ban damu da duk abin da kike ji ba, wannan ke ta shafa ba ni ba, burina ɗana ya rayu, ki lafiya ko kar kiyi matsalar ki ce, akan ina Magana kina mini gaddama, mussaman a kan abin da ya shafi cikin nan, sai na ɓata miki rai" yana gama maganar ya shiga janta, wanda jan nan da yake mata ji take tamkar yana ƙoƙarin rabata da ƙasusuwan hannunta.
"Adnan Allah yana kallonka fa" ta faɗa cikin tsananin rauni.
"Kar ki sake gatsa mini sunana haka kamar ke kika raɗa mini, mara tarbiyya shi ma uban riƙon naki baki samu tarbiyya a hannunsa ba kenan, da har kike iya kallon tsabar idona ki kirani da sunana".
Ja tayi ta tsaya tare da riƙe ƙofa ta ce "Zan iya haƙuri idan ka zagi mahaifina, saboda ban san shi ba ban san mai ya haɗaku ba, amma ba zan juri ka zagi Abbina ba duk wani rashin mutunci da zaka yi mini ya ƙare a kaina ban da Abbi, kuma da ka auroni ai ina ɓoye sunan naka, amma na ga lamarinka babu mutunci dan haka na faɗa ADNAN ALIYU MATAWALLE, aka faɗi sunan Annabi ma balle sunan Azzalimin mutum irinka" rigarta ya sa ya shaƙo wuyanta yana huci, idanun Abra suka yo waje tana wani irin kakari, ya ƙarasa janyota cikin falon, ya jefata kan kujera. Ya ɗauko Abinci ya dinga ɗura mata tana kuka tana kakarin amai, amma babu tausayi ko imani a zuciyar Adnan.
Zaune take a kan wasu irin katafaren kujeru, tana zaune hannunta riƙe da waya, tana jujjuya wayar fuskarta ɗauke da damuwa, a hankali ta fara daddanna wayar, sannan ta kara a kunnenta, sai da wayar ta kusa katsewa sannan aka ɗauka, sallama tayi tare da yin ajiyar zuciya.
Daga can ɓangaren cikin wayar aka amsa mata.
"Kana ina ne Yanzu?".
"Ina nan lafiya, akwai damuwa ne?".
"Ina son in ji Yaushe zaka zo ne, saboda akwai damuwa, ina son mu tattauna wata magana da kai"
"Wace irin damuwa ce haka wadda har kike son in zo?".
Ta sake sauke ajiyar zuciya, fuskarta na bayyanar da tsantsar damuwa ta ce "Nifa gaba ɗaya na kasa gane kan kasuwancin nan, shekara da shekaru abu yaƙi gaba yaƙi baya, akwai buƙatar mu dakatar da deal ɗin nan, zan tsayar da duk wasu harkokina na nan ƙasar, in sako jami'an tsaro da manyan accontants a gudanar da bincike, a gano a ina matsalar take"
Daga cikin wayar mutumin ya ce "Haba Khair, kamar ba musulma ba, baki yadda da ƙaddara ba? Ki bi komai a hankali mana, idan kika dakatar da harkar kasuwanci shikenan a daina juya kuɗaɗen su lalace a haka? Bai kamata a dakatar da kasuwanci ba, a cigaba da harkokin idan ya so sai ayi binciken zuwa ƙarshen shekara idan Allah ya kaimu".
"Na gaji ne, na gaji da irin yadda abubuwa suke gidana a harkokina, akwai wani abu wanda ban sani ba, da nake buƙatar gano shi a nan kusa".
"Kiyi haƙuri ki bi komai a hankali, ki kwantar da hankalinki komai zai tafi daidai insha Allah"
"Shikenan, amma yakamata ko mai kake yi ka zo, ka san ka daɗe dai baka zo ba"
"Haka ne, zan zo insha Allah"
"Ok sai an jima" ta ajiye wayar jiki a sanyaye tana tunani.
Sallamar Abdallah ce ta katseta daga dogon tunanin da take yi.
Ta amsa masa ya ƙaraso ya zauna, a ɗaya daga cikin kujerun falon. Ya dubeta ya ce "Lafiya kuwa Ummi?"
Ummi ta ɗan girgiza kai ta ce "Abdullah, Ina cikin damuwa a kan harkar kasuwanci na, gaba ɗaya na kasa gane kan harkar nan, nayi waya da shi, ya ce mini yana nan zuwa, amma abin yana damuna".
Abdallah ya ce "Kiyi haƙuri tin da yace zai zo da kansa, ki ɗan ƙara haƙuri".
