Showing 72001 words to 75000 words out of 231718 words

Chapter 25 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14696

ƙuncin".

Abbi yace "Ki dena damuwa, in basu baki ba a canza miki wata".

Na'ima da tun ɗazu ba tace komai ba tace "Wane irin a canza mata wata, ka sani ko ana musu karatu tana wasa da waya ne?".

"No ba haka 'yata take ba, koma mene zanga abunyi, a canza wata idan be baki ba, amma ki dena damuwa kinji?"

Tace "to Abbi".

Salman ne ya miƙe ya nufi hanyar kitchen, ganin Kamar Salman yana fushi da ita, yasa ta miƙe itama ta nufi kitchen ɗin".

"Ina zaki?" Na'ima tayi maganar tana zazzarewa Abra ido.

Abra tace "Mami banci Abinci ba, zanje in zuba ne".

Ba dan ta so ba, tai shiru saboda Abbi yana gurin.

Da sauri Abra ta ƙarasa cikin kitchen, ta tarar da Salman a tsaye yayi shiru, da alama ma ba wani abu ya shiga yi a kitchen ɗin ba.

Yana ganin ta shiga, shi kuma ya nufi hanyar fita, da sauri tace "Faris"

Ya waigo ya kallta ba tare da yayi magana ba.

"Fushi ka ke dani?".

"Me ki kai mini da zan fushi dake?".

'ga alamu nan a fuskar ka, me nayi maka? Kuma ina shigowa ka juya zaka fita".

"To ya kike so inyi, ina ta binki ki gaa mini me ke damunki amma kin ƙi".
Abra tace "Haba Bloody na, rashin wayata ne kawai duk ya dameni, You know am so much attached to my Phone, am sorry"

Ta yi maganar tana murmushi tare da jan dogon hancinsa, ji yayi yana neman shiga wani hali, kasancewar kusacinsu da Abra yayi yawa, gashi sai ƙamshin turare take yi.

Cikin shagwaɓa ta ce "to kace mini ka haƙura mana".

Lumshe ido yayi, yana kallon yadda take cigaba da shagwaɓa.

"Talk mana".

"Ta yi maganar tana girgiza shi".

"Tom na haƙura" ya faɗa a taƙaice.

Ta girgiza masa kai tace "See how you frown your face, gaskiya ba kaa haƙura ba"

"Na haƙura Angel, let me go and rest please"

"Wai to ya na ga duk ka wani canza ne?"

Yace "Stress ne kawai na school, see you later" yayi maganar yana kashe mata ido ɗaya, ya fice daga kitchen ɗin.

Murmushi tayi a hankali ta furta "Faris sarkin rigima, am imagining ma life without you, you are so much caring bro, Allah ya biya ka" ta ƙarasa Maganar da ajiyar zuciya.





"Kai yanzu Adnan, fisabilillahi daga cewa zakaje wani Assigment a Kano ka dawo, sai kaje ka yi zamanka, kullum kana gaka nan gaka nan, mahaifinka duk ya damu".

"Am sorry Hajiya, ni kaina ban yi zaton aikin zai ja mini dogon lokaci haka ba, amma Alhamdilillah an yi Nasara a aikin ai".

"To barka, haka ake so dama, amma aikin na ku ne sai a hankali, yau mutum yana nan gobe yana can, ga ƙasar nan babu cikakken tsaro sam".

Yace "Hakane Hajiya, dama aikin ɗamara kasada ne, amma gara a rasa rai ɗaya idan har zai silar rayuka da yawa su samu kwanciyar hankali".

Hajiya tace "A'a Adnan, ai duk rai rai ne, mai shi yana son abunsa, Allah dai ya tsare mana ku".

"Ameen, uwata ta kaina, baki mini Addu'a ba yau".

Ta yi murmushi ta ce "Addu'a kullum cikinta muke ai, yanzu haka ma ai na yi maka".

Yayi murmushi yace "Allah ya ja kwanan Hajiya Mama"

"Ina, ai mu mun kai gangara, fatan ƙarshe mai kyau muke, ku muke yiwa Addu'a, Allah ya raya mana ku".

Ja yayi kamar ta zuba masa wuta abunda ta faɗa, life without his Mum, haka kurum ya ji jikinsa yayi sanyi, miƙewa ya yi daga in da yake zaune yace "Sai da safe"

"To Allah ya tashe mu Lafiya, kar ka manta kayi Addu'a"

Bai amsa ba, kuma bai waigo ba ya wuce ɗakinsa.

