Showing 15001 words to 18000 words out of 231718 words

Chapter 6 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14662

yi daga jikinsa a hankali saboda yanda take ƙoƙarin fama masa ciwukan jikinsa. Cikin dauriya ya kwantar da kanta akan kafaɗarsa, Gently ya shiga bubbuga bayanta alamar rarrashi cikin sauke ajiyar zuciya ba tare da ya ce komai ba.

Lumshe idanunsa ya yi yana shaƙar ƙamshinta da ya yi bala'in missing ɗinsa. Tsahon 5 minutes suna haka sannan ya ɗago ta ya shiga share mata hawaye tare da girgiza mata kai. Ta gane me yake nufi, hakan yasa ta haɗiye kukanta. Cikin muryar da ta ci kuka ta ƙoshi ta ce. "My Man, sun kusa kashe mun kai ko?" Hannunta ya kamo ya shiga murzawa slowly cikin tsananin ƙaunarta ya ce. "Ba su kusa ba, tunda Allah bai yi ba gani a raye."

Ta ɓata fuska ta ce. "Wannan manyan raunikan dake jikinka fa My Man? Na san ba dan Allah ya yi da nisan kwananka a gaba ba da tuni na rasa ka." Ta ƙarashe maganar tana sakin kuka. Cikin sanyin murya ya ce. "Aikin sojan kenan My Wife, kar ki manta sai da muka rantse za mu kare rayukan al'umma kafin mu fara aikin. Ki bar kukan nan haka, just pray for me." Ta ja hanci ta ce. "Allah ya baka lafiya My Man." Karan hancinta ya ja tare da ɗan yin murmurshi ya ce. "Ameen My wife, ya aka yi kika san ina nan har kika zo?" Ta zauna a gefensa tana kallon cikin idonsa ta ce. "Ta yanda labarin irin bajintar da kuka yi ya zagaye duniya, kafafen yaɗa labarai ko ina ana ta sanarwa, kuma an kira Baffa an sanar masa.


Yana shafa cikinta a hankali ya ce. "How was My unborn Baby? I missed both of you so much."

Kwantar da kanta ta yi akan kafad'arsa ta ce. "We missed you too, Baby yana lafiya, sai dai jiya na san yanda ban yi bacci ba shima bai yi ba, saboda yanda ya dinga wutsil-wutsil kamar zai fito duniya ya tarewa Dad ɗinsa harbin da aka yi masa."

Murmurshi ya yi irin wanda shi kansa ya manta rabon da ya yi kamar sa ya ce. "Zai iya ai, tunda shi ma Jarumi ne kamar Babansa." Dai-dai nan aka turo ƙofar ɗakin aka shigo.




Share, share share Please
Nimcyluv
Zee kumurya
Ayshercool.


'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
[9/30, 8:55 PM] Abk: *✷ DARE DA DUHU ✷*

Bright pens✍🏾
Nimcyluv
Ayushercool
Zee kumurya

*5.....*
Elegant Online writer's

_Domin samun Complete labaran mu, na littafai kala-kala, kuyi following wannan Acct ɗin a Arewabooks👇🏾_
https://arewabooks.com/u/nimcyluv



Wani irin kallo Captain ya bi Faruk da shi, yana son gazgata abun da kunnuwansa suka jiye masa ya fito daga bakin Faruk.

"Do you mean my Abra?" Yai maganar yana nuna kansa da yatsansa.

Faruk cikin damuwa yace "eh, Abra ba'a ganta ba, na duba duk in da ya dace a cikin barrack ɗin nan ba'a same ta ba"

"Shhhhhh, kar ka gayamin maganar banza mana Faruk, ya za'ai ace yarinyar nan ta ɓata how comes? Kaga, i have no option for now am going make sure you bring back my daughter"

"Haba Captain, ta ya zan maka ƙarya, Wallahi a.....

Be ƙarasa maganar ba Captain Khamal ya ɗaga masa hannu yace "na gama Magana, duk in da 'ya ta take ka tabbatar ka nemo ta ka kawo min a bata"
daga haka ya cigaba da takunsa sannu a hankali me kama da na ƙasaita yaa bar Faruk a tsaye a gurin.

Faruk yace "ya salam, Madam Halima kin kashe ni ina kika bar yarinyar nan ta tafi? Ya a kai ta ɓata?" ya ƙarasa maganar yana sauke wani irin nannauyan numfashi, kafin daga bisani ya juya cikin sassarfa ya nufi wani sashi na barrack ɗin.

