Showing 99001 words to 102000 words out of 231718 words

Chapter 34 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14817

ta tashi zaune, ta riƙo hannayensa a cikin nata, muryarta na rawa ta ce "Please Faris, dan Allah kar ka tafi ka barni, I can't survive without you, Faris kai kaɗai ne nake da shi a matsayin ɗan uwa, bana son kayi nisa da ni Please Faris".

Shiru Salman yayi, ya ƙi Magana.

Hannunta ta saƙalo a wuyansa tana kuka, "Talk mana Faris, please talk Brother"

Kasa magana yayi, sai ɗora fuskarsa akan tata, suna iya jin numfashin juna, a hankali hawaye ya fara zuba daga idanunsa, Abra tana masa so na 'yan uwanta ka, shi kuma yana mata so irin na Aure".

"Faris talk" ta kuma Maganar tana sake maƙalƙalo shi, wanda hakan ya jefa Faris ɗin cikin wani mawuyacin hali.

Ba zato ba tsammani Farisa ya shammaceta, ya haɗe bakinsa da nata, jikin Abra ya hau rawa, saboda yadda taji abun ba tsammani, ga rashin sabo, sai dai tana jin yadda jikinta ke karɓar saƙonsa.
Sosai idonsa ya rufe, yana shafa gashin kanta.

Da sauri Abra ta farga, tare da tuna Faris ne fa ƙaninta, ture shi tayi da sauri tana mai da numfashi.

A hankali Salman ya ce "Am sorry Please, zanje reception, kan Mami ta dawo".

"In ka je gida, ka taho mini da wayata Please".

"Ok" shine abun da ya faɗa ya bar ɗakin.



Meenal ce zaune a wani katafaren Joint, ta kammala cin abinci, ta tashi tana niyyar tafiya.
"Hi beauty" ba tare da sanin da wa ake ba, ta waigo domin taga waye.

Wani kyakykyawan matashi ne a tsaye a bayanta, yana murmushi.

Ya kuma cewa "Tun da kika shigo gurin nan, nake jiranki ki kammala kar in takura miki".

"Ok what happens?" Ta tambayeshi cikin iyayi.

"Wow, beb you are so beautiful fa" yayi Maganar yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa. Yadda duk wata surar jikinta a bayyane take, cikin doguwar rigar jikinta.

"Anyway, if you have nothing to say, i have something to do".
Ya ce "Well, ko zanyi dropping ɗinki, a in da zaki?".

Car key ɗin hannunta ta ɗaga masa, alamar da motar ta tazo.

Yayi murmushi tare da gyara tsayuwarsa ya ce "Can i have your number please?".

Ba musu Meenal ta bashi lambar wayarta, saboda ita kanta ya burgeta, ya haɗu gayen. Suka yi musayar lambar waya, sannan ta wuce ta tafi.

A yau ne aka fara sauraran ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar a kan General Ibrahim mai retire, tare da wasu tsofaffin manyan mutane da suka riƙe maƙamai a ƙasa, da wasu daga cikin jami'an tsaro, da manyan 'yan ta'adda a gaban kotu, da tuhume-tuhume daban-daban, akan haɗin baki, tare da yiwa ƙasa zagon ƙasa akan harkar tsaro, ga cin hanci da kisan kai da ake zargin General Ibrahim mai retire.
An gabatar da shedu da hujjoji, da aka fara gudanar da shari'a. Ba yadda Manyan lawyoyi ba suyi ba masu kare su General Ibrahim, akan a bada belin su, amma lawyoyin gwamnati suka yi suka, Alƙali ya hana ba da su beli.



Salman yana tafe a hanya wayar Abra sai vibrating take, saƙonni suna shigowa.
'Unknown' ya maimaita ko waye kuma unkown oho mata, sai kuma Adnan da ke ta kiran wayarta ba ƙaƙƙautawa.
A fusace Salman ya ɗaga wayar ya ce "Dan Allah malam ka tsahirta haka da kiran wayar nan, tana Asibiti ba lafiya Malam".

Adnan yayi murmushi ya ce "Matata babu Lafiya amma a kasa gaya mini Faris"

"Ai ka bari a ɗaura Auren, kafin ka kirata matarka, kuma kar ka sake kiran wayar nan yanzu".

Adnan yayi murmushi yana jujjuya maganar Salman, ya kasa gane meyasa yaron nan baya ƙaunarsa.

