Showing 3001 words to 6000 words out of 231718 words
Chapter 2 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
'yan ta'addan sun san da zuwansuz duk sun samu nasarar kashe zaratan sojoji masu ƙoƙari, ciki har da makusantan abokansa, Miƙewa ya yi, gaba ɗaya jikinsa jini ne kayansa duk sun yage, ga yunwa, ƙishirwa.
Yana zaune a ƙasa yaji shawagen Helicopter, da alamar General ne ya ƙaraso,yasan ɗauki gaggawa aka kawo musu, kasa Miƙewa yayi har sai da wani soja yazo wajansa ya ɗaga sa, yana faɗin "Komai yazo ƙarshe Captain"
Sauran gawarwakin aka kwashe zuwa cikin wata babbar motar sojoji, raguwar 'yan ta'addan da sojojin suka kama suka ɗaure, suma aka zuba su cikin mota, suma sauran mutanen da suka tsitstsinto anyi garkuwa da su, a wata mota aka zuba su, Khamal ya miƙe ya na tafiya a hankali, kamar daga sama kunnansa ya fara jiyo masa kukan ƙaramin yaro, tsaye yayi, yai shiruu, jin kamar ba kuka bane yasa ya cigaba da tafiya. yana ƙoƙarin sanya ƙafarsa cikin mota, ya ƙara jiyo sautin kuka, a wannan karon kuma ya tabbatar gaskiya kunnansa ya jiyo masa, kuka ne da gaske, fasa hawa motar yai, sauran sojojin na kiransa amma be kula ba, a hankali yake tafiya jiki a sanyaye da ƙyar yake ɗaga ƙafarsa saboda wahala, ganin baiga kowa ba sai ya fara tunanin ko aljanu ne? Ko kuma kukan wata dabbar ce, wani kukan ya sake jiyowa da sauri ya juya zuwa inda yake jin kukan, ya ƙara nausawa cikin dajin, ware idanunsa yayi kan ƙaramar yarinyar dake zaune a ƙasa ta ƙanƙame jikinta waje guda, Idanunta rufe da alama gaba ɗaya a firgice take, Khamal ya ware idanunsa akan yarinyar gaba ɗaya ba zata shige shekara uku ba (3Years) fara ce sosai kamar buzuwa kamar kuma Balarabiya, tafi kama da ruwa biyu (Half-caste) domin gashinta wanda yafi ƙarfin kanta ya sauka har ƙasa kasancewar a zaune take, farar fatar jikinta tayi baƙi sosai, ga raunuka a jikinta..
Sosai Khamal ya girgiza da ganin ƙaramar yarinya a cikin jejin nan, sai ya fara tunanin ko dai Aljana ce?ko a cikin matan da akai kidnapping take, Samun kansa ya yi da cewa
"Ke" shiru tayi masa sai kukanta take tana ƙanƙame jikinta, cikin rashin sanin cewa yarinyar nada ƙarancin ji a kunnanta yasa Khamal ƙara cewa "Kee" nan ma tayi masa shiru.
"kada ka kuskura ka ɗauki yarinyar nan, ita ba kidnapping ɗinta mukai ba, ita tamu ce, rainonta za muyi, 'yar mu ce" Cewar wani mutum da ke tsaye, hannunsa riƙe da bindiga.
Captain Khamal ya kalli mutumin sai kuma ya kalli Yarinyar, kana yaja baya kaɗan yace "To me zan da ita tun da taku ce?" Ya faɗa yana Juyawa, mutumin ya sunkuya zai ɗauki yarinyar kenan yaji saukar bullet a bayansa, ihu ya saki yana faɗuwa ƙasa, cikin zafin zuciya Khamal ya fisgo Yarinyar yace "Keeee...." Sai a lokacin taji saukar muryarsa a kunnanta, fararen idanunta ta ɗaga, wanda yasa zuciyar Khamal bugawa, Yarinyar ta washe bakinta ta nufi wajan Captain Khamal tace
"Abbi..." Ta faɗi hakan tana ƙanƙame ƙafafuwan Khamal, “Abbi?” Khamal ya maimaita a zuciyarsa a fili kuma sunkuyawa yayi ya ɗauki yarinyar a kafaɗarsa, kai tsaye ya nufi in da motocin su suke da ita yana ƙoƙarin shiga cikin mota yaji saukar wani abu mai kama da kibiya ko mashi a gefen cikinsa, a hankali kuma yaji zafin saukar abu a jikinsa tsananin azaba yasa sam bai kawo cewa harbinsa akai ba, ƙafarsa ya ɗaga da ƙyar yana sauke Yarinyar muryarsa na rawa yace
"Shiga ciki" watsa hannunta tayi tace "Abbi" alamar bata gane zan can nasa ba, da hannunsa yayi mata alamar ta shiga cikin motar, sauran sojojin na ciki basu san meke faruwa ba, bayan ta shiga cikin motar Khamal ya ɗaga ƙafarsa da ƙyar zai shiga cikin Motar ya ƙara jin saukar wani harbin a gefen cikinsa...