Ya shiga banɗaki ya watsa ruwa, ya fito yayi shirin kwanciya bacci, gefen pillow ɗin sa ya kalla, wayar Abra ce da aka ishe shi da ringing ya sakata a silent.

Ya danna wayar, kusan 25missed calls, wanda duk daga Bloody sai Faris.
Sliding ɗin screen ɗin wayar yayi, saiga hoton Abra akan screen lock ɗin wayar, kanta babu ɗan kwali, ta saki gashin kanta, da ya rufe mata gefen fuska, ta turo laɓɓanta gaba, wanda suka kasance pink.
Shiru yayi ya zubawa hoton nata ido, kamar mai nazartar wani abu, daga bisani yayi wata nannauyar ajiyar zuciya, ya kashe wayar gaba ɗaya ya ajiye, ya kwanta.




Duk da zuciyar Ihsan cike take da fargaba, amma haka ta ɓoye tsoronta, ta dake dan karta ɓata musu shiri, ta dube shi tace "Nifa Yallaɓai babban dalilin zuwana nan shine, ciki ne a jikina har watanni huɗu dan haka nazo ka bank kuɗi inje in cire shi, ka san dai babu da wanda na taɓa mu'amala sai kai.

Haɗe rai yayi yace "Na sani ko bayan na buɗe hanyar, kin cigaba da leƙe-leƙenki, kuma wace irin sokuwa ce ke, da zaki bari ciki ya shiga jikinki har Wannan lokacin?"

"Kar ka sake ce mini sokuwa, kawai ka bani kuɗi inje in zubar, kar Asirina ya tonu".

Gajeren tsaki yayi Yace "Naji, zan baki 20k kije a cire shi".

Wani banzan kallo ta yi masa tace "sai kace cikin jikin Akuya? Dubu ɗari aka ce zan ajiye, sannan a cire cikin ya zanyi da wata 20k".

"Kina da hankali kuwa, a wannan marrar ne zan baki har 100K?".

"A Arziƙin da Allah yayi maka mecece 100K? Ko nice a bar banza?"

"Kinga zan bani 50K, daga haka ba zan ƙara ba".

"Gaskiya ba zan karɓi 50K ba, a ina zan samu sauran?".

Yace "Wannan ya rage naki kuma" wani irin baƙin ciki ya turnuƙe mata zuciya da tarin nadama da dana sani, ba yadda ta iya, haka ya tura mata 50K.
Ba kunya kuma bayan ya tura mata ya fara lalubarta, abun mamaki sam ba ta masa musu ba, suka gama sheƙe ayarsu, Sannan ta kintsa jikinta, ta koma masaukin su.

Baby ta dinga jinjina mata, domin kuwa duk abunda suka yi, ta naɗo tsaf a video ba tare da ya san tayi haka ba.

Nan Baby ta sake shirya mata abunda zata yi masa, dan wanda ya yiwa Janna, sai da ya ajiye mata dubu ɗari biyu da hamsin, dan haka suma sai sun wanki wannan Yallaɓai.

Dan haka suka tsara message tare da videon nan nasa, suka tura masa!.


Innalillahi wa Innalillahi raji'un, tashik hankali da ba'a sa masa rana, Yana gurin aiki, amma haka ya miƙe jikinsa na tsuma, yaran nan sun san waye shi a cikin ƙasar nan kuwa? Yayi harka da manyan karuwai, amma wannan da ba su fi 'ya'yan cikinsa ba, sune za su ƙulla masa wannan tsiyar? Dole ya ɗauki mummunan mataki akan yarinyar nan, wanda nan gaba idan aka ce ta yiwa wani haka ba za tai ba.





Abra tun tana kewar rashin wayarta, har ta saba ta haƙura da rashin wayar, gefe guda haka kurum take jin ta yi missing ɗin me turo mata messages ɗin nan a wayarta, ko ba komai wani mutum na musamman ne da ya shigo rayuwarta, ta wata siga da babu wanda ya taɓa shigowa ta haka.
Guntun tsaki ta ja, bayan tuna Adnan ya tafar mata da wayarta.
Sosai ta maida hankalinta kan karatunta, tun daga ranar da Adnan ya tafi da wayarta, ba ta sake ganinsa ba, tun tana tunanin zata kuma ganinsa ya bata wayarta har ta dena, ta cigaba da al'amuranta, sai cewa ma take wa ya sani koma ɓarawon wayane, wayar yake son ya sace shiyasa yake ta binta.