Likita ya ce ba zai sallami Abra ba, saboda jininta yana hawa yana sauka.

Salman ya je Asibiti ya tarar da Abra tana bacci, ya ƙura mata ido, hawayensa na ɗiga a kan fuskar Abra, ya durƙusa ya sumbaci goshinta, ya ajiye mata wayarta a gefen pillown ta, har ya kai ƙofa ya tsaya ya waiwayo ya kalli yadda take baccinta Hankali kwance. Ya juya ya fice.

Abbi ya biya duk bills ɗin da Abar taci, Ba yadda Mami ba tayi ba, a kan a sallami Abra a daren amma abu ya gagara, kuma ga Abbi na nan ba damar tace ba zata kwana a gurin Abra ba.

Sai cikin dare Abra ta sake farkawa daga baccin da takeyi, tayi alwala tayi sallar da ke kanta.

Mami nata baccinta, Abra ta ɗau wayarta, ta shiga duba saƙonnin da ke wayar tata.

Saƙonnin unknown ba adadi a wayar nan, yana bata tabbacin kowane lokaci zai iya bayyana mata kansa.

Ajiyar zuciya tayi tai masa reply da "Is too late!!!".

Ta buɗe what's app ɗin ta, Adnan yayi mata messages kala-kala na soyayya da sannu. Murmushi tayi ba tare da tayi masa reply ba.

Lambar Salman ta nemo, ta kirashi ƙarfe biyu da rabi na dare.

Ba tsammani ta ji ya ɗaga wayar "Hello Angel"

"Na'am Bloody na, ba kayi bacci ba?"

"Na kasa bacci Angel".

"Faris why?"

"Nothing, ya jikin naki?"

"Naji sauƙi Alhamdilillah, ina ga da safe in Allah ya kaimu za'a sallameni, kaina ne kawai yake ta ciwo, kamar zai fashe".

"Sorry, ki kwanta kiyi bacci kar kan ya cigaba da ciwo"


"Faris, ya batun tafiyar nan, ai ka fasa ko? Abbi ya janye tafiyar ta ka ko?"

Ajiyar zuciya yayi ya ce "Kiyi bacci Angel".

"Faris ka gaya mini mana, hankalina ya kasa kwanciya, kuma ban sake ganin Abbin ba".

"Zamuyi magana da safe insha Allah, sleep well Dear" ya katse wayar.

Abra tayi shiru tana tunani kala-kala a zuciyarta.


Wayewar gari ma Abra da matsanancin ciwon kai ta tashi, sai kuka take yi, hakan ya sake tilasta wa likitoci yi mata allurar bacci, saboda daren sam ba tayi bacci ba, ta kwana kukan ciwon kai.

Da safe da Salman ya dawo duba Abra, bacci take yi, dan haka ya juya ya koma gida.
A harabar Asibitin ya ci karo da Adnan, ƙarfe tara da rabi na safe, har Adnan ya dira a garin Kano.
Wani irin mugun kallo Salman ya yiwa Adnan, ji yake tamkar ya shaƙe Adnan ya huta.

Adnan kuwa murmushi yayi ya ce "Faris our lil Brother, ya Jikin matar tawa? Ina fatan tana samun sauƙi, na kasa samun nutsuwa gaba ɗaya, a wani ɗakin take ne? Naje can gida aka ce mini kuna nan Asibitin".

"Idan ka shiga idanunka sa gane maka" Amsar da Faris ya iya bashi kenan ya nufi mota, Adnan bin Faris yayi da kallo yana murmushi.

Adnan Ya shiga ya tambaya a reception, aka gaya masa lambar ɗakin da Abra take, yana zuwa ya tarar da Mami a zaune tana waya.

Cikin girmamawa suka gaisa da Mami, yayi mata ya mai jiki, ta amsa masa da sauƙi, daga nan ta tashi ta basu guri.

Gaban gadon Abra yaje ya tsaya, ya zubawa kyakywar fuskarta ido, da uban gashinta da yake baje a kan pillown da take kai.
A hankali ya kai hannu ya shafa gashin na ta, dan tabattar da ko nata ne, ba ƙari bane gashin Abra ne, fal da shi akan pillow. A hankali ya kai hannunsa inda hearing aid ɗin ta yake a kunnenta.
A hankali yake taɓa aid ɗin yana tunanin, wannan meye amfaninsa a kunnenta?.
Ya koma ya kulle ƙofar ɗakin, ya dawo ya zauna a gefen gadon, ya ɗago Abra daga kwanciyar da take.