😂😁 Ya kuka ji salon Bright pens?..... Daban ne... Share share share as so much as you can!.
#Nimcyluv
#Zee kumurya
#Ayushercool
[9/30, 8:55 PM] Abk: *✷ DARE DA HUDU ✷*
_Bright pens of✍🏾_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee kumurya
Ƙirƙirarren labari me, ba mu yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba, idan yai kamanceceniya da rayuwar wani ko wata Arashi ne.
Littafin DARE DA DUHU haƙƙin mallakar mu ne, bamu yar da a juya shi ta kowace siga ba, ko a sashi a wata kafa ba ba tare da izinin mu ba.
BISMILLAHIRAHMANIRAHIM
ELEGANT ONLINE WRITER'S
P2.....
Jin sautin harbin da ya sake tashi ne, ya sa yarinyar fitowa daga cikin Motar da sauri ta tsaya tana kallon Captain.
Jini ne ya shiga zuba a gadon bayansa, ga na cikinsa da yake zuba shi ma, cike da jarumta irin ta soja yake ƙoƙarin tsayuwa kan ƙafafunsa, ya kuma ƙoƙarin ya yunƙura ya ɗaga ƙafarsa, sai dai yaji jikinsa yai masa nauyi, ga wani danshi da yake ji ya jiƙa masa kaya, sai a lokacin ya fuskanci harbi ne, a nan take duhu ya maye gurbin hasken ranar da ya haska dajin a idon Captain, a hankali yai baya ji kake timm ya faɗi ƙasa.
Sam ba ta san me ya faru da mutumin ba, wanda ya karɓo ta a hannun waɗan nan mutanen, sai dai ta zuba masa manya manyan idanunta, sai jujjuya ƙwayar idanunta take a kansa.
Sautin Wani harbin ne ya kuma tashi, cikin azama wani soja ya fito daga cikin Motar, ya danƙi yarinyar ya kwantar da ita flat a ƙasa, ya shiga danna nakiyar ta sa bindigar shima a saitin in da ƙarar harbin ke tasowa.
Sautin Command ɗin Commander Land army ya jiyo nesa kaɗan da in da suke, yana bawa tawagar sojojin umarni, cikin dakakkiyar muryarsa dake amsa kuwwa a dajin, tare da ƙarar motocin sojojin na yaƙi, hakan ya tabbatar masa, da an turo wasu sojojin domin kawo musu ɗauki.
Nan da nan ƙarar harbi ya sake cika dajin, tamkar za'a tsaga dajin.
Tai lamoo a ƙasa, duk wannan ba ta kashin, da ƙarar bindigogin da ke tashi, can ƙasa ƙasa take jiyo sautin kaɗan kaɗan a cikin kunnenta.
Gaba ɗaya hankalinta yana kan mutumin nan da ya ɗakko ta, da yake kwance a ƙasa, ba ya ko motsi.
Ba tare da tunanin komai ba, ta miƙe zata nufi in da yake ƙasa a kwance, sojan nan da ya kwantar da ita flat a ƙasa, ya fizgota cikin tsawa yace "Lay down before they shoot you" shiru tai tana son gane me yake cewa.
Ya sake kwantar da ita a ƙasa, hellcopter nan kuwa tuni ya tashi ya fara shawagi a sama, suna communicating da sojojin dake ƙasa.
An kwashi kusan awanni biyu ana wannan musayar wuta a tsakanin 'yan ta'addan da kuma sojojin, wanda a ƙarshe Allah ya bawa sojojin nasarar fatattakar maharan, suka kashe na kashewa.
Sai bayan da ƙura ta lafa, sannan Lieutenant Faruk ya migirna a hankali, saboda harbin shima da akayi masa a dantsensa.
Cikin jarumta ya miƙe tsaye, sai dai jiri ne ke ɗibar sa, saboda jini da yake zubarwa a dantsen nasa, yana tashi ita ma yarinyar ta tashi tsaye, sannu a hankali ya ƙarasa in da Captain yake kwance a sume cikin jini, ya durƙusa ya ɗago shi, tare da kara kunnensa a saitin zuciyarsa, can ƙasa ƙasa yaji bugun zuciyarsa alamar yana da rai.