"Shikenan, bari ya zo ɗin in ji shawaa da zai yanke, amma zan gaya masa dole a bincika yadda al'amuran nan suke gudana".
Abdallah ya ce "Hakane, Allah ya yi mana jagora".
Ta amsa da "Ameen"
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, kusan satin su Abra biyu a Dubai, al'amarin Adnan babu sassauci, dan ko zata ci Abinci tana amai sai ta ci, ko tana so ko ba ta so. Kuma bai fasa zuwar mata da buƙatarsa ta Aure ba, duk da yadda yanayin jikinta yake.
Abra ita kaɗai ta san irin wahalar da take sha a kan cikin nan, yana tsufa tana cigaba da shan baƙar wahala, wani irin zazzaɓi take wanda ba ta taɓa tunanin akwai irinsa ba, taji kamar ana sassara ƙasusuwanta, ga wani irin azabar raɗaɗi da take ji a ƙasan fatarta abin ba ya misaltuwa.
Ta ƙara wata uwar rama ga duhu tayi sosai, ga gashi yana ta zubewa ta rasa abin da yake mata daɗi, gaba ɗaya ta sake zama wata so silent.
Satinsu biyu, suka baro Dubai sai dai babban abin da ya yiwa Abra daɗi da bata taɓa zato ba shi ne yadda suka sauka a Kano, wanda rabonta da Kano tun da aka ɗaura mata Aure aka kaita gidan Adnan.
Taji daɗin ganin Mami, sai dai Mamin ta tsorata da ganin yadda Abra ta koma, amma sai tayi zaton kawai laulayi ne ya mayar da ita haka, ga cikin ya fito Sosai kai kace da ta durƙusa za ta haife shi.
Bayan Adnan ya kaita gida, a Hotel shi yaje ya sauka, ita kuma ya barta a nan gidan.
Ganin gidan ta din ga yi duk ya sauya mata, ta dinga tuna irin rayuwar da tayi a gidan, duk da irin cuzguna mata da Hajiya Na'ima ta din ga yi, amma rayuwar gidan ta fi mata daɗi a kan wadda take yi a yanzu.
Sai dai tana tuna cewa ba gidan mahaifinta bane, ita ɗin Tsintacciya ce, sai jikinta ya ƙara yin sanyi, amma duk da haka rayuwarta da Faris ta faɗo mata, rayuwa mai cike da ƙauna da soyayya.
Jiki a sanyaye ta ce "Mami, wai kuna waya da Faris kuwa? Nifa bani da lambarsa duk ina cikin damuwa".
"Wallahi Abra duk lambobinsa ba sa shiga, ina ta lallaɓa Abbinku ya je ya dubo mini shi".
"Garin yaya lambobinsa ba sa shiga? Ni tun da yaje gidana ban samu na karɓi lambarsa ba".
Cikin mamaki Mami ta ce "What? Me kike nufi yaje gidanki fa ki ka ce?".
"Eh mana Mami, bai gaya miki ya zo ba?".
Shiri mami tayi sannan tace "Yaushe ya je gidan naki?".
"Almost 5 Months ago, wai be zo nan ba?"
Mami ta ce "No ya zo, ban san yaje gidanki ba ne" da haka ta kawar da wannan hirar.
Abra kuwa satar jiki tayi, ta tafi ɗakin Salman, komai yana nan yadda yake, gani take tamkar zata ganshi kamar yadda ta saba, ta kalli katafaren hotonsa da yake ɗakin da wanda suka yi su biyu, a saɓule ta zauna a kan gadonsa, ta fashe da kuka "Please Faris come back to me, i need you my caring brother, am missing you, kalli halin da Yaya ta shiga, mai yasa kayi nisa da Angel ɗin ka, ma one and only caring brother" ta ƙarasa Maganar cikin kuka mai tsuma zuciya.
A hankali ta tashi zaune, ta shiga Gmail ɗin ta, ta fara rubutawa Salman saƙo mai cike da tsantsar nuna kewa, mai matuƙar ratsa rai da girgiza zukata, tana rubutawa tana zubar da hawaye, ta kammala ta ajiye wayar tare da lumshe idanunta.
Meenal ce zaune a kan makeken gadonta, tana kiran layin Usman, tun safe take kiran wayarsa amm yaƙi ɗagawa, ba ta haƙura ba ta cigaba da nacin kira, sai da babu zato ba tsammani taji ya ɗaga bai ko yi mata Sallama ba ya fara faɗa "Wai me kike nema a gurina ne, tun safe kin hanani sukuni kin addabeni da kira meye haka?".
"Haba Usy, ai ka ɗaga