"Mhmm Faris" ta faɗa cikin shagwaɓa.

"Ba Faris bane Baby, Adnan ne"

A hankali ta buɗe idonta akan Adnan.
Zaro ido tayi, ta tashi daga jikinsa tana faɗin "Yaushe ka zo?".

"Yanzun nan, na kasa samun nutsuwa jiya na kira wayarki, Faris ya ɗaga yace mink baki da lafiya, meyake damunki ne?"

Kawai Abra ta fashe da kuka.

"Angel menene kuma?".

"Wai Abbi ne ya ce sai Faris ya tafi China karatu".

"To shine me?".

"Dan me za'a ɗauke mini shi? Wa zan dinga gani, na saba da Faris".

"Ni ɗin kuma fa?" Adnan yayi Maganar in a serious tone.

"Kai mijina ne, Faris kuma jinina ne, the only Brother i have, ni ji nake Kamar in fasa Auren nan".

Ɗan shiru Adnan yayi ya ce "Baby kin dena sona kenan?".

"A'a ina sonka, amma bana son in rasa Faris ɗina".


"To shikenan, ki kwantar da hankalinki, kin ji Babyna ba in da Faris za shi ya barki, ai ni in cewa ki kai a gidana a ginawa Faris ɗaki, ku tare a tare ba matsala" yayi Maganar cikin sigar rarrashi.

Adnan da shi aka wuni a Asibiti, Ana jinya, Su Ammi na ta yabawa kyawu da nutsuwar Adnan, a matsayin siriki.


Abra sai tambaya take ina Faris, amma ba wanda ya bata wata gamshashiyar amsa, ta kira wayarsa amma shiru ba ta shiga.

Bayan la'asar aka sallami Abra, Sai da Adnan ya rakasu har gida, wanda a nan ne Abbi ya sanar masa da larurar Abra, na rashin ji sosai sai da hearin aid, da kuma halin da take shiga idan ta shiga firgici da damuwa.
Adnan ya nunawa Abbi babu matsala, A nan Adnan ya sanarwa da Abbi Kaduna zai kai Abra, a nan Abbi ya ce bai amince ba, ba ta da kowa a Kaduna, kuma ga batun karatunta, kasancewar su Shureim ma suna gidan, su suka yi tausar Abbi, sun nuna masa aure ba in da baya kai mace, kuma sai a mata transfer, ko ta sake fresh tun da karatun ba nisa tayi ba.

Ƙarfe takwas na dare, Abra ta ɗaga hankalin kowa a gidan, a kan ina Faris ɗinta, ta je ɗakinsa baya nan.

Abba ya zaunar da Abra ya ce "Abra, ni mahaifinku ne, ba zamu taɓa zaɓa muku abunda zai cutar da ku ba, Faris jirginsa ya tashi ƙarfe sha biyu na rana, yanzu haka ya kusa China!!!

LITTAFIN RUƊI NE ₦300 NE
Via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750
[10/6, 5:01 PM] Abk: Kallon Abbi kawai Abra take yi kamar ba ta fahimci me ya ce ba, idanunta duka a waje cikin kuka ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, why Abbi, me ya sa za ku nesanta ni da jinin jikina, Abbi dan Allah ka dawo da shi, ba zan iya rayuwa babu Salman a kusa da ni ba." Cikin rarrashi Abbi ya ce. "I'm sorry Daughter, na san dole ki ji babu daɗi, amma haƙuri zaki yi, ni ma ba son raina ba ne hakan." Kuka ta fashe da shi tare da faɗin. "Amma Abbi me ya sa ya tafi ba mu yi sallama ba? Me ya sa bai zo na gan shi ba?"

"Ya zo da safe kina bacci." Abbi ya yi maganar tare da kamo hannunta, za ta kuma magana ya hana ta da faɗin. "Just pray for him Daughter, shi ne kawai soyayyar da zaki nuna masa, ki bar wannan koke-koken kin ga baki da lafiya, kar ki ƙarawa kanki wani ciwon." Numfashi ta sauke mai zafi tare da miƙewa ba tare da ta ce komai ba, ɗakinta ta shiga ta faɗa kan gado ta shiga raira kuka mai tsuma zuciya. 'Shikenan Salman ya tafi? Ya yi nesa da ganin ta? Anya za ta iya rayuwa mai tsayi ba tare da Salman ba? Faris ɗinta mai share mata hawaye akodayaushe, mai fifita farincikinta akan nasa. Wata irin kewar shi ta ji tana nuƙurƙusar zuciyarta.