Bin su kawai take da ido, tana sake zura kai tana kallon Captain da idanunsa ke rufe.
Tawagar sojojin da suka shigo dajin kawo musu ɗauki ne suka fara ɓullowa, suna ta tattara gawarwakin 'yan uwansu, da wanda a kaiwa rauni.
Cikin hanzari suka ƙaraso in da su Captain suke. Lieutenant Faruk na zaune rungume da Captain a jikinsa, Chief Commander yace "Are you ok?"
Faruk yace "Yes sir, but Captain K Buba needs first aid, he is seriously bleeding"
"Is he alive?" Ya sake tambayarsa.
"Yes, but am not sure"
Nan da nan aka ɗauki Captain zuwa inda aka kwantar da wanda suke buƙatar taimakon gaggawa, wanɗanda akaiwa rauni.
Nan Army doctors, likitocin sojoji suka rufu akan Captain dan ceto rayuwarsa, aka fara ƙoƙarin cire bullet ɗin dake cikinsa.
Sun yi nasarar cire na bayansa, amma na cikinsa ba su samu cire shi ba, sukace sai an koma can Barack za'a iya cire shi a Asibiti. Nan su kai ƙoƙarin tsaida jinin da ke zuba a jikinsa.
Lieutenant Faruk ma an cire masa bullet ɗin da ke damtsensa, an saka bandage an nannaɗe masa hannun.
"Hey, what this little baby is doing here?" Chief Commander ya faɗa yana nuna yarinyar da Captain ya tsinta.
Faruk yace "Captain ne ya tsinto ta".
"Is she among the victims?"
Faruk yace "No, I don't think so, maybe she was kidnapped too, I don't actually knows where she belongs to"
Ita dai bakunan su kawai take bi da kallo, Tare da son fuskantar me suke faɗa.
Mota daban aka ware, aka tara gawarwakin sojojin da suka rasa rayukansu akan ceto wannan ɗalibai da akai garkuwa da su (may the gentle soul of the fallen heroes, rest in perfect peace).
Aka samu wata motar aka saka wanɗanda suka ji rauni, tana ganin an ɗauki Captain ita ma ta miƙe ta bisu, dan kar su ɓace mata, aka saka shi a mota ita ma ta fara ƙoƙarin shiga Motar.
"Hey, Carry this girl with you" Commander yai maganar yana nuna wani soja.
Ganin ya danƙi hannunta zai shiga da ita wata motar ya sa ta fashewa da kuka.
"Shut up!" Yai mata tsawa, duk da ba ta iya jin sautin abunda ya faɗa sosai amma ba ƙaramin razana ta yai ba, gaba ɗaya tsoron su ya shige ta, har ta fara tunanin ko irin mutanen da suka sato ta ne.
Lieutenant Faruk ne ya ƙaraso, ya kamo hannunta suka shiga wata Motar, sai leƙa window take, tana nunawa Faruk motar da aka saka Captain a ciki, bai kula ta ba ya jingina da jikin kujera tare da lumshe ido.
A daidaita sahu ce ta tsaya a ƙofar wani Babban Asibiti, mutane sai shiga suke suna fita, tare da salallami, fuskokinsu duk babu daɗi.
A gigice wata mata ta sakko daga cikin adaidaita sahun, hannunta ɗauke da wani yaro da bai fi shekaru huɗu ba, jikinsa sai rawar sanyi yake, haƙoransa na datsewa.
Bayan ta sallami mai a daidaita sahun, cikin gudu_gudu sauri_sauri ta shiga cikin Asibitin, ta nufi ɓangaren Accident and emmrgency, wato sashen bada taimakon gaggawa.
Teburin Nurses ta nufa hannunta riƙe da yaron tace "Bayin Allah dan Allah ku taimaka min, yaro na kawo".
