Showing 126001 words to 129000 words out of 231718 words
Chapter 43 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
da ya bar Abra, a nan ya tarar da ita, ko motsi ba ta yi daga gurin ba, ya kalli agogon da ke ɗakin, tun takwas da rabi ya fita, yanzu ƙarfe uku da kwata amma tana kwance a gurin a ƙasa.
Durƙusawa yayi, ya ɗauke ta, ya shimfiɗeta a kan gadonta, ya kalli yadda gashin kanta ya baje a gurin, gashi idan tana bacci wani irin kyau take ƙara yi, ya ɗan taɓe baki, tare da furta "kyan ɗan maciji, mahaifinki shine kyau, kuma ya haifi kyau amma sai baƙar zuciya da muguwar aniya".
Ya ɗauko ruwa mai sanyi a fridge, ya ɗagota ya dinga zuba mata ruwan nan a fuska, ko tsoron ya shige mata hanci ba yayi. Ganin ko motsi ba yi ba, ya sanya ya cire mata rigar jikinta, ya buɗe robar ruwa yana zuba mata, a gigice ta motsa tare da wata irin ajiyar zuciya, cikin muryar fita hayyaci ta ce "Faris!"
"Dalla buɗe idonki malama, ba Mayen naki bane nine nan"
Sauke numfashi take, tana kallon Adnan tare da jin ina ma mafarki take yi ba gaske ba.
Sai yanzu ta lura da babu riga a jikinta, da sauri ta janyo rigarta tana rufe jikinta, tsaki yayi ya ce "Malama ki tashi ki je ki dafa mini abun da zan ci, ina jin yunawa ba zan iya cin abinci a waje ba"
"Baby kaina ciwo yake, jiri nake ji" ta faɗa a raunane.
"I don't care, ki tashi kawai" ya ƙarasa maganar cikin tsawa.
Abra ta sauko a hankali daga kan gadon, tana dafa bango ta bar ɗakin.
A hankali take gudanar da komai a kitchen ɗin saboda ji take tamkar zata faɗi ƙasa. Allah sarki, da a gida ne duk da faɗan Mami, idan ta shiga wannan yanayin Mamin ma na ɗaga mata ƙafa, ko ba zata je kanta ba, amma tana ƙyaleta ta huta, her Faris kuwa yana kusa da ita yana sannu, da ta motsa zai fara "me kike so?"
Take maganganun da Adnan ya gaya mata da safe suka faɗo ranta, ta tuna ko salloli ba tayi ba, tuno maganganun nasa tayi, kamar saukar wuta a kanta, cikin rashin sani, da firgici ta ture tukunyar da ke kan gas, aikuwa ruwan zafin ya zubo mata a ƙafa.
Wani uban ihu ta saki, wanda ya sanya Adnan tasowa da sauri, ya shigo kitchen ɗin, ya kalli yadda tunkuyar ta faɗi ƙasa, ruwan zafi ya zube mata a jiki da ƙafarta, sauran ya malale a kitchen ɗin.
"Wai ke wace irin Yarinya ce mara hankali da nutsuwa? Mai yasa baki da tunani ne? Ko da yake babanki ma haka yake, ba shi da lissafi balle tunani, Wallahi kika kuma yi mini ihu haka a cikin gida sai na tattakaki" yayi maganar yana huci ya juya ya bar kitchen ɗin.
Toshe bakinta Abra tayi, ta dinga wani irin kuka, mai tsuma zuciya, a hankali tana ɗingisa ƙafarta da ke mata wani irin azabar zugi, ta fito falo, sai dai ta kasa cigaba da tafiya saboda yadda ƙafar tayi jawur, take mata wani irin zafi.
Adnan ne yake waya a falon "Wallahi Abbi duk lafiyar mu ƙalau Alhamdilillah".
"Adnan lafiya kuwa har yanzu wayar Abra ba ta shiga, hankalin mahaifiyarta ya tashi da nasu Ammi, ta ce tun da aka kawota ba su kuma waya ba, nima sai dai muyi waya da kai amma ba'a samunta?".
Adnan ya ce "Abbi wayar nake so na canza mata, ban zauna bane abubuwa sun yi mini yawa sosai, amma a satin nan nake sa ran za'a kawo mata".
Abbi ya ce "Ok, shikenan haɗani da ita dan Allah".
Adnan ya kalli in da Abra ke zaune, ta zubo masa idanu tana jiran ya bata waya, amma sai ya ce "Abbi bacci take yi".