Kuka sosai Abra ta yi akan tafiyar Salman, tunda ta shiga ɗaki ba ta fito ba har bayan isha'i, Sallah ce kawai take ɗaga ta, ita ma da ƙyar take iya tashi ta yi saboda wani azababben ciwon kai da yake damun ta, ji take kamar kan nata zai tsage gida biyu. Tana jin wayarta na ta vibrate amma ba ta kula ba, duk da ta san Adnan ne yake kiran ta.


Hajiya Na'ima ce zaune a gefen Khamal cikin farinciki, zuciyarta fess take jin ta yau, tamkar wadda aka yiwa bushara da wani babban albishir. Kallon ta Khamal ya yi na wasu sakanni cikin murmurshi ya ce. "Wai yau nishaɗin me kike yi ne Wifey? Na ga kamar ma ko kewar ɗan gaban goshin naki ba kya yi?" Yalwataccen murmushi ta saki ta ce. "Ai ko da bakina na faɗa maka ban yi kewar Salman ba na san ba za ka yarda ba My Man, kawai ina ɓoyewa ne saboda ban san na damu kaina akan abin da ya zama dole, nishaɗin da nake yi kuma na kasancewa tare da kai ne Mijina." Ta ƙarashe maganar tare da kashe masa ido. Murmushi Khamal ya yi ya ce. "Bayan wannan kamar akwai wani abun a ranki, ki faɗa mini mana sai na taya ki farincikin."

"Babu komai, idan ma da akwai bai wuce na zumuɗin ganin ranar Auren Daughter ba."

"Uhm, saboda kin kusa zama surika ko?"

"Suruka kuma ta nawa? sai dai ka ce saboda na kusa zama granny."


Murmurshi suka yi a tare, duban time Abbi ya yi ya ce. "Har 9 ta kusa amma Daughter ba ta fito ba? Allah ya sa ba jikin nata ba ne?" Taɓe baki Na'ima ta yi ta ce. "Ko dai sakarcin nata ne ya motsa ba, na san yanzu tana can tana ta aikin kuka saboda tafiyar Salman."


"Kin ga lefinta dan ta damu? Ni kaina sai bayan ya tafin kuma jikina ya yi sanyi, na san tsananin shaƙuwar yaran nan, ba ƙaramar damuwa za su shiga da rashin juna ba."

"Ai gara su saba, tunda ko ba su rabu ba yanzu za su rabu lokacin da za ta yi aure, bari na je na dubo ta." Na'ima ta faɗi haka tare da miƙewa.


"Abra! Abra."

A hankali ta buɗe idanunta da suka gaji da tsiyayar da hawaye tare da juya kanta da ƙyar ta dubi Nai'ma. Cikin raunin murya ta ce. "Mami Faris...."

"Shiiiii! kar ki ishe ni da wani zancen Faris, ki tashi ki ci abinci ki sha magungunanki."


"Bakina ɗaci Mami, ba zan iya cin komai ba, Faris kawai nake son gani, dan Allah Mami ki lallaɓa Abbi ya dawo mini da ɗan'uwana kusa da ni." Ta yi maganar wasu hawaye masu ɗumi na kwaranyo daga cikin idonta. Cikin takaici Mami ta ce. "Sai dai nai uban lallaɓa Abbi, yarinya sai masifar tsiya, ina murna hankalina ya fara kwanciya kina ƙoƙarin tayar mini da shi, saboda wannan damuwar da kika yi har ya fara cewa jikinsa ya yi sanyi da ma bai tura shi karatun ba, nan gaba kuma na san zai iya cewa zai dawo da shi, tunda ba ya son ganin ki cikin damuwa. Wallahi idan baki bar koke-koken banzan nan ba sai na saɓar miki, ki tashi ki je ki wanke fuskarki mu tafi parlour ki ci abinci, saura kuma idan kin je ki cigaba da nuna wannan damuwar, ni da ke ne."


Cikin dauriya Abra ta tashi ta shiga toilet, Na'ima ta bi ta da harara. Sai da ta sake yin wani kukan sannan wanke fuskarta ta fito.