Yau ba lokaci ɗaya Abra za su tashi da Salman ba, dan haka akwai snacks a jakarta, ta tafi department ɗin su Salman, domin suci sai ta jira har ya gama lectures, Sannan su tafi gida, dan ta san idan taje gidan ma, ba daɗinsa za taji ba.

Ajin Su Salman ta nufa, ta ɗan leƙa ta window, taga ana yi musu lectures, Malmin ya raba ajin gida biyu, yana yi musu kacici_kacici, yace duk rukunin da suka ci, suna da maki goma-goma dukaninsu, amma sai ya kammala lectures ɗinsa na yau za'ayi.

Ajinsu Faris Maza sunfi yawa akan mata, dukkansu suna sanye da fararen lapcoat akan kayansu, sun tattara nutsuwarsu akan malamin.

Ba wanda ya ganta, tana nan tsaye aka gama lectures ɗin, aka fara Quiz.

Anayi tana ta murmushi, abun yana burgeta sosai da sosai.

Can aka yiwa rukunin su Faris wata tambaya, abunka da manyan professors, sai da ya rikita tambayar, yadda ba za su fahimta ba.
Sai ya basu option yace su zaɓa, ganin sunyi shiru suna mazari ya sa Abra tai farat tace "Faris Ba ne amsar fa" gaba ɗaya ta manta a jikin window take, tana leƙe.

Aikuwa gaba ɗaya suka waigo suna kallonta, sai kuma tayi shiru tana rarraba ido.
Prof ɗin nan yace "Zo nan" jiki a sanyaye ta zagaya ta shiga ajin, tana sunkuyar da kai, saboda ba ta son kallo.

Ya kalleta yace "Me kike yi a jikin window?".

"Brother na nake jira mu ci Abinci" ta faɗa kai tsaye.

Yai murmushi yace "Sai kace a Nursery? Waye brother ɗin naki?"

Tace "Faris ne"

"Waye Faris?".

Ta kalli Salman da ido, Salman wata kunya ta kama shi, Sam Abra bata da wayo wasu lokutan.

Prof ɗin yace "iyee, cire facemask ɗin nan".

A hankali ta sauke face mask ɗin, tana sunkuyar da kai, harda masu cewa wow, tubarkallah abunda ya sa Salman sake tsuke fuska.

Prof Jibiya yana da barkwanci sosai, dan haka yace "Salman, is she your sister?".

Salman yace "Eh ƙanwata ce".

Zaro ido ta yi, za tai magana, amma Salman ya harareta, hakan ya sata yin shiri.

Jibiya yace "Masha Allah, to yanzu yi mana bayanin, meyasa kika zaɓi B a matsayin Amsa?".

A nutse Abra tayi masa bayani, wanda in ba me kaifin hankali ba, babu wanda zai iya gano amsar.

Ya jinjina kai yace "Kai Masha Allah, Madalla da basira irin taki, me kike karanta ne?"

Ta gaya masa, ya jinjina nai, gaba ɗaya ba science tayi ba, amma ta iya bada wannan amsar.

Prof yace "Yanzu kiyi tafiyarki, kije ki ci Abincin ki, dan wannan ba yanzu zai fito ba".

Tace "To, amma zan iya ba shi nasa kan su fito?" Ya jinjina mata kai, 'yan ajin sai dariya sukewa halin ƙuruciya na Abra.

Taje gaban seat ɗin Faris, ta ɗakko wata leda ta ajiye masa tace "zanje inyi karatu in kun gama sai mu tafi".

Faris ya kalleta, a hankali yace "Dan Allah Angel yaushe zaki girma ne? Yarinya ba wayo gaba ɗaya".

Tace "Ni ba zan kulaka a nan ba, sai munje gida".

Daga haka ta yiwa lecturer godiya, ta fice, prof ya cigba da koɗa Abra da baiwarta, har da tambayar Salman anya uwa ɗaya uba ɗaya suke? Ko dai su larabawa ne, sai da Salman ransa ya ɓaci, ya tsuke fuska.



Tana tafe tana ƙoƙarin samun gurin da zata zauna, ta ci Abincinta tayi karatu.
Wani irin mahaukacin parkig aka yi a gabanta, wanda sai da ta razana, ta runtse idanunta.
Jin shiru ba'a bugeta da motar bane ya sa ta buɗe idanunta a hankali.

Ido huɗu suka yi da shi, wanda sai da ya fuskanci halin firgici da ta shiga.