"Bacci kuma da la'asar haka?".
"Eh ba ta jin daɗi ne, an mata allurai".
Abbi ya ce "subhanallah, amma shine baka gaya mini ba? Mai ya sameta?".
Adnan ya ce "Abbi ɗan menstrual pain ne, kuma an mata allura ta samu releif".
"To shikenan, a kula da ita please, in an jima zan kuma kira inji jikin nata".
Adnan na gama wayar, ya kashe wayar gaba ɗaya ya ajiyeye a gefensa ya cigaba da kallo.
Wani sabon kukan ta sake fashewa da shi, mai tsuma zuciya da nuna tsantsar damuwa, amma Adnan ko a jikinsa, ƙarshe ma sai tashi yayi ya bar mata falon gaba ɗaya.
Da ƙyar ta ja jikinta ta koma ɗakinta, tayi sallolin da suke kanta, ta nemi guri ta zauna ta takure, tana sake jujjuya maganganun Adnan, da ƙoƙarin gano gaskiyar lamari, sai dai babu yadda za'a yi ta san gaskiyar lamari, in dai bata bakin wani taji a gidan su ba, wani irin abu mai ɗaci ya zo ya tokare mata tun daga ƙirjinta zuwa wuyanta da kan harshenta, ƙirjin yayi mata wani irin nauyi, da ƙyar take iya numfarfashi saboda tsananin damuwa.
Daf da magariba ta kuma jin fitar Adnan, wata irin yunwa ce ta ke sassaƙarta, haka ta kuma fitowa ta tafi kitchen, ta fara ƙoƙarin ɗora abincin dare.
Abbi yayi mamakin yadda yake cigaba da kiran wayar Adnan, amma shiru ba ta shiga, haka Salman ma kusan wata guda kenan, ba'aji daga gareshi ba.
Gefe Na'ima ta uzzurawa Abbi da kira, da cewar ba fa ta samun yaran nan a waya gaba ɗaya, mussaman Salman, da ta tsorata da lamarin Salman sosai da sosai, dan alamu sun fara nuna cewar abun da ya bar mata wasiƙa na shirin faruwa, gashi babu damar ta sanar da Major abun da ya bar mata a wasiƙa.
Da daddare Adnan ya dawo, ya tarar Abra tayi girki, ba kunya ya zauna yana cin Abincin sa, har Abra ta fara shirin kwanciya, amma ta fasa ta fito falo, tana ɗingisa ƙafarta.
Kusa da Adnan taje ta zauna, bai ko kalli in da take ba, ya cigaba da abun da yake yi.
"Baby" ta faɗa a hankali.
Ya amsa mata da Angel, ji tayi sunan ya tsirga mata kamar yau ya fara gaya mata, duk da suna ne da Salman yake kiranta da shi, amma idan Adnan ya faɗa jin sunan take na musamman a bakin sa.
"Baby, dan Allah dan Annabi, tun da kace ba Abbi ne mahaifina ba, ka gaya mini waye mahaifina ka nuna mini shi".
Wata makirar dariya Adnan yayi ya ce "Ashe ma ba fansar zan ɗauka ba, idan har zan haɗa ki da shi, ai Abra ke da mahaifinki ya sanya ki a idanunsa sai a lahira, dan nayi ƙoƙarin toshe duk wata kafa da zata sada ki da shi har Abada"
"Dan Allah kar ka yi mini haka, ka yafe masa koma me yayi maka, dan girman Allah ka haɗani da shi ko sau ɗaya ne, ba dan halina ba".
"Tashi ki bani guri, kafin in tashi in ƙwallo dake a gurin nan, zancen mahaifinki kawai in ana yi ji nake tsanarsa da duk wani abu da ya raɓe shi yana sake ninkuwa a zuciyata, ki tashi ki bani guri kafin in miki illa, 'yar zuriyar masu baƙin hali"
Abra ta miƙe, maganganun Adnan na mata amsa kuwwa a kunnuwanta 'yar zuriyar masu baƙin hali! Gani take tamkar an canza mata Adnan ɗin ta, da ta san haka Aure yake, da har gaban abada ba zata yi shi ba.
Ta koma ɗakinta, ta takure a kan gado, tana ambaton sunan Allah, ko ta samu sassauci a zuciyarta.
Tana nan zaune a kan gado, fitilar ɗakinta a kashe, Adnan ya shigo ɗakin, yana shigowa gabanta ya faɗi, dan ba ta san da wacce ya zo ba a wannan tsohon daren.