Ɗaya ta ɗago ta kalleta tace "Ba mu da gado"
Cikin tashin hankali tace "Dan girman Allah ku duba min yaron nan, kar shima in rasa shi, duk 'yan uwansa babu sai shi kaɗai ku temaka dan Allah"
A fusace wata Nurse tace "kinji mace, muka ce miki ba mu da gado, ko ransa a hannunmu yake? In Allah ya ga dama karɓar shi zai yi, ko kina so ko ba kya so, waɗanda kike gani a kwance ma sallamar su za muyi, likitoci yajin aiki zasu tafi, in kina da kuɗi kuma zaki iya kai shi Asibitin kuɗi a duba shi"
Cikin kuka tace "Wanne zan kai shi wanda zan samu likita a dubamin shi"
Nurse ɗin tai murmushi ta ce "yanzun nan aka kira likitan da yake duba marasa lafiya a nan, duk ranar Talata yske zuwa, kuma awa uku kawai yake ya tafi, doctor G.Y ya tafi Asibitinsa, ki je ki same shi a can sai ya fi duba miki yaron yadda yakamata, a bashi duk abunda yake buƙata".
"Au dama ba'a shiga yajin aikin ba?" Ta tambaya tana rarraba ido.
Nurse ɗin ta ce "eh ba'a shiga ba tukuna, amma ai na gaya miki bamu da gado ko? Kuma ana shirye-shiryen tsunduma yajin aikin likitoci"
"To shikenan, ina ne Asibitin nasa?"
Suka kwatanta mata Asibitin, haka ta kuma fitowa da yaron, cikin tashin hankali ta tafi in da aka kwatanta mata.
G.Y BULAMA HOSPITAL AND MERTERNITY, shine a rubuce a katafaren ginin, Manyan motoci na ta shiga suna fita a cikin harabar Asibitin.
Tana rungume da yaron ta shiga cikin Asibitin, kai tsaye ta nufi in da wasu Nurses ke zaune tace "Sannunku, dan Allah mara lafiya muka kawo" tai maganar tana nuna musu yaron da ke hannunta.
"Kuna da file a nan ne?" Wata Nurse ta tambaya.
"A'a, Wallahi mun je Asibiti uku duk sai ace mana ba gado, a na ƙarshen ne aka ce mana wai yajin aiki likitoci za suyi, shine aka kwatanta mana nan"
"To ai Hajiya sai kun buɗe file sannan likita zai ganku"
Ta ce "To nawa ne buɗe file ɗin?"
"Naira dubu biyar ne, single file"
Turus tai, dan kuɗin hannunta dama dubu bakwai ne, sun ƙarar da biyu a yawon Asibitoci.
Dubu biyar ɗin kenan ta rage a hannunta, a sanyaye ta ce "To a buɗe mana"
Haka ta biya kuɗin nan, aka buɗe musu file, bayan an buɗe aka ce su biya dubu uku kuɗin ganin likita.
Ta kalli Nurse ɗin ta ce "Wallahi suke nan a jikina, ki taimaka min baiwar Allah, kar in rasa ɗana, dan Allah ku duba shi"
"Baiwar Allah, ba fa Asibiti na bane, kuma ba Asibitin gwamnati bane, haka ƙa'idar Asibitin take.
Ta koma gefe kawai ta fashe da kuka.
Wani dogon mutum ne fari sol, ya fito daga wani ɗaki jikinsa sanye da farar rigar likitoci, Nurses na biye da shi sun riƙo masa files, ganin mace ta saka ɗa a gaba tana kuka ya sa ya tsaya ya kalleta ya kalli yaron ya ce "Lafiya baiwar Allah, baki san akwai marasa lafiya a kwance ba kika ware murya kina wannan kukan?"
Cikin kukan ta ce "dan Allah likita kai min rai, ka dubamin yaron nan, dubu biyar ɗin kenan na biya kuɗin buɗe file, kuma yanzu ance sai na biya na ganinka dan Allah ka dubamin shi".
Ɗan shiru yai yana kallon ta, daga bisani ya durƙusa ya tattaɓa yaron, ya buɗe idon yaron, sannan ya miƙe tsaye yace "ku biya naira dubu hamsin, kwantar da yaron za'ai ya galabaita sosai"
Daga haka bai kuma cewa komai ba, ya fara tafiya.
Take hawayen idonta suka bushe jin an ambato dubu hamsin, dan basu da ita ba su da dalilinta, dan Mai_ gidanta ɗan acaɓa ne.
Jiki na rawa ta ɗakko 'yar ƙaramar wayar ta mai madannai, ta nemi lambar mijin nata, cikin kuka tai masa bayanin halin da ake ciki.
Yace "ki kwantar da hankalinki, kice su yi masa duk abun da ya dace, zan bada jinginar babur ɗina, in kawo kuɗin.