Sosai Abbi ya dinga lallaɓa Abra tare da ba ta baki, dan duk da ta ɓoye damurta amma kallo ɗaya ya yi mata ya san tana cikin damuwa. Ya sanar mata Salman ya kira ya ce ya sauka lafiya, lokacin tana ɗaki. Da sauri ta ce. "Abbi ba ni numbern da ya kira in kira shi."

"Ba numbernsa ba ce ara ya yi, sai gobe idan Allah ya kai mu zai siya nasa sim ɗin, na san kuma ke zai fara kira da shi." Abbi ya ba ta amsa cikin murmurshi.


Murmushin yaƙe ta yi ba ta ce komai ba ta cigaba da cin abincin dake gabanta, wanda take jin shi tamkar maɗaciya a bakinta, da ƙyar take iya taunawa ta haɗiye. Kallon seat ɗin da Salman yake yawan zama ta yi idan za su ci abinci, ƙwalla ce ta tarar mata a ido, ƙoƙarin mayar da ita ta yi tare da lumshe idanunta, can ƙasan mak'oshi ta ce. "I'm missing you Bloody, yaushe zaka dawo gare ni?"





Adnan ne zaune akan two seater a guest parlour'n gidan Fayyad, hankalinsa gabaɗaya yana kan wayarsa yana tura wa Abra text, na k'auna da irin missing ɗinta da ya yi daga yamma zuwa dare da bai ji muryarta ba, sai tarin addu'oi da fatan samun lafiya. Fayyad dake kallon shi ya yi murmurshi ya ce. "Thank God, yau Allah ya nuna mini wannan ranar, kamar a mafarki sai ga Adnan a cikin soyayya dumu-dumu." Murmurshi Adnan ya yi bai ce komai ba.

Gyara zama Fayyad ya yi ya ce. "Ya kamata zuwa yanzu a ce mun fara shirye-shiryen abubuwan da za a yi a bikin nan fa, na ga kai ta soyayyar ka kawai kake, kuma ga lokaci yana ta motsowa."

"Shirye-shirye like how?"

"Su dinner da sauransu."

"No need, ɗaurin Aure kawai za a yi a kawo mini matata."

Hararar shi Fayyad ya yi ya ce. "Wallahi ba ka isa ba, dole mu warwasa." With serious Adnan ya ce. "Sai dai ku warwasa ku kaɗai, amma babu wani abu da zan yi, kawai matata ta yi kwalliya a gama kalle mini ita, a yi ta mata pictures ana ɗorawa a media kowane kare da biri ya gani, ba zai yiyu ba gaskiya." Murmurshi Fayyad ya yi ya ce. "Mayar da wuƙar Baban kishi, mu duk da aka kalle namu matan ai ba ma son su." Ɗage kafaɗa Adnan ya yi bai kuma magana ba.



Sai after 10 na dare sannan Abra ta kira Adnan, time ɗin ya koma masaukinsa fitowar shi kenan daga wanka ya ji wayarsa na ƙara, with special sound ɗin da ya saka wa Numbern Abra. Cike da zaƙuwa da son jin muryarta ya ɗaga kiran.

"Matata!" Ya faɗa cikin tsantsar k'auna.

A hankali ta ce. "Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "I missed you Baby, ya jikin naki?"

"Alhamdulillah, na ji sauƙi."

"Are You sure?"

Gyaɗa masa kai kawai ta yi, saboda da ƙyar take iya magana.


"Ya na ji muryarki haka kuma? Ko dai jikin ne Sweetheart?" Ya yi maganar cikin kulawa.

Ya sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi, hakan ya sa ta fashe masa da kuka. A rud'e ya ce. "Subhanallahi, Angel what happened? Are you okay?" Cikin kuka ta ce. "Faris ya tafi China."

"Oh My God, sorry Angel, yaushe ya tafi?"

"Ɗazu, kuma ko sallama ba mu yi ba."

Cikin rarrashi ya ce. "Stop crying please My love, ai dan ya yafi China ba yana nufin kun rabu ba ne har abada, tunda ga waya duk time ɗin da kike so zaki yi magana da shi. Please ki bar damun kanki, ko so kike in kasa bacci?"

"A'a."

"To ki yi shiru, na yi miki alƙawari bayan mun yi aure da kaina zan kai ki ki ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login