Ba kunya ta ga ya hawo kan gadonta, ba tsoron Allah, ya janyota jikinsa da ƙarfi, ba wani tunani ko tausayawa ya nemi haƙƙinsa na Aure, ya sauke mata duk wata gajiyarsa ta wunin ranar kamar wata Akuya ba ɗan Adam ba, kuma ya tashi ya shiga toilet ɗinta, ya tsarkake jikinsa ya fice ya bar ta ko kallonta bai yi ba.
Al'amarin Adnan ya dai na bawa Abra mamaki, sai dai tsoro babu alamar rahama ko tausayawa a tare da shi, zuciyarsa a dake take, ta bushe da rashin imani.
Adnan kam, baccinsa yayi mai daɗi ya bar Abra da matsanancin ciwon jiki, duk lokacin da zai kasance da ita, yana tsintar kansa cikin tsantsar nishaɗi da jinsa free from any sadness, halin da zata shiga kuwa sam baya damunsa.
GY BULAMA HOSPITAL AND MATERNITY.
Nurse Jamila ce tsaye a gefen Bulama, yana duba wani scaning da ta kawo masa na wata mata, rufe file ɗin gabansa yayi ya kalli Nurse Jamila ya ce "Yi min magana da mijin matar nan, aiki za mu yi mata"
Ɗan waro idanu ta yi ta ce "Doctor, na ga kamar scanic ɗin ya nuna bakomai, kamar peptic ulcer ne kawai, kuma kace aiki zaka yi mata"
"To doctor Jamila, mai Yakamata ayi?"
Shiru tayi, bayan tuna cewar ya hanata yi masa shishshigi a cikin lamarin aikinsa, ba ta kuma cewa komai ba ta fita ta kirawo mijin matar .
Nan Bulama ya din ga yi masa wani surkullen bayani irin na su na likitoci, yadda mutumin ba zai wani gane ba, ya ce mutumin ya je ya biya kuɗin aikin a shiga da ita da gaggawa.
Lamarin Adnan da muguntarsa ƙara gaba yake yi, dan yanzu duk lokacin da ya buƙaci Abra ko da dare ko rana, haka yake zuwar mata kansa tsaye.
Hakan ya ƙara jefa Abra cikin tsoro da firgici, ko muryar Adnan taji sai gabanta ya faɗi hankalinta ya tashi, ga tsananin damuwar rashin jin Muryar kowa daga gida dan ba ta da waya. Tana cikin wannan zullumin Dodon nata wato Adnan ya shigo, tana ganinsa jikinta ya hau rawa.
A kausashe ya ce "In Allah ya kaimu anjima, su Hajiya Mama za su zo, idan kin ga dama ki yi wani misbehaving ki ga yadda zan yi dake". Ba tace masa ci kanka ba, ya gama maganganunsa ya fice.
Kitchen ta shiga ta shirya girke girke, domin tarbar su Hajiya Mama, dan iyayen Adnan ba dai karamci ba.
Sai azahar sannan suka zo, Abra taji daɗin zuwansu, sai dai a kallon Farko da Maman ta yiwa Abra, ta ga yadda yarinyar ta ƙara ramewa, tai duhu.
Mama ba tace Komai ba, suka dinga hira da Abra, sai da zasu tafi sannan ta bi Abra ɗakinta ta kalleta tace "Abra, meke faruwa ne?"
"Mama me kika gani?".
"Abra alamu sun nuna akwai wata damuwa a ƙasa, menene ke faruwa?".
"Ai kamar Mama ta taɓo mata abun da yake mata ƙaiƙayi, ta fashe da kuka, sai da tayi mai isarta sannan Mama ta ce "gaya mini ina jinki"
Abra ta ce "Mama ni gida nake so, gida zan koma".
"Haba Abra, saboda me?"
"Bakomai, kawai gida nake son komawa"
Mama ta ce "kiyi haƙuri, haka Aure yake a hankali kowa yake sabawa, ke dai ki kwantar da hankalinki ki dinga ci kina ƙoshi". Ita Abra ma sam ba ta gane me Mama ke nufi ba.
Bayan sun fito daga ɗakin Abra sai ga Adnan ya dawo.