Zaune take a kan gwiwonwinta, ta zubawa kyakkyawar yarinyar me kama da 'yar larabawa idanu, hawaye ne kwance akan fuskar yarinyar, hannunta ɗaya riƙe da teddy bear, ta zura yatsanta ɗaya a baki tana tsotsa kamar me shan nono.

"Hey look up, kina son chocolate?" Tai Maganar tana kallon idon Abra.

Shiru Abra tai tana binta da kallo, dan sam ba ta ji me tace ba.

"In baki chocolate, ai zaki sha ko?* Still Abra bata amsa ba, kallonta kawai take kamar wata gunki.

Salima ta tashi ta ɗakko jakarta,ta ciro Chocolate ta miƙawa Abra, maimakon Abra ta karɓi Chocolate ɗin, se ta fashe da kuka tana kiran "Abbi, Abbi".

"Shhhhhh, is ok i will take you to your Abbi, amma ki yi shiru, I have plenty chocolate and teddies, zan baki idan ki kai shiru"

Ƙaro sautin kukan Abra tai, tana kiran sunan Abbi.

"Ji min makirar yarinya zata ɗaga min hankali, will you shut up?"

Babban abunda ya bawa Salima mamaki, be wuce yadda sam Abra ba ta responding ga Maganar da duk za tai mata ba, kukanta kawai take yi.

Salima tace "what so ever, da ke zanyi amfani in cika burina, se na nunawa matar Khalid bariki iyawa ce, sena rusa gidan da mijin da take taƙa ma da shi.

TWO DAYS BACK. Kwana biyu da suka shige!

tun bayan faɗan nan da Salima sukayi da Naima, Salima ba ta sake komawa gurin Khamal ba, se ta fita waje ta kama Hotel tai zamanta, sakamakon rashin posting ɗin su da ba'a yi ba.

Tun abun da ya faru a tsakanin ta da Na'ima matar Khamal, tace se ta ga abunda ya turewa buzu naɗi in dai akan Khamal ne, se ta gwadawa Na'ima kalar nata rashin mutuncin da iya barikanci.

Khamal kuwa da ƙyar ya rarrashi Na'ima, kasancewar ta mace me tsananin kishin tsiya, ba ta da haƙuri ko kaɗan akan kishi, ita da ta zo dubiya ƙarshe se da su kai faɗa da Khamal akan Salima.

Na'ima ta daɗe da sanin Salima na bibiyar Khmal, amma tafi kowa sanin halin mijinta, mutum ne kamili da be ɗau duniya da zafi ba, sam ba shi da wannan ɗabi'ar ta kule kulen mata, hasali ma mutum ne me tsare gida, wanda ba'a kawo masa wargi, amma Salima ke ta cusa kanta a wajensa.
Tun kan ya Auri Na'ima, Salima take son sa, amma kasancewar Salima ba mutuniyar arziki ba ce ya sa ko saurararta ba ya yi sam, ya sha yi mata gargadi da jan kunne, akan ta fita daga rayuwar sa amma taƙi, se da ta ƙure shi ta kai ga ta sa ya gaya mata miyagun maganganu, amma still ta ƙi barin rayuwarsa, sannan tai alwashin se ta ga bayan Na'ima, se ta raba shi da ita.

A ranar da Na'ima su kai faɗa da Salima, washegari ta shirya tace ba zata cigaba da zama ba, tafiya za tayi gida.

Captain yace "dear, yanzu tafiya zaki ki barni a nan, nika ɗai?"

"To zaman me zan cigaba da yi, ka san EDD ɗina ma ya kusa, gara ina gida haihuwa ta zo min, tun da suna kula da kai kuma an kusa sallamar ka"
Haka ya ƙyaleta, tai shirinta ta juya Kanon dabo.

Washegari da safe wajen ƙarfe sha ɗaya na safe, Salima tai wanka ta shirya ta koma gurin Khamal, a hanyar da zata sada ta da ward ɗin da yake, ta haɗu da Faruk hannunsa ɗauke da Abra.

Ta tsaya suka gaisa, ta kalli Abra tace "ina ka samo wannan cute Babyn haka?"
Nan Faruk yai mata bayani yace "a gurin operation Captain Khamal ya tsinto ta, tana gararanba a cikin daji, Kuma ikon Allah, Allah ya haɗa jininsa da ita sosai"

Salima tace "ita ma kidnapping ɗin nata a kayi?"

Yace "Sanin gaibu se Allah"

Tace "ikon Allah, to an gano iyayenta?"

Yace "A'a, ba'a gano su ba, tana gurin wata staff ɗin mu ne, Madam Halima matar Captain Abdussamad Goza"

Tace "ok, Allah sarki shes cute Masha Allah, to yanzu ya za'ai da ita? Tun da ba'a samu iyayenta ba?"

Faruk yace "Ai da kyar ne idan ba Captain ne ze ɗau yarinyar nan ba, dan kamar sun daɗe da sanin juna, yana son yarinyar sosai dan har ya raɗa mata suna, it ma Abbi take ce masa, kamar sun san juna,. Se dai be gayan abun da ya yanke ba amma nafi kyautata zaton da ita ze koma, ya riƙeta kan a ga iyayenta"

Ɗan shiru Salimaa tai kan daga bisani tai ajiyar zuciya tace "thats good" daga nan ta wuce zuwa in da Khamal yake.

A wannan karon ma bata samu kulawa daga Khamal ba, sema tijarar da yai mata ya koreta daga ɗakinsa.
Idan da sabo ta saba da wannan abubuwan na wulaƙanci da hantara da yake mata, amma sam ba ta damuwa, ita dai burinta ya amsa yana sonta.

Washegari ta koma cikin barrack, cikin ikon Allah ta bi ta compound ɗin su Madam Halima, abun mamaki ta ga Abra a tsaye hannunta da teddy ɗinta, tana rarraba manya manyan idanunta tana ƙarewa gurin kallo.

Ƙarasawa in da take Salima tai, ta durƙusa a gabanta tace "cute baby, how are you?"

Ɗan ja da baya Abra tai tana kallon Salima.

Wani tunani ne ya faɗowa Salima, ta kuma matsawa kusa da Abrar tace "ina da sweet, ai zaki sha ko in baki?"

Still Abra ba ta amsa ba, saboda ba ta iya jin abunda Salima ke faɗa.

"Ok, zomuje in kai ki gurin Abbi"

Bakin Salima ta ƙurawa ido, taga kamar Abbi tace.

Ta miƙawa Abra hannu, aikuwa ba musu ta bita, saboda ganin laɓɓan Salima sun ambaci Abbi.

Salima ta ɗauki Abra ta tafi da ita.

Yadda a kai Abra ta fito kuwa shine Madam Halima ce t fita  tare da Abra, da suka dawo ne, taga Abra ta tsaya tana kallon murguza murguzan karnunkan da ke kaiwa suna komowa a compound ɗin, ta ɗauke Abra ta shiga da ita gida, a zatonta ko tsoronsu take ji, sedai bayan shigarta wanka, Abra ɗin ta sake fitowa tana kallon karnukan, wanda a nan ne Salima tai awon gaba da ita, tare da ƙudurce wani abu a ranta.

Tun da Madam Halima ta farga Abra ta ɓata ta shiga cikin tsananin damuwa da tashin hankali, saboda Abra ta shiga ranta matuƙa, sannan da ya zata fara bayanin yarinyar da aka bata ajiya ta ɓata?.

Captain Khamal kuwa ji yake tamkar zuciyar sa zata fashe, maimakon yai murna ze koma garinsa da yai wata da watanni baya nan, amma ya kasa farinciki saboda ɓatan Abra, ji yake kamar 'yar cikinsa ce ta ɓata, haka nan yaji yana ƙaunar yarinyar, dan har a wani sashi na zuciyar sa yana jin idan iyayenta suka bayyana be san ya zeyi ba, sakamakon tsananin ƙaunar yarinyar da yake yi.

Shiru yai yana tuna innocent face ɗinta,tana kiransa da Abbi, wanda har cikin ransa yake jin sunan da take kiran na shi da shi. Tunani yake akan how taje Wannan dajin? Waye ya kaita? A yaya ta rayu? Suwaye iyayenta? Gashi tun da ya tsince ta shi dai be ji tai wata magana ba, da zata ba shi haske game da ita ba, Abbi kawai shi ne abun da yaji bakinta yana faɗa.

Wata zazzafar iska ya furzar daga bakinsa, yana jin tamkar ya koma Naija State, tabbas ba dan an riga an gama shirya dawowarsa ba, da ba in da za shi se an nemo masa Abra ɗin sa, amma a yanzu ma ba ta ɓaci ba, nan da 'yan awanni idan ba'a ganta ba, dole ya koma Naija state, jikinsa ya na ba shi Akwai wani al'amari me girma game da Yarinyar.

Faruk kansa ya shiga damuwa da tashin hankali, akan ɓatan Abra, balle Madam Halima da megidanta, sun fi ɗaga hankalinsu akan kowa, nan da nan aka baza cigiyarta a cikin barrack ɗin.

Salima kuwa Abra ta addabeta da kuka, fafur yarinyar nan ta ƙi jin rarrashi, gashi maganar duniya ta ƙi sauraron Salima.

Salima ta ɗauketa ta fita da ita, wani babban shop ta kai Abra tai mata siye siyen, kayan ci da na wasa, se dai duk da hakan Abrar ta ƙi sakin jikinta da Salima, yadda take nunawa ma kamar tsoronta take ji.

Salima ba ta damu da hakan ba, burinta kawai take fatan ya cika, ta tafi da Abra gurin wasan yara, ta din ga yiwa Abra ɗin hotuna.

Sai magariba Sannan suka koma masaukin Salima, sedai  suna komawa Abra tace ba ta san zace ba, ta ɗora da kukanta a in da ta tsaya tana kiran "Abbi"

Salima tace "Ohh God, this pikin want spoil ma plans"

Ta kaɗa ta raya, amma Abra ta ƙi bacci, kuma taƙi yin shiru, tai rarashin tai shouting ɗin, amma kamar ta na yi da gunki.

Ba shiri ta ɗau Abra ta nufi cikin barrack ɗin, kai tsaye ba tare da shakkar komai ba, ta nufi gidan Madam Halima, ai kuwa ta tarar da su a ƙofar gida tare da Faruk, da wasu sojoji, Faruk ya rasa in da ze sa kansa, saboda yadda ya sha kiran waya a gurin Captain Khamal akan Maganar Abra.

"Wa nake gani haka kamar Abra?" Yai maganar yana kallon in da Salima ke tahowa. Duk da dare ne amma ko ina da hasken fitilu.

Salima ta ƙaraso tace "lafiya na ganku a tsaye haka?"

Faruk yace "wacce irin magana ce wannan, kin ɗagawa mutane hankali, a zatonmu Yarinyar nan ɓata tayi".

Salima cikin ko in kula tace "No, na zo wucewa ne na ganta, na ɗauke ta mukaje na sai mata ice cream, that's all"

Mijin Madam Halima yace "amma haka akeyi, ki ɗau yarianya ba excuse ba wanda ya sani, duk kin ɗaga mana hankali, yarinyar nan fa ajiyar ta aka bamu"

Salima tace "to ai ni banga wani laifi da nayi ba, yanzu ba gashi na dawo da ita ba"

Abrar kuwa Faruk take miƙawa hannu, tana maimaita Abbi.

Ya karɓeta tare da rungumeta a jikinsa yana faɗin "Am sorry dear" se jera ajiyar zuciya take.

Ban da Allah yasa Faruk da mijin Madam Halima na gurin, da se sun bawa hammta iska, dan ba ƙaramin haushin abunda Salima ta aikata ba Madam ta ji, yadda ta ɗaga musu hankali da yawa.

Faruk kuwa ya dudduba Abra ya ga ba abunda ya sameta, dan haka ya ƙudurce, a gobe zuwa jibi ze gaggawar zuwa Kano, ya danƙawa Khamal Abra, idan ya so koma ya ze da ita yayi, tun da Salima ta fara ɗaukarta ba wanda ya sani, nan gaba be san me za tai mata, saboda ya san Salima farin sani, sun taɓa aiki tare, ya san irin yadda take faɗi tashin samun abunda zata samu shiga a gurin Khamal.