Juyawa tayi za ta canza hanya, amma cikin zafin nama ya fito daga motar, ya danƙo hannunta, ya jefata a cikin motar ta sa, ya rufe motar ya zagaya ya shiga, ya fizgi motar da gudu, ya bar makarantar.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ina zaka kai ni, na shiga ukuna, wayyo Abbina, Faris dan Allah a temake ni"

"Shut up, ki dena yi mini ihu" yai mata wata razananniyar tsawa.

Abra cikin kuka tace "dan Allah kayi haƙuri, ka ƙyaleni dan Allah" shiru yayi Mata ya cigaba da tafiya.

Wani gurin cin Abinci yaje, yayi parking ya kalleta ransaa a haɗe ya ce "Fito" Cikin tsoro da fargaba ta fito tana zare ido, gurin ba mutane sosai suka shiga cikin gurin cin Abincin.

Yayi mata umarnin ta zauna, haka ta zauna tana cigaba da waige-waige, tsoronta Allah tsoronta kar wani wanda ya santa ya ganta yaje ya gayawa Abbi.

"Me za'a kawo miki?" Yayi Maganar yana kallonta.

Ta girgiza masa kai alamar babu.

"Ba sace ki nayi ba, Cin Abinci kika rako mijinki, dan haka You Are safe, ki saki jikinki, bana sace mutane" Kallonsa take, kamar ba shi ne ya gama yi mata tsawa ba.

Yayi musu order Abinci, amma taƙi ci.

"Nifa Mutum ne ba dodo ba, stop looking at me, like this"

"Dan Allah ka mai da ni, dan Allah kayi haƙuri"
Wani irin kallo yake mata, wanda sai da ta ji tsigar jikinta na tashi.

Sauke idanunsa yayi, ya cigaba da cin abincinsa.

"Ki dena kallona kar in ƙware".

"Ai ba kallonka nake ba" ta faɗa a raunane.

"Ya maganarmu ne?".

"Wace Maganar?"

Ya ɗago ya kalleta yace "ina tambayar ki, ki na tambayata?"

Ta sunkuyar da kanta ƙasa.

"Abra talk" yayi Maganar in a cool voice, kamar ba shi ba.

Shiru tayi bata amsa ba.

Adnan yasa hannu ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna.

Ya ɗan kashe mata ido yace "Yaushe zan zo gidanku in ga Major? Kinga ni ba ƙaramin yaro bane, ki dena mini wasa da hankali, ina ta binki amma kina mini wasa da hankali?"

Tace "bakomai"

A hankali ya saki haɓarta yace "muje mota, in baki wayarki, sai muje in ga gidan naku".

"Za'ai mini faɗa a gida"

"Ba za'ai miki faɗa ba, tashi muje".

Gaba ɗaya Abra tsoron sa take ji, duk da tayi mamakin yadda yake Magana yanzu kamar ba shi ba.
Haka ya sata gaba, zuwa cikin mota, a motar ya bata wayarta.

Har bakin layinsu ya kaita, ya kalleta yace "Ranar Saturday zan zo insha Allah, ki shirya karɓa ta"

Ba tace Komai ba, ta fara ƙoƙarin buɗe motar ta fita.

"Wai ke ba ki iya godiya bane? Ko nace na sallameki ne?"

"Nagode" ta faɗa tana tsoron kar wani ya ganta, dan ma motar tint ce.

Yace "Well, a sauka lafiya Angel" da sauri ta waiwayo tana kallonsa.

"In baki gama kallon nawa ba, sai in juyo" ba shiri ta buɗe motar ta fice, tana waige-waige kar taje wani ya ganta.




Ihsan ce tai wani ɗan ihu tace "Janna, Baby kunga Mutumin nan ya rikice, wai Zai zo ya sameni, ko nawane zai sai videon in goge shi".

Baby tayi dariya tace "A siyar masa a farashi mai tsada, sannan ki goge amma muna nan da shi ai, zai gane kuskuren sa, duk da ya saki kuɗi, da ba'ai haka ba, yanzu mu dai zamu fita, ki janyo shi nan, ya zo ki tatse mana shi.

Haka suka cigaba da shewa, suna shawarwarin nawa zasu tatse shi.

Suka shirya tsaf suka tafi nasu guri, suka bar Ihsan kawai tana jiran zuwan Yallaɓai.

Su Janna basu koma ba sai bayan la'asar daga nasu gantali, Sai dai abunda suka gani ne ya girgiza su, cikin tashin hankali Janna ta ƙwala ihu, gawar Ihsan ce kwance a cikin jini!





Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423  Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750.
[10/1, 2:40 PM] Abk: jiki a sanyaye ta koma ɗakimta, tana zuwa ta zauna a bakin gado cikin confuse, kanta ya kulle gabaɗaya ta rasa tunanin ma me za ta yi. Salman kuma? Girgiza kai ta yi cikin sauri tare da faɗin. "Impossible! Faris ba zai taɓa mini wannan wasan ba, amma ko ma wanene ya san ni sosai." Latsa wayarta ta yi ta ƙura wa last message ɗinsa ido, kamar ta yi reply sai ta fasa ta ajiye wayar ta kwanta tare da lumshe idanunta.

A hankali ya turo ƙofar ɗakin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, bai jira amsarta ba ya ce. "Angel me ya faru ne?" Buɗe idonta ta yi tare da tura baki ba ta ce komai ba. Idanunsa a cikin nata ya ce. "Ko shagwaɓar ce ta motsa?" Harararar shi ta yi, ɗan murmushi ya yi ya ce. "Mami ce ta ce na kira ki." Da sauri ta tashi zaune ta ce. "Ni kuma?" Ya ce. "Eh, girki za ki ɗora." Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa suka fice tare.

Zaune take akan ɗaya daga cikin royal chair ɗin dake parlour'n tana latsa wayarta, ta ci kwalliya cikin wani tsadadden farin less, idan ba faɗa maka aka yi ba za ka ce ta haifi Meenal ba saboda gayunta. Ɗaya daga cikin masu aikin gidan mai suna Asabe ce ta fito daga kitchen hannunta riƙe da plate, cikin sauri take tafiya har ta ƙaraso ta zube a gaban Hajiya.

"Ranki ya daɗe Barka da yamma, ga wainar nan na kammala." Asabe ta yi maganar cikin ƙanƙan da kai.

Wani wulaƙantaccen kallo ta ɗago ta wurga mata, cikin izza tamkar wata sarauniya ta ce. "Ubanki na ce ki dafa ne tun ɗazu ba ki gama ba sai yanzu?" Cikin kyarmar jiki Asabe ta ce. "Ki yi hak'uri Hajiya Saudat."

"Dalla Malama tashi daga gabana, kafin ki kashe ni da warin ƙashi, Idiot kawai." Ta faɗa mata haka cikin tsawa.

Ko gama rufe baki ba ta yi ba Asabe ta miƙe jiki a saɓule ta bar parlour'n.

Ajiye wayar ta yi ta miƙe ta ɗauki plate ɗin ta haye upstairs. Meenal tana kwance akan gadonta na alfarma suna chatting da Usman Mahaifiyarta ta shigo ɗakin. Ɓata fuska Meenal ta yi ta ce. "Mommy sai yanzu?"

"Sorry Daughter, tashi ki ci, ke ma da tsifa kike wallahi, duk abubuwan da ke gidan nan amma ki ce sai wata wainar fulawa za ki ci?"

A shagwaɓe ta ce. "Ita kawai nake sha'awa ne Momy."

"Ai gata nan." Hajiya ta faɗi haka tana ajiye plate ɗin akan bedside drawer, sannan ta juya ta fita ta koma ƙasa.

Zamanta babu jimawa wani mai aiki a gidan ya shigo parlour'n, cikin respect ya gaishe ta, a wulaƙance ta amsa masa cikin yatsina fuska, sanar mata ya yi tana da baƙi.

"Maza ne ko Mata?" Ta tambaya kamar ba ta san magana.

"Mata ne." Ya amsa mata.

Da hannu ta yi masa alamar ya shigo da su.

Idanunta akan ƙofa bayan fitar Ilya ta ga waɗanda ba ta yi tsammani ba sun shigo, miƙewa tsaye ta yi da sauri cikin shouting ta ce. "What! Su waye waɗannan a cikin parlour na?" Iliya da ya yi musu jagora ya ce. "Su ne baƙin Hajiy...." Bai ƙarasa ba ta dakatar da shi cikin tsawa da faɗin. "Shut up! Wannan abubuwan za ka shigo mini da su har cikin parlour? Ubanwa ma ya ba su damar shigowa gidan nan har suka ƙetare main Parlor su shigo mini nan?"

Kansa a ƙasa yana sosa kai ya ce. "Am Haji..."

"Hajiya me? ashe ba ka da hankali Ilya ban sani ba? Tunda kake a gidan nan ka taɓa ganin mutane irin waɗannan sun zo gurina? Ko a bakin gate ɗin gidana ka taɓa ganin talaka yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login