"Mama wai tafiya zaki yi ba tare da kin ganni ba, wato tunda kinga Angel shikenan"
"Eh shikenan Mana, kai ɗin da kusan kullum sai ka zo gida ka isheni, ai gara in zo in ga 'ya ta'
Adnan ya kwaɓe fuska ya ce "My Angel kin ƙwace mini Mama, gaskiya kishi nake, haka ake yi". Kallon Adnan take da mamaki, a gaban mutane yayi ta nuna mata kulawa, amma daga ita sai shi, yayi ta cuzguna mata.
Ya dage a kan Mama ba zata tafi yanzu ba, ƙanwar Mama da suka zo tare, wato Hajiya Bilki ta ce ita kam tafiya za ta yi, ta bar yara a gida.
Abra ta bawa Mama da Adnan guri dan su yi hira.
Mama ta kalli Adnan ta ce "My son, magana nake son mu yi"
Ya ɗan yi jimm, yayi zaton ko Abra ta gayawa Mama wani abu, ya maze ya ce "To Hajiya".
"Duk da bai kamata in maka katsalandan a lamarin Aurenka ba, amma ni uwa ce, kuma 'ya mace ce, yarinyar nan Abra, ta rame da yawa, na yi imani da Allah idan iyayenta suka ganta haka ba zasu ji daɗi ba, dan ba a haka suka baka 'yar su ba.
Kai kuma kalli yadda ka yi wata uwar ƙiba, kai tsaf da kai, na yi magana da ita, amma ba ta ce mini komai ba, sai kuka tana cewa ita gida.
A ɗan abin da na fuskanta, kana takura yarinyar nan Adnan".
"Mama takurawa kuma? Me nake mata? Ki tambayeta ni abin da nake mata".
Mama ta ce "Ƙaniyarka, ni zaka mayar ƙaramar yarinya, ai ka gane sarai me nake nufi" sai kuma ya kama sosa ƙeya yana ɗan basarwa.
"Ba ina nufin yi muku shishshigi bane, amma dan Allah a dinga ɗaga mata ƙafa, ramar ta yi yawa".
"To Hajiya" ya amsa cikin jin nauyi.
"Yawwa kirawo mini ita muyi sallama"
Adnan ya kira Abra dan suyi sallama da Mama, amma Abra ta fara kuka ta ce "Mama dan Allah zan biki".
"Abra kiyi haƙuri, na yi masa faɗa, ba yadda za'a yi da aurenki ki bar gidanki ki biyo ni".
"Haba Angel, ya kike haka kamar wata ƙaramar yarinya, me kike so in sai miki? Ku mu fita yawo yau" yayi Maganar yana rungumeta a jikinsa cike da kulawa.
Abar kuwa sororo tayi tana kallon Adnan, suka yiwa Mama sallama, har mota ta tafi.
Yana dawowa ya tarar da ita a falo, ta na ta gyarawa, ya zuba mata ido, tana ɗagowa suka haɗa ido, sai da ta sha jinin jikinta.
"Shi ne ki ka kawa mahaifiyata ƙarata ko?".
Ta shiga girgiza kai ta ce "Wallahi ban kai mata ƙararaka ba".
"Idan ma ƙarar ta wa ki ka kai mata, ko sani, ba yadda za a yi in sanya kuɗi na in Auroki in kasa karɓar hakkina na Aure, ba dan iya fansa kawai na Aureki ba, na Aureki ne dan ina da buƙatar yin hakan ne. Kuma duk in da baiwa take a ubangidanta yana da iko a kanta, dan haka ba zan fasa ba sai dai ki mutu. Kuma Wallahi ki ka bari wani ya san irin zaman da nake da ke, sai kin gane shayi ruwa ne"
Abra tayi shiru, tana sake jinjina azabar rashin imani irin na Adnan.
Ba ta karaya ba, ta bishi ɗakinsa, ta tarar yana ƙoƙarin shiga wanka, ya kalleta ya ce "Uban me kika biyo ni ki mini".
"Baby alfarma nake nema".
"Ina jin ki".
Ta ƙaraso gabansa ta durƙusa a kan gwiwowinta ta haɗa hannayenta ta ce "Idan kana son ganin Annabin tsira, ka bani wayata, ko ka haɗani da Abbi na a waya, dan girman Allah".
"Annabin tsira insha Allah zan ganshi, wayarki kuma ta tafi kenan, dan ba zan baki waya ki dinga Magana da Wannan mayen naki ba, Suleiman yake ko wa?"
"Dan Allah, ka taimaka magana nake son yi da Abbi na dan Allah" wayar Adnan ce ta fara ringing, ya ɗauka ya duba, yayi murmushin mugunta ya ce "Gaskiya wannan baban naki na riƙo yana ji da ke, dama shine babanki mahaifi, da kin ji daɗi".
Ya gyara tsayuwarsa ya ɗaga wayar, suka gaisa da Adnan.
Abbi ya ce "Adnan anya kuwa lafiya, yarinyar nan mahaifiyarta da kkanninta duk sun isheni ba'a samunta a waya, ni jikina yana bani kamar ba ta cikin farinciki, a weekend zan zo in ganta, kai kan ka wayarka ba ta shiga".
"Abbi Abra tana lafiya ƙalau fa, ga ta ma a kusa dani".
"Bani ita maza".
Ya miƙawa Abra wayar jiki na rawa ta karɓa "Hello Abbi na".
"Na'am Babyna, yaya akayi bana samun ki, kina lafiya kuwa?".
"Abbi, Abbina" tayi Maganar tana kuka.
"Ina jinki Abrana, mai yasa kike kuka? Meyafaru ni jikina gaba ɗaya ya gama bani babu lafiya" Abbi yayi Maganar a rikice.
"Abbi wai da gaske ba kai ne babana ba?"
Ras!!! Gaban Abbi ya faɗi, dan yaji maganar ta ta a bazata.
"Waye ya gaya miki wannan banzar Maganar?".
"Abbi dan Allah ka gaya mini, ba kai ka haifeni ba ko? Wai tsinto ni ka yi ka riƙeni".
"Abra waye ya gaya miki wannan maganar? Naima ce ko?" Abbi yayi Maganar cikin wata irin razananniyar tsawa.
Abra kasa magana ta yi, sai kuka.
Adnan ya fizge wayarsa ya ce "Abbi kaji dalilin da ya sanya na ƙwace wayarta, na kuma hanata wayata ku yi magana, ta isheni da koke koke, ban san a ina ta ji wannan maganar ba.
Ai Abbi bai ba shi amsa ba, ya katse kiran.
Adnan yayi murmushi ya ce "Ina fatan ko wannan rikicewar da Abbin naki yayi, ya isa ya tabbatar miki da ba shine ya haifeki ba, saboda kin gano sirrin da ya ɓoye duk ya rikice, tabbas yana miki so irin na 'ya da uba".
Abra ta ɗora hannunta a ka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku, waye babana? Dan girman Allah ka gaya mini wanene ya haifeni, suwaye iyayena" ta riƙe hannun Adnan tana Magana cikin kuka.
Shi ba halin da take ciki ne ya dame shi ba, sai yadda ƙamshin turarenta da yadda kwalliyarta suka yi turning ɗinsa on ne suka dame shi, kamar kullum yayi abun da Allah ya nufe shi da yi, duk da halin da Abra take ciki na damuwa da tashin hankali.
"Kaji tsoron Allah, ko tausayin halin da nake ciki baka ji? Buƙatarka ce kawai a gabanka" tai maganar tana kuka.
"Halin da kike ciki ke ya dama ba ni ba, dan haka damuwarki ba zata hana ni jin daɗin rayuwata ba.
Mami ta rasa sukuni balle mafita, gaba ɗaya gidan yayi mata faɗi, tana zaune tana ta jujjuya takardar da Salman ya bari, ta kira Anty Suwaiba ko zata samu mafita, bayan ta gama korawa Anty Suwaiba bayani, Anty Suwaiba ta jinjina kai ta ce "Taɓɗijan, shi Salman wannan wane irin hali ne? Daga wannan sai wannan, ki sanar da mahaifinsa kawai".
"Anty Suwaiba ta yaya zan sanar da mahaifinsa, bayan bai san na gayawa Salman ɗin cewar bani na haifi Abra ba?".
Anty Suwaiba ta ce "kin ga wannan maganar ba ta waya bace, kinga bana gida amma insha Allah wajen jibi zan shigo gidan naki".
'To shikenan, Allah ya kaimu"
Mami na gama wayar, taji jiniyar motocin sojoji, alamun Major ya sauka a gari.
Mamaki ne ya kamata, ta fito falo, kamar an wurgo shi haka ya shigo a birkice.
Mami ta ce "Yallaɓai lafiya kuwa? Yana ganka a gida yau ba ko sanarwa?". Wani mugun kallo ya yiwa Mami ya wuce part ɗin sa.
Binsa ta yi cikin mamaki "Yallaɓai dan Allah ka gaya mini meke faruwa?" Ko kallon in da take bai yi ba, ya