Labarin da aka tashi da shi yau ne, yai matuƙar girgiza al'ummar ƙasar, 'yan ta'adda sun tare manyan motocin cike da ɗaliban jami'a masu zuwa excution, sun yanka wasu daga mazan ciki, sun yi awon gaba da 'yan matan da malaman su zuwa cikin daji, a can Jihar Kaduna.
   Lamarin ya girgiza al'umma da dama dake ƙasar Nigeria, kasancewar ba a warke daga jimamin, ɓatan ɗalibai 'yan makarantar Sakandire da aka kwashe ba, wanda sojoji suka ƙwato su da kyar, katsam se ga wannan mummunan labari ya sake cika gari.
A ranar da aka sace 'yan makarantar washegari 'yan ta'addan suka saki video suna demanding 200millon as a ransom, a cikin kuɗin da gwamnatin tarayya za ta karɓa na tallafi daga ƙasashen turai, suka bada sati guda cewar idan ba'a biya kuɗin ba, za su dinga yiwa matan Fyaɗe suna yanka su ɗaya bayan ɗaya, kuma muddin aka tura sojoji za su kashe su baki ɗaya, Innalillahi wa Innalillahi raji'un.

Tun bayan dawowar Khamal, 'yan dubiya da 'yan Sannu da zuwa suka cika gidan, aka dinga tururwar zuwa duba Khamal, Na'ima se rawar kai take gami da taraiyar sa, da yi masa hidima iya iyawarta, dan a duniya ba ta da burin da ya wuce ganin ta sanya Khalid farinciki, saboda tsananin soyayyar da take masa.

Duk da tsufan da cikinta yai, shima da raunin da ke jiinsa, da batun ɓatan Abra da yake damunsa, be hana su nunawa juna tsantsar soyayya da yadda su kai kewar juna ba.

Faruk kuwa se farinciki yake, akan yadda ze  mayarwa da Khamal amanarsa, ya san ze farinciki ƙwarai.
 

Cikin tsananin tashin hankali da kaɗuwa, Captain Khamal yake kallon labarai, da tashin hankalin da al'ummar wannan ƙasa suka tsinci kansu a ciki, su gasu da su kai wannan opretion ko warkewa ba suyi ba, an kuma kai wani harin, wanda wasu sojojin za'a kuma ɗiba suje fafutukar karɓo su, babban abunda ya sake ɗaga masa hankali be wuce yadda ya shiga tunanin ya akai 'yan ta'adda suka san za'a bawa gwamnatin tarayya tallafi? Bayan ba aji hakan daga bakin gwamnatin ba, anya babu haɗin bakin wanda suke jikin gwamnatin? Yanzu iyalan su Jamil da aka kashe, babu wani tartibin abu da Gwamnati za tai wa iyalansu, da ze rage musu raɗaɗi, wanda gwamnati zata nuna damuwarta da rasa ɗan ƙasa da akai, a bakin aikin kare ƙasarsa, haka za'a kuma kwasar wasu a kai su daji.
Wani mugun sarawa kansa yai, tare da tunanin meye mafita akan wannan lamari da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.

Ƙarfe huɗu daidai, Faruk yana cikin garin Kano tare da Abra, shima ya warke daga harbin da ke hannunsa.

Khamal yana kwamce akan 3seater, Na'ima na jikinsa a kwance tana rarrashinsa, ganin yadda ya shiga damuwa, saboda wannan abu da ya sake faruwa mara daɗin ji, se ƙoƙarin kwantar masa da hankali take, saboda ya shiga damuwa sosai.

Knocking ɗin ƙofar falo aka fara yi, Na'ima tace "Baby bari in buɗe ƙofa"

Khamal yace "No dear, zauna inje in buɗe ki huta, kar ki wahal da kan ki da babyna"

Murmushi tai tace "My sweet, kar ka damu dama ance in dinga exercise, bari in buɗe"

Ya jinjina mata kai, ta miƙe tsaye tana tafe sannu a hankali, cikin salon tafiya irin ta masu juna biyu.

Tana buɗe ƙofar ta ga Faruk tsaye, cikin ƙananan kaya, murmushi yai tare da sara mata.

Ita ma murmushin tai tace "kai ne a tafe ba sanarwa? Ya jikin naka?"

Faruk yace "Alhamdilillah"

Ba shi hanya tai ya shigo, se yanzu ta lura da ƙaramar kyakywar yarinyar da yake tafe da ita.

Abra na hango Khamal, ta ruga da gudu ta nufe shi tana kiran "Abbii"

Da azama ya tashi zaune, duk da haryanzu yana jin ciwo a in da aka harbe shi.
Abrar ta faɗa jikinsa ta ruƙunƙume shi, Captain ya rungumeta sosai a jikinsa yana faɗin "My daughter, i missed you" ta ɗago tana bin idon Khamal

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login