Allah sarki uwa, kamar zata zare haka ta kuma tashi, ta nufi ofishin likitan nan, ta tarar yana duba wani mara lafiya, a hanzarce ta ce "likita dan Allah ka zo a fara bashi magani, babansa yace gashi nan zuwa zai zo ya biya kuɗin"
Cike da ƙosawa da ƙufula ya ce "hajiya baki ga mara lafiya nake dubawa bane? Mu nan Asibitin bama haka, ki je idan kun kawo kuɗin a bashi maganin, kar ki sake shigo min office haka ba izini"
Da ƙyar ta iya jan ƙafafuwanta da su kai mata nauyi, ta bar office ɗin, ta koma in da ta kwantar da yaron, sai jijjiga yake, jikinsa rauu da zazzaɓi, bakinsa se zubar da dafara yake, ta samu guri ta zauna ta ɗora yaron a kan ƙirjinta tana jin yadda zuciyar sa ke bugawa, kamar zata fasa ƙirjinsa ta fito. Ta lumshe ido tana zubar da hawaye tana kallon yadda kumfa ke fite a bakin yaron, amma cikin ma'aikatan ba wanda ya kalle su da idon tausayawa.
Tana nan a zaune sai ga mijin nata kamar korarrare ya shigo hankali a tashe, ya ƙarasa in da take zaune da yaron yana faɗin "Zainabu, an duba shi kuwa?"
Kasa Magana tai sai sake rushewa da kuka, yace "ki kwantar da hankalinki, na bada jinginar babur ɗina, na karɓo kuɗin a gurin maƙocinmu, a ina za'a biya kuɗin?"
Ta nuna masa reception, in da zai je ya biya, ya je ya biya ya zo ya ɗauki yaron, ya rungume shi a jikinsa, da receipt ɗin biyan kuɗin a hannunsa.
Aka nuna musu ofishin likitan, Ya shiga da yaron a jikinsa, likitan ya kalle shi ya nuna masa gadon da ke cikin Office ɗin yace ya kwantar da yaron ya je waje.
Haka ya kwantar da shi ya fice, ya koma in da ya bar matarsa ya dinga rarashinta yana bata baki.
Nurses ɗin jira suke suga doctor ya taso ya duba yaron, amma yace "This boy will not survive, da tun zuwansu sun ba da kuɗi ne, da maybe mu iya ceto shi, but for now, ba zai surving ba"
"But doctor, da an jarraba dai ko Allah zai sa a ceto shi" wata Nurse tai Maganar cike da tausayawa.
"Will you shut up, zaki koyamin aiki ne?" Yai maganar yana zazzare ido.
Ta ce "No am sorry Sir"
Wata matashiyar budurwa ce, sanye da uniform ta shigo hannunta da file ta kalli likitan ta ce "Doctor, 'yan uwan matar nan da za'aiwa CS a cikinsu duk babu me irin blood group ɗinta, Amma an samu mai O negative a cikinsu, wanda zeyi daidai da jinin Alhajin nan da aka rasa samun jinin da za'a saka masa"
Ya ce "ok, yanzu abunda za'ai shine, ku ɗebi 2 pints of blood, a jikin shi mai O negative ɗin, sai kun ɗiba zuwa anjima sai ku ce musu kun sake gwadawa jinin bai yi ba, su sake samo wasu mutanen, idan ya so a siyarawa da Alhajin jinin, 20thousands each pints, leda biyu 40 thousands kenan"
Tace "ok Sir"
Ya cigaba da sabgar gabansa, yayin da wannan yaro na kan gado ya cigaba da convulsing, ya kai mintuna talatin a haka, daga bisani rai yai halinsa.
Sai da yaron ya rasu, Sannan Ya miƙe ya saka safar hannu, yai parking ɗin gawar, sannan ya fita daga office ɗin, cikin rige rige iyayen yaron suka ƙaraso suna tambayar ya jikinsa, cikin ko in kula doctor GY yace "He's gone, Allah yai masa rasuwa"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shi suka dinga maimaitawa, yayin da mahaifiyar yaron ta koma gefe tana zub da hawaye, shikenan guda ɗaya yaron, shima gashi ta rasa shi.
Shi kuwa doctor G.Y yai gaba abunsa.
Wasu daga cikin patient suka dinga bata baki, akan tayi tawakalli Allah ya bata wani.
Cikin kuka ta kalli Nurses ɗin tace "Wataƙila da kun taimaka mana, ko da magani ne lokacin da muka zo yana suma, da wata ƙila bai rasu ba"
Wata Nurse tace "ki ji min mata kamar jahila, maza kiyi saɓo kinji, mutane kamar ba musulmai ba ba tawakalli"
Duk dauriya da jarumta irin ta namiji, sai da mahaifin yaron yai kuka, yace